3
by @autarmanya
*SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*003*
Ita kuma tayi saurin taɓe baki tayi raurau da manyan idanunta waɗanda suka ciko da hawaye ta ƙura masa idanun nata duka tana kallon shi.
Murmushi yake yi har Lokacin hannunsa yana dafe da goshinsa.
"Ni da kika bugawa wannan ƙaton Goshin naki banyi hawaye ba sai ke?"
Hannu tasa ta kare fuskarta tana Murmushi ga hawaye kuma na ƙara zubowa.
Ya ƙara matsowa gabanta ya fita tsayi nesa ba kusa ba hakan ya sa ta ƙara komawa ƴar ƙarama a gabansa.
"To ni yaufa naga takaina Kinga dan Allah zoki rama Duk da nima dai naji zafi"
Dariya ta saki tana cewa.
"Kai kawu Saadik tsokanar kafa nake yi wai ina zaka je Sai ƙamshin turare kakeyi?"
Ta faɗa cikin sigar tsokana
Ya tsuke fuska kaɗan.
"Dama bana saka turare sai zan fita Hawwa'u?"
Saurin dafe baki tayi tana wara ido.
"Wasa nake maka fa"
Ya ɗan kalleta.
"Wai bana ce na soke kawun nan ba su in sun cemin kawu kema sai kice min kawu maza sai wata tazo tana cemin my love ke kina faɗin wani kawu"
Ƙafafu ta hau dirawa ta fara Kukan ƙarya Raɓeta yayi zai shiga ɗakin shi dake soro da sauri ta bishi
Ya tsaya a bakin ƙofar ya kare hanyar da zata shiga ɗakin ya tsareta da ido.
"Abinchi na kawo maka na miƙo maka?"
Ta faɗa tana Waigawa bayanta tare da ɗaukar Kular data zubo masa Abinchin.
Cikin tsananin so da tausayi ya dubeta.
"Bana hanaki kawo abincin nan ba yanzun nan muka kammala cin tuwon innah nida Baba"
Turo baki tayi kaɗan.
"Nima Gas ɗinmu ne ya ƙare seda ummah tayi wa Yayah Fa'izu waya ya kawo mana shiyasa ban kawo maka abincin da wuri ba"
Yadda take maganar Jiki a sanyaye ta ɗan bashi tausayi shikam ya rasa wani irin so yarinyar take mishi wanda yake ganin son da take mishi kamar yafi nashi duk da shima yana sonta.
Ya zira hannunshi ɗaya ajikin aljihun wandon shi.
"To ni yanzu yaya zanyi da wannan abincin tinda nidai cikina ya ƙoshi"
Yanda yayi maganar ta bata haushi sai kawai ta juya tare da ficewa daga soron.
Beyi gigin bin bayanta ba dan yasan rigima ce zata kaure musu ƙarshe inta saka mai rigima ya karɓi abincin ba iya ci zai yiba inya bayar kuma taji haushi.
Sai kawai ya shiga ɗaki cikin hukuncin Allah yana shiga ana kawo Nepa ya jona cajin ƙaramar wayarsa.
Yana ƙoƙarin cire shirt ɗin jikinsa ƙaramar wayar tasa ta shiga Ƙara alamun kira yana shigowa Bayan ya ɗaga Muryar Abokin shi Nura saiti ta cika masa cikin kunnen shi.
"Wai dan Allah dagiya ina ka shiga ne?"
Saadik ya ɗan ja tsaki kaɗan.
"Yanzu dai meke tafe dakai ko tambayata ka kirani kayi? kaje shagona baka ganni bane koka zo gida bani nan?"
Saiti yayi dariya tare da cewa.
"To sarkin fushi nai maka magana ne naji shuru, ko baka kunna Data bane yau?"
Takaicin ɗazu ne ya faɗo masa ya fesar da huci mai zafi.
"Bari kawai Nura wayar ma bata wurina Allah yasa sim ɗin yana wannan wayar"
Da sauri Nurah yace.
"Garin yaya matsala ta samu?"
Cikin son kauda zancen sabida shi gwanin zurfin ciki ne yace.
"Ya ake ciki ne kana shagone koka shigo?"
Nura yace.
"Yau na sami cinkoso ne a wajan IBB Road kasan hanyar tamu sai a hankali, Amman gani nan dama Najika shuru ne nace bari na taɓaka kako san yau Za'a Buga wani zazzafan wasa?"
Duk yanda Saadik ke son kallon Boll sam yau ya mance zasu je kallo kwata kwata sabida haka tsaki yaja dan baida karsashin fitar ma gaba ɗaya Nafila zai yi kawai ya kwanta yasan Baba zai fita waje shan iska bayan ya gama jin Labaran sha ɗayan dare ya rufo gida shiyasa zeyi kwanciyar sa.
"Nura Kuje kawai kaida su Babu danni gaskiya yau ɗinnan ba zan iya zuwa gidan kallo ba"
Daga haka ya kashe wayarsa gaba ɗaya ya mayar chaging ya koma ya kwanta ya zurfafa acikin tunanin wannan lamari mai girma daya faɗo masa ko a kanshi bai taɓa tunanin Baba zai masa auren dole ba, dan shi kam wannan aure na dole ne yana zaman shi lafiya Baba ya bashi Umarnin zuwa inda za a ɓata mishi rai.
Maganganun Baba na jiya da daddare ne suka soma dawo masa cikin kansa.
"Sadauki!Waye mahaifinka?"
A lokacin sun kammala cin abincin dare ne duk suna zaune a Rumfar Baba shida Baban da Innah wadda take cin Gyaɗa marau marau.
Ya Nutsu sosai tare da cewa.
"Baba duk duniya ban san wani a wannan matsayin na uba ba face kai"
Baba yaji daɗin kalamin shi duba da yanda yayi Murmushi a lokacin haɗi da samai albarka kafin ya fara dirar mashi da maganar data haifa masa ɗaukewar Numfashin wucin gadi.
"Sadauki jiya mahaifin Wannan yarinya Hauwa'u mai haƙuri da kawaici ya kirani akan maganar auren ku sabida karatunta daya kusan zuwa ƙarshe, Bayan nai masa na'amm da maganar sai na ɗauki wayata na Kira ɗan uwana wanda duk duniya bani da kamarshi Amadu uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya nina saki Nono ya kama na shaida masa batun Auren ka"
Baba yaja fasali.
Saadik yaji wani irin farin ciki a zuciyarshi.
Innah ma sai ta hau murmushi sabida Jiddah ta cancanta ta zama surukarta duba da yanda yarinyar ke son ɗan nata tilo tal namiji aduniya kuma auta acikin ƴaƴanta waɗanda dukka mata ne Allah ya bata shi kaɗai ne namiji acikin su kuma shine auta.
Maganar baba wadda ta katse Murnar Innah da Saadik ita ce ta cika Kunnuwan su.
"Sai dai Amadu ya katsen hanzari, ya mini kyauta kuma na amsa tinda bahaushe yace yaba kyauta tukwici dik da kyautar dama bata yanzu bace amman Lamarin daya zo ya cuɗe a tsakanina da shi yasa na fidda rai akan kyautar ta shi Sadauki Amadu yace kaje ka Nemi auren ƴarsa RABI'AH duk da maganar ba sabuwa bace a wajena nida Hafsatu mahaifiyarka Tin ranar da Aka haifeka da Amadu ya ɗaga ka yace In har Matar sa ta haifi ƴa mace yayi ALƘAWARIN ba tada Miji sai kai to yanayin yadda Zumuncin mu ya lalace da shine yasa Ban ɗauka zai cika wannan Alƙawarin ba sai kuma gashi ya cika don yace sadaki kaɗai zaka bada Rabi'atu dai ƙanwarka ce da ubanta dani cikinmu guda dan haka In har ni na haifeka kamin alfarma kaje ku sasanta In yaso ita Hauwa'u sai ka aure ta inta kammala karatunta ba zan hanaka auren wadda kake so ba Amman Nima ka auri wadda Mukai Alƙawari Nida ɗan uwana ko Allah yasa silar auren ku zumuncin mu ya daidaita"
A lokacin jikin Saadik babu abin da yake sai rawa hatta bakin shi Gumi ya jiƙa masa rigar shi, Dama ga zafin ɗaki dan lokacin babu wutar Lantarki.
Inna zatai magana Baba ya ɗaga mata hannu alamun baya buƙatar cewarta, Sai taja baki tayi shuru.
Numfashi ya dinga ja yana ambaton sunan Allah kafin ya samu Nutsuwar Furtawa Baba Kalmar.
"Amman Baba hakan ba zai jawo mana ƙasƙanci ba, Mutumin da baya neman ka Yana matsayin ƙaninka amman ya nuna yanzu Shi mai Kuɗi ne ya janye zumuncin dake tsakanin ku, Baba ka rabu da shi Ka Nema min Auren Hawwa'u ita ce wadda take matiƙar sona domin Allah Nima Kuma nake sonta Amman ita waccan da ban santa ba bata sanni ba Ko sunanta ban sani ba tayaya zan aureta Baba?"
Baba yayi murmushi irin nasu na manya kana yace.
"Ka bar batun Amadu Yaro ne ɗan halak Shu'umar macce kawai Ya haɗu da ita Ina son ka auri Rabi'ah ne Ko ta sanadin auren ku Allah zai sa Zumuncin mu yayi ƙarfi nida ɗan uwana, Fanni zamantakewa kuwa nasan Autana Ba ragon namiji bane in mace Huɗu ya aura zai iya ɗaukar Nauyi ci da shanta Hauwa'u Kuma In Allah ya yarda bata da Miji Sai Kai Kodan karamcin Mahaifanta garemu"
Yayi Biyayyar Amsawa Baba tare da amsar Auren ne badan komai ba sai dan tsananin Biyayya Mirginawa yayi bayan ya dawo daga duniyar tunanin maganar su ta jiya da mahaifin sa, yana cije laɓɓansa yana ƙara hasko Yanda take Masa kallon ƙasƙanci ya Murza yatsun hannunshi ya bada sauti mai ƙarfi.
Baccine ya ɗebe shi mai cike da tsabar gajiya.
A bakin fanfo ta tsaya ta tokare tana aikin nata kuka! ta ɗauki tsayin Lokaci tana kukan shashsheƙar kukanta Umma taji ta fito tsakar gida.
"An banu Jiddah dama kukan ki nake ji tin ɗazu aini na ɗauka ko kunne nane Zo muje ciki Naji mai ya haɗaki da Mutumin naki domin nasan dai wannan Kuka naki baze rasa nasaba da Saadik ɗinki ba"
Bin bayan umma tayi har cikin ɗakinta hasken farin ƙwan ɗakin ya haska fuskarta sosai Kyan Jidda a bayyane yake fara ce jajir Siririya marar Jiki mara son magana sosai In kaji tana surutu to da Umma ne ko Saadik, ko kuma Baffa mahaifinta.
Umma ta dubi yanda Jidda ta wani haɗe girar sama data ƙasa tana Faman kuka tace mata.
"Kinga bana son wannan sakarcin kukan me aka miki zakizo bakin fanfo kina Gursheƙen kuka kamar wadda aka ce mata Uwarta ta rasu?"
Seda ta shaƙi hanci sannan tace.
"Kiji fa Umma duk wahalar daka sakwarar nan dana ci dana kai masa wai ya Ƙoshi yaci tuwon Innah"
A lokacin umma dariya tai sosai.
"To in ban da abinki sai yaƙi cin girkin mahaifiyar sa yaci naki?"
Da sauri tace.
"A'a fa umma ni bance haka ba, Kiji fa wai cewa yayi shi cikin shi ya cika, Kalamin sun bawa umma dariya matiƙa amman gudun rigimar Jidda yasa taja baki tayi shuru a haka Baffa ya shigo shima dai rarrashin Jidda yayi har suka samu ta shiga ɗakinta.
Baffa da Murmushi ya dubi umma bayan fitar Jidda daga cikin ɗakin yace; "Ni kuwa saratu anya soyayyar Wannan yarinya ga wancan Yaro batai yawa ba?"
Da sauri umma tace masa.
"Kasan kowa da yanda yake ɗaukar lamarin shi Duk suna son Junansu Nikuwa yaya kukai da Mahaifin shi Abubakar ɗin?"
Baffa ya ce.
"Ashe akwai yarinyar da sukai alƙawarin bashi auren ta sabida haka zai fara auren yarinyar ne kafin nan ita Hauwa'u ta kammala makarantar ta sai ai maganar nasu auren"
Fuskar umma ta ɗan sauya yanayi zuwa na damuwa.
"Kaji irin halin mutum ko ashe shi yana tare da wata daban ni yana nan yana haukata mini ƴata da soyayya to in har hakane ni kam Jiddah ta haƙura da auren shi tinda ba autan maza bane"
Duk yanda Baffa yaso dakewa seda yayi dariya wato su lamarin mata fa se a hankali duk halin su ɗaya wani zubin akwai su da gajan haƙuri, Bata tsaya taji kan zance ba kawai harta yanke Hukunci wato tana taya ƴarta Kishi kenan.
"Haba Hajiya Saratu seki saurara Kiji yadda Mukai da mahaifan sa Maganar Allah shima Abubakar bai san da maganar waccan yarinyar ba aure ne na zumunci za'ayi Musu dan haka Ni kuma na yarje Musu Ba mamaki rabon waccan ne a gaban na Hauwa'u fata dai Allah ya bashi wiyan ɗauka tare da yin adalci a tsakanin su"
Tagumi Umma ta rafka sarai tasan halin Jidda Da zafin Kishi bare akan wanda take so amman zata mata nasiha sosai Tare dayi mata addu'a akan Allah yasa haka ya zama alheri.
Hira suka shiga yi da Baffa har Lokacin kwanciya yayi.
Daga ɗakin Jiddah ta jima batai Bacci ba tana ta juyi ga shi dare yayi bare ta ɗauko wayar Umma ta kirashi don ita ba'a bata waya ba seta yi Candy tukunna dan haka duk wayar da suke dashi a wayar Umma ne.
Sai kuma zance da yake zuwa duk ranar Juma'a shima Bisa sahalewar Baffanta ne.
Da ƙyar bacci ya ɗebe ta cike da tunanin Shi tare da zaton ko maganar turaren datai masa ne ya ɓata masa rai sabida tasan halin shi sarai Ba ƙaramar Wahala taci ba kafin Allah yasa Soyayya ta Ƙullu a tsakanin su Ita kanta tasan Haƙuri ne silar soyayyarsu tare da juriya tana son shi tana jin in ba da shi ba bazata iya rayuwa da wani Ɗa namiji ba.
***