SO DA ALƘAWARI

4

by @autarmanya

*SO DA ALƘAWARI..!*🌹

     

     *NA*

*AUTAR MANYA*


           *004*


Zama tayi a gefen gadon Momi tana jiran ta sabida ta jiyo alamun saukar ruwa wanda ya bata tabbacin wanka momi take yi.

Babu jimawa Momi ta fito daga cikin toilet Jikinta rufe da Ƙaton Hijabi ganin haka yasa Adaah fita falo domin ta bawa Momi damar shiryawa kusan awa Guda da fitar tata Momi ta biyo bayanta.

A kusa da ita ta zauna tana jan tsaki.

"Shalele Mahaifin ki yayi min shigar sauri a lamarin auren ki sai dai ni kuma zan nuna masa Nina haifeki wallahi Koda kin Auri yaron nan ba zaki Zauna lafiya a gidan ba har sai Kin kaso wannan ƙaddararren aure na kwaɗayi sabida anga ke ɗaya ya haifa shine za'a ƙaƙaba maki auren dangi"

Taɓe baki Adaah tayi tana Jin zafin furucin kalmar auren nata da Momi ta faɗi kafin tace.

"Yanzu Momy ke kina tunanin zanyi rayuwa da shi? Haba Momy kimin Fatan alheri mana dan wallahi dana aure shi gwara na auri Habib duk da Habib ɗin ba wani shigemin rai na yayi ba"


Da tarin takaici Momi tace mata.

"Inda dama mahaifinki ya bayar akan ki fidda Miji ni kaina dana haɗaki da Yaron Hajiya Lubna 

Maheer amman kina kallo fa umarni ya bamu bawai dama ba wannan makircin Na rasa daga ina ya fito hatta Mahaifiyata anje an faɗa mata ƙarya da gaskiya"

Zaro ido Adaah tayi haɗi da saurin cewa.

"Iyah aka faɗama maganar auren nawa? Wayyo! Shikenan yanzu zata ce in baki bari ba Bata yafe ba Haba Abbah yaya zeyi min haka ya rasa da wa zai haɗani sai Ƙasƙantaccen Mutum ɗan talakawa"

Kuka Adaah take mai cike da tsananin ƙiyayyar Auren da za'ayi mata Tin Momy na rarrashinta Har abin ya faskara sai ta zuba mata ido tana kallonta domin duk yanda take zato Adaah ta fita Ƙiyayyar Auren har akai sallar Magarib tana zaune batare data Miƙe Domin gabatar da sallah ba tana ta kuka a wurin Gajiya Momi tayi ta Tashi ta nufi Bedroom Domin gabatar da sallah.


Ana idar da sallah Abbah ya shigo Jin Shashsheƙar Kukanta yasa shi ƙarasowa wajanta ya fasa hawa saman dayay niyya Gyaran Murya yayi tare da Zama a kusa da ita Wanda Itan kuma tai saurin Zamewa ta zauna a ƙasa tana Goge hawayenta.


Da sassauci acikin Muryar Abbah ya dube ta.

"Rabi'atuna kukan mai kike Ɗiyar Abbanta kome Kike so ki faɗa min Kinji bana son damuwarki"


Jin wannan kalmar daya ambata sai taji zuciyarta tayi sanyi ta ƙara Goge sauran hawayenta tare da cewa.

"Abba dan Allah karka aura Min shi wallahi har cikin raina bana son shi"

Tsira mata ido Abba yayi tare da kamewa sosai ya kalleta na wani Lokaci sannan yace.

"Ko kina da dalilin Ƙin Yi mini Biyayya wadda bata saɓawa Allah ba? Ni Mahaifin ki na zaɓa maki Mijin Aure Kice zaɓina bai maki ba Ko kina da zaɓin ki? sannan Ki bani dalilin Ƙin wannan aure da Kike?"


Daburcewa tayi seda ta aro jarumta wurin furta kalmar.


"Abbah ka duba Gidannan ka duba tsarin shi sannan ka duba tarin dukiyar dake gareka sannan ka duba yanda na taso Sannan Abbah kace zan auri wanda Da ƙyar In yayi karatun Boko ma daga ganin shi yafi kama da ƴan jagaliyar anguwa Abbah na roƙeka karka aurawa Ƴarka tilo ɗaya tal wanda ba tsaranta ba kuma ba ajinta ba"


Ɗaga mata hannu yayi tare da dafe saitin zuciyar sa.

"Innalillahi wa'innah Ilaihirraju'un"

Ya furta a fili yaushe Rabi'ah ta ɓaci haka yaushe ne ta zama mai raini da ƙasƙanci ga mutane tabbas ba laifin kowa bane face na Mahaifiyarta shiba zama yake a gari ba yawanci In yazo baya daɗewa yake tafiya dalilin daya sa harya ƙauracewa zuwa gidan Yayan nasa kenan sedai ya aika masa da kayan abinci da kuɗi wanda takanas Shi Kuma Baban Chiranci ya aiko masa da cewar Ya daina amsa shiba wannan yake soba Zumunci yake so Yanayin kasuwanci yau ya fita ƙasa kaza gobe ya fita ƙasa Kaza shine silar tarwatsewar Komai, Gudun kar Ƴarsa ta Koyi Wata Tarbiyar yasa ya hanata Karatu a ƙasar waje ashe Gudun Gara yayi domin ya mance yawanci Ƴaƴa suna samun tarbiya ne daga wajan Iyayensu mata.


A fusace ya shiga Kiranta.

"Maryam! Maryam!!Maryam!!!

Da tsananin zafi ita kuma da tsananin sauri ta ƙaraso Falon.


"Alhaji sallah na idar ina addu'a kana kirana da ƙyar na shafa wallahi ka ɗagamin hankali"


"Dole na ɗaga miki hankali Maryama Kin kyauta da tarin tarbiyar da Kika bawa Ƴarki Amman Ina so a daren nan Ki shaida mata waye Abubakar a wajena waye mahaifinsa wacce Irin Rawa mahaifinshi ya taka a rayuwata Kuma ki sanar mata In Mutuwa tayi zan kaita Gidan Mijinta daga nan a suturtata akaita makwancinta Amman Auren ta da Abubakar Babu fashi In har Nine mahaifinta"


Fuww Ya tashi yabar wajan Tagumi Momi ta zabga wato duk yadda take zaton lamarin so yake ya fi ƙarfinta, Mijinta mai son ta da ƙaunarta Ko magana zai mata baya mata ita cikin faɗa sai a hankali sabida Gudun Ɓacin Ranta kasancewarta mai kirsa yanda take wa Alhaji ba zaka ce Wannan matsala zata zo ta shiga tsakanin suba duk yadda takai da kirsarta a Lamarin Auren nan ta kasa dannewa jita ke ba zata iya Gani talaka yazo ya aurar mata ƴaba kuma Ama rasa daga ina zai fito sai daga gidan maƙiyanta dan Momi a duniya bata Ƙaunar Baba da Innah domin sai da takai ga har Gida taje ta Yiwa Innah gargaɗi akan mijinta ada sanda Yake Musu Hidima sosai kafin ta janye shi da Kinibibinta.


Duk da sanyin falon Momi zufa take Adaah kuma na kuka wayarta dake Gefen Kujera ta janyo ta shiga Kiran Ƙawarta Lubnah.


Hajiya Lubna dake zaune Tare da Ɗanta Maheer suna tattaunawa taga wayar Ƙawarta Murmushi tayi tare da cewa.

'Kaga ƴar halak kamar tasan zancenta Muke"

Da sauri Maheer yace.

"Mama ki ɗaga mana Kiji"

Gyara zama tayi tare da ɗaukar wayar daga ɓarin Momi a gigice ta shiga zayyanewa Hajiya Lubnah Halin data ke ciki.

Tsaki Hajiya Lubnah tayi.


"Ga Hanya mafi sauƙi na faɗa Miki kizo mu fita da tuni wata maganar ake Keni In ba zaki bi malamai akan wannan matsalar ba dan Allah karki sake Kirana"


Tana Ƙoƙarin kashe wayar Momi tace.

"Zani wallahi dole ma naje inya so saina nemi gafarar Iyah In komai ya daidaita Amman ba zan ga wannan abun na bari ba wato in suka aura masa Ita shikenan Komai Namu ya koma Gindinsu Daga ƙarshema su gaje Dukiyarmu tinda Ƴar tawa dana Ke tutiya da ita ta koma cikinsu wallahi Hafsatu ba zata ci galaba akaina ba"


Dariya Hajiya Lubnah ta saki gami da cewa.

"To ai tuni nake faɗa maki karki ga kin sami daula dole sai kin Miƙe tsaye to gashi nan dai Kirsar da kike cewa kina da Ita bata hana Mijinki Botsare miki ba"

Momy ta ɓata rai.

"Keni kada ki faɗa min magana mafita kawai nake Nema Amman Ni nasan Kirsata tai Min maganin waɗancan tsinannun"


Taɓe baki Lubnah tayi tare da cewa.

"Yanzu dai turo min wani abun Da zan turawa malam ya fara Bincika mana Halin da ake ciki"


Da sauri Momy tace.

"Baki da matsala bari na sako Miki Kuɗin nan ƙawata Aminiyata ta duk duniya dan wallahi Kinfi min ƴan uwana don basa damuwa dani kamar Ke"

Lubnah tai dariya tare da cewa.


"Karki damu Komai nai miki kaina nayi wa Kin manta taren fa bata yanzu bace, Nima Kin min Komai a rayuwata duk da Mijinki yafi nawa arziƙi Amman baki taɓa yada ni ba Komai naki sai kin saka dani Allah dai yabar mu tare"


Bayan sun kashe wayar Momi ta rarrashi Adaah Ta nufi ɗaki domin sallah, Ita kuma Momi ta zauna tana turawa Hajiya Lubnah kuɗin data Buƙata Bayan Awa Biyu Hajiya Lubnah ta Kira Momi tare da ce mata Lamari fa ya wuce nan dole seta zo sunje tare dan bayani a waya ba zai yuwu ba.


Tashin hankalin ƙaryar da zatai wa Abbah ta shiga domin tasan Ba zai barta Ta fita cikin sauƙi ba Koda kuwa da Jikin Iyah tayi ƙarya A haka ta kwana tana Juyi tare da saƙe saƙen yanda zatai Cikin Ikon Allah ma washe gari da asubah Abbah ya zo mata sallama akan zashi lagos sati ɗaya zai yi wato rashin Jituwar da basa yine bai faɗa mata ba, Itama babu wata walwala tai masa fatan dawowa Lafiya ta Juya ta cigaba da uzirin gabanta.


Sai da taji fitar shi sannan ta kira Hajiya Lubnah Akan fitar tasu da magagin Bacci Lubnah ta miƙe se Lokacin ma tasan Asubah tayi Ta shiga Toilet dan ta kintsa domin a cewarta fitar wuri zasu yi.


Itama Momi Kintsawa ta shiga yi tasan Adaah inta farka taga bata nan ba damuwa zatai ba dan haka data kammala shirin sai ta zauna tana Jiran isowar Aminiyar tata.


Abbah Har ya nufi Airport Sai ya cewa driver ya koma da baya suje Chiranchi tinda akwai sauran Lokaci kafin tashin Jirginsu Suna tafe yana duba hanya don ya kwana Biyu bai zo wajan Ɗan uwan nashi ba sanda Motar su ta shiga Layin Baba yana Addu'ar fita daga gida sabida sammako zaiyi Abbatuwa wajan sarin nama domin Idan kana son Nama mai Arha sai kayi Asubanci.


Da sauri Abbah ya Ɓalle Murfin Motar ya fita ya ƙarasa gaban Baba ya tsugunna har ƙasa tare da cewa.

"Yaya barka da Asuba"

Baba ya miƙawa Abba Hannu cikin so da ƙauna irin ta Jini Abba ya kama Hannun Baba ya miƙe suka shiga Cikin Gidan.


Da Saadik suka ci karo wanda yake zaune a bakin Rijiya yana Brush cikin sakin fuska Abba yace.


"Malam Abubakar ashe yau zamu haɗu barka da asubah"

Sai da ya wanke baki sannan ya shiga gaida Abba wanda yaketa Kallon Saadik cike da son Ƙulla Alaƙar Aure tsakanin shi da Ƴarsa shiko Saadik ɗaki ya wuce ba wata cikakkiyar walwala a tare dashi domin shi Mutum ne mai gudun ƙasƙanci.


Abba yabi bayan ɗan uwanshi yana waigen Saadik aranshi yana Jin amintar bashi Ƴarshi domin Irin Yaron da wiya mace ta raina shi, Har Saadik ya shige Abba na waigen shi Tare da Jin rashin daɗin yanda baya sakewa dashi daga gaisuwa shikenan kwanakin baya babu yanda bai da shi ba akan ya dinga zuwa kasuwa wajan shi Amman fafur Yaƙi Yace shi Gwangwan ɗin shi ta fiye mishi zuwa kasuwa.


Innah dake fitowa daga Kitchen hannunta Riƙe da Ludayin Miya wanda take Juya Miyar da zatai Ɗumaman tuwon Ƴammakaranta ta saki fuska sosai tana amsa gaisuwar Abbah


"Dama Amadu kana duniya yaushe rabon duniya da ayyaraye rabon dana ganka har na mance fa"

Abbah ya sosa kai Zai bata amsa Baba ya ɗaga Murya yana cewa.

"Amadu Rabu da Hafsa yau wasan ƙanin Miji take maka zo mu gaisa Ina sauri"


Jiki a sanyaye Abbah ya shiga Rumfar da Baba ke zaune a nutse suka gaisa dan tsananin Kunya Abbah yama kasa ɗagowa ya kalli Baba shiko Baba sai jan Abba yake da Hira koda wasa bai masa maganar komai ba.


Tuwon dawa miyar kuka sai tashin ƙamshi daddawa yake Innah ta shigo masu da shi tare da Koko mai zafi.

"Wato Amadu yasa dole sena karya zan tafi kasuwa, Kin san Hafsatu fa da tuni nakai Titi Amadu wanke hannu a silba Muci tuwo".


Abbah ya ɗauki ruwa ya na wanke hannun shi tare da cewa.

"Wato na jima banci tuwon Innah ba kuma ina marmarin tuwon innah kasan Yaya yawanci matan yanzu ba ko wacce bace ta iya tuwon dawa kamar na Innah"


Aiko mai innah zatai In ba dariya ba ta fice tana cewa.

"Kai Amadu kodai zolaya ta kake yi nikam ba zan tsaya jin daɗin bakin kaba nayi nan"


Daga shi har Abba dariya suke Suka saka hannu tare da Bismillah suka fara cin tuwon Abbah ya zage yaci sosai yasha Kokon Shi kam Baba bai ma ci da yawa ba Ya tashi ya wanko Hannu Abbah ne yakai kwanukan bakin Rijiya ya wanko hannu shima ya dawo.


Bayan sun zauna Abbah yace.

"Dama Yayah batun auren yaran nanne Ina ganin idan na dawo daga wannan tafiyar sai a ɗaura musu Auren, Batun Hidimar Aure dama nace maka bana buƙatar Komai sai sadaki Zan basu gida sannan don Allah maganar Kasuwa har yanzu Ina Barar yazo wajena Ya nemi abincin shi na bawa wasu ma waje bare kuma nawa"


Baba ya nisa kana yace.

"Haƙiƙa Amadu a baya nayi Fushi dakai sabida yadda ka ƙaurace mini ka daina zuwa inda nake, Amman yanzu na huce sabida haka Bari na kira Sadauki! inya Aminta da tayin naka sai ayi komai a nutse dama bai fara Ginin Gidanshi ba kasan yadda lamarin yake yadai sayi fili anan bayan Gidannan"


Baba ya fita yasa Ummi tayi Kiran Saadik wadda tai shirin makaranta Cikin Blue Ɗin Uniform ɗinta.


"Ke Ummi in kika fita ki kira min kawun ku a ɗakin soro"


Ummi ta amsa wa Baba tana nufar soron sai dai ta ga Khadija a raɓe tana share hawaye Ummi tai saurin cewa.

"Ke kuma keda wa kike faman share hawaye?"

Cikin ƙasa da Murya Khadija tace.

"Kibi a hankali kayan kari Innah ta bani na kaiwa kawu Saadik wallahi bakiji ranƙwashin daya Min ba wai banyi sallama ba kuma nayi fa"

Dariya Ummi tayi tana cewa.

"Ba lallai Kinyi ba kuma kinsan halin Kawu su Ya Umar ma shakkarshi suke bare mu"

Ummi ta wuce A bakin Ƙofa tayi sallama sai da yaja aji kafin yace.

"Waye ne?"

Ummi tace.

"Kawu dama baba ne"

Bata ƙarasa ba jin yayi shuru sai can yace.

"Ni kike faɗawa ko ƴan Ƙofar Gida?"

Fahimtar mai yake Nufi yasa taja Labulan ɗakin nashi Ƙamshi da wani Irin sanyi ne suka bugeta daga Nesa dashi ta durƙusa duk Girmansa ya cika ɗakin.


Murya a hankali tace "Dama Baba ne yace kazo"

Ta faɗa tana Raba ido sabida yadda yayi mata masifar kwarjini.

Batare daya kalleta ba yace.

"Kice gani nan"

Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa daga bakin katifar.


Da.

"To" Ummi ta amsa tana miƙewa ta fita daga ɗakin taje ta sanar da Baba Saƙon sannan suka tafi makaranta Lokacin ƙarfe bakwai da rabin safiya tayi.

***