KIRJIN MAI HANKALI!!! (AKWATIN SIRRIN SA)
Last free page (5)
by @mssxoxo
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_LAST FREE PAGE 5./ SHAFI BIYAR NA KARSHEN PAGES DIN KYAUTA_
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
***Tashin su kenan daga allo suka karasa cikin gidah…. Sun tasa ainun sosai. Kana dake inna goge akai akai take haihuwa tuni ta tara yara da dan yawa bayan Rumana wadda take ta farko, akwai Karin Alasan da Mamuda da Garzali da haruna...
Yayin da gwaggo abule ke da yara uku kachal. Mata uku reras ba sirken maza mashaa Allah . .. akwai Karin Rayyanatu da Sharifa. iyalan Malam Nata'ala suka zama su biyar Yayinda na Malam idi su uku...
Dükkanın şu matan su daya daya ne dasu har yanzu basu Kara ba. Kuma Masha Allah şuna kokarin zama cikin aminci da rashin tashin hankali Sai dai wanda baa rasa ba na faccaloli, Idan kishin ya haura, amman duk da haka şuna kokarin zaman lafiya dubada gidan na şu d’aya . Naizan kuma ba agidah suke zama ba ko da Yaushe bacci ne ke kawo şu ko wani abun na musanman ko muhimmiya wanda yake dole Sai anje Gidan
Yaran Malam (almajirai) ne suka fara shiga da kayayyaki aledoji da buhunhuna biyu. Yayinda dayan Almajiran dake karshe na rike da Hannun wani yaro ya kuma goya d’aya abayan da. Sai kuka yaran ke tsarawa sun shiga unguwar.
Rumana da Zaytuna da shigar şu gidah Keda wuya Kamar tare suke da yaran sukayi hanzarin Juyawa. Alokacin Rumana tana nunke hijabi yayinda zaytunah ke tattare kofar dakin su.
“Assalamu Alaikum wayyyyyyoooooo” karshen zancen da tafashe da wani matsanancin kuka mai firgita mutum. Ba Wai na tausayawa ba, a’a Saboda tsananin karar sa daya cika gaba da baya ga muryar tata tanada karfi yadda kasan lasifika aka kukkunna.
Almjiran suka dire komai suka juya. Şuka fara kokarin gayshe ta, sukayi kanta şuna masu amsa sallamar ta cikin tsantsar tashin hankali da fargaba.
“Haire kahiiii.”
Dayan yaron da almajiran suka dire akasa ya fada yana riko kafar babar tasu data kifa kai tana kuka da kururuwa.
Mutanen garin Sai aike suke ana tambayar lafiya? Yayinda Matan dake kusa suka shisshiga. Wasu kuma ta saman katangar su da batada tsayi suka lalleka.. Suna jiyo zantukan da ake.
Şu Gwaggo Haule suka babba matan hakuri da karin cewar babu komai. Sabani ne kawai Na yau da kalau na rayuwar wani abun. Amma ba babban abu bane. Da haka duk suka tatafi.
“Haire kahi"
“Malafar kan uban ka tanko ,Nace kan uwar uban ka. "Ta amsa shi Cikeda fada tana shure kafafu.
“Rumana maza saka hijaban ku ku kira su baban ku. Dan Allah haire Kiyi hakuri ki dena kukan nan.
“Tashi muje kayi kaji? Zo ka cire wandon anan” cewar gwaggon abule l..
Yaran ya maqe kansa yana tsuke baki.
“Abinci zanci” Dayan yaran ya fada yana turo baki gaba
Bai gama rufe baki ba. Dayan babban daya tasa yace,
“He da ya mata hegen duka tukun sannan yace mubar mihi gidan hi. Hi isaka nuka taho bayan ya hyarara nata mari duka kuncinanta”
"Kuma Kuma... Ranto kudin adaman ladi tayi Mai zobo. Bayan tanabin ta murtala takwas" dayan karamin ya fada yana sosa hancinsa dake tsiyayar da ruwan majina,
"Allah ya kyauta ya rufa asiri" inna goge ta fada tana tasa dayan..
Yayinda gwaggo abule ta nisa ainun kana ta jijjiga Kai cikeda madaukakin mamakin magangunan tache,
"Ubangiji Allah ya shiga lamarin ya kawo dauki Amin"
"Aban ruwa... Wayyo ni wayyo wayyo ni yar marainiyar Allah. Gatana ya kare Kuma" gwaggo haire ta fada cikin kururuwa tana sake zunduma ihu.
Mata sai Leke ake ta Katanga ana sauraron ife ifen haire. Su gwaggo abule suka shiga bata hakuri. Aka debo mata ruwan a randa aka bata. Ta kurba tana tirje kafafu
Cikin haka sai ga isowar su malam Nata'ala da malam Idi. Suna neman a musu iso su shiga. Tamkar ko da yaushe basa shiga gidan Kai tsaye sai sunyi sallama an musu ison su shiga babu Wanda ba muharrami ba tukun don gudun shiga aga abunda bai kamata ba. Na daga matan da ba nasu ba. Ko abunda zai zama kamar ziina ce ga idanun su..
Su zaytuna ne suka shiga . Daga baya Kuma su malam Nata'ala suka biyo bayan su bakunan su dauke da sallama....
Gwaggo haire na jiyo muryoyon su ta sake rafka uban ihu ta zunduma shi Mai matukar Kara, ta barke da sabon Kuka tana yi tana Kara sautin sa tamkar wata karamar yarinya...
Su malam Nata'ala sukayi kanta suka mata magana hadi da bata baki. Suna rarrashinta sosai. Dakyar ta iya dena kukan tana sauke ajiyar zuciya....
"Mai ya faru haire? Iyi? Dan Allah ki dena kukan nan kinji?"
"Aa Yaya. Mu shiga daga ciki sai muyi magana ko?"
"Hakan yayi. Tashi haire mu shiga daga ciki."
Dakyar haire ta mike tana tangadi hade da Saka kasan zaninta ta sharce hancin ta tana cigaba da kananun kuka suka shiga dakin malam Idi dake dauke da katuwar tabarma da katifa babba aciki....
Zama sukayi baki daya. Sunata jan haire da magana dai harta tsaya suka gaysa.
"Menene haire? Muna sauraron ki? Kina da wasu ne bayan mu da zaki bayyanawa SIRRIN ki banda mu?"
Ta girgiza kanta tana gyara zama.
"Mu din dai mune yan uwan junan ki haire. Kuma kedin amana ce agare mu baki daya.. shin meke tafe dake. Menene damuwar ki? Maganar zuwan ki da rusgar kukan ki, kar bakin kasuwa. Shin menene damuwar ki eh? Sanar da mu?"
Haire ta ja majina tana gyara kafafunta tache,
"Tanko ya shika ni .. shika ba daya ba har uku. Tare da doriyar duka da marika a duka kuncina na....
🎗️
_Duka dika anan na kawo karashen free pages na wannan littafi mai suna, KIRJIN MAI HANKALI (Akwatin sirrin sa)_
Kada ku bari a fara paid pages Baku mallaki naki ba, Shin kuna son littafin da zai gigita ku da abubuwan ban mamaki, soyayya, sirrika da ƙaddara? To, wannan littafin na musamman ne gare ku!
Abubuwan Da Za Su Tsuma Zuciyar Ku, Zuciya Mai Sirri da Soyayyar da Ba Ta Samu Fuska:
Capt. Fawaaz soja ne mai tsananin miskilanci. Duk da yana ƙaunar Dr. Nabeeha har cikin zuciya, ba zai iya gaya mata hakan ba. Ya ɓoye SIRRI sa cikin kirjin mai HANKALI, yana barin Nabeeha cikin ruɗani: "Shin miskilancinsa ƙiyayya ce, ko tsoro ne ya hana shi bayyana soyayya?"
Hmm akwai, Gwagwarmayar Zaytunah da SIRRIN aurenta: Zaytunah ta fuskanci mummunan ƙaddara da gwagwarmaya a gidan mijinta, Alhaji Uzairu. Amma me ya sa ta bar gidansa da yara ƙanana har ta koma gidan da ba ta da alaƙa da su? Kuma wane SIRRI take ɓoyewa da har ita kanta Nabeeha ba ta sani ba?
.. hmm waani Sirri Da Zai Canja Duk Rayuwar Su: a cikin tsananin soyayya da rudani, sirri guda ya bayyana wanda zai iya rushe dangantakar Nabeeha da Fawaaz, tare da barazanar rikitar da rayuwar su gaba ɗaya.
..Soyayya Da Tsakanin Soyayya:
Fawaaz zai iya yin biyayya ga zuciyarsa, ko kuwa soyayyar Nabeeha za ta rushe kamar guguwa? Wannan tambaya ce da za ta ci gaba da tsuma zuciyar mai karatu!
.Tambayoyi Da Ba Su Da Amsa:
Zaytunah ta ce ba za ta iya komawa gidan tsohon mijinta ba saboda an mata asiri da aka ƙulla ta hanyar ƙiyayya. Amma me yasa wannan ƙaddara ta faru da ita? Shin akwai wani boyayyan lamarin ne?
Abin Da Littafin Zai Ba Ka,KIRJIN MAI HANKALI: AKWATIN SIRRIN SA ba kawai littafin soyayya ba ne; ya haɗa da gwagwarmayar rayuwa, sirrika masu ban mamaki, da ƙaddarar da ke koyar da juriya. Wannan labari zai baka damar nutsewa cikin duniyar tunani mai zurfi da abubuwan tsoro masu ban sha’awa.
Kada ka bari wannan daman ta wuce ka!
---
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga ***_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
****.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*****
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*