Page 6
by @gureenjoh
RUBUTU A KAN RUWA
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*
*SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏
*Aleesha collection*
''Jira jira jira Lantana Ina za ki na ga ki na sauri haka?"
"a a larai kyale ni yanzu zamanin nan idan kin ga mace ta zauna ita ta so, gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata''
''A a wannan shahararen campany da suke taimakawa mata masu son fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida akan farashi mai Kama da kyauta za ki? jirani kawai lantis marainiya 10k dina zan je na ga ko zan samo abin da zan fara maida taro sisi''
Hajiya ta zo ki ji wani zance, ki na son ki fara sana'a ko Kuma har yanzu ba ki gaji da tambayar mai gida ko saurayi kudin biki da na suna yana sha miki kamshi ba, to idan kin shirya nima na shirya tsaf domin ba ki kayana sari akan farashi mai sauki ke ma ki je ki nemi na ki.
Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp ***
Sai kun zo
FREE PAGE 6
A hankali ta kai hannunta ta fara zame hular sbd kama kanta da yayi garin zarewa ta haɗa har da ƴar karamar ribbon da ta kama gashin dashi tuni gashinta ya baje yana yauƙi shi kaɗai kaman haɗin baki Ƴan ajin suka yi ihun
"wooooow"
Da sauri Aysher ta zare ribbon din ta sake fara kokarin kama gashin idanunta cike da hawaye, Maryam dake kallonta ranta ya sake baƙi kirin ina ma ace yarinyar bata da gashi da sun sha dariya, ta tsani competition se gashi ta samu wacce daga zuwanta ta tsole mata idanu, makarantar suna da wani ɗabi'u na turawa kaman contesting na model of the school, face of the school, festivals, field trip da dai sauransu.
Su kan zabi face of school ko model ne daga js 1 har Ss3 za'a fidda mutum ɗaɗɗaya, in an samu six a cikin wannan six ɗinne za'a fidda ɗaya ayi mata picture da uniform kala kala a mammana a duk hallway na makarantar, ita ce wannan kambu ke hannunta be taɓa fita ba amma ga dukkan alama wannan yarinyar zata kawo mata cikas cikin al'amura yadda take ganinta wata goddess of beauty.
Ita dai Aysher tana nan zaune tana kallon malamai don kallo zata ce sbd yadda gabaɗaya take tsarge ba wani mai da hankali take ba har aka tashi karfe ɗaya da minti ashirin, cafteria ta koma ta sake sayan snacks ta nufi inda aka tanada don ajiye motoci a nan ta samu driver ɗin da ya kawota ta buɗe ta shiga tana gaishe shi, shima gaishe ta yayi suka nufi gida.
Se dare ya kawo mata abinci tayi godiya, haka rayuwarta ya cigaba da tafiya abunda ya chanza shine zuwan malamin dake mata islamic da yamma hakan ya rage mata kaɗaici, kuma ba laifi tana kokarin ganin tayi picking karatun, kan sati ya ƙare ta ɗan yi rama sbd matsalar Maryam ta zame mata bully, har aikenta suke cikin izgili da raini, har wani tsoron Maryam din ne ya shige ta na masifa ko muryarta taji se jikinta ya hau rawa, hakan ya samu tasiri ne sanin cewa duk wadda ta gani a makarantar ta san ɗan wani ne saɓanin ita da alfarma taci har Allah ya kawota nan ɗin, sannan tana da zurfin ciki shiyasa bazata iya faɗawa kowa ba to yo ko ta so faɗa din ma wa zata sanarwa? Babu.
Yau Jumma'a tunda suka tashi daga school ta dawo gidan tana kwance idanunta a lumshe ko uniform bata cire ba, banda hawaye babu abunda take sbd irin fusgan gashinta da su Maryam suka dinga yi a chan baya wurin garbage na makarantar, ta aike ta shawarma taje ta kawo shine wai Meyasa ta sayi me Sausage bata san bata ci ba, suka dinga gayamata maganganu marasa daaɗi har da fisge mata gashi, wani irin sarawa kanta ke yi..
Buɗe kofar ɗakin taji an yi da sauri ta share hawayenta tare da Miƙewa zaune, a take ta saki murmushi ta sauƙa da wuri taje ta rungume Asma'u
"Aunty Asmy sannu da zuwa"
"yauwa ɗiyarmu, me ya faru na ganki so silent haka? Yanzu ko uniform baki cire ba tunda kika dawo?"
Asma'u ta faɗa tana zama bakin gadon ta ɗakin kal kal, itama zama tayi tana cewa a hankali cikin hausarta
"Kaina ne ke ciwo shine na ɗan kwanta ko ze lafa"
"sannu ɗiyarmu, baki sha magani ba?"
Kai ta gyaɗa ina zata ga wani magani yau kwananta uku daga matar har mijin bata sanya kowa a ido ba, driver ɗin dake kaita school dae kan kawo mata abincin dare bata san wa yake sanya shi ba.
"Akwai firt aid a kitchen ai muje ki sha maza... Tsaya ma ke ga fa dinkunan ki nan ya gama kinga yadda suka yi kyau?"
Ta faɗa tana fiddo kayayyakin daga cikin leda, da sauri Aysher ta fara dagawa tana yaba kyaun su gaskiya yayi kokari, wani batik Red nd peach ta ɗaga ya zuba mata adon Red lace a jiki sannan an yi mata tail kaman me zuwa dinner haka, fitted ne ya mugun yi mata kyau tace
"kai Auntyna bari nayi wanka na sa wannan gaskiya ya min kyau"
Dariya Asma'u tayi tace
"ciwon kai har ya ware kenan ana ta santin kaya"
Murmushi kawai tayi ta shige toilet wanka tayi tana feeling sulɓin skin ɗin ta sbd yadda take samun kulawa na Mayuka da abubuwan wanka, ramarta kuwa bayanna kyaun surarta ya kara, hancin ta ya kara tsawo idanunta suka kara girma, a gaban madubi ta zauna tana shafa ƙasan gashinta da scalp din yayi Red sbd fusgan da ya sha.
Wani abu me zafi ta haɗiye kan ta shafa mai tana kallon Asma'u dake zaune tana ta dannan waya, bayan ta gama ta fesa turare ta ɗauki rigar ta saka wow wow wow, ita kanta ta yaba da yadda yayi mata mugun kyau, barin ma da ta kama gashinta sako sako ta ɗaura dankwalin daga gaban gashin baya da gaban goshinta dake kwance lublub ya bayyana.
"Auntyna!"
Ta Kira Asma'u da hankalinta ke kan waya, ɗagowa tayi se ta zaro idanu
"wooooow i got a fine daughter, ke kinga yadda ya miki kyau? Yanzu muje ki sha magani"
Miƙewa tayi suka fito suka shiga kitchen, First aid ta ɗauko ta duba pcm ta bata ta kuma ce mata ko gaba zata ji wani ciwo akwai magani anan tayi anfani dashi.
"Aunty Asma'u Don Allah ki koyamin yadda ake anfani da wannan"
Ta Nuna gas ɗin ta faɗa ne sbd ta gaji da cimar da take samu tana missing abubuwan su na ruga kuma shi take so amma bata iya anfani da abun ba tana kuma tsoro shiyasa bata yi kiriniya ba..
"Kinga har na manta kuma wlh Ya Murad ce min yayi in zo in koya miki sbd ki samu abunda zaki ke ci na san matar gidan ba girki ta iya ba, ina ma izzarta ze barta shiga kitchen"
Ita dae Aysher bata ce komai ba.
A hankali Asma'u ke koya mata, kunna gas ita dae taga wani abu kaman bindiga kuma wai ashana se jujjuya shi take, bayan nan ta nuna mata ɗayar da ba se da ashana ake kunna shi ba kana murdawa ze kawo wuta, se suka ɗaura ruwan zafi, locker locker take buɗewa tana nuna mata abubuwa se mamaki take chan tace
"Auntyna yanzu da ba'a dafawa basa ɓaci?"
"Ruɓewa kai sede a zubar, shiyasa lokaci lokaci ze sa a turo ma'aikatan gidanmu su kwashe ya saka sabbi ke farkon auren su fa har shinkafar garar Aunty Naina ya zama gari basu buɗe buhun ba, kina taɓawa ze wargaje sbd ajiya"
Murmushi kawai Aysher tayi amma zuciyarta fal mamaki, shinkafar tuwo suka fitar ba wani tsinta suka wanke suka zuba cikin ruwan da suka ɗaura suka ɗan sa muciya suka juya kan suka rufe, komawa gaban frigde na kitchen ɗin suka yi, Buɗewar ma da yake ba normal bane seda Asma'u ta nuna mata frozen chicken, fish, beef gasu nan birjik se kayan miya babu abunda babu a gyare suke tsab cikin ziplock daban daban sun kankare har dusa dusa suke.
Kaza Asma'u ta fiddo ta sa a cikin bowl da ta sanya Aysher ɗaukowa ta ajiye kan ta zari ziplock ɗaɗɗaya ta dibi kayan miyan da zata buƙata, suka koma gaban blinder wadda na buchimix ne a hankali ta nuna mata yadda ake anfani dashi, ita kuwa tana dauka a kanta tace
"kai na gode Auntyna kinga yanzu zan yi duk abunda na san zan iya ci"
Murmushi Asma'u tayi tace
"kin ma yi kokari ai sati guda kina nan kina ta kame kame duk kin rame".
Dariya Aysher tayi tace
"ba fa kame kame Abba yana kawo min abinci"
"da ke da Abban duk kuna cikin wani hali"
Tayi maganan cikin alhini wadda ya sa Aysher sakin dariya.
Ɗaya frigde din da suka buɗe kayan madara madaran kamfanin Alhaji ne jibge se Aysher taji sha'awar shan nono me ɗauke da dakkere.
"Auntyna akwai turmi kuwa?"
neman turmi suka fara da kyar suka samu, Ayusher ta koma inda taga hatsi a robobi masu kyau ta dibi gero, ta baya suka fita bayan Asma'u ta sa kazar da ta fiddo ta sa mishi spices ta ɗaura kan dayan gas ɗin, ruwa take zubawa kadan kadan cikin geron tana surfa shi har ya surfu, a bakin pampon bayan suka wanke shi tas suka rairaye duk wani ƙasa dake tare dashi, ta ɗan baza shi suka koma kitchen tuwon Asma'u ta bar mata ta tuke ita kuma ta komawa kazar, ta zazzare ƙashin tas kan ta zuba mishi ruwa da manja ta sake wani haɗi da daddawa tayi adjusting seasoning din kan ta rufe ta dawo wurin Aysher tana nuna mata yadda ake kulla tuwo a leda don ta tambaye ta tace duk abincin da ake kawo mata in tuwo ne se ta ganshi a ƙulle a leda ya ake yi? Shine take koya mata.
Bayan sun gama tace
"bari na duba gero na in ya sha in daka"
"kaii wani irin daka kuma ga fa buchimix blender dutse ne kaɗai ba zaki markade a ciki ba, komai yana yi"
Cikin rashin amincewa tace
"dakan hannu ai yafi daaɗi"
Ita dae Asma'u bata ga wani bambanci ba haka ta bita suka koma ba wani yawa kuma abunka da wadda ya riga ya saba a take ta dake shi ya zama gari suka tankade suka koma kitchen.
Lokacin Miyar ta gama nuna yadda ya kamata sbd sirrin kuka na cikin nunar shi, kaɗawa da whisk Asma'u tayi be yi kauri ba yayi daidai se kamshi yake, namar kazar yayi daga daga a cikinshi, ta kwashe a ɗan namiyar kular da suka zuba tuwo.
A bincikensu suka samu gammo irin na kaba ɗin nan da Fulani kan yi, kila ma daga cikin kayayyakin kyautar en uwa su na kauye ne suka kawowa matar yayan da alama ko sanin anfanin shi bata yi ba, harda kwarya me ɗan girma da fai-fai da ludayi na asali, wankewa Aysher tayi don duk yayi kura tunda ba anfani ake dashi ba taje ta buɗe frigde se ta tsaya tunani.
Asma'u tace
"matsa je ki murje dakkeren don ni ban iya ba bari na fiddo madarar da naga Ammi na hadawa idan zata yiwa Alhaji kawai dae nashi ba masu sugar bane"
Komawa tayi ga garin geron in ta baɗa ruwa se ta murza ta murza ta ɗaga kwaryar ta kaɗa shi tsakiyar hannunta take yake shure wa a hankali hankali tana fiddawa har ya ƙare, Asma'u se kallon ta take, lallai yarinyar ta samu horo me kyau don tana da tsabta, dama Ammi kan ce mata in ta ganta tayi wani abu Fulani ba'a san su da kazanta ba, bata tabbatar ba se yanzu ji wannan daga Ruga take amma tsabtar ta wanda ma yayi karatu ba lallai yana dashi ba anan, a steamer Asma'u ta saka musu shima tana nuna mata yadda ake har ya dahu, madarar ta zuba kala har uku a cikin kwaryar kan suka zuba dakkeren, Asma'u ta ɗauko kankara ta zuba da sugar kaɗan ta kara flavour ɗan kaɗan take ya bada wani kamshi na musamman.
Se zumudin son sha Aysher ke yi Asma'u ta hanata suka kwashe komai suka kai dining, suka dawo suka gyara kitchen din fes kaman yadda suka same shi, kan suka koma dining din kofi da cokali Aysher ta ɗauka taje ta dibi damammiyar nonon.
"Yanzu ba zaki bari ki fara cin abinci ba?"
Shagwaɓe fuska tayi tace
"Ni dae se na sha damimmayar Nono tukuna in iya cin wani abu, a andi no mi wairi kuje ɗo(kin san yadda nayi kewar abin nan kuwa? Hmmm)
Tana soma zubawa aka dannan door Bell, Asma'u dake cin tuwonta tace
"ɗiyarmu duba kofar nan"
"To Aunty Asmy bari na gama zubawa"
Se dariya Asma'u ke mata kaman ze gudu?
Seda kuwa ta gama zubawa ta sa cokali tayi tasting tana lumshe idanu kan ta nufi kofar rike da kofi da spoon din ta.
A hankali ya fara sauke idanunshi bisa kofin da take ta kaɗa cokali a cikinshi kan ya ɗago zuwa dogon wuyanta dake bayyane, ɗauke idanun yayi ya mayar fuskanta da yayi fayau, murmushi ta sakar mishi a bazata, ɗauke kanshi yayi tare da lasar lip ɗin shi yana jin zazzakar muryarta na cewa
"Abba sannu da dawo..."
Bata ƙarasa ba sbd Naina da ta fito ta bayanshi ta hankade ta a bazata tuni tayi baya zuwa ƙasa kofinta ya hantsila ya zube mata a jiki daga wuyanta zuwa kan kirjinta, sanyin ya ratsa ta wadda a take ta lumshe idanu ta fara hawaye sbd ta matukar firgita.....