11
by @autarmanya
*SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*11*
A lokacin da take zama a saman kujerar, lokacin yayi daidai da sanda gabanta yayi mugun faɗuwa hannu ta ɗora a ƙirjinta wanda ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi a hankali ta lumshe idanunta ta buɗa akan shi wanda shi sai murmushi yake yi mata tsintar kanta tayi itama da sakar masa murmushin tana jin wani abu na fusgarta mai kama da so!
Ya matso kusa da ita ya zauna ƙamshin su ya gauraya wuri ɗaya.
A hankali ya miƙo hannu zai taɓa nata hannun sai tai maza ta zame tana yin ƙasa da kanta.
"Yaya jikin naki?"
A hankali ta furta.
"Da sauƙi Alhamdu lillahi"
Cikin ƙwarewa da iya hira da ƴammata yace mata.
"Baby tin jiya ban kwana cikin daɗin rai ba, sabida tinanin ciwon kanki"
Cikin sanyin murya tace.
"Ai naji sauƙi fa"
Bata da wani saurayi sai Habib duka shima sau ɗaya ta bashi dama sukai hira ranar daya kawota gida sabida haka sam bata da ƙwarewa a hira da Saurayi tinda ba zancen takeyi ba, sabida haka Mahir ne ya dinga hirar tana amsawa da "Eh" Ko ta ɗaga masa kai bai tafi ba sai bayan magariba har bakin Motarshi ta rakashi.
Ita dai koman ta ya tsaya tin sanda sukai ido huɗu da shi bata sake samun sukuni ba, Wani irin sonsa ne taji yana fisgarta.
Sam wannan aibun nashi data dinga gani jiya ya gushe a guje ta faɗa falo tana kiran Momi.
Cikin sauri Momi ta fito gabanta na faɗuwa zatonta ko wani abun ne sai dai ga mamakinta ganin Adaah tayi tana murna tana tsalle cikin farin ciki tace.
"Momy wallahi yayi min ashe Jiya ban zauna da shi bane, Nikam Ina sonshi Momy har yafi Min Habib sau dubu"
Momi ta rungumeta itama tana murnar tare da cewa.
"Barka Ƴar albarkata"
Nan suka shantake suna hirar yadda zata kaya ba tare da tinanin ayi sallah ba bare azo kan Azkar!
Da maɗaukakin farin ciki Mahir yake tuƙi ya matsu yaje gida ya faɗawa Hajiyarsa yadda sukai da Adaah sabida haka da farin ciki yakai gida shima tindaga bakin Ƙofar falo yake kiran Hajiyar tasa, Wadda itama ta taso tana cewa.
"Me ya faru ne wannan kira haka?"
Kamota yayi suka zauna ya shiga bata labarin yadda sukai da Adaah sosai tai farin ciki da jin yadda komai yazo cikin sauƙi.
Jin hankalinta take yayi mugun kwanciya kuma ta shaida alƙawarin aikin malam daya mata akan lallai sai ya juya hankalin Adaah ya dawo kan Mahir wanda ga shi kuwa tin kafin aje ko ina aikin yaci kwalliya ta biya kuɗin sabulu ƙarashen ne ya rage mata.
******
Washe gari da safe Saadik ya shiga cikin gida wajan Baba yaje suka gaisa wanda yayi shirin fita kasuwa.
Shima bai wani zauna ba ya fita Ƙofar ruwa yaje wajan wani mutumin sa wanda suke harkar Ƙarafe dashi cikon kuɗin da ya biyo mutumin ya karɓa daga Ƙofar ruwa kawai Gidan Aunty Aminah ya wuce rana gatsal a garin haka ya shiga gidan duk Gumi ya gama rufe shi.
A falonta ya zauna suka gaisa Miƙewa tayi ta shiga cikin ɗaki Sai gata da manyan ledoji har guda uku ta aje a gaban shi.
Sannan ta fita kitchen ta haɗo masa abinci da ruwa mai sanyi ta kawo masa gaban shi tana zama a kusa da shi tare da cewa.
"Auta sha ruwan sanyi kaci mutuniyar taka shinkafa da wake sai muyi lissafi"
Ya sha saman kanshi tare da yunƙurawa ya fita bakin famfon tsakar gida yaje yayi alwala ya fita masallacin dake layin yayi sallar azahar, sannan ya dawo Sanda ya shiga gidan an kawo nepa saboda haka a falon ya zauna yaɗan tsakuri abincin ya sha ruwa ita kuma Aunty Aminta tana gefen shi tana Gyaran Turaren wutar data zuzzuba a kwalba da yake tana yin su na siyarwa.
Ture plate din abincin yayi gefe yana Jan ledojin data aje masa a gabanshi tsala tsalan atamfofi ne a babbar ledar ta biyun kuma Laces ne ɗayar kuma material ne da mayafai atamfofin zasu kai Turmi Biyar Laces kuma uku material Biyu mayafai Uku.
Cikin mamaki ya ɗago yana cewa.
"Yaya minau gaskiya kuɗina ba su kai asai waɗannan kayan ba shiyasa na biyo na kawo maki sauran cikon"
Murmushi tai tare da cewa.
"Ai kaga ma magana ta sauya na kira Hajjo da farida tin ranar da kazo nan mun tattauna shine suka ce kabar kuɗin ka kagan su a gefena na fito maka da shi du wannan kayan Hajjoh ce ta bada kuɗin aka siyo farida tace zata sai akwatina ni kuma zan ƙarasa sauran har kayan kwalliya wannan shine gudun mawar mu dakai auta"
Amaimakon ya yi farin ciki sai ya ɓata fuska yayi kicin kicin tare da cewa.
"Gaskiya ni baku kyauta min ba tayaya ko wacce tana fama da kanta a wannan rayuwar tare da ƴaƴanta sannan kuce zaku Min lefe salon ma a zageni"
Me Aunty Amina zatai in ba dariya ba harda ƙwalla.
"Kai Saadik matsala ta dakai kafiya wannan kaci sunan naka Dagiyar wato kai ba za'a maka komai ba abikinka mu muke hidima kake mana duk da ba'a biki da ɗan uwa amman ai kamanci kamata mu haihu kai mana kai mana abikin ƴaƴanmu Kai kaɗai Allah ya bamu Namiji acikinmu In bamu yi maka ba wa za muyi wa?"
Bai ce komai ba sai Miko mata kudin daya ke har lokacin dariya take kafin ta kwantar da murya sanin halin shi in har batai masa dubara ba wallahi ba zai amshi kayan ba sai dai su aje.
"Haba kawu saadik Innah fa tace bayan ka auri Adawiyya zaka auri Jiddah kaga akwai sauran Hidima akanka tinda wannan tamu ce mu mun maka ita kuma Jidda sai kai abin ka da kanka yanzu wannan kudin ka aje ka sai kayan abinci tinda Baba yace Hayar ma har ka fidda kuɗin Biyanta to wannan kasai kayan abinci dasu"
Ya mayar da ajiyar zuciya tare da furta.
"Allah ya saka da alheri"
Itama murmushi tai tare da cewa.
"Yauwa ko kai fa yanzu cikin wannan satin zamu kawo kayan Gidan ku in yaso ƴan uwa suka gama gani sai akai"
"Kinga Ya Minau nifa ko taro Innah baza tai ba karma ku faɗawa kowa dan babu wani abu da za'ai a bari in zan auri Jiddah sai ayi taron ƴan uwa"
Ita dai dariyar rikicin Saadik take har ya ƙare maganar shi ya Miƙe yana mata sallama zai tafi har waje ta raka shi da yake Gidan nata ba kowa acikin yaran nata ya zaro dubu Uku yace ta bawa yara ta sa hannu ta amsa tana godiya don tasan in bata ansa ba fushi zaiyi ya tafi.
Daga gidan ya minau shago ya wuce aiko ya sami masu jiran shi sabida gaba ɗaya bai buɗe shagon ba yau sakamakon Umar na hutun karatun jarrabawa Shiyasa ya dakatar da Usman yace Shima ya huta a gida sabida umar ya fisu Hankali In suka zauna za'a iya samin matsala.
Bayan buɗe shagon ya shiga sallamar Cincirindon matasan dake jiran shi wasu sun kawo rodi ne wasu ƙarfe wasu Robobi bai sami kan shi ba sai da akai la'asar ya kulle shagon ya tafi sallah bayan ya dawo ma sallamar mutane yake har akai magariba sannan ya kulle ya nufi gida.
Ya dakata a bakin wani shagon awo dake gab da layin su ya sai shinkafar tuwo da garin tuwo aka zuba masa a ƙatuwar leda ya ƙarasa gida.
Bai shiga ciki ba a ɗakin shi ya aje kayan daya sayo yayi alwala ya tafi masallaci da yake jikinsa babu datti domin idan zai awon ƙarafe yana amfani da safar hannu ne ta leda sannan kuma yawanci ma yana aje ƙananun kayan da yake sakewa in yana shago duk da yau yaje amakare kuma bai amfani da kayan da yake sawa ba hakan bai saka ya ɓata na jikinshi ba.
Daya dawo daga masallaci wanka yayi ya saka jallabiya Mai ruwan toka ya fesa turare mai sauƙin ƙamshi ya ɗauki ledar Shinkafar tuwon da gari ya ƙarasa Cikin gidan.
Muryar Aunty Hajjoh yaji tana cewa innah.
"To Innah ga autan naki nan hankalin ki sai ya kwanta"
Da sauri innah ta fito daga rumfarta tana cewa.
"Kaiko sadauki ina ka shiga aikena tara da abinci shagon ka baka nan"
Kamo hannunta yayi suka zauna a saman tabarmar rumfar tare da cewa.
"Ki kwantar da hankalin ki innah ba zan ɓata ba ina gidan Ya Minau muna lissafi bayan naje kasuwa na karɓi kuɗi can na wuce"
Innah ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da furta.
"Alhamdulillahi ina ta kiran wayarka sai wannan baturiyar taita yarika kala kala"
Sayyidah mai zatai in ba dariya ba Khadija nayi ummi nayi Juyawar daya yi ne suka daidaita kansu.
Aunty Hajjo itama dariyar take tare da cewa.
"Wato shiyasa sayyidah tace Min Ummi don Allah kije dani gidan Innah naci dariyar soyayyarta da kawu saadik wai niko Hajiya Innarmu zaki bar ɗanki ya tare a wani gun wannan ƙauna haka"
Haɗe rai saadik yayi tare da tashi zai fita dama ya saba jin tsiyar Yaya Hajarah duk sanda tazo gidan sai yaji haushin tsiyar data ke mai ya fita ya bata gu Da sauri Innah ta riƙo hannun shi.
"Kinga Hajara ki fita daga idanuna zoki haɗa ƴarki ku bar min gida wallahi bamai ɓata min ran sadauki"
Ƙunshe sauran dariyarta ta yi tare da miƙewa ta basu guri domin tasan akan saadik zasu iya rabuwar faɗa da innah.
Tashi tayi bayan barin gun da su Aunty Hajjo sukai.
Ta shiga kitchen ta ɗauko masa abinci harda ruwan shayi a fulas
"Innah nikam a ƙoshe nake naci abinci gidan ya minau sai dai Ruwan shayin zan amfani da shi anjima"
Ta ɗan ɓata fuska.
"Kaiko kaci dambu ne na tsaki mai daɗi irin namu na mutan da"
Ya kalleta dama duk sanda taga ba zai ci abinci ba sai tai masa wannan dabarar yake ci.
Aiko janyo kwanon yayi ya sa cokali ya hau ci duk da ya ƙoshi amman haka yake cusawa a cikin sa don hankalinta ya kwanta ta ga dai ya ci ɗin.
Kaɗan ya rage yayi Hamdala sannan ya kira Ummi yace takai kwanon kitchen tare da Ledar Daya shigo da ita.
"Kinji innah su Ya minau sun min lefe"
Innah tai murmushi tare da cewa.
"Yanzu muke maganar da Hajjo faɗa take tayi wai akan mai yasa ba'a faɗa musu da wuri ba da sunyi shirin daya fi haka"
Ya lumshe ido wato ada yana jin takaicin tasowar shi, shi ɗaya acikin mata kuma shine ƙaramin su amman daga baya sai ya dinga ganin Cewar Matan suna da matiƙar jin ƙai da tausayi uwa uba kuma suna son shi sosai.
"Ni kam innah faɗa ma nahau yi don me zasu ɗorawa kan su nauyi"
Innah tai murmushin jin daɗi tare da cewa.
"Haba sadauki in su Hajjo ba su maka ba wai wa za su ma duk duniya ka ma daina maganar nan Ni dama burina Allah ya haɗa min kanku yau daɗin dana ji ko yanzu Allah ya ɗau raina babu abin da zan ƙara masa sai Godiya domin nasan zaka zame musu uba su kuma su zame maka iyaye"
Buɗa Aunty Hajjoh take daga cikin ɗakin Innah kafin ta fito tana cewa.
"Wai innah dole muyi ƙara'i a bikin ɗan auta, ranar kawai nake fata tazo nasha rawa son raina"
Innah ta hau salati.
"Haba Hajjo da ƴaƴanki har kina shirin karɓar jika kiyi rawa wannan son rawa taki naga ranar denawa"
Da sauri Saadik yace.
"Innah kima faɗa musu babu taro in taro za su yi su bari sai bikina da Jiddah don wannan auren dole ne"
"Kai da kata bafa zaka hanamu sakewa ba kaji da gulmarka kuma duk ranar dana ga kana kuka akan soyayyar adawiyya sai na maka tunin wannan maganar kuma abin da nake so dakai shine tin yanzu ka koyi adalci duk matan kane in ma kana son wata to ka barshi a ranka amman batun auren dole duk bai taso ba, Adawiyya ƙanwar ka ce daga baba sai kawu Amadu duk duniya bamu da kamar mahaifinta a cire maganar mahaifiyarta da ita kanta a kalli Zumuncin Allah duk wanda ya ɗauki ɗansa ya baka wallahi ya gama yi maka ƙarshen ƙauna"
Innah ta zubawa Hajarah ido tana kallon yadda take zabgawa Saadik faɗa shi kuma yay ƙasa da kanshi domin ba zai iya musu ba dama duk ƴaƴan nata Hajarah ce tsayayya bata ɗaukar raini sannan akwai tsage gaskiya shiyasa suke shakkarta dama gata ma sha Allah duk tafi su ya minau girma in ka dubeta sai kace ita ce ma babba acikin su.
Sosai Aunty Hajjoh tai masa faɗa mai haɗe da Nasiha sannan ta cewa ƴarta ta haɗa musu kaya zasu tafi gida shiya raka su titi har suka je babban titi tana ƙara Yi masa nasiha da koya masa dubarun zama da iyali.
Shiya biya mata na Mota sannan ya wuce shagon su Nura Saiti.
SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank, ko kuma,9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa ***, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.