6
by @autarmanya
*SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*006*
Kallo ɗaya yayi mata yayi saurin kawar da kanshi, Gaba ɗaya shigar da take jikinta bata kamata ace ɗa namiji ya sameta a cikinta ba, Juya masa Baya tayi ta cigaba da danna wayarta bata jin zata masa magana idan zasu shekara a haka.
Shima daga ɓarin shi gefe ɗaya ya zubawa ido sabida Gudun kar Idanunshi su ƙara mugun gani, Sai dai daga cikin zuciyar shi tafasa take kamar zata tsaga masa ƙirji ta fito wannan wace irin Yarinya ce wadda bata da Kunya bata da Tarbiya ko kaɗan sam baiji sha'awar auren ta ya kawota gidan shiba, Inda yana da dama da ya warware maganar auren su saidai Iyayensu sun riga da sun yi Alƙawari babu yanda za'ai yayi silar Rusa wannan Alƙawarin.
A fusace ta yunƙura daga kwanciyar ta nufo ƙofa zata fita Jikinta sanye da Doguwar riga mai hannun shimi wadda tai matiƙar kama mata jikin nata surarta mai ɗaukar Hankali ta bayyana kanta babu ɗankwali Siririyar kalaban dake kanta duk ta Miƙe tsaye sabida ita bamai yawan gashin ka bace.
Ƙoƙari take ta raɓe shi sai dai hakan ba ze yuwu ba sabida Ya riga ya tokare ƙofar.
"Malam zan fita ka wani zo ka cika mana wuri sai kace gidanku"
Har ga Allah shi bema san ta ƙaraso ba hankalin shi ya tafi tunanin neman mafitar zamewa auren ta sai jin dirin muryarta yayi a gab dashi cike da rashin kunya.
Yana ɗago kanshi da nufin ya kalleta tana mai juyawa ita kuma da sauri wannan ruwan da Maimuna ta kawo mata ta ɗauko babu tunanin komai tayo kanshi da ruwan mai yawa a cup ga ɗan karen sanyi ta juye masa shi tas a jikinsa damma tsayinta bai kai ko kafaɗar shiba da tindaga saman kanshi zata zuba Ruwan.
Tsayawa yayi yana kallonta ruwan na ɗiga daga jikin rigar shi Adaah dariya ta sa tana Nuna shi da yatsa.
"In banda kai sakarai ne ta yaya zaka yarda da maganar aure na kalleni"
Ta faɗa tana juya jikinta sannan ta nuna shi.
"Kalleka dan Allah kayi kama da kalata jiba kayan jikinka wani ƙazami dakai wawa Mtsss"
Ta faɗa tana Ƙoƙarin Nufo shi.
Ƙura mata ido yayi wanda yayi jajir har wani ruwan bala'i ne ya kwanta Jijiyar dake kanshi ta Miƙe babu abin da jikin sa yake sai rawa yana mazari kamar wanda yasha maganin tauri Ƙafarsa ke takawa tana wa gangar Jikinsa linzamin Isa gabanta, wanda ita kuma Adaah keja da baya gaba ɗaya idanun shi ya tsoratata ga gida babu kowa yana binta tana yin baya tana yarfe hannu.
Cikin Hukuncin Allah sai da yakai ga sunje ƙarshen Falon ta raɓe da bango ta ɗora hannunta duka a fuskarta ta rufe gaba ɗaya yanayin sa ya firgitata sai tace ita bata taɓa ganin Namiji mai Irin suffar shiba Ingarman namiji ne kamar wanda yake cin ƙarfe.
Hucin Numfashin sa mai zafine ya daki fuskarta hannu yasa ya tokare bangon data raɓe ɗin wanda Sauran kaɗan fitsari ya biyo ta jikinta sabida kaɗuwa.
"Dani da ke waye sakarai?"
Ya nisa kafin ya cigaba.
"Sakarai shine mai cusa kanshi inda ba'a neman shi, tallanki aka min aka liƙamin ke yau ɗinnan sai da Ubanki ya biya gidanmu ya ƙara roƙata akan nazo wurin ki To bari Kiji bakya Birgeni baki min ba cutar dani akai da Biyayya zan karɓeki danni bana Bijirewa mahaifina Amman wallahi ban taɓa ganin halittar dana tsana na ƙyamata Lokaci ɗaya ba kamar ki, Kisa a ranki zanyi auren cikon Umarni ne dake ba domin soyayya ba ƙazama wadda bata san Ciwon kanta ba bata san martabar Jikinta ba shasha sha"
Ya faɗa tare da jan wani irin tsaki mai ƙarfi ya juya da sauri yabar falon
Da wani irin yanayi Adaah ta zame daga tsaye ta zauna ta ɗora hannu aka tana rusa Kuka.
Ba'a taɓa Yarfata kamar yanzu ba ya cuceta ya danƙara mata maganar data fi marin daya mata Jiya illah.
Tashi tayi tana watsi da kayan falon tana kuka tana ihu tana Jin dama Allah zai karɓi ranta kafin Lokacin auren su yayi.
Da sauri yake fita daga gidan Ko ina na jikinsa Rawa yake har Lokacin idanunshi a juye suke kamar ya sha ƙwaya Allah ne kaɗai ya kaishi Titi Lafiya ya tari abin hawa zuwa gida.
Ya ci alwashin Ba zai ƙara komawa wajanta ba, Kuma Yana fatan Allah yayi gaggawar Watsa lamarin auren su baitaɓa ganin Mace irin ta ba wai dame taƙe taƙama ne haka? Gumi ne ya cigaba da yanko masa ta ko ina Kirjinshi na masa zafi da taimakon Allah ya ƙarasa Gida yana shiga ya faɗa ɗakin shi ya rufe kanshi.
Babu abin da yake se mayar da Numfashin Bacin rai, a haka ya zauna har Lokacin magariba yayi lokacin yaji zuciyar shi tayi sanyi sai yayi alwala ya fita masallaci.
Tin suna tafiya mai daɗi har sai da Momi ta ƙosa ta dubi Lubna wadda take ta Hira da Drivern ta da alamun sun saba irin tafiyar.
"Waini Lubna ina zaki kaini ne har yanzu bamu ƙarasa ba duk sammakon da Mukayi"
Lubna tayi dariya tare da cewa.
"Cinikin kanki zanyi don Kin san Kanki zeyi kuɗi"
Dariya sukai Driver yana karkata kan motar suka nausa Cikin Jeji Momi ido kawai take zarewa Ko yaya Motar ta Bugu Momi seta hau salati Gaba ɗaya tsoro ya kamata haka sukaita tafiya har sanda suka shiga ƙauyen.
Tafiya kaɗan sukai suka ƙarasa Ƙofar Gidan Mai Rumfar Kwano mata ne zazzaune ga masu awara nan da masu wainar Gero ga masu Nama driver yayi parking Suka fito Ƙafafun Momi duk sun kumbura sabida zama Hajiya Lubna wajan mai nama taje ta siyo Musu Ita kuma Momi wajan zama ta samu don ta gaji sosai.
Bayan Lubnah ta miƙawa Driver Ƙullin Nashi ta iso wajan Momi suka fara ci batare da tunanin Yin sallah ba.
Seda akai la'asar layi yazo kansu Lubnah ta dakatar da Momi ta fara shiga sannan daga baya ta Kira Momi.
Babban mutum ne zaune akan farin Buzu ya sha manyan kaya ɗakin sa babu wata alama da zata Nuna wa Mutane yana Tsubbu Irin sune masu ci da Buguzun Suna tsubbu ta ƙarƙashin ƙasa a fili Kuma suna Nuna wa jama'a su Na Allah ne.
Seda ya cewa Lubna ta rufe ƙofa sannan ya janyo kwanon sha ya zuba ruwa ya ɗora hannu akai ya tura gaban Momi.
Zaro idanu Momi tayi tare da cewa.
"Ranka ya daɗe wannan Ƴata ce Adawiyyah da Mijina a cikin Ruwa"
Dariya yayi tare da shafe saman Ruwan Hoton su Adaah ya baje.
Kafin yace.
"Kinzo da Buƙata Biyu ta farko a Juya kan Mijinki akan auren Ƴarki Na biyu Kuma a raba shi da Ɗan uwan shi kwata kwata"
Momi ta Gyara zamanta sosai Cike da mamaki tace.
"Ƙwarai Ranka ya daɗe, Ƙawata ta jima tana gayan yadda ka shahara a fannin aiki amman naƙi zuwa sai yau Allah yayi, wallahi yayan Mijina ne ya sakoni a gaba na samu ada na rabasu da Kisisina, To yanzu kuma kwatsam suka Bullo da Maganar haɗin gida da ɗan shi da yarinyata Kuma wallahi ba dan Allah suka shirya hakan ba sedon kwaɗayi da son cin dukiyar Mijina"
Ɗaga mata hannu yayi tare da ƙara janyo kwanan sha ya Ɗora Hannu.
Akai ya kuma tura mata gabanta.
Zare ido tayi ganin Hoton Mahir Ɗan Hajiya Lubna na yawo akan Ruwan.
Ya kuma janye Ruwan ya maida kwanon sha ɗin yace.
"Waye kika gani a ruwan?"
Da sauri tace.
"Yaron wajan Hajiya Lubnah ne Mahir"
Yayi dariya sannan yace mata.
"Kinga wannan yaron shine mafitarki da ƴarki Sabida haka zan baki maganin da zaki zubawa Mijinki a ruwa in ya sha zai baku damar Fito da zaɓinku Ina so bada ɗaukar Lokaci ba Ki zaɓa mata wannan yaro domin Shi aljanu suka Nunan a matsayin Hasken Ƴarki"
Cike da ɗunbin mamaki Momi tace.
"Jiya ma sai da nayi maganar Mahir da Adaah take cewa ita Inda Abban ta ya bata zaɓi data Fito da wani saurayin ta shine nace mata Ga Mahir Nan Ɗan aminiyata ashe kaga na faɗa akan Gaɓa Ni wallahi da wancan auren ƙaddarar gwara Mahir Ɗari Bisa Ɗari"
Fuskar Hajiya Lubna ta Bayyana da tsantsar farin ciki bata zaci Komai zaizo da sauƙi haka ba.
Maganin daya bawa Momi Ta ɗauka ta bata tasa ajaka, Kuɗi masu kauri Momi ta Kuma dire masa ta fita tabar Lubna aciki domin suyi sallama.
Zuciya ɗaya Momi ta ƙarasa Mota.
Bayan fitar Momi Hajiya Lubnah ta Matsa gaban Malamin tare da cewa.
"Wallahi ban zaci abin zaizo da sauƙi ba, Ita ce ƙawar tawa dana so na kawo maka ita amman da yake tana da wata Irin Uwa Mai Kafiya ita ce ta hanata Bin malamai wanda Nina fahimci kamar mahaifiyar tata ta gano Wasu al'amurane ko zaka duban?"
Ya janyo ƙasa yayi abin da zaiyi sannan yace.
"Kawai macece mai ibada amman bayan nan babu komai, Kuma Ƙawar nan taki zata baki haɗin kai sosai akan haɗin auren ƴaƴanku sai dai banyi zaton wannan lamarin zai kunno ba da takan Mijin nata zamu fara bi, Sabida mutanan suna da ƙarfin Ibada aikin zaiyi wahalar shiga Jikinsu sai dai ita Yarinyar zamu tura mata nata aikin duk da tana da kafiya da taurin kai"
Hajiya lubna tace.
"Nima bata gaya min ba sai da taga abin yafi ƙarfinta kasan a hankali nake so mubi abin sabida bana son wata Ƙofa da zata nuna cewar da wata manufa Mahir zai Auri Ƴarta, Malam Mijinta Ƴarta kaɗai ya haifa kaga Idan ɗana ya auri yarinyar zamu sami dama sosai tinda Ni yanzu mai gidana ba kamar daba abin kawai fafa ce nake Musu dan bana son ƙawayena suga gazawa ta amman wallahi ranar da Maryam tace min Yayan Mijinta ya turo ɗansa Auren Ƴarta ban Rintsa ba Ni ina nan ina faman yadda zanyi na Ɓullo mata da Maganar su kuma suna can sun Min shigar sauri"
Dariya yayi tare da cewa.
"Aiko furucin data wa ƴarta na Auren ɗan naki aikin dana sa a gabane mai zafi ƙawarki ta fiki son duniya fa Lubna Amman zaku sami alheri sosai In Auren nan ya haɗu sabida naga dukiya sosai"
Shirya yadda zata kasance suka yi har ta Miƙe sukai sallama ta ɗauki Jakarta ta fita.
Jiki a sanyaye ta shiga motar Momi tai mata Murmushi.
"Wato Lubna naji daɗin maganganun Malam se naji kamar nayi tsuntsu naga wannan aure ya tabbata"
Lubnah tace "Kayya Maryam baki gani Mahaifin Mahir bai kai mahaifin Adaah ba?"
TsakiMomi tayi.
"Haba Lubna ta yaya zaki faɗi haka bayan Kuma kuna da shi daidai gwargwado ai dama ƙwarya tabi ƙwarya ne wallahi da Adaah ta auri wancan gwara Mahir ɗin sau dubu mayi tuwo na mai na nida ke"
A zuciyar Lubnah Murna take tana fatan haƙonta ya cimma ruwa batun yau take kwaɗayin ɗanta ya Auri Adaah ba sabida su Gaje arziƙin mahaifin Adaah ganinta ta Hanyar auren ne kaɗai zata Iya haɗa kafaɗa da Maryam wadda ta fita jin daɗi ta ko ina.
Momi keta jan Hajiya Lubna da Hira Amman ita Lubna gaba ɗaya bata tare da Nutsuwarta Idanunta ya rufe akan tunanin cikar Burinta tana Jin Kozata rasa Komi nata seta san yadda akai Mahir ya aure Adaah Domin da arziƙi a garin wasu gwara a nasu garin, Don ba tin yau Ni'imar Maryam take tsone mata idanu ba.
Basu ne suka shigo gari ba sai bayan Isha'i a ƙofar Gida suka sauke Momi wadda Hajiya Lubna take ƙara gargaɗinta akan tafa yi amfani da maganin nan kartayi wasa dashi.
Da shigar Momy Gida Room ta wuce tai wanka sannan ta zauna rama sallolin kanta babu tunanin komai ta kwanta a saman gado sai bacci.
Wajan taran dare wayarta dake yashe acan gefe ta soma ƙara ɗauka tai ganin Kiran Abbah Sama sama suka gaisa ya shiga tambayarta Abbakar yazo wajan Adaah rasa yadda zatai tayi seta Amsa masa da yazo kashe wayar yayi ita kuma ta Miƙe da hanzari ta nufi ɗakin Adaah sabida gajiya bata barta taga halin da ƴar tata ta wuni ba.........................
Bayan idar da sallar Isha'i Jidda ta fito daga cikin Gidansu Hannunta ɗauke da Jug wanda ta ciko shi da Kunun aya Shi take son kaiwa sabida yau azumi tayi bata gama abincin dare ba.
Tana Ƙoƙarin saka ƙafa a soron Gidan shima yana Ƙoƙarin Shiga Yana kallonta ya ƙaraso Ita kuma ta dakata tana Juya masa Baya........SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa ***, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.