KIRJIN MAI HANKALI!!! (AKWATIN SIRRIN SA)
Free page 3
by @mssxoxo
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳✈️🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_FREE PAGE: 3_
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
*** Marayar bokezuwa maraya ce da aka sani da dimbin tarihin ilimi na addinni. Sunyi matukar tsefe Kai wajen zama gagga gaggan haziqan mahaddata alqurani Mai girma...
Su din yan gaba gaba ne kusan sunfi har manyan birane da sauran kauyuka da sukayi suna wajen rike addinnin Allah da hannu dubu bama biyu ba...
Musanman makarantun tsangayoyi... Sunyi fice wajen rubuta alqurani Mai girma cikin kwarewa da Kuma tsantsar sani... Wato makarantar allo..
Makarantar allo ita ce tsohuwar hanyar koyo da koyar da karatun Al-Ƙur’ani mai girma a kasar Hausa. A garuruwa kamar Kano da Katsina. A Kano ana sa ran shigowar wannan karatu tun kusan shekaru ɗari (100) shida da sittin a baya, zamanin sarki Yaji Ɗan Tsamiya a shekara ta alif (1349 – 1385) lokacin da Fulani Wangarawa suka zo garin na Kano. A Katsina kuma, ana ganin tun shekaru ɗari shida da sittin da uku baya da suka gabata a zamanin Sarki Muhammadu Korau a shekara ta alif (1384 – 1398) lokacin da Sheikh Abdurrahman Zaite da jama'arsa suka je Katsina.
Wannan makaranta a cikinta ake koyon karatu, rubutu da kuma haddace shi Al-Ƙur’anin baki ɗaya. Malaman makarantar allo su suke rubuta Al-Ƙur’ani kodai da ka, ko kuma ta hanyar mai-da-kama....
°°°°°°°°
A zaune malam Idi bokezuwa yake acikin rumfar makarantar tsangayar su.. Yayinda Yara masu daukar karatu sun zagaye shi kowanne da allo yanayi. Yayinda wasu ke rubutu a alluna da tawaduu a gefe..
Shi Kuma da zabgegiyar bulala a hannun sa. Yana bin karatun da yaran suke suna hada Kai...
Wata zungureriyar motace ta karaso wajen daga gefe ta faka. Mota ce data amsa sunan mota mai nishi...
Malam Idi bokezuwa yayi murmushi yana duba lokaci a yar wayarsa rakani kashi..
Mutanen suka fito daga bayan mota. Maza ne baki daya ba mata .. malam Idi bokezuwa ya Mike da sauri ya nufe su.
Yayinda suma suka nufo shi fuskokin su dauke da murmushi... Daga can bayan bishiya akwai tabarma dama awajen inda su malam Idi ke zama suyi karatu da sauran dattaawa idan sun daddawondaga wajajen neman abincin su...
Suka zazzauna akan tabarmar suka fara gayshe gayshe... Malam Nata'ala ma ya karaso da lemuka da ruwa a hannunsa daya Sayo musu. Ya zauna suka gaysa shima
Daga bisani suka dunguma cikin gida bayan an musu iso. Suka gayshe da ahalin nasu malam Idi.
A ka kawo musu yaran suka daukesu suna yaba kyawun su da rashin kukan su. Domin ba irin sauran yara bane masu Kuka idan sukaji bakin hannu
Daga nan suka basu abun arziki Kuma suka koma koma can waje inda suka sassauke kayayyakin da suka kakkawo musu na abunn arzuka. Suma sun babbasu kayan kauye fal..
Anan ne daya daga cikin bakin yake sheda musu da yaran sun Kara tasawa zaa kawo su su dauki karatu...
Daga nan suka musu rakiya mota suka tafi suna masu jinjina kirki da mutantaka irin ta su malam Nata'ala da dan uwan sa malam Idi..
Haka zalika su malam Idi suma sunata yaba kyawun halinda dattakon bakin nasu..Wanda dama daka ga yadda suke alamura suna gaysawa kasan sun San juna suna Kuma kaunar junan su..
****BAYAN WASU LOKUTA******
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga ***_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
****.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*****
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*