BAYA DA ƘURA

Trailer!

by @nanahaleema11

*BAYA DA ƘURA.*

Fitattubiyar2025

      

 Trailer!!!



      ........A yadda ya shigo falon zai tabbatar maka da ransa a ɓace yake, cikin fuskar sa da bata da alamun walwala a ko yaushe dan kana kallon sa zaka fassara shi a mutum mara fara'a, kuma baza'a rasa faɗa a wajan sa ba. 


Kyakykyawa ne mai duhun fata da madaidaicin jikin, yana da ido da dogon hanci siriri, fuskar sa ɗauke da zagayayyen gashin da ya kewaya ko ina. Ya kalle ta tana zaune kafin yayi magana cikin fusata tace, "wai kai waye gaba tsakani na dakai ne? Yayar ka ma Farida gaba nake da ita balle kai da zaka dinga min shishshigi a cikin lamarin rayuwata, ina ruwan ka da abinda na zaɓarwa kaina, har nawa aka ke da zaka dinga nuna min daidai da ba daidai ba?."


Wanda take yiwa maganar yana tsaye yana jin ta ya kalle ta yace, "ba yaya ta ba, ko kece kika haife ni baki isa kina yi abu ba daidai ba na zuba miki idanu ina kallon ki. Yasan yana son ki meyasa ya rabu da ke? Ya san zai dinga bibiyar ki har ki dinga shiga motar sa meyasa ya miki sakin da bazai iya mayar dake na?."

"Ina ruwan ka dani?, haka na zaɓa baka isa ka hana ni ba wallahi."

"Ai kuwa zaki ja masa, na rantse da Allah na sake ganin sa ƙofar gidan nan sai na saka n kulle shi ya kwana biyu a cell, in kina musu ki sake gayyato shi kiga nida ke waye zaiyi nasara."


Anty Maryam ta harzuƙa matuƙa kamar zata kifa masa mari tace, "baka isa ba walalhi, ƙarya ka ke Bebi baka isa ka hana ni abinda nayi niya a cikin gidan nan ba, gidan ubana ne kamar yadda yake gida uban ka, ina da iko kana da iko, baka iya ka hana ni abinda nake so ba. In kana hana ƙanen ka ni Yayar kace." Ganin Mamt tazo wajan sai baice komai ba ya juya ya fita ransa a ɓace sosai.


Yana fita ta kalli Mamy tace, "yaron nan yana neman raina min hankali, Mamg kiyi mana tsakani dashi, ni yayar sace babu ruwan sa da abinda zanyi."


Mamy ta kalle ta tace, "Gaskiya yake fad'a miki ai, kishin ki yake matsayin ki na yayar sa shiyasa yake tsaye akan lamarin ki. Ke kuma banza shashasha mara kamun kai miji ya sake ki amma ya dinga bibiyar ki kina masa dariya saboda baki san abinda yake miki ciwo ba. Ya san hana son ki ya miki saki har uku?."



Yana zaune yana cigaba da duba takardun hannun sa yaga wayar sa na haske ganin sunan Abba ya saka shi kulle ido ya buɗe ya ɗauka da sallama yayi shiru alamun ana amsawa kafin ya tashi ya fita waje. Kai tsaye ɓangaren Abba ya nufa ya same shi a zaune a kan kujera ya shiga da sallama ya amsa ya ƙarasa ya zauna a kasa yace, "barka da dawowa Abba, ina fatan an dawo Lafiya."

"Lafiya lau Adna, ya aikin naka?."

"Alhamdulillah" ya amsa a takaice daga nan bai sake cewa komai ba.


Abba yace, "sai haƙuri aiki ne suke min yawa ga shirye-shiryen zaɓe mai zuwa shiyasa abubuwan sai a hankali." Adnan yace, "amma Abba duk mahimmacin abinda ka saka a gaba bai kai mahimmacin iyalan ka ba."

"To iyalai na me suka rasa Adnan? Babu abinda babu a gidan nan koda babu ni na tabbata baza ka bar wani yayi kukan babu ba. Yadda kake kula da iyayen ka da y'an uwan ka ko ni bana kula dasu, indai kana da rai ragamar gıdana tana hannun ka dan na yi shekara bana gida bazan damu ba."


Adnan ya kalle shi dan daman shi ne kawai mai iya faɗa masa gaskiya yace, "Amma Abba ko mu yaran ka babu haƙƙin mu a kan ka akwai iyayen mu mata, dukkanin suna buƙatar kulawar ka wacce a wajan ka kawai zasu samu, ni da ka bar min komai a hannuna bazan iya samar musu da kulawar da zasu samu a wajan ka ba. Idan zan iya kula da y'an uwana su kuma fa Abba?." Alhaji Mu'azzam Alhassan Tofa ya kulle ido ya buɗe yace, "Haba Adnan! Iyayen naka bafa yara bane da kake wannan zancen a kansu, dukkan su babu wacce bata aurar da yara a cikin su ba har da jikoki, to me suke nema a wajena kuma?."


"Kulawar ka suke so Abba domin matan ka ne, na tabbatar ka san suna buƙatar hakan." Yayi murmushi yace, "gashi ai na dawo, zan kuma yi sati a nan duk kulawar da suke so zasu iya samu a cikin kwanakin da zanyi." Kallon sa Adnan yake yi zuciyar sa gabaɗaya babu daɗi yaja bakin sa yayi shiru bai ce komai ba kafin Abba yayi magana Mamy da Mama suka shigo da sallama ya amsa sai Adnan ya miƙe yace, "Abba sai da safe."


"Allah ya tashe mu Lafiya, da safe kafin ka fita kazo nan Ina son ganin ka, koda ina bacci ka jira ni. Maganar da na kira ka muyi bamu samu ba zamu yi daga baya." Ya amsa da to ya fita. Kallon Mamy da Mama yayi da suke zaune ko wacce fuskar sa babu yabo babu fallasa yace, "ko wacce ta shigo tana shan kunu kamar wanda aka yiwa dole."


Mama tayi murmushi kawai bata ce komai ba ta miƙe tace, "barka da zuwa muka zo muyi maka daman, da fatan an dawo Lafiya." Yabi Mama da kallo ita kuma ba shi take kallo ba yace, "Sannu da zuwan ce sai an tashi tsaye?."

Mama tace, "Ina sauri ne zan je na kwanta, sai da safe" ta fad'a tana hanyar fita Mamy ma ta miƙe tace, "jira mu koma yadda kuka shigo tare" ta fad'a tana tashi tsaye itama.


Mama ta kalle ta tace, "baza ki zauna a nan ba?."

"Lissafina ya kwnace bazan iya banbance wacece ma ya kamata ace ta kwana a nan ɗin ba, ga dai abinci nan Maryam zata kawo yanzu" ta fad'a tana fita ta bar Mama a tsaye dan har ta riga taficewa. Mama na shirin fita tace, "kar ki fita Saddika, dawo ki zauna muyi magana." Ta juyo ta kalle shi tace, "ko meye ma tattauna da safe in Allah ya nuna mana, ka kwana Lafiya" ta faɗa tana fita ya bita da kallo yana murmushi.


Shi kam mamaki matan nan masa suke bashi ko wacce ta girma a cikin su amma basu daina mararin neman wani abuna wajan ba ba, shi ɗauka yake gabaɗaya ma an ɗauke musu wata sha'awar sa tunda ko wacce har jikoki tana dasu. Har gwara ma Mama tafi Mamy ƙarancin shekaru amma mamy tafi Maman nunawa. Shafa fuskar sa yayi dan shi kam yana da ɗanye jini a waje bai ga abinda zai nema a wajan wannan tsofaffin matan nasa ba, shiyasa ko a jikin sa in suna wannan abubuwan, duk waccs ta kawo kanta ita ta sani, ni ban damu ba.


*********


Sake kallon kanta take yi kafin tace, "Allah bai yi za'a haife ni a irin wannan gidan ba, da a wannan gidan nake ai sai nafi haka kyaun gani, da wannan gidan na dace ba waccan ba."


Bily ta katse kiran tace, "ke kullum kika zo gidan nan sai kin maimaita maganar nan, dallah ki shiga kiyi wanka mu wuce bana son ɓata lokaco." Bata ce komai ba ta shiga banɗakim tayi wanka ta fito ta zauna tana shafa mai Bily ta kalle ta tace, "Gaskiya Mubeena dole ki dinga baƙin cikin haihuwar ki da aka yi a gidan ku, ke kin ganki kuwa?, kina da kyau sosai, kawai farin Manal da yake mai haske ne yafi burge ni, dan kin ga ita babu masu wannan hasken da yawa a cikin nigeria. Ke kuwa haske dai wanda kowa ya sani ki ke dashi, amma kina da kyau."


 Mubeena tace, "bari kawai, bayan talauci ma ga uwa makauniya, ga mai riƙon namu ma talaka, ga ƙanwa soloɓiyo babu abinda ta iya kulluɓ cikin kiyi haƙuri da duniya take faɗa min. Shiyasa ko a school ban taɓa bari na nuna ta matsayin ƙanwa balle kuma na nuna babar ta mu balle kuma gidan namu gabɗaya." Dariya Bily tayi tace, "Shege talauci. Amma bai kamata ki cewa Mama haka ba, kuma a ko ina zaki iya nuna Mama saboda ta fi ki kyau. Kawai dai da ace ke ƴar Alhaji ce da an gama magana." Itama dariyar tayi tace, "Ina jin daɗin haɗuwat mu dake, ke kan ki farkon haɗuwar mu kin ɗauka irin wata shegiyar nan ce ni baki san ganye na baro su suna ci ba."


A tare suka sake yin dariya Bily tace, "Wallahi baki da kirki, ke baki bar kowa ba har Mama." Mubeena ta tashi ta buɗe kayan Bily ta ɗauki kayan da take so ta saka ta tsaya tana kallon kanta a mudubi dan ita kanta tasan tayi kyau ba kaɗan ba. Bily ta bita da kallo tace, "Gab nake da daina baki kayana domin in kika saka sai naga sun fi miki kyau a kaina."

Dariya Mubeena tayi ta shirya tsaf tayi kyau sosai suka dauƙi jaka suka fita ko mummy basu yiwa sallama ba dan su ƴan boko ne babu ruwan su basa tauyewa Bily hakkin ta Bily taja mota suka fita daga gidan.


*******


Tsitt yayi ya sunkuyar da kai ƙasa Mama tace, "ni zaka dinga kallon ido kana cewa baka son jinin ƴar uwata wacce muke uwa ɗaya uba ɗaya Adnan?, ni ka ke kallo kana ce min baka son yarinyar da na raina a cikin gidan nan?, ashe ko da gaske baka son nata baza ka iya yi kin kara ba taci albarkacina ka aure ta?. Inda ina da wani ɗa namijin ba kai ba zan saurare ka ne Adnan?. Kai kasan bazan bi ta kanta ba, dan kai duk yadda mutum ya kai ga yi maka abin kirki baka gani."


"Ku ka haɗa kai da ƴan uwan ka aje a samu mahaifiyata akace wai baka son Rumana na tilasta maka sai ka aure ta kai kuma baka so, sannan wai ita lokacin da tace bata son ka an ƙyale ta amma kai yanzu an kasa ƙyale ka. Ashe zaman namu da rashin darajar da bani da ita a wajan kahar ya kai haka Bebi?." 


"Ki yi haƙuri" ya furta a hankali zuciyar sa tayi rauni sosai. tayi tsaki tana girgiza kai tace, "haƙuri ai ya zaunar min dole saboda ka haɗa ni da wacce ta isa dani, Tunda ni ina jin maganar ta dole nayi abinda tace. Kai da baka jin tawa ai tsallake abinda nake so kayi ka kai ƙarata wajan uwata. Kaga nima da bana jin maganar ta irin ka da baka jin ta uwar ka sai naje na samu na sama da ita na faɗa masa shima yaje ya mata magana."


Shi wallahi gabaɗaya ma komai ya fita daga ransa jin Mama na faɗa tana cewa bata isa dashi ba duk sai yaji nadamar abinda yayi ga dabaibaiye shi, ji yake ina ma bai kai kansa wajan Manal ba, ina ma ya tsaya akan Rumana ɗin kamar yadda Mama take so?. nan take yaji zai iya auren Rumana duk da baya so.


"Hajiya tace kar na sake maka maganar auren Rumana na barka ka auri wacce ka ke so kamar yadda aka bata dama, zanyi hakan saboda bin umarnin wacce ta haife ni. Sannan zan baka umarni a matsayina na mahaifiyar ka nima, in zaka bi kanka in baka bi bana kan ka, sai kaje ka zauna da wacce ka ke so ɗin tunda ka zaɓ soyayyar ta akan farin ciki na." Da sauri yace, "kiyi haƙuri Mummy, ki yafe min don Allah, ko me kike so zanyi."


"Baka da adalci wallahi, ka san irin kukan da Rumana tayi da maganar nan taje kunnen ta? Kaga yadda ta shiga tashin hankali saboda kai?. Duk wannan bai nuna maka tayi nadamar auren wani da tayi ba kai baBebi? Kai kaɗai ake yiwa laifi ne a duniya? Meyasa baza ka haƙura ba?, meyasa baza ka yi tunanin daman Allah yayi sai ta auri Jawad ba kafin kai? Baka san ƙaddara ba?."


Yayi shiru bai amsa ba dan Mama tayi zafi sosai shirun yafi alkhairi ta sake cewa, "tunda haka ka zaɓa na amince ka auri wacce ka ke so kamar yadda uwata tace, tace na saka maka albarka a auren jaka zan kuma yi hakan. Amma ina so ka sani sai dai ka auri mata biyu a rana ɗaya." 


Da sauri ya kalli Maman suka haɗa ido ya sake sauke kai ƙasa tace, "in kuma ba haka ba, naji ka fara auren wacce kake so ɗin tunda umarnin Hajiya ne, amma ina so ka sani shekara ɗaya na baka kai da ita ku gama zaman ku, da zarar ranar da aka ɗaura auren ku ya dawo anyi shekara ɗaya a wannan ranar Rumana zata shigo gidan matsayin amaryar ka. Ko ka yarda, kokar ka yarda haka za'ayi, in ba haka ba kaje ka auri wacce kake so ba da albarka ta ba, sannan bazan taɓa kaɓar ta matsayin sirikata ba."


Da sauri ya kalle ta yace, "na amince Mummy, Allah ya wuce zuciyar ki, ki yafe min ɓata miki ran da nayi. Na amince da hakan Alalh ya nuna mana lokacin, Allah ya sa muna da rai da lafiya."


"Kar ma ka amince mana Adnan, kar ka amince ka nuna min budurwar ka ta fi ni."

"Har abada, ki yi haƙuri, ki yafe min tuba nake." Ta harare shi cikin ɓacin rai tace, "Tashi ka bani waje." 


Ya miƙe a sanyaye yana sake bata haƙuri zai fita tace, "Daga yau duk wani shiri da zaka fara na aure ka dinga yin guda biyu, in lefe ne ka siyi na mata biyu, in ma ginin gidan naka ne ka saka a rushe ya dawo baya ayi ginin mata biyu, in baka da ra'ayin hakan ka tabbatar kana gina inda Rumana zata zauna. In kana ganin hakan bai maka ba Hajiya tana raye."


Juyowa yayi ya duƙa yace, "hakan za'a yi in sha Allah. Ki yi haƙuri."


*********


Jikin ta rawa yake sosai, hankalin ta ya kai ƙarshe wajan tashi kallon hotun take yi cikin kiɗima da nadama mara amfani. yana kira hannu na rawa ta ɗauka daga can ɓangaren yace, "har ni ina miki waya ki daina ɗauka? Na baki haƙuri meyasa baza ki haƙura ba Maryam?." Maryam tace, "Kamal kace min ka goge hotunan nan."


"Akan me za'a goge bayan gashi yayi min amfani yanzu?."

"Kamal ya kamata ace ka goge shi saboda ni ba matar ka bace ba. Barin tsairicina a wayar ka haram ne."

"Zan goge, amma Ina so ki fito anjima ina so mu yi magana."

"Bazan sake zuwa inda kake ba, na daina zuwa inda ka ke, baza ka kuma ganina ba ko me zai faru." Yayi dariya yace, "Maryam kenan, kina so kice kin daina ganina?."

"Na daina ganin ka, na kuma daina zuwa inda ka ke, kuma ka fita daga rayuwata."


"Ni kuma wallahi yanzu na fara jin daɗin rayuwa dake, a baya ji nake kamar ma ban taɓa wata mu'amala dake ba kamar yadda ya faru yanzu. Maryam ki fito mu haɗu yanzu in ba haka ba wallahil azim zan ɗora hoton nan na ki a Facebook da tiktok." Gaban ta ya faɗi matuƙa murya a sarƙe tace, "me ka ce?." Yayi dariya yace, "ai kin ji abinda nace, ko ban saka hoton fuskar ki ba zan saka na jikin ki, ke kina gani kin san jikin ki ne. Kuma zai zaga ko Ina babu inda bazai je ba ke kin san yadda hoton tsaraici yake zaga ko ina, Balle ma da fuskar ki zan ɗora dan babu amfanin kullewa."


Kasa magana tayi shiru hankalin ta ya tashi sosai ta rasa ma abinda zata ce, gaban ta faɗuwa yake yi nadama ta mamaye ta lokaci ɗaya har zazzaɓi take ji, yace, "in kin shirya ganin hoton ki a social media kar ki fito Maryam, in kuma baki shirya ba zan miki text na inda zamu haɗu ki tabbatar kin je wajan. in ba haka ba wallahi sai na watsa hoton nan media, ke kin san ba iya hoto nake dasu ba har videos ina dasu. Videos ɗin ma sun fi komai kyaun gani, saboda....." sai kuma yayi dariya yace, "Na san ma kin sani, Sai na jiki" yana faɗa ya katse wayar. Faɗuwa tayi a wajan jagwab hankalin ta ya kai maatuƙa wajan tashi, me hakan yake nufi...? kenan blackmailing ɗin ta Kamal yake da hotunan tsaraicin ta wanda take tura masa a zaman auren su ko kuma me? Yanzu ya zata yi? Dama zata ɗauka ko haggu?.


********


Numfashi ta sauke tace, "ni bawai bana so ba ko ban yarda da kai ba, kawai tsoro nake ji ne wallahi. Na faɗa maka ko riƙe hannuna wani bai taɓa yi ba, dole na ji tsoro." Mujahid da yake kan wayar yace, "Sweetheart mafita nake neman mana fa, bawai ina hakan saboda jin daɗi na ko wani abun ba, mafita nake so mu samu mu yi maganin damuwar mu. Kina sona Ina son ki, aure muke burin yi Yayan ki ya hana faruwar haka, shine nake nemar mana hanyar da za'a samu masalaha cikin sauƙi. Kar ki saka a zuciyar ki kamar abinda nazo nema kenan a wajan ki, ko kusa ba haka bane ba Lubna, neman mafita ce babu yadda zan yi hakan shine kawai zai faru a aura min ke ko da Adnan baya so." 


Lubna tace, "Na sani Sweetheart, amma.....!" Katse ta yayi yace, "Lubna don Allah in zuciyar ki na rawa a kan maganar nan a barta kawai, kar ki yi tunanin zan karɓi virginity ɗin ki ne saboda haka nake so a zuciyata. Wallahi sam-sam ba haka bane ba my love, in a son raina ne sai bayan mun yi aure na mallake ki kin mallake ni, hakan shine burin na ba abinda yake zuciyar ki ba. Allah ya sani so nake na mallake ki a matsayin matata, duk wannan faɗi tashin da nake yi saboda ke ne, don girman Allah in kina ganin kamar wayo nake miki don na mallaki jikin ki daga baya na guje abar zancen nan kawai. Kin san ni ba mutumin banza bane, har yanzu ban taɓa riƙe ko da hannun ki ba, in da ace da wannan manufar a zuciyata da yanzu kin fahimce ni."


Lubna tace, "bawai ban amince da kai bane ba fa, na amince kawai tsoro nake ji ne wallahi. Ban taɓa aikata hakan ba kai ma ka sank, zuciyata rawa take sosai, shiyasa kaga kamar Ina kokwanto a kan ka amma bawai don ban ban amince da kai bane. Na amince da kai ɗari bisa ɗari, in ba dan kai ɗin ba bazan iya yin maganar da kowa ba."


"Tsoron me kike ji? Tsoron kar nayi amfani dake nan gaba na gudu na barki...?. Hmmm! In da wannan niyar nazo gare ki da zuwa yanzu kin fahimta Lubna, ban zo wajan ki da niyar lalata miki rayuwa ba, nazo da niyar auren ki amma Yayan ki ya hana faruwar hakan.Ban san me na yiwa Bebi ba, ban san meyasa baya sona, ban san meyasa yake son hana ni ke ba. A ganina duk laifin da nayi masa tunda har yanzu nazo nace neman aure nake bai kamata ace ya hana ni ba, saboda aure sunan sa aure, Kuma raha sunnar annabin mu nake so nayi. Ban san me nayi masa ba wallahi, a bayana saurayin Mimi yazo yanzu gashi an saka ranar auren ta."


*******


"Mama me yake faruwa ki sanar dani don Allah, kin saka zuciyar mu a ruɗani mun kasa gane inda kika nufa. Mama meyasa ki ka ce mu taho gida? Meyasa kika ce bakya so Dr ya kawo mu a motar sa?, Mama meyasa kika ce zaman aurena dashi ya ƙare?."


Mama ta kalle ta cikin ganin da bai wadace ta ba sosai tace, "Manal na taɓa miki abinda zai cutar dake ne?." Manal ta girgiza kai tace, "a'a Mama, amma Ina so na sani, Meyasa kika canja tunda ki ka ga mahaifin sa?." Mama ta ja dogon tsaki ta dafe kai tace, "Dole ki bar aure Adnan koda bakya so, dole ya sake ki ko yana so ko baya so, zaman aure tsakanin ku bazai taɓa yuwa ba." Manal kanta ya sake kullewa kamar zata yi kuka tace, "saboda me Mama?."

"Saboda wanda aka nuna min shi matsayin uban sa kema uban ki ne Manal!."


Manal ta tsorata sosai ta kalli Mubeena da take tsaye a gefe itama cikin tashin hankali ta sake kallon Mama tace, "Mama kin saka mu a ruɗani, ki cire mu daga cikin tashin hankalin don Allah." Mama ta kulle ido ta buɗe tace, "baza ki taɓa fita ba Manal, baza ki fita daga cikin ruɗanin da kike a yanzu ba, ba gwara ki yi ƙoƙarin daidai ta hankalin ki."


Mubeena tace, "Kenan Mama mahaifin Adnan mijin Manal shine mahaifin mu ko me kike nufi? Bamu gane ba ki ganar damu don Allah."


"In zuciyar ku haka ta ɗauka ki ɗauka haka ne, in zuciyar ku ba haka ta ɗauka ba ku ɗauka ba haka bane. Abu ɗaya na sani kawai, auren Adnan da Manal tamkar rubutu ne a kan ruwa."

"Mama don Allah ki fahimtar damu" Mubeena ta faɗa cikin nata tashin hankalin.


Mama ta daka mata tsawa tace, "baza ku fahimta ba, na faɗa muku baza ku gane ba meyasa kuka cika naci ne? A bar maganar a wajan nan bana so a sake tayar da ita." ta kalli Manal tace, "ki rubuta a zuciyar ki babu ke babu Adnan" tana gama faɗar hakan ta bar tsakar gidan duk suna tsaye ko wacce da kalar nata ruɗanin.



********


Tashi yayi a sanyaye ya fita ya daga falon dan zama a ciki zai iya saka shi hauka na wucin gadi, mota ya shiga ya fita daga gidan a guje. Sai da yayi nisa ya tsaya a kan hanya ya kifa kansa a kan sitiyarin motar cikin tashin hankali da tsoro mai yawa. Zuciyar sa bugawa take yi sosai ji yake kamar yayi hauka, tunanin sa yana ga abinda Abba ya faɗa masa, da gaske dai matar Manal ƙanwar sa ce ta jini ko wasa ake masa?, in hakan ya tabbata ya zai yi? In hakan ya tabbata me zai faru wanne hali zai shiga? In hakan ya faru ya zai yi da ransa?. Allah ya sani yana matuƙar qaunar Manal, yana kallon ta matsayin abokiyar rayuwar sa kuma bugun zuciyar sa, kallon matar sa ma'ajin sirrin sa yake mata, kallon Manal yake matsayin uwar yaron sa da yake cikin ta. Taya rana tsaka ake so a juya ta ta koma ƙanwar sa wacce suke uba ɗaya?, in hakan ya faru da wanne ido zai iya kallon ta matsayin ƙanwar sa da suke jini ɗaya? Ya matsayin ɗansa da yake cikin ta? Ɗan sa ne ko ƙanin sa?.


"In sha Allah hakan bazai faru ba, bazai tabbata ba in sha Allah!" Ya faɗa a bayyane yana sauke numfashin wahala, a wahale maganar take fita saboda nauyin da zuciyar sa tayi masa.


BAYA DA ƘURA! On first January 2025.


#Coming soon!

#New year

#2025

#Nana haleema

#Fittatubiyar

#***

0#701 809 8175

#Arewabooks