SO DA ALƘAWARI

12

by @autarmanya

*SO DA ALƘAWARI..!*🌹

     

     *NA*

*AUTAR MANYA*


           *12*


Sadiq Babu, Nura saiti, babawo duk suna cikin shagon Nuran suna Buga lido ga kofunan shayi nan irin ƙananun nan na buzaye a gefen su ihun su ya cika shagon, duk sallamar da Dagiya yake yi basu ji shiba tsaki yaja kaɗan ya nemi gefen katifar saiti ya zauna.

Babu ne ya kula da shigowar Saadik sabida haka ya dakata da Buga lidon hannun shi ya zabga ihu tare da cewa.

"Sai angon mata biyu na rabi da hauwa mai abin mamaki" Saadik ya haɗe fuska ya sha kunu ya na lalubar wayar shi da ke ringing, Nurah ya ƙunshe dariyar sa ganin rabin hararar akan shi take sauka.

"Haba Dagiya auren ka guda ya tashi amman ka kasa faɗa mana sai a bakin Nurah muke ji?"

Cewar Babawo daya juyo yana kallon Saadik, Shidai bai tan ka suba kuma bama shi da niyyar ya tanka sun sai ma hararar da yake sakarwa Nurah wato bin da yay masa rakiyar dubiyar Jidda shine ya zo yana tsaigunta wa su Babawo lamarin auren nashi daya jiyo, ƙwafa yayi tare da tashi yana ƙoƙarin fita daga shagon da sauri Babu ya tare mai hanya yana cewa.

"Mu zaka mayar marasa hankali mu kome muka yi sai mun faɗa maka amman auren ka guda ka kasa faɗa mana bada ban Saiti ya bika duba tafisu ba da bama zamu ji ba"

Saiti ya cafke da cewa.

"Ai kasan dana ji a wurin maman tafisu wajan Baba naje shiya faɗan komai na auren nashi, wallahi kai dai Dagiya ka daina haka zurfin cikin nan naka har ya fara isata, to me kake nufi da sai dai muji auren naka daga sama ko yaya, ka fa tina mu yanzu mun wuce Abokai wallahi mun zama ƴan uwa in ma kai a abokai ka ɗauke mu to mu a ɗan uwa muka ɗauke ka"

Ganin duk sun masa caa sai jikin shi yayi sanyi sanin kan shine ya san bai kyauta ba, ko yace ma baya kyauta wa su suna faɗa masa duk wata damuwar su hasalima shike kawo musu masalaha in wani abun ya taso musu amman shi da wiya suji lamarin shi haka tsarin shi yake kuma hakan halitta ce daga Allah wani bin ko innah baya faɗawa damuwar shi sai dai abin yayta cin ranshi.


Komawa da baya yayi ya zauna a saman kafitar Saiti ya dafe kan shi da hannu biyu, Ya jima a haka kafin ya ɗago idanun shi ya sauya kala ya koma ja, alamar damuwa ta bayyanar masa.

Gyaran murya yayi kamar kullum cikin ƙasa da murya kasancewar sa mutum marar son hayaniyya ko ɗaga murya.

"To babawo yanzu mai kuke son nace muku? so kuke na fito fili na bayyana muku cewar Baba auren dole zai mini ko yaya?"

Mai su Babawo za suyi in ba dariya ba Babu harda ƙwarewa ganin yanda Saadik ya taƙarƙare yana cewa auren dole.

Ganin zasu mai da shi sakarai yasa ya ƙara miƙewa a fusace ya bangaje saiti ya fice daga cikin shagon.

Saiti ya tsagaita dariyar tashi yana cewa.

"Kunga ku zo mu bishi dole ai zama akan auren nan, Domin Dagiya ɗan halak ne ba zamu bar shi da ɗawainiya shi kaɗai ba kuma don Allah kubar dariyar haka ai maganar hankali, Kun san halin shi kamar kuturu yake zuciya da fushi ba sabon abu bane wurin shi"

Ta shi sukai suka rufo shagon suka bi bayan Saadik da yake basu da nisa tuni suka shiga gidan su saadik ɗakin shi dake soro suka shiga baya ciki da alamun yana banɗaki Nura ya zauna a saman kujerar roba su babawo kuma suka zauna a saman carfet ya kusa minti goma a bayin kafin ya fito shige su yayi ya nufi hanyar ƙaramar wardrobe ɗin shi, ya ɗauki abin da zai ɗauka ya koma bayin Minti kaɗan ya fito cikin farin wandon polo da farar rigar polo marasa nauyi da alamun na baccin sa ne, ya ɗauki turare ya fesa sannan ya shinfiɗa darduma yayi sallar isha'i ganin yayi sallama yana kokarin mai da ta nafila Nura yayi gyaran murya.

"Kaga muma fa musulmai ne na ƙwarai tinda kayi sallar Isha'i ka bari muyi magana muma muje muyi tamu in mun fita sai kayi Nafilar"

Dan dai kawai ɗakin shi suka zo ne bai son suji ba daɗi shiyasa kawai ya juyo yana fuskantar su.

"Mu yanzu a matsayin mu na abokanka zamu ɗauki nauyin wasu abubuwan kama daga kayan abinci zuwa sauran hidimar tura motoci zuwa gidansu amarya"

Sai da ya ɗauki lokaci bai magana ba sannan yace.

"To nagode" a taƙaice.

"To ya batun mazauni fa?"

Cewar babu.

Ya shafa kanshi yana cewa.

"Nan gidan dake kallomu na kama kasan masu gidan zasu tashi shine ni zan shiga"

Babawo yace.

"Kai gaskiya yayi maka kaɗan kuts ni kaf arear nan ma akwai ƙaramin gida kamar wannan kuma har mata biyu zaka saka aciki"

A zafafe ya ce.

"To daidai ƙarfina kenan uban wa yace maka duk su biyun zan aura lokaci ɗaya ina zan kaisu Jiddah sai ta gama karatu kafin nan na fara ginina In sha Allah ko ɗaki biyu nayi saisu koma su duka mu zauna a muhallina"

Nurah yace.

"Eh to tinda mace ɗaya ce ai ya isa sai ai maganar gyare gyare zan saka Mizambilun gidanmu yaje yaga gidan tinda ya iya painti sai yaje yayi maka shafen ɗakuna dana tsakar gida"


Saadik yace.

"Wasu ɗakuna ɗaki ɗayane ciki da falo sai kicin da bayi amman bakaji kuɗin da suka sawa gidan ba haka dai zan biya tinda nina fi son kusa da innah gaskiya"


Nurah yace.

"Okay ba matsala sai batun lefe kuma?"

Ya ɗan haɗe rai.

"Nikam titsiye ni kuka zo yine to ban yi ba"

Babawo yayi dariya tare da cewa.

"Kaifa ka zama ɗan alallaɓa yanzu Angon Rabi in ma bakai lefe ba mu sai muyi karo karo"

Wani kallo ya watsama Babawon tare da cewa.

"Kasan dai ni ba rago bane babu abin da yake firgitani, Lefen yana gidan Yaya Minau kun san gidan sai kuje ku gani"

Saiti yace.

"Baka isa ba dole a kawo min kayan madam nai mata ɗinkuna masu fisgar hankali tasan ta auri abokin telan mata"

Ta shi yayi cak ya tada sallar shi sukam maganganun su suka cigaba dayi akan bikin kafin su miƙe su fita.

Shikam ya jima a sujjadar shi yana ƙara jaddada neman zaɓin Allah akan lamarin auren wanda dama wannan addu'ar yake ba dare ba rana in har yayi sallah sai ya miƙa koken shi wurin Allah akan lamarin auren nashi.


Bayan ya sallame ya na ɗe abin sallar ya kashe ƙwan ɗakin yayi kwanciyar shi.


Da asubahi suka haɗu da baba a masallaci wanda baban yake masa magana akan shirin auren bayanin yadda ake ciki yayi ma baba cikin ladabi, baba ya ƙara da cewa, mahaifin jiddah ma yay masa magana jiya akan wai sukai kuɗin aure in yaso in ta kammala karatun sai ayi bikin.

"Baba ka basu haƙuri kaga duk ƴan kuɗaɗen hannun nawa na haɗa zan kai kuɗin gidan can su min alfarma bayan biki sai na bada akai"

Baba ya murmusa tare da cewa.

"Hakane sadauki, amman tinda suka nemi akai to akai ɗin ni zan bada kuɗin akai musu kaga sanda zamu kai kuɗin Amadu yazo min da batun auren ka da rabi'ah to kar suga kamar ba zaka auri ƴarsu bane mutanan nan babu abin da zamu ce musu sai godiya da irin ƙaunar da suke nuna mana sabida haka Amadu yace jibi zai dawo kano in ya dawo zan bada Kuɗi suje su kai gidan su jiddan shida sauran ƴan uwan mu na ƙauye"

Saadik ya rissunar da kai ƙasa tare da cewa.

"A,a Baba Kana ta kanka ka ɗorawa kanka wahala ka bari bazai gagaraba in sha Allah, Burina akai lefen sannan na bawa masu gidan can kuɗin su sai hankalina ya kwanta"

Baba yace.

"Banda abin ka Sadauki In da ni mai hali ne ai da na ɗauke maka komai na hidimar aure, to ni babu mahaifiyarka babu sai kai kaɗai da Allah ya bawa ƙarfin zuciyar nema ga shi yanzu Nauyi zai ƙara ninkuwa akanka bayan namu Allah ya maka albarka kuma zan cire kuɗin auren akai Musu In sha Allahu"

Daɗa rissunawa yayi yana wa baba godiya sannan suka ƙarasa gida.

Ɗaki ya koma ya sake kaya dan ko wanka bai yi ba, a gurguje yaje suka gaisa da Innah ya fice shago tin sassafen don abin kari ma sai Usman ne yakai masa dole yabar Usman a shagon Shi kuma ya wuce Ƙofar ruwa.



Wajan ƙarfe Sha ɗayan safiya gaba ɗaya iyalan na Innah suka hallara agidan Aunty Amina da Ƴaƴanta jawahir wadda ba a jima da bikinta ba sai Hussaina wadda za'a ma biki kwanakin nan, Aunty hajjo da Fatima ƴarta wadda ke dauke da tsohon ciki sai Sayyidah, Sai faridah data zo tare da Sajidah da Sajjad ga kuma su Ummi nan don bama suje Makaranta ba ranar shiyasa gaba ɗaya gidan na Innah ya gama cika da Ƴaƴanta da Jikokinta ƙatuwar tukunya Khadija ta wanke aka ɗora wake da shinkafa a tsakar gida wadda za a ci da rana.

Babu komai da yake ta shi sai hayaniyar su, ta surutun su kuma duk akan bikin auta ne suke ta faman maganganu na yadda bikin zai tafi.

Shigowar Sayyid da Hassan ce ta sa surutun ya ɗan lafa, Sayyid ɗan Aunty Hajjo Hassan ɗan Aunty Amina, Suka shigo da akwatina niki niki da alamun daga kasuwa suke sai da suka shigo da akwatina saiti Biyar cif da ƙatuwar gana Hassan yay miƙa yana cewa 

"Washh Allah Ummah ba ƙaramar wahala muka sha a kasuwa ba, da ƙyar Abba ya samo ɗaya atamfar nan fa"

Aunty amina ta fara janyo akwatinan tana cewa.

"Allah dai yay muku albarka dama nasan za a ci wahalar kafin a samo, da kuka amso ne kuka je gida kuka ɗauko akwatinan? to kun sallami mai ɗan sahun daya kawo ku?"

Sayyid yace.

"Eh mun sallame shi yama tafi Ummi nina wuce school"

Ya faɗa yana kallon Aunty Hajjo.

Innah da bakin ta ya ƙi rufuwa cewa take.

"A,a ku bari kuci abinci mana Allah ya maku albarka kuma ya ninka musu abin da kukai"

Matasan dai fita sukai sunawa Innah murmushi, tare da amsa addu'ar da tai musu suko su Ya Minau kayayyakin sukaita ɗagawa don an karo wasu kayan akan na da faridah ce mai shirya kayan ko wanne tana haɗe shi a inda ya dace.

Kafin Ya Minau ta cewa su Ummi suje maƙota su farfaɗa azo aga lefen kawun su saadik aiko Su Ummi fita sukai gida gida sukaita faɗa kafin kice kwabo gidan Innah ya cika da mutane ƴan kallon Lefe.

Sai dai mahaifiyar Jiddah furr taƙi zuwa ta kuma kafawa Jiddah takarar ko kallon saadik karta ƙara yi ranar Jiddah taci kuka ta godewa Allah, domin Wata irin ƙaunar Saadik ce ke ƙara ninka mata ruhinta.

Maƙota kowa yazo sai ya tambaya gidan su Jidda za'a kai sai Faridah ke musu bayanin Ai ƴar ƙanwar Baba zai aura Jiddah kuma sai ta kammala karatun ta wasu suyi fatan alheri wasu kuma su tafi suna ƙus ƙus ranar har dare ana shigowa kallon Lefen wanda kowa ya gani sai ya yaba shi kan sa Baba yayi mamakin rawar ganin da ƴaƴan nashi sukaiwa ƙanin nashi aiko sai saka Musu albarka yake.

Saadik bai shigo gida ba sai bayan Isha'i shima wayar innah ce ta saka ya tawo sabida a kwanakin nan cikin taskar Allah yana samun ciniki ne fiye da yadda yake yi ada shiyasa yake jimawa a shagon.

Tin daga bakin layi yaji mutane na masa Allah ya sanya alheri wani maƙocin su ne ya tare shi sanda zai shiga gida yana ce masa.

"Malam saadik ashe lokaci yayi to Allah ya sa alheri"

Dama da mamakin yadda ake masa Allah sanya alheri ya ƙaraso sai kuma ga wannan maƙocin nasu shima ya tare shi yana masan.

Ƙaƙalo murmushin dole yayi tare da cewa.

"Amin ya rabb! nagode"

Ya faɗa yana ƙoƙarin shiga gidansu.

"Amman Saadik kaji tsoron Allah naji ance ba Waccan yarinyar jiddah zaka aura ba, ƴar ƙanin mahaifinka zaka aura mai kuɗi shiyasa ma kuka haɗa lefen ƙarya, amman gaskiya bai ci kaiwa Jiddah haka ba kowa yasan yadda kake da yarinyar nan amman ka yaudare ta"

Da sauri ya ɗagawa maƙocin nasu hannu tare da faɗawa soron gidansu da sauri.........

SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa ***, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.