JARABTAR SO

4

by @muslimerhabba

Ammi ta kalle ta da mamaki tace " Arfa, ke da wa kuke waya? Kin shigo ɗaki kin zauna ke kaɗai me yasa na ga yanzu duk kin canza ne? Ko dai wani abin ke damin ki? Wani lokacin walwala wani lokacin kuma kamar kina ciwo, ni gaskiya abin ya fara damina. Ki faɗa mini gaskiya in ba ni ba wa zaki faɗawa?"

Ta wani sheƙe d dariya, Ammi ta saki baki tana kallonta kamar wata shashasha, yanda take dariyarta hankali kwance kai kace babu abinda ke daminta, dan tuni itama Ammin abin ya koma bata dariya, dan tunaninta ya hararo mata dama iskancin Arfan ne kawai ya motsa take miskilanci idan ta ga dama.

"Ai shikenan Arfa se kiyi ta mayar dani kakarki, sanda ciwon damuwa ya murɗe ni na kasa kece za ki fi kowa asara, ina miki magana kin zauna kina sheƙa mini dariya" Ammi ta miƙe kamar za ta fice daga ɗakin.

Da sauri ta miƙe ta rungumo Ammin tare da cewa. "Yi haƙuri Ammina ni kaɗai ba ta su Yaya da Yaya ba, kinsan fa bana jurewa idan kikai fishi dani. Wallahi dariya kika bani ne daƙyar ma na tsayar da ita, ki kwantar da hankalinki kawai Ammi kin kusa yin siriki inaga" ta faɗa hankalinta kwance tunda tasan abinda take so kullum shi Ammin ke so, not realizing how shock her Ammi is.

Ammi ta kalleta a hankali tace "Arfa siriki fa kika ce. A ina na sami sirikin kuma yaushe?"

Sosai ta zage taiwa Ammi bayanin tun farkon haɗuwarsu da Sadiq har zuwa yanzu da ta kira shi a waya. Jiki a sanyaye Ammi ta fice tace za su yi magana akan issue ɗin later.

Tas ta zayyanawa Khaleel yanda dukai da ƙanwar tasa, sosai kuma ta nuna masa damuwarta da yanda taji sam al'amarin bai kwanta mata ba. Ko kaɗan ba ta son abin da zai taɓa lafiyar autar tata.

Cikin sigar lallashi ya kalli Ammin yace " Wallahi wannan ba abin ɗaga hankali bane Ammi, nidai ina ganin in har yana sonta itama kuma tana sonsa ai babu wata matsala. Kawai yanzu yaron zan nema ina so na ɗan tattauna da shi kan a bashi izinin neman aurenta".

Ba dan taso ba ta yi shuru se dan ta san tunda khaleel ya kasa fahimtar ta to bubu kuma wanda zai wani fahimce ta, ko kowa ya kasa fahimtar ta tana sanar da Khaleel yake ganewa ya fahimce ta, amma this time around shi da kansa ya nuna damuwarta bata da wani anfani.

Ɗakinta ya nufa yana barin ɗakin Ammi, ga mamakinsa har ya shiga ba ta ma san ya shiga ba sabida yanda ta shagala tana waya. Yana tsaye a gefe guda har lokacin da suka tanada dan yanke kiran yayi sannan ya kira sunanta.

"Mimi, in kin gama wayar pls let discuss something special".

"Wowwww My Yaya, you said special" ta gyara zaman ta da sauri tace "come closer my Yaya".

"Mimi" ya kira sunants da sanyin murya sannan yace

"wata magana naji a wajen Ammi, wai kin sanu wanda kike so, hakane,?"

Tana wasa da yatsun hannunta ta buɗa bakinta a hankali tace "Hakane Yaya".

Still yana karantar yanayinta yace "A ina yake".

A taƙaice tace "cafee ɗin da nake zuwa aikin project".

"Arfa kina da system, muna da printer a gida we also have light. Amma kika nuna ba za ki iya zaman yin komi da kanki ba you prepare kikai a maki, kenan dama sabida yaron ne kike son zuwa wajen?"

Ta yi shuru ta kasa ɗago kai, ya girgiza kai yace

"Soyayya tana da tarin ƙalubale, ba wai ina tsoratar da ke bane ba, a'a ina so ki tsaya ki nutsu ki so mutumin da ya dace ki so. Kuma ina so ki bani phone contact na yaron za muyi magana da shi".

Jikinta duk yayi sanyi, amma yana cewa ta bashi number tai sauri ta shiga karanto mishi not knowing cewa jikinta har rawa yakeyi.

Cike da mamaki gami da tausayin Arfa Khaleel ya bar ɗakin, wannan wane irin abu ne haka so lokaci guda, ko da dai dama ya jima yana nazarin akwai wani abin da yake faruwa game da ita wanda taɓoye a ranta not telling anyone, kuma tabbas yana da assurance wannan issue ɗin ne.

Direct ɗakin sa ya nufa, yana shiga ya zauna at the bedside chair yayi dialing number, 'Sadiq Lawal' ya ga true caller ta nuna masa sunan user ɗin, tana ta ringing ba'a ɗauka ba hakan yasa yai deciding he will call again later. Ya jima a zaune yana nazarin wannan sabon al'amarin kamin ya sanya hularsa a kansa ya fice....