Page 4
by @gureenjoh
RUBUTU A KAN RUWA
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*
*SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏
FREE PAGE 4
"Wai Big bro?"
Kai Aysher ta dage daidai suna shiga hadaddiyar SUV lighter brown wadda ya kasance motar Asma'un ce, bayan sun zauna tana yiwa motar key tace
"Ai Big bro babban surgeon ne da ba Nigeria kaɗai ba har ƙasar waje suna matukar ji dashi, duk wani harka da ya shafi tsaga mutum musamman a ciki to ya kware anan, na san Dukda ruga kike kila ba zaki rasa jin CITY CLINIC ba nan ne asibitin shi baya zuwa ko ina banda kasashen waje in kana bukatar aikinshi kayi booking appointment ka zo asibitin shi ya maka aiki, kai ko a Abuja babu asibitin da yake musu aiki, kuma kin san me?"
Ta tambaya tana kallon Aysher da wasu bayanan ta fahimta wasu ko bata fahimta, girgiza kai tayi
"Big bro na da zafi matuka a harkar aiki baya son sakaci da aiki baya yarda ka mishi wasa da aikin hakan ysa duk wadda yake aiki karkashin shi yake taka tsan-tsan da kuskure, sannan sam ba'a tsawwalawa a asibitin yana iya kokari wurin ganin da Talaka da mai kuɗi sun zo asibitin kuma sun ji daaɗi sbd da matukar wuya yayi aiki ba'a samu nasara ba, shiyasa kullum zaki ga yana asibiti ko ya tafi wata ƙasa Dukda tafiye tafiyenshi da sauƙi tunda se ayi booking daga Kasar waje a zo Nigeria yayi aiki a koma"
Ajiyar zuciya Aysher ta sauke a ranta tana ji dama ita ce, wannan shine burinta da na mahaifinta sede tunda ta shigo Abuja ta fara tambayar kanta zata iya kuwa? Har suka isa shopping mall suka yi parking suka fito tunani take yayinda Asma'u ke ta mata surutu wani ta amsa wani tayi murmushi har labarin gidan seda ta bata...
"Kinga Alhajinmu asalinshi haifaffen rugar ku ne, mahaifinshi me kuɗin gaske ne a cikin Fulani sbd ya mallaki dabbobi masu yawan gaske kama daga shanaye, tumaki, akuyoyi, zabi, kaji da dai sauransu, yana da mata har uku da mahaifiyar Alhajinmu itace uwargida amma Alhj shi kaɗai ne ya fita da namiji duk sauran ƴaƴansu mata ne, na biyun tana da yaya mata har biyar, na ukun ƴaƴa matan ta guda biyu se hajiyarsu Alhajinmu dake da guda Alhajinmu da kuma kanwarshi wacce ta rasu da jimawa bayan tayi aure ta haihu shima yana wurin Ammin mu ne da zama tun daga yayenshi har yau.
Kakanmu Dukda be yi boko ba sede yayi sha'awar ɗan shi kwalli ɗaya tal yayi hakan yasa tun da Alhajinmu yayi wayau ya kai shi cikin birnin yola inda anan yayi karatu tun daga farko har ya kamallah jami'a ya karanci business, bayan bautar Kasar shi a wani company a Kano se suka riƙe shi a matsayin sun bashi aiki sede yaje ruga ya dawo, bayan ya ɗauki tsawon lokaci yana aikin suka maida shi Abuja a wannan komawanshi da New appointment na promotion babanshi yayi mishi aure inda ya aura mishi Hajiyarmu ya dawo da ita Abuja.
Sun ɗauki tsawon lokaci da Hajiya bata haihu ba wadda hakan ya kawo mata tsana a familyn mijin ta yadda bata isa taje ruga ta dawo cikin natsuwa ba, barin ma hajiyar Alhaji bata iya ɓoye ƙin ta Sam a ranta, daga karshe ta ba Alhaji umarnin kara aure, mahaifinshi be ja ba sbd a lokacin ma ba wani lafiya ta ishe shi ba, shi kam ya san iya biyayya Hajiya wacce ainihin sunanta Zaliha tana yi mishi, zaman su bata taɓa saɓa mishi ba wannan rashin haihuwa kuwa ya san daga Allah ne in lokaci yayi zata haihu saide hajiyar shi ta kasa fahimta, dole a wani zuwa da yayi suka tafi wurin dukiyar Alhaji dake chan wani ruga daban ya Ga Ammin mu ya yaba.
Kama kama aka ɗaura auren su da Ammi, Hajiya tayi namijin kokari a zaman su sbd kowa ya sani muddin Kaga gida zaman lafiya ya mishi karanci mafarin uwargida ce kaman yadda idan Kaga yayi kyau to duk uwargida ce, ta riƙe girmanta ta kyautatawa Ammi fiye da tunaninki, ta janyo ta a jiki Dukda irin gargadin da dangin Alhajinmu suka dinga yiwa Ammi, itama dake ba me son fitina bace ta rungume kishiyar ta suke wanzar da zaman lafiya me girma a tsakaninsu.
Ammi bata shekara ba ta haifi Big bro, a sunan Big bro babu irin cin kashin da ba'a yiwa Hajiya ba wadda har Ammi seda ta taya ta kokawa don haka se ta sakarwa hajiyar ragamar Big bro ta ɗauke idanunta kwata kwata a kanshi kullum in zasu je ruga to mitar hajiyarsu Alhaji shine yadda Aka bar Emran hannun kishiyar uwa, lokacin yayenshi tasa dole aka kai mata shi, mafarin amintarsu da mahaifinki kenan, sun taso tare a ruga don kama kama seda Emran ya shafe sama da shekaru huɗu a ruga yana rayuwa dasu sbd kawai a nesanta shi da Hajiya, a cikin wannan shekarun ne Allah yayiwa Alhajinsu Alhajinmu rasuwa, an raba gado an ba kowa nashi sbd yawan na Alhaji se ya fara wani tunani akai.
Wasu ya sayar a lokacin shanu na da daraja sossai ya dawo Abuja ya samu fili ya fara gina campany na kanshi, wasa wasa se ga Alhaji ya tashi da ma'aikata babba ta yadda aka koma aka kwaso mishi dabobbinshi yayi paultry farm daga karshen companyn ya dibi ma'aikata da kwararrun turawa aka fara sarrafa madarar shanu, zuwa youghut, su madarar gari, su fresh milk da dai sauransu, hatta kyankyashar kaji da waye waye duk ana yi, bunkasar companyn yasa ya sake buɗe wata inda ake sarrafa fatun dabbobin zuwa abubuwa dayawa takalma, jakunkuna, da dai sauransu.
A zaman Big bro a ruga kar kice da son iyayenshi kawai ba yadda suka iya ne don Ammi har ta sake haihuwar Ya Salma har ma an sakata play class Big bro be fara makaranta ba, da kyar da suɗin Goshi Alhaji ya lallaba mahaifiyarshi suka dawo Abuja ya sama musu gida na musamman ita da Asma'u kanwarshi da naci sunanta bayan rasuwar ta, sauran matan kam sun ƙi sbd yadda hajiyarsu Alhaji bata raga musu ko da wasa suka kama dukuyoyin ƴaƴansu suka cigaba da rayuwar su.
Dawowar Hajiya nan yasa aka saka Big bro karatu yana gama primary Alhj ya fitar dashi waje inda a chan yayi secondary yayi degree na farko da na biyu, shi da Nigeria sede hutu kuma yawanci in ya zo ze je ruga sbd mahaifinki kawai ko yini guda ya kan yi ya dawo, a shekarar gama degreen shi na uku Allah ya karɓi Hajiyar su Alhaji ta aurar da Asma'u da shekaru masu yawa...
Ammi kuwa bayan Ya Salma ta haifi Ya Nurain da Ya Murad, bayan haihuwar ya Murad da jimawa ne aka haifi Ya Naufal wadda mahaifiyarshi ta rasu wurin haihuwarshi se Alhaji ya karbo shi ya baiwa Ammi Dukda Hajiya ya so bawa se ta ƙi sbd Ammi ce kawai mahaifiyarshi ko da take raye ta kuma bada uzurin sashen Ammi ne da yara se ya fi sakewa, a lokacin Big bro na chan Kasar waje yana practical wadda daga nan ne za'a bashi matakin professor a harkar likitanci.
Bayan zuwan Ya Naufal gidanmu da shekaru kusan biyar tukuna aka haifo ni, Alhaji ya mayar min da sunan Asma'u kanwarshi, kowa ji dani yake barin ma Ya Naufal tunda sunan mahaifiyarshi naci Maaama yake kirana yayinda sauran daga me Auta se Big bro da Asma'unshi kai tsaye... Ta faɗa tana ɓata fuska.
Ehen Ya Salma tayi aure tana nan cikin Abuja itama da yaranta, Ya Nurain yana Cyprus tunda ya tafi karatu yaki dawowa sede zuwa ya auri wata baturiya yaransu biyu, kwararre ne a harkar ƙarafuna, Ya Murad na nan da Alhaji shi yake taimaka mishi a komai na companies ɗin su na nan don field ɗin shi kenan se Ya Naufal da yace shi irin aikin Big bro yake so, The young surgeon kaman yadda Big bro yake kiranshi, se Ni ta nuna kanta ina karatun harkar karbar haihuwa da kula da jariri wato unguwar zoma. Toh kinji tarihin gidan Zubair mai yaƙi da iyalanshi".
Tana wannan surutun suna nan suna zagaye ne tana ɗaukan abubuwa yayinda Aysher ke tura chart ɗin, ya cika makil da abubuwa kama daga mayuka, turaruka, gowns, kananun kaya, atampha, laces, shoes da bags.
Aysher na ta murmushi Dukda tana fahimta sbd zallar hausa take yi bata sa turanci se kaɗan kaɗan kuma ta fahimta sossai, Allah sarki hajiya ta ayyana a ranta, irin su Allah yayi musu tanadi me girma ranar gobe.
Wurin biyan kudi suka tsaya Asma'u ta bada Atm card dinta aka cire ko rabin kuɗin da Big bro ya tura mata basu ci ba, komawa Asma'u tayi ta jidi choculates masu yawa aka saka musu a leda daban, daga nan Saloon ta kaita ana ta santin gashinta aka warware aka yi mata gyara na musamman, bata son kitso se aka bar mata kan a haka bayan an gama, daga nan suka yi wurin tailor ɗin Asma'u ta fidda mishi atampha da laces ta bashi kudinshi suka yi akan express ne rana irin ta yau zata dawo ta karɓa ta kai mata gidan Big bro.
Daga nan gida suka dawo a gajiye likis ga yunwa don ma sun yi sallah a Saloon, la'asar da ake kira yanzu kawai suka yi suka nemi abinci Ammi kam tana chan wurin Hajiya don ta kan je a matsayinta na karama su yi hirasu kan ta dawo.
Bayan sun ci abinci suka sake bajewa duk wani abu da suka saya wadda Aysher bata san anfanin shi ba seda Asma'u ta nuna mata, wani shakuwa suka yi na nan take hatta shaving stick seda ta nuna mata yadda ake anfani dashi da cream ɗin veet da ta saya mata na shaving, abu kaɗan se tace
"ɗiyarmu ki dage ki zama yar gayu kika wanku ba karamin gwara kan samari zaki yi ba"
Se Aysher tayi dariya ta ce
"kai Auntyna"
Wannan Auntyna da take faɗa ke fasa kan Asma'u take kara ƙaunarta, se tace
"Ba wannan kaɗai ba ɗiyarmu Big bro baya harka se da Ƴan gayu baki ga Aunty Naina ba? Kaman zata chanza fata sbd kyale kyale da gayu?"
Aysher murmushi kawai take tana ayyana yadda zata saje a cikin matasan gayun Abuja, taji daaɗi kwarai zuwanta gidan don da dare da driver ze maida ta harda kwallarta Asma'u tace zasu dinga ziyartar juna kar ta damu, dama bata zuwa gidan ne sbd Aunty Naina se tayi ta dagawa mutane hanci kaman tafi karuna arziki, amma zata ke zuwa sbd Aysher...
Ko da suka iso drivern shi ya taya ta shigar da kayayyakinta har parlor, me gidan na zaune matar kwance kanta akan kafafunshi yana anfani da waya tana ɗan mishi hira jefi jefi, ya sauya kaya zuwa kananu wadda suke matukar amsar shi su ɓoye shekarunshi, da idanu Naina tayi ta bin tulin ledojin har drivern ya gama shigowa dasu kan ta kalli Aysher ta juyo ta kalli Emran
"wannan fa?"
Se a lokacin ya ɗaga kai ya kalli kayan kan ya kalli Aysher da ke gaishesu ya amsa ya maida kanshi kan wayar, ganin babu wadda ya amsata yasa ta miƙe ta nufi kayan tayi ta bubbudewa tana mamaki harda super sheraton zanin da yayi 200k yanzu? Ga egyptian Abayas na 40-40k har kusan bakwai, man shafawa ma kaɗai na CreaVe aka saya mata.
"Emran waennan kaya duk na wannan village girl ɗin?"
In dutse ya tanka to ko Emran ya tamka ko kallon ta be sake yi ba, kokarin tattare kayakin take cikin muryar gargadi yace
"Ki ajiye mata kayanta Naina, wai whats wrong with you ne?"
"Ko de whats wrong with you ba! Taya zaka kashewa wannan yar kauyen wacce ko anfanin kayan bata sani ba irin wannan kuɗi? And ina magana ka ba banza ajiyata a gaban yarinyar salon ta yi ma kanta kallon kan mu ɗaya?"
"Naina! Naina!!" Ya kira sunan yana kallonta, hawaye ta fara tare da zubar da kayan tayi ball dasu ta wuce kaman iska zuwa ɗakinta, idanunshi ya lumshe.
Duƙawa tayi ta tattare kayan ta mayar leda sam bata ji wani haushin matar gidan ba, taji dae rashin daaɗin ganin yadda fuskan Abban nata ta nunawa damuwa, a nan ƙasa ta tsuguna bayan ta gama mayar da kayan leda, sam be san tana wurin ba se chan ya buɗe idanunshi don Miƙewa har ta fara tunanin bacci yayi a hakan ne ko yaya se suka haɗa idanu, saita Muryar shi yayi yace
"Da wani abu ne?"
"A'a, dama zan ce ne na gode Allah ya saka da alkhairi ya kara buɗi"
Da Ameen ya amsa tana nan tsugune kaman ta tambayi wannan matar patient din na dazu se bata yi wannan katsalandan ba taji yace
"se da safe ko?"
Tayi saurin Miƙewa tana cewa
"se da safe"
A hankali tayi ta tattare kayakin har ta shigar, a tsakiyar ɗakin ta zube su kan ta yaye gyalen ta ta isa gaban wardrobe se kallon kanta take tana mamakin wai itace wannan, nace tukuna ma.
A natse tayi ta shirya kayan tana tuna yadda tsarin na Aunty Asma'u yake tana shirya nata tsab se ga ɗakin ya fito kaman na Ƴan mata, tsalle tayi ta faɗa kan gado tana jin daaɗi, ta jima tana juyi kan ta yi toilet ta ajiye kayan wankanta da su shaving stick din, tayi alwala tazo tayi isha'i, zuwa wardrobe tayi ta buɗe tana tuna abunda Asma'u tace
"kin ga anan birni, waennan night wear ake kiransu akwai na matan aure akwai na en mata shiyasa na ɗauka miki riga da wando riga da wando dogaye, da daddare duk kayan dake jikinki zaki cire ki saka su se kin fi jin daaɗi, sannan babu maimaita kaya kina cire na jikinki ki saka shi cikin basket na wanki, in ta kama ma duk dare kan ki kwanta kiyi wanka ki sa turare zaki ji yadda zaki ji daaɗin bacci a wannan rana"
Murmushi tayi ta dauki sabon towel shima seda ta jadadda mata dashi ake wanka in an fito a goge jiki se a shafa mai kan a shanya shi a sa kaya, kayan jikinta ta cire ta haɗa da na saƙinta da ta sanyo a leda ta zuba cikin basket da ta gani irin shi a ɗakin Asma'u na kayan wanki, bayi ta shiga ta farke sabon sosonta ta buɗe shower gel kaman yadda Asma'un ta nuna mata, Allah ma ya sa tana da kwakwalwa bata manta duk zantukan Asma'un ba, wanka tayi da ruwan dumi ta fito ta shafa mai sama sama ta fesa turare kaman yadda ta nuna mata yadda ake sawa tun kan su tafi mall, ta sanya Cotton riga da wandon ta se taji wani daaɗi na ratsa ta, se shakar kamshin jikinta take haka ta kwanta a gadon tare da lumshe idanu bacci me daaɗi ya ɗauke ta...
Be bi ta kan Naina ba ya wuce ɗakinshi yayi shirin kwanciya ya kwanta abun shi.
Hawaye take tsakanin ta da Allah
"Mommy wai kinga abubuwan da yake yiwa yarinyar nan? Ni abubuwan ma basu dameni ba, ya kaita duk inda ze kaita sannan ya mata na tsani yarinyar ba tare da na san dalili ba"
"wai yaushe kika zama haka ne? Ina ke kika gaya min yadda ya dinga lallaba ki akan in ba zaki taimake shi akan yarinyar ba ki fita harkar ta? Wannan abunda kike yin shi ze sa ta raina ki, ki kama kanki a matsayinki na me ilimi kuma matar gida, tun yaushe baki maida ita ƴar aikin da ya ƙi samar miki ba!"
Shiru tayi tana nazarin maganan maman tata, hakane kuma fa, kuma ta san fushinshi bashi da kyau shiyasa be cika yi ba don in ya birkice kaman wadda ya sha shaferin Fulani, zata fita harkar yarinyar ta kama abunda ke gabanta tunda ta riga ta zame mata ƙashin wuya.
Sun ɗan kara tattaunawa da mommy kan ta miƙe tayi wanka ta shirya cikin wasu sexy nighties ta nufi ɗakinshi don bashi hakuri irin ta masoya, ta san kayanta cikin lokaci kankani ta samu ta saukar da fushin suka sha baccinsu ita kanta ta san mijinta na son ta to me na wani damun kanta akan yar kauye?....