06
*ƘAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*06*
*State Servidor Public Hospital, Rua Borges Lagoar,1083 Vila Clementino, Sao Paulo, Brasil.*
PEDRO POV.
A bakin titi taxi ɗin da ya hau ta sauƙe shi, ya fito yana goya jakarsa a baya, kai tsaye cikin asibitin ya shiga, ya wuce reception ya nufi elevator. Yana shiga ya danna lambar hawa na biyar, sannan ya ja baya yana rungume hannayensa. Elevator na isa hawa na biyar ta tsaya sannan ƙofarta ta buɗe ya fito ya raɓa mutanen da ya iske tsaye a bakin elevator ɗin suna jiran fitowarsa domin su shiga su ma.
Tun kafin ya karasa ɗaki mai lamba 89 ya fara jiyowa hayaniyarta, kansa kawai ya girgiza sannan ya bude ƙofar ɗakin ya shiga kai tsaye, abin da yake hasashe shi ne ya tabbata, ya san in har ba lokacin shan maganinta ne ya yi ba babu abinda zai sa suna musu da nurses irin haka. Zaune take a kan gadon marasa lafiyar dake ɗakin, ta tsare nurse ɗin dake tsaye a cikin ɗakin da manyan idanuwanta tana mata masifa, a shekaru ba za ta haura sha bakwai ba, fara ce sosai irin farin turawa, sanye take da kayan marasa lafiya na asibitin, baƙin dogon gashin kanta daga gefe ya kwanta a kan kafaɗarta, daga ɗaya ɓangaren kuma an yi gajerun kitso guda biyu da ba su kai ƙarshe ba, (wato side braid), manyan idanuwanta ta janye a kan nurse ɗin ta kalle shi.
“Yauwa Hard Rock, gara da ka zo, ka gayawa wannan matar cewa ba a mini dole, a kan me za ta ce sai na sake shan magani, bayan ɗazu da Ibrahim ya zo ya bani na sha...”
Pedro ya ƙanƙance idonsa yana mata kallon nazari, sai kuma ya kalli nurse ɗin, ba tare da ya tambaya ba ta girgiza masa kai alamun ba ta sha maganin ba. sai ya sauƙe hannayensa dake harɗe a ƙirjinsa ya soma takowa zuwa cikin ɗakin.
“Ni kallonta ma ba na so, ka ce ta fice”
“Juliana?”
Ya ƙira sunanta cike da tuhuma, kanta a ƙasa ta ƙi yarda su haɗa ido, kamar da aka ce idan suka haɗa ido asirinta na ƙaryar da ta yi ta sha maganin sanda Ibrahim yana nan bayan ba ta sha ɗin ba zai tonu.
“Tun muna shaida juna ni da ke ki karɓi magungunanki ki sha!”
Idanuwanta ta fara ƙifƙiftawa, tana ɓata baki alamun za ta yi kuka, hannu ya miƙawa nurse ɗin ta ɗamƙa masa tray ɗin hannunta dake ɗauke da magungunan Juliana ɗin. Ya zauna a gefenta yana aje tray ɗin a tsakaninsu, sannan ya sauƙe jakar bayansa ya fito da ruwan roba daga ciki. Ya ɓallo maganin da ya san shi ne wanda take fara sha ya miƙa mata, tana wasa da sarƙar dake wuyanta me pendant ɗin cross ta dube shi bakinta na rawa, alamun gaf take da fashewa da kukan, ƙarshen girarsa ta ɓarin hagu ya ɗage yana sake miƙa mata alamun karɓi mana.
Sharrr hawaye suka zubo daga idonta, ta miƙa hannunta ba dan tana so ba ta karɓa, ta ɗaga kanta sama ta cilla maganin, sannan ta karɓi robar ruwan da ya bata ta kora da shi. Ta sauƙe kanta tana grigiza shi, da ɗacin maganin ya ziyarci sashen ɗanɗanonta sai ta fashe masa kukan sangarta.
“Da ma ai na san ba ka sona, na san ka tsaneni, Allah sarki Julia marainiya, ba ta da kowa, shi ma Badar ɗin ya daina sonta, tun da ya tursasata kan sai ta sha magani mai daɗi...”
Kamar ɗazu, yanzu ma haka ya tsaya kawai yana kallonta, kuka take har da su face manjina.
“Kin gama?”
Ta kalle shi jin abin da yace.
“Ga maganinki, maza shanye dika”
“Wai yanzu ba za ka ji tausayina ba Hard Rock?”
Ta ƙarashe tana kama damtsen hannunsa da duka hannayenta biyu, ta maida fuskarta yanayin ban tausayi, har da su ƙif-ƙifta masa ido duk dan ya tausaya mata.
“Gata ɗaya zan miki shi ne kula da lafiyarki, maza ki shanye wannan”
Ya ciro hannunta daga jikin hannunsa, sannan ya buɗe tafin hannunta ya zuba mata ƙwayar maganin, sannan ya ɗanka mata ruwa a ɗayan hannun nata. Ta kalli ruwan da maganin, sannan ta kalle shi.
“Na sha?”
Ta tambaya kamar ba ta san abin da yake nufi ba ke nan.
“Maza sha My Fairy”
“Shikenan, Jesus loves me”
Ta tari aradu da ka ta jefa ƙwayoyin a bakinta ta bi su da ruwa, tana haɗiyewa ta ƙanƙame jikinta saboda yanda take jin ɗacin maganin har ƙirjinta.
“Yauwa Julia May god be with you... zan je na ga Dr Lima, ki haɗa kayanki da na dawo za mu tafi gida”
Ya miƙe ya fita ya barta zaune tana ta binsa da kallon haushin abin da ya mata yanzu. Kamar yanda yace sai da ya je ya biya bills sannan ya nufi office ɗin Dr Lima, a hanya wani mutum ya bige shi ba da sani ba, hakan yasa takardun dake hannunsa suka daɗi.
“Ka yi haƙuri ban kula ba”
Cewar mutumin da ya bige shi ɗin.
“Ba komai”
Ya faɗa yana shirin tsugunnawa domin ɗaukan takardun da suke zube a ƙasa kusa da ƙafafun mutumin, ƙiris ya rage hannunsa ya kai kan takardun wani abu kamar wulgawar walƙiya a cikin hadari ya wuce a idonsa, wani abu da ya faru a can baya, lokacin da suke gidan marayu.
_“Na ji an ce me cin abinci a ƙasa kare ne...”_
Maganar da har ya mutu ba zai taɓa mantawa da ita ba ta kutso cikin tunaninsa, abin sai ya zame masa kamar yanzu yake faruwa, domin a wancan lokacin ma ya tsugunna a ƙasa kamar haka, ya ɗaukan wani cake dake yashe a ƙasa, sannan kamar dai a wancan lokacin, ƙafafun Mateus na kusa da cake ɗin bayan ya gama mitsike shi a ƙasa. Mateus! Wani mutum ɗaya da ya azabtar da rayuwarsa kamar yanda mahaifiyarsa ta masa... Yatsunsa da ya miƙa dan ɗaukan takardar ya dunƙule, sanna ya miƙe ya kalli mutumin dake tsaye har yanzu.
“Kai ya kamata ace ka ɗauko mini su”
Ya nuna takardun dake kusa da ƙafafun mutumin, wani irin kallo ya masa na rainin hankali.
“Ban gane ba”
“Bari na ganar da kai…”
Ya faɗa yana tattare hannun rigarsa alamun zai kai duka, da sauri mutumin ya tsugunna ƙasa ya kwaso takardun, sannan ya miƙe ya damƙa masa su ya taɓa shi ya wuce da sauri yana faɗin ko dai ba shi da hankali ne. A hankali Pedro ya juyo bayan ya bi shi da kallo, ya ci gaba da tafiya. Yana isa office ɗin Dr Lima ya ƙwanƙwasa ƙofa, daga ciki aka ba shi izinin shiga, ya bude kofar kai tsaye ya shiga, ya rufeta lokacin da suka haɗa ido da Dr Lima dake cikin office ɗin.
“Pedro? Ƙaraso ka zauna”
Cewar likitan da fara’arsa, wani guntun murmushi Pedro ya masa sannan ya amsa ya ƙarasa ciki ya zauna a wurin da Dr Lima ya nuna masa.
“Yau na kawo Julia an mata gwajin da kace za ayi… yanzu haka ma tafiya za mu yi, shi ne na ce bari na zo mu yi magana a kan aikin da za a mata”
Dr Lima ya jinjina kansa bayan Pedro ya gama masa bayanin.
“Ai na ganta ɗazu… Kuɗaɗen aikin sun samu ne?”
Kansa ya girgiza yana ƙarawa da.
“A’a tukunna dai, amma ina da tabbacin nan da sati mai zuwa zan gama haɗa kuɗaɗen, tun farko na gaya maka cewar ba zan zuba ido ina kallon Julia ta mutu ta barni ba, zan yi komai domin ceton rayuwarta”
Dr Lima ya yi murmushi.
“Na sani Mr Santos, amma akwai buƙatar ka ƙara ƙaimi wurin haɗa kuɗaɗen nan, domin har yanzu babu abin da ya sauya a ciwon nata, dole a gaggauta mata aiki in ba haka ba za ta iya mutuwa yau ko gobe!”
SA'AD POV.
Murmushi ne kwance kan fuskarsa yayin da yake chat da sabuwar budurwar da ya yi, a kai a kai Aysher dake cin abinci a can gefe kan wata kujera da aka aje a falon tare da table ke satar kallonsa tana ƙunƙuni. Bayan shi da ita akwai Kairat da yayanta Mujahid a falon, wanda suke zaune kusa da Sa'ad, ita Kairat na zane-zane a cikin littafinta na makaranta yayin da yayanta Mujahid ke buga game a Tab ɗin Aysher.
Kairat da Mujahid dai yaran matar Mai matarba ta uku ne, wadda Allah ya yi wa rasuwa shekaru biyu da suka wuce, ta mutu ta bar yaran nata guda biyu da suke da ƙarancin shekaru, domin du-du-du shi kansa Mujahid bai wuce shekaru goma sha biyar ba, ita kuma Kairat ba ta haura shekaru goma ba. Zamansu ya dawo hannun Fulani Amrya ne bayan rasuwar mahaifiyarsu, kuma Fulani Amrya ta riƙesu kamar ita ta haifesu.
"Tun yaushe ka yi sabuwar budurwa?"
Maganar ta fito daga bakin Aysher ba tare da ta kalle shi ba, kuma ya san da shi take, dan haka ya ɗauke idonsa daga kan wayar ya kalleta.
"Bai shafeki ba 'yar sa ido"
"Hump! Bai shafeni ba kam, Playboy!"
Ta faɗa tana ɗage kafaɗunta alamun ba ta damu ɗin ba.
"Lallai yarinyar nan kin rainani da yawa, amma zan yi maganinki"
"Ya Sa'ad ai da Ya Hammad ne ba ta isa ta masa haka ba"
Mujahid ya sa baki.
"Ƙyaleta Mujahid, ni ɗin ma dan ta ga ina mata wasa shi yasa ta maidani karkatacciyar katanga mai daɗin ƙetara, ai shi dodon nata ko ido ba ta isa ta haɗa da shi ba..."
Kairat ta yi dariya.
"Na ɗauka ni kaɗai nake yi wa Ya Hammad kallon dodo"
"Ni fa ban taɓa ganin Ya Hammad ya yi murmushi ba..."
"Ku gama gulmar tasa, ni kuma na ƙira shi na gaya masa"
Aysher da ta taso ta faɗa tana tsayawa a kansu.
"To ki gaya masa mana, tsoronsa ake ji?"
Cewar Sa'ad, Aysher ta yi murmushi kawai tana zama a kan kujera.
"Mujahid ka ƙira Haula ta zo ta ɗauke kayan abincin nan"
Mujahid ya amsa mata da to, sannan ya miƙe ya fita falo na biyu, a nan ya ƙira Haula ɗaya daga cikin hadiman sashin Fulani amarya, suka dawo tare da ita, ta shigo falon tana musu sannu da hutawa, sannan ta kwashe kayan abincin kamar yadda aka sakata.
"Ya Sa'ad za ka zana mini kifi, tun ɗazu nake gwadawa amma na kasa zana mai kyau"
Cewar Kairat tana nuna masa takardar littafinta, inda alamun zanen pencil ya fito, duk kuwa da an saka eraser an goge shi bai kasa fitowa ba.
"Miƙo na gani"
Ta tashi ta miƙa masa littafin.
"Kairat sau nawa zan gaya miki cewar in ana zane ba a sakawa pencil ƙarfi, kar ki zana shi sosai yanda zai yi baƙi da yawa, dan wannan eraser ɗin taku ba za ta iya goge shi ya fita dika ba!"
Ya faɗi yana duba yanda takardar ta ɓaci.
"Wannan ta ɓaci gaba ɗaya, dole mu yageta"
Ya kama takardar littafin ya yage, sannan ya karɓi pencil ɗin dake hannunta, yana shirin fara zana mata Aysher dake kallonsu tace.
"Wai zana mata za ka yi?"
"To kar na zana mata?"
Ya maido mata tambayar yana kallonta bakinsa a buɗe cikin mamaki.
"Yanda ka ƙware a zane idan aka gani dole zanenka da nata ya bambanta, sai ka sa ta faɗi a homework ɗin"
"Aikin banza, su ma malaman nasu ai sun san cewa wasu a cikinsu ba za su iya zanawa da kansu ba"
Ya bata amsa yana ɗora pencil ɗin a kan paper'r littafin, sannan ya fara tsara mata zanen kifin cikin salo mai jan hankali da birgewa.
"Wai yaushe za ka koma Abuja ne?"
Aysher ta sake jefo masa tambayar, murmushi kawai ya yi ba tare da ya kalleta ba.
"Nan da sati ɗaya"
"Sati ɗaya? Ba ka ce sati huɗu za ka yi ba? Kuma na ga ba ka fi sati biyu da zuwa ba"
Ya jinjina kansa a hankali.
"Takawa ne yace kada na haursa sati ɗaya a garin nan... Da ace na yi magana a lokacin kuma da na bar garin nan tun a ranar"
Aysher ta sauƙe numfashi.
"Me zai hana ka faɗawa Ammi, Wata ƙila idan ta sa baki ya barka ka ƙarasa hutun da ka ɗauka"
Ba shiri ya ɗaga kansa ya kalleta.
"Karo na farko da kika yi magana ta hankali a rayuwarki ke nan, kin kawo shawara mai ma'ana yarinya"
Ta juya idonta alamun kai ka sani tana buɗe wayarta. Kamar daga sama haka aka banko ƙofar falon da suke ciki, abin da ya furgitasu ke nan, gaba ɗayansu suka miƙe dan ganin wanda ya zo da wannan gadarar, dan hatta bayi da hadiman fadar ba kasafai suka cika shiga falon ba.
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un Ya Sa'ad ka zo"
Cewar Muhibba da ta shigo hankalinta gaba ɗaya a tashe, Sa'ad ya nufeta yana tambayar.
"Me yake faruwa?"
Ta kasa magana, sai hawaye take tana yarfe hannu tana maimaita ta shiga uku.
"Muhibba me ya faru ne?"
Aysher ma ta tambaya tana ƙarasawa wurin da take tsaye.
"Ya Maryam! Ya Maryam ce..."
Sa'ad bai tsaya ya gama jin abin da take son faɗa ba ya raɓata ya fita daga falon da sauri, ita da Aysher kuma suka take masa baya. Kafin su ƙarasa sashin Adda har sun ƙagu, barin ma Sa'ad da yake ganin nisan tafiyar fiye da ko yaushe.
Tun da suka ƙarasa sashin suke jiyo ihunta, hakan ya bashi damar ƙara sauri kai tsaye ya nufi sashin da ɗakinta yake, tun a hanya yake cin karo da hadiman sashin sun yi tsilli-tsilli da su halan ya ƙara tabbatar masa da lallai yau abin na Maryam ba ƙarami ba ne.
Yana isa ya iske Adda da jakadiya tsaye a ƙofar ɗakin Maryam ɗin, yayin da suke jiyowa ihunta ita da wata da bai ma san wacece ba, ba tare da ya ce komai ba ya nufi ƙofar, yana zuwa ya kama handle ya murɗa da ƙarfi, ƙofar na buɗewa ya yi arba da Maryam ta shaƙe wuyan wata daga cikin masu musu hidima.
Ai da gudu ya faɗa cikin ɗakin, ya shiga ƙoƙarin ɓanɓare hannunta a kan wuyan matar, amma da yake ƙarfin ba nata ba ne sai ya kasa, ita tana ihu, haka ita ma wadda aka shaƙe ɗin ihun naiman taimako take. Sa'ad bai haƙura ba ya ci gaba da ƙoƙarin ƙwatar matar, da ƙyar ya yi nasarar cire hannunta a wuyanta, ai ko tana jin iska ta fara isa huhunta yadda ya kamata ta miƙe ta yi waje a ɗari uku da sittin tana kuka.
A hankali Maryam ta miƙe tsaye kanta a ƙasa, ba ta ɗago ba ballantana ta kalli fuskarsa.
"Maryam!"
Ya ambaci sunanta a hankali yana leƙa fuskarta, amma har yanzu kanta a ƙasa, sai ta soma ja da baya da baya, tana kaiwa bango ta juya ta fara buga kanta da bango tana kuka faɗi take.
"Maryam me yasa ba kya kyautawa? Me yasa ba kya jin magana? Maryam ki yi wa kanki faɗa, Maryam ke fa abar tausayi ce, Maryam!..."
Ganin tana shirin illata kanta yasa Sa'ad ya riƙota ta fara kiciniyar ƙwacewa.
"Ka ƙyaleni! Ka ƙyaleni na mutu! Mutuwa zan yi! Gara ma na mutu!"
"Ba za ki mutu ba Maryam"
Ya faɗa yana kallon jajayen idanuwanta da kallo ɗaya za ka musu ka san cewa me su ba ta cikin hayyacinta, tun tana ƙoƙarin ƙwacewa yana riƙeta har ta saduda, jikinta ya saki, a hankali ya ɗauketa ya ɗorata saman gadonta, sannan ya zauna yana tofa mata addu'o'i. Ya jima a ɗakin bai fita ba, dan gani yake kamar idan ya fita za ta iya farkawa ta ci gaba da wannan abin ne.
Bamm! Aka banko ƙofar ɗakin, ya ɗaga kansa ya kalli Sadiq mijin Maryam ɗin, gaba ɗaya yanda ya shigo zai sa ka gane a birkice yake, duk alamun tashin hankali sun bayyana ƙarara a tare da shi.
"Sa'ad me yake faruwa?"
Ya tambayi Sa'ad da ya miƙe yana kallonsa.
"Abin nata ne ya tashi, har ta shaƙe wadda ke kwana tare da ita, amma ba komai, ta samu bacci..."
Sadiq da idonsa ke kanta ya furzar da numfashi yana jin zufa na ci gaba da tsattsafowa a goshinsa.
"Waye ya gaya maka abin da yake faruwa?"
Sa'ad ya tambaya, dan ya san dole wani ne ya gaya masa, domin babu yadda za ayi Sadiq ɗin ya ɗauko ƙafa ya zo fada da wannan daren.
"Muna cikin waya da ita abin nata ya tashi, shi yasa na taho hankalina gaba ɗaya a tashe..."
Sa'ad ya sake kallonta jin ta yi motsi.
"Ruwa! Ruwa"
Ta furta ba tare da ta buɗe idonta ba, Sa'ad na ƙoƙarin tashinta zaune Sadiq ya riga shi, ya zauna bakin gadon yana kallonta.
"Baby ruwa kike so?"
Ta jinjina kanta tana dafe shi, saboda ɗan banzan ciwon da yake mata. Shi dai Sa'ad juyawa ya yi ya fita daga ɗakin, a falo ya samu Adda, Muhibba da Aysher zaune, kowa a cikinsu hankalinsa a tashe yake.
"Ku je ku kwanta tun da ta wartsake"
Ya faɗa yana kallon Muhibba da Aysher.
"Ya Sa'ad..."
Wani kallo da ya yi wa Aysher yasa ta yi shiru, duk da yana sakar musu fuska su yi wasa idan ya zama serious su kansu tsoransa suke ji, dan halin Hammad ne ya fito fili, shi ma Sa'ad ɗin sai dai in ba a taɓa shi ba. Babu wadda ta sake musawa a cikinsu suka ta shi suka fita Muhibba na faɗin za ta tafi sashin Fulani Amarya wato Ammi ta kwana a can tare da Aysher.
Adda ta gane dalilin hakan, tsoro ne cike fal a zuciyar 'yar tata, ba ta so ta kwana a sashin saboda halin da Maryam ke ciki. Kuma ita ba za ta hanata tafiya can ɗin ba, dan tsakaninta da kishiyarta ne kawai suke kishinsu, shi ma ba wani sosai ba, amma tsakanin yaransu kansu a haɗe yake, Takawa ya yi iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya haɗa kansu duka. Kuma ya cimma nasarar hakan, ta wuri ɗaya ne kawai aka samu tangarɗa, wato tsakanin Hammad da Sa'ad duk da su ma har gobe yana so su shirya amma abin ya ci tura.
A hankali ya zauna a kan sofa yana shafa kansa, Adda kuma na kallon wani ɓangare na falon, Allah ne kaɗai ya san irin abin da take tunani a cikin zuciyarta a halin yanzu. Dole ta damu sosai, domin jinyar Maryam kullum gaba take ba ta baya, kullum da sabbin abubuwan da take zuwa da su, a baya sai dai ta yi ƙoƙarin guduwa ko ta faɗi tana koke-koke, amma yanzu abin ya yi ƙamari ta yanda har ta fara kaiwa duka, suna zaune a falon babu wanda ya yi magana har Galadima ya shigo, ya samu wuri ya zauna Adda na tambayarsa wa ya gaya masa abin da ke faruwa.
"Ni na ƙira shi ranki ya daɗe"
Cewar Sadiq da ya shigo kansa a ƙasa, Adda da Sa'ad suka bi shi da kallo har ya zo ya zauna a falon.
"... Bai jima da ƙirana ba yace zai zo gidana mu yi magana, sai na ce masa ya bari ni da kaina zan zo fada"
Cewar Galadima. Jin cewa magana za su yi yasa Adda ta tashi faga falon suna mata sai da safe.
"Ranka ya daɗe magana ce a kan ciwon nan na Maryam, a gaskiya na fara tunanin cewa wannan matsalar tata ba ta asibiti ba ce, abin ya fi kama da shafin aljannu ko kuma sihiri... Yanzu da kanta take gaya mini cewar tun da ta fara shan magungunan nan da aka rubuta mata su a asibiti jikinta ya ƙara rikicewa, dan haka a ganin zai fi kyau mu aje magungunan nan na asibiti, mu dage mata da addu'a da kuma naiman maganin gargajiya, wata ƙila Allah yasa a dace!"
"Ni kaina a yau na tabbatar da ba ciwon hauka Maryam ke fama da shi ba, sanda na kalli idanuwanta na ga wani abu kamar bijirewa, kamar duk abubuwan da take ba yin kanta ba ne, kamar kawai ana controling ɗinta ne ba tare da ikonta ba"
Cewar Sa'ad yana tuno abin da ya gani a cikin idanuwanta a ɗazu.
"To kafin dai mu kai ga yin komai dole sai mun sanar da Takawa, duk abin da yace shi za ayi kawai"
Faɗin Galadima.
"Na san insha Allah takawa ba zai ce a'a ba..."
Sadiq ya amsa.
"To Allah yasa" Duka suka amsa da Amin.
_____________
_Me?_
_To wai ni wannan Julianar ba ita ce yarinyar da Pedro ya ceceta shekarun da suka wuce ba?_
_To yanzu ya aka yi suke tare da Pedro a Sao Paulo ba a Lencois town ba?_
_Me ya faru da su har ya kaisu ga zuwa gidan marayu?_
_Ina iyayensu suke?_
#SalmaAhmadIsah
#MiniCandy
#Bahaɗejia
#ƘawaZuci