JARABTAR SO

5

by @muslimerhabba

Soyayya ce mai girma da ƙayatarwa ke wanzuwa tsakanin Sadiq da Arfa, their relationship blossomed, and ko wace rana shaƙuwa ce ke qara wanzuwa a tsakaninsu. Kowa na gidan, hatta Ya Umar na jin daɗin yanda kullum Arfa ke rayuwa cikin farin ciki da soyayya banda Abba da Ya Khaleel. Sosai Khaleel ke ji a ransa yana tsoron lamarin, unlike Ammi da yake ganin a yanzu ba ta jin wata fargaba game da yaron, wanda a baya shi ke rarrashinta.

Sosai yanzu take yabon yaron, tare da nuna cewa yana da respectful nature. Kusan ko yaushe suka zauna da Abba yai ƙorafi game da yaron, Ammi sai tayi ta praising Sadiq's kindness and generosity. Ko zama sukai da Arfa sai ta riƙa cewa "Arfa, Allah ya ba ki soyayya da rahama, Allah ya dawwamar da farin ciki a rayuwarki Mimi na" while deaf cikin ranta abinda kowa bai sani ba, wani irin tsoro take ji da fargaba na dirar mata, duk da tana alaƙanta hakan da sharrin shaiɗan, dan ita har iya ganinta ba taga wata makusa ba a ɗabi'un yaron kaman yanda Abba ke faɗa, ta dai fi yarda da cewa Abban na ƙin yaronne sabida wani dalili nasa.

Watarana Sadiq yazo bayan sun yi waya da Arfa, kan cewa zai zo ya ɗauki meener su je yawo, inda Ammi ta tafka kuskure shine barinsa ya fita da Meener ba tare da sanin Abba ba.

Ba ƙaramin hasala Abba yayi ba, kuma sosai ya gargadi Ammi. "Ke wani lokacin ba ki da hankali wallahi Hajara, ban sakarci da wauta yaushe kika san yaron da har zaki damƙa masa yarinya ya fita da ita. Daga yau ma kar ya kuskura ya ƙara shigo min gida, ai ba gidan ubansa bane ba, kuma 'ya tawa ce ni ba zan bashi aurenta ba, dan ina da tabbacin ba dan Allah yake son ta ba.

Kuma billahil Azim duk wanda ya kuskura ya sake karya min doka zai ga mummunan ɓacin raina. Sannan na baki nan da minti talatin duk inda Meener take a dawomin da ita cikin gidannan, tunda kin nuna kema tunaninki irin na yaran ne".

Har ya juya zai fita ya dawo a zafafe yace "Ina ita Maryam ɗin take?"

Arfa da ke rakaɓe a gefen step ta ƙaraso jiki na rawa gaban Abban tace "gani Abba". Ita kanta se yanzu take jin cewa bai dace Sadiq ya fita da Meener ba, gashi har yanzu shuru ta kuma kira wayarsa ta ƙi shiga.

Abba yana kallonta da rinannun idanunsa yace "look Maryam" Saida gabanta ya faɗi dan rabon a ya kirata da aininihin sunanta ta manta, indai ba Arfa ba to sai dai yace Mimi, kanta a ƙasa ta kasa ko ɗagowa ta kalle shi fatanta Allah yasa dai ba wani mummunan abinne ya sami Sadiq ɗin da Meenan ba. Abba ya katse mata tunani ta hanyar faɗin, "Na ɗauka kina da hankali, na ɗauka iliminki zai baki damar gane cewa iyaye basa taɓa kin farin cikin 'ya'yansu, ce miki fa nayi ki bani lokaci na gama bincike akan yaronnan, bance miki bana sonsa ba kai tsaya sabida na san za kiji babu daɗi. Kuma kamar yanda nace ɗin haka nake bincike akansa babu dare babu rana.

Yanzu kin ɗauki ƙaramar yarinya kun bashi ya fita da ita, duk da babu mai babban laifi irin uwarku, ita da ta nuna taurin kai da rashin bin umarnin miji, toh a taƙaice dai yanzu nake samin labarin har 'yandaba yaronnan yake bi".

Zumbur Ammi ta miƙe sa'in da Arfa ta zaro ido tana kallon Abba, tana mamakin anya kuwa ya san abinda yake faɗa kuwa.

Tayi saurin katse shi ta hanyar fadin "Abba wallahi ko qur'ani zan dafa sharri ake yiwa Sadiq, kawai dai an ci Sa'a kaje bincikensa wajen maƙiyansa, amma duk inda mutumin kirki yakai Sadiq yaje wallahi yanzu ma na san wani akasin aka samu.

Abba ya ja tsakin takaici. "Mtsssssss, cike da takaici ya sa kai ya fice, wannan wace irin masifa ce ya ma rasa me ke damin Arfa haka.

Arfa ta kalli Ammi murya na rawa tace "Ammi wallahi ba gaskiya aka faɗawa Abba ba, babu yanda za'ai Sadiq yayi wata alaƙa da 'yan daba.

Sai kuma ta miƙe tana hawaye tace "Ammi bara naje shagon su na tambaya ko wani yasan inda suke ko ya ji labari, Innalillahi Meener ki yafe mini"

Ammi na shirin bata amsa suka ji an turo ƙofa, Meener ce da gudu hannayenta niƙi niƙi da ledoji cike da farin ciki ta faɗo parlon, da gudu Arfa ta rungume ta sa'in da Ammi ke sauke a ajiyar zuciya.

Suna cikin yiwa Meena tambayoyi Umar ya shigo parlon.

"Ammi, me Yaronnan Sadiq yayi Abba ya sa a kama shi, naji yana waya a compound kamin nashigo nan...  Me ya sa Abba ya tsani yaronnan ne, ita wadda yake yi dan itan wallahi idan ba mai mugun sonta ta samu ba wahala za ta sha, dan rawar kanta tayi yawa, ko ni ba ni da lokacin nuna wa wata soyayya haka.

Ta can ɓangaren kuma Abba da Khaleel sun zama skeptical akan intentions ɗin Sadiq. Sosai suke tattauna some worried glances, sosai Abba yaiwa Khaleel bayanin tarihin alaƙarsa da mahaifiyar Sadiq, da irin rashin kunyar da Sadiq ɗin ya keta masa kwanakin baya, wanda hakan yasa yake tsoron makircin da zai iya shukawa a cikin ahalinsa, a cikin gurɓataccen tunaninsa na ɗaukan fansa.

Ƙarshe dai sai da Sadiq ya kwana a station sannan Abba ya haƙura aka sake shi, wanda kamin nan ya sha magiya wajen Arfa da Ammi, dan Arfa dawowa tayi kamar wata zautacciya bayan da ta ji labarin Abba ya sa an kama Sadiq, ta sa Ammi a gaba ta riƙa yi mata kuka da sambatu.

"Me yasa Abba zai yi haka, danne haƙƙin wanda bai ji ba bai gani ba fa kenan Ammi, kawai sabida ya ji baya sonsa? To me ya tare masa? Mene laifin sa dan yace yana son 'yarsa, Ammi ko dai aurenne Abba baya so nayi ne? Ni indai hakanne ya sa a saki Sadiq wallahi ni na haƙura da auren" ta qarashe tana komawa jikin Ammi tare da fashewa da kuka.

Duk abinda Arfa ke faɗa sarai Abba ya ji komi, shigowarsa kenan ya ji sanda Ammi ke yi mata nasiha, wanda shi ya shigo ne da zummar suyi magana da Ammin yayi mata bayani ko zata fahimce shi, gabaɗaya sai jikinsa yayi sanyi da kalaman Arfan, cike da ƙarfin hali ya ƙarasa ɗakin.

"Salamu Alaikum" Abba yai Sallama. Ammi ce kawai ta amsa Arfa kuwa tayi kamar bacci take yi, dan sosai shigowar Abba ta ƙara mata jin wani irin zafi da nauyi a cikin ƙirjinta.

"Nasan idanunki biyu Mimi, kaf naji bayanin da kikewa Hajara, amma ina so ki sani, duk abinda nake yi dan ke nake yi, me yasa zan kinwanda kike so haka nan, kawai dai ke so ya rufe miki idanune, kuma dan ina sonki ko dan ina so kiyi aure hakan ba zai sa na barki ki kai kanki inda zaki cutu ba".

Sai da ya ja ajiyar zuciya sannan yace " Zancen yaro dai yanzu zan sa a sake shi, amma ina nan akan baka na babu aure ko soyayya a tsakaninku, dan bincike na kaf ya nuna yaron bashi da halin kirki"

Sosai Arfa ta sake fashewa da kuka, cikin shashsheƙar kukan ta kalli Abba da kumburarrun idanunta waɗanda saida suka sa Abba ya razana da ganin yanayinsu.

"Indai Sadiq zai huta na haƙura da auten Abba, indai za ka sa a sake shi ni na sadaukar da soyayyar da nake masa" tana gama faɗa ta koma jikin Ammi tana cigaba da kukan tamkar zata shiɗe.....



As tensions simmered beneath the surface, Sadiq and Arfa's love continued to flourish. But for how long would their happiness last, and what secrets lay hidden, waiting to disrupt their blissful relationship?