SO DA ALƘAWARI

13

by @autarmanya

*SO DA ALƘAWARI..!*🌹

     

     *NA*

*AUTAR MANYA*


           *13*


Da tsananin ɓacin rai yake shiga cikin gidan nasu, yadda ya tarar da mutane a tsakar gidan nasu suna ta ɗaga kayan cikin akwatinan abin ya bashi mamaki ba kaɗan ba.

Ya tokare a bakin rijiya tare da zuba hannayen shi a saman ƙirjin shi sabida yadda ranshi ke ɓace baya tinanin ma na tsakar gidan sun ji sallamar da yayi.

Innah ce ta farga da tsaiwar ta shi ta taso ta iso inda yake tana cewa.

"Sadauki! lafiya na ganka a tsaye ka ƙaraso mana, Allah ya sa ƴan uwan naka basu tafi ba dama kai suke jira"

Ya ɗago tare da zuba mata jajayen idanunshi murya a raunane yace.

"Yanzu innah sai da kuka aika azo aga lefen nan fisabilillahi mai iyayen jiddah zasu ɗauke ni?"

Sai ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana cije bakin shi, sauran maganar ta tokare a maƙoshin sa.

Innah ta zuba mai ido tana ƙara jinjina son da yake wa jiddah tinda har yana gudun ɓacin ranta da kuma na iyayen ta.

"To sadauki ya za'ayi da ƙaddarar Allah tinda Ubangiji ya ƙadarta ba Jiddah bace matarka a farko ba, yaya zamuyi gaba ɗaya haƙuri zamu yi tare da addu'ar alheri acikin lamarin"


Jinjina kanshi yayi tare da cewa.

"Tin da kika ce Allah magana ta ƙare"

Bai iya faɗa mata maganar da maƙocin nasu ya tare shi da ita ba sabida masifar zurfin ciki.


Ya na ƙoƙarin juyawa ya koma ɗakin shi su Ya minau suka ƙaraso wajan da shirin tafiya gida faridah sai tsokanar shi take yayi mata banza ya wuce ya barsu a wajan.

Innah tai murmushi tana kallon Aunty Hajjo tare da cewa.

"Yanzu goben ƙarfe nawa za a kai kayan? sai na kira Nafi kuje da ita amman ban da abinku da kun bari maza sun kai yanzu yaushe rabon da ku ga mata sun kai lefe?"


Da sauri faridah tace.

"Ban da abin Innah mazan su waye zasu kai? abu duk ɗaya Mu dai ki bari Muje mukai"

Ba yadda Innah ta iya ta amsa musu kamar yadda suka buƙata Ya Minau ce tace.


"Innah ni naga Saadik na haɗe rai wai meke faruwa ne?"

Innah cikin basarwa tace.

"Ke rabu da shi ya ƙarata da Ƙuncin sa"

Har soro innah ta raka iyalan nata tana musu addu'ar fatan gamawa da duniya Lafiya suka fita titi ko wacce ta hau motar gida.


Ba jimawa da fitar tasu Baba shima ya shigo gida lokacin mutanen dake ganin kayan lefen duk sun tafi sai su Khadija dake tattare tsakar gidan.

Baba ya zauna a saman tabarma a rumfa Hasken farin ƙwan tsakar gida ya hasko har cikin rumfar da yake zaune yabi akwatinan da kallo Fuskar shi dauke da maɗaukakin farin cikin haɗin zumuntar da zasuyi da ɗan uwan shi ya dubi Innah dake haɗa masa abinci yace.


"Haƙiƙa Hafsatu naji daɗin wannan aure ina fatan Ubangiji yasa sai mutuwa ce zata raba su, tabbas Amadu ya wanke duk wani laifi da ya min abaya domin duk duniya ba wanda zai iya riƙe Ƴar amadu kamar Sadauki kinga munyi tuwo na mai na"

Ya faɗa yana sakin ƙayataccen Murmushi, Itama Innah Murmushi tayi tana cewa.

"Allah dai yasa ayi lafiya a gama lafiya niko burina na goya ƴaƴan ɗan auta tin da ƙwarina Kuma Allah ya cika min, sai batun kai Lefe kunyi magana da shi Amadun ne? waɗan nan yara fa sun kafe sun ce sai sune zasu miƙa kayan"


Baba ya ɗaga kofin da innah ta cika mai shi da ruwan sanyin randa mai daɗi yace.

"Munyi waya ɗazu yace min Gobe da safe zai sauka kano Wajan yamma sai su miƙa abu duk na gida nida ma niyata ma a bata kayanta ranar ɗaurin aure, to tinda sunce zasu kai kar a katse su duk cikin murna ne"


Ire iren hirar bikin suka cigaba dayi har zuwa Lokacin kwanciya bacci.

*******

Adaah bata san waya bawa Mahir Numbern wayarta ba amman tafi zaton Momi ce ta tura masa shiyasa sanda taga kiran shi cikin dare batai mamaki ba hira mai cike da so da kulawa yake mata har sai da ya tabbatar ya dasa mata son sa acikin zuciyarta sannan ya barta aiko daren bata rintsa ba duk juyi shi take tunani abin ka da farin shiga.

Washe gari sai wajan taran safiya tayi sallar asubah sabida wayar da suka sha da Mahir ta makara ne tasha baccinta ta gode Allah wanka tayo ta shirya cikin Riga da skirt na Jar Atamfa Java bata ɗaura ɗankwaliba a haka ta fito Parlour tana kiran Maimuna da sauri maimuna ta ƙaraso ta rissuna tana cewa.

"Gani uwar ɗakina Barka da asubah"

Cikin halin ko in kula tace.


"Kije ki wanken toilet ki gyaran ɗakina ki kunnan turare akwai undies ɗina da zaki wanken washing machine ɗin toilet ɗina ya lalace"

Har lokacin maimuna bata ɗaga kanta ba har sai da Adaah taja aya sannan maimuna tace.

"An gama uwar ɗakina ga break ɗin ki can na haɗa komai kawai ci zaki yi"

A ya tsine ta amsa wa maimuna da.

"Ok"

Sannan ta wuce dining ta zauna ta haɗa tea ta ɗauki bread tana haɗawa da soyayyen ƙwai tana ci da yake Allah ya ɗora mata ci kamar gara ita Ko irin rashin cin nan ma na ƴaƴan masu kuɗi bata da shi.

Sai da ta share wannan bread da ƙwai tas sannan ta goge bakin ta da tissue ta ƙarasa cikin parlour ta kwanta tana canza channel.

Momi ce ta fito sai baza ƙamshi take.

Ta ƙaraso gaban Adaah tare da cewa.

"Tashin ki kenan na lalleƙa ki naga baki farka ba, Nima fita zanyi yanzun nan zan dawo"

Adaah tabi momi da kallo kafin ta kawar da kanta, ba tare da gaishe da mahaifiyar tata ba.

Momi tana ƙoƙarin fita daga Parlourn Sukai Kiciɓus da Abbah wanda shigowar sa gidan kenan hannun shi riƙe da ƙaramar jaka ta matafiya.

Momi zamewa tai a wayance ta zauna a saman kujera tana aje ƙaramar jakar hannunta dama lefen ƴar ƙawarta zata je gani sam bata kawo Abba zai dawo yau ba shiyasa zatai gaban kanta sabida ana faɗin irin dukiyar da aka laftawa ƴar ƙawar tasu.


"Sannu da shigowa Alhaji, amman dawowa babu sanarwa"

Ta faɗa tana sosa kai alamun rashin gaskiya.

Bai kulata ba sai Neman gurin zama da yayi da sauri Adaah ta diro tana sauka ƙasa har tana ƙwarewa wajan yiwa mahaifin nata barka da zuwa sabida shi tana shakkar shi ba kamar Momi ba.

Abbah ya bita da kallo ba tare daya amsa gaisuwar tata ba.

"Rabi'atu mai kike agida yau baki je makaranta ba?"

Sai ta hau kame kame sabida sarai tana da lecture ranar amman taƙi zuwa.

"Wato asarar kuɗina nake a banza ba karatun kike soba ko da yake ai magana ta ƙare dama abin da yasa na rabu dake na zaci zaki dage ki karatu ne, amman tinda baki son makaranta zan faɗawa Mijin naki ko bayan aure karya barki Fita ki haƙura haka abin da kika samu Allah yasa mai albarka"


Haɗe rai tayi nan da nan ruwan hawaye ya fara firfitowa daga idanunta ta jefa kallon ta ga Momi wadda ta kafe Abbah da ido tana jijjiga ƙafa.

"Wannan wace irin magana kake Alhaji wai shi wannan auren dole ne? haba yarinya bata so nida na haifeta bana so gaskiya ba zan lamunci a cusawa ƴata ƙatoton jahili ba, ce maka akai bata son karatu bayan ita kaɗai Allah ya bamu Tarin dukiyar da Allah ya baka in baka barta tai karatun ba waye zai riƙe mana ita nan gaba"

Abbah ya zubawa Momi ido cike da ɓacin rai, sam tinda lamarin auren nan ya tashi momi bata saurara mai bata masa ta sauƙi hatta ga kalamanta kawai yana kai zuciyar shi nesa ne yana duba wasu abubuwan jiba yanzu yadda take masa magana agaban ƴarta ba ladabin harshe ko tauna magana.



"Maryam sai fa Rabi'a ta auri Saadik koda gawarta ce wallahi zan kai gidan ƙarewar ƙiyayya in an aura masa ita tasa Ashana ta kunnawa kanta ta Ƙone ta mutu Ki sanar da ƴan uwanki anjima Za a kawo lefe"

Daga haka ya miƙe yabar Parlourn zamewa momi tayi daga saman Kujerar tana yarfe Zufa.

Da sauri ta ɗaga waya tana Kiran Hajiya Lubna.

Daga ɓarin Lubnah dake kwance domin har Lokacin bata tashi daga baccin safe ba.


Ta ɗaga wayar tana jan ƙaramin tsaki.

"Maryam yaya akai wannan wayar da farar safiya?"

Momi ta yarfe zufa a karo na barkatai kafin tace.

"Kinji wata sabuwa anjima zasu kawo lefen Adah ni kaina ma ya kulle"

Da sauri Lubna tace.

"Kamar yaya dama baki zuba masa magani a ruwan ya sha ba har ya sami zarafin maganar auren?"

Momi ta juya tana kallon hanyar da Abbah yabi taga ya ƙullewa ganinta sai tace.

"Yau fa ya dawo gari yanzun nan ya sauka yake wannan bayani wallahi bai ma bani fuskar na bashi ruwan ba bare akai ga na saka ke nifa gani nake suma aiki suke akan Alhaji duk yabi ya birkice min kamar ba shi ba"


Ƙaramin tsaki Lubna taja ido rufe da son biyan buƙatar kanta tace.

"Duk yadda za'ai karki yarda da wannan aure nima zanyi ƙoƙari na ta nan, Nifa ko ba Mahir ba wallahi nafi son Adaah ta auri Miji na kece sa'a irin yadda ƴaƴan ƙawayen mu suke aura haba ƙiri ƙiri za'a tauyeki ƴa ɗaya da Allah ya baki za'a cutar da ke a bata Ɗan jagaliya talaka faƙiri marar ilimi wanda ba lallai yasan darajar mace ba Niba burina Adaah ta auri ɗana ba Burina ta sami Mijin nuna sa'a mijin da zamu nunawa duniya cewa ƴarmu ta auri Namiji, wallahi inda ina da ƴa mace Budurwa Maryam kota halin ƙaƙa sai na shiga na fita na nemo mata wani ƙusa a ƙasar nan Ina zan yarda ƴata ta auri talaka"


Kalaman Lubna suka ƙara Raunana momi suka kuma ƙara bata ƙarfin gwiwar Tsanar auren da za'ai wa Adaah a raunane tace.

"Lubnah wallahi bada ban kar nai ƙarya ba sai nace kinfi kowa sona da damuwa dani, Tinda lamarin nan ya kunno ke kaɗai kike bani ƙarfin gwiwa duk da malam yace Adaah ta auri mahir amman ke ba burin ki ma ta aure shin ba ke burin ki ta tsallake ta sami miji na kere sa'a ya zanyi yanzu yau fa zasu kawo lefe?"

Ta faɗa tana kuka!


Lubnah ta cije baki ita kaɗai tasan meke ƙasan zuciyarta sai kuma Allah kafin tace.

"Karki musun zuwan su wannan ma wata dama ce da zaki ci musu mutunci karma ki gayyaci kowa daga dangin ki ke kaɗai zaki zauna su zo ki ci zarafin su tass kwaɗayayyun banza kinga daga nan suma in suka ji haushi zasu koma da ɓacin ranki nan ma wata damar ce da zaki wargaza auren"


Da sauri momi tace.

"Haka ne lubna dama wa zan faɗawa a dangina Allah na tuba Ai wallahi dama ni burina in Adaah ta sami miji ku zaku yi komai cikin girma ba tare da kun bani kunya ba"

Sai da suka gama tattauna komai sannan sukai sallama momi ba abin da take sai girgiza ƙafafu Adaah ta ja jiki ta ƙaraso wurin Momi.

Murya cikin rauni tace.

"Allah momi ina son ya Mahir ɗin Momy lubna yanzu bani jin zan iya rayuwa da wani idan ba shi ba momi kada ki bari Abba yayi mini auren dole"

Momi ta janyo Adaah jikinta tana rarrashinta


Har ta samu ta saki ranta.

Cikin shiri Abbah ya sakko sabida zai fita kasuwa zasu gana da wani mutum dake jiran shi duk da yana buƙatar hutu amman hakan ba zai samu ba.


Har lokacin bai da sukuni a fuskar shi ya ce.

"Maryam sai ki sanar da Ƴan uwanki nan da lokaci kaɗan zasu kawo kayan lefen akwai Lemuka da ruwa dana sa akawo sai ki sa masu aiki suyi musu Girki ki ɗauki kuɗi a ɗakina ki sallame su duk da ƴan gida ne amman yaba kyauta tukwici"

Idan kujerar data ke kai ta tanka to ta tanka wa Abbah har ya ƙare ya fita itama Adaah da ƙyar tai masa Adawo lafiya aiko yana fita tai ɗaki aguje tana kuka.

Momi da takaici ya hanata motsi a nan ta cigaba da zama koda mai kawo ruwa da lemuka ya turo mai gadi cewar ya ƙaraso cewa tai ace ya mayar dasu basa buƙata haka ya juya har akai azahar tana zaune sai da ta gaji dan kanta sannan ta miƙe ta shiga ɗaki tayi sallah ta ƙara dawowa parlourn jira kawai take masu kawo lefen su zo.



Ƙarfe ukun yammaci daidai Maimuna tai wa su Ya minau Iso babban parlourn gidan ƙanin mahaifin nasu wanda in za a kashe su ba zasu iya cewa ga yanayin gidan kawun nasu ba sabida ba zuwa suke yi ba.


Ya minau ce, sai Aunty hajjo, da Faridah da Aunty Nafi ƙanwar Innah sabida innah tace karsu faɗawa kowa daga cikin danginta domin basu san kalar tarar da zasu samu ba gudun abin kunya, gwara Aunty nafi ƙanwar Innah ce cikinsu ɗaya bazzawara ce take zaman gida.


Su Ya minau suka nemi guri suka zauna Umar ne ya dinga shigo da akwati nan ya jere su reras a parlourn.

Momi tana kallon su batare data amsa sallamar su bare akai ga batun ta amsa gaisuwar da suke mata ba.

Aunty nafi ta ce.

"Ina mutan gidan ne muna ta sallama kamar babu kowa"

Tsaki mai ƙarfi Momi ta saka tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ƙaro Ƙarfin Tv.

Aunty Hajjo ce tace.

"Innah Maryam barka da rana ga abin arziƙi mun kawo kuma mun zo kamar baku shirya zuwan namu ba naga babu ƴan ɗaga kaya koda yake abune duk gida ina amaryar tamu?"


A fusace Momi ta ɗago tana watsa musu harara kafin ta taso har gabansu.

"Ku wasu irin mayu ne? wai ba'a faɗa muku bama ra'ayin haɗin auren nan ba kwaɗayi ne yasa Za'a ɗauki ƴata a bawa Ɗan uwanku to ni dana haifeta bana so Itama bata so don Allah ku ɗauki gayyar tsiyarku kuje kucewa Ubanku bama........

Da sauri Anty Nafi tace.

"Kai kai baiwar Allah ya kike abu irin na Mutane marasa kan gado Shin ba mijin kine ya kawowa Baba tallan ƴarki ba har kike kiran kayanmu da gayyar tsiya wallahi ke kam baki gaji arziƙi ba duk inda kika fito daga tsiya kika fito Yau inda ina da iko sai na hana Saadik ya auri ƴarki sai kace autar mata kije kiga yadda ƴammata suke tururuwa akan shi ke an samu an liƙa masa jarabar ƴarki har kina da bakin magana"

Anty nafi ta kai maganar cikin Ƙunar rai.

Tabbas yadda su Farida suke jin zuciyoyin su bada ban taci darajar Baba Amadu ba da babu abin da zai hana su gargasa mata baƙaƙen maganganu amman wata fuskar tafi gaban mari taci arziƙin auren ƙanin mahaifin su sabida haka da sauri suke ficewa daga parlourn.

Momi dan izzah da ƙasƙanci takan akwatinan ta dinga bi tana takawa tana tafiya zuciyar Aunty Nafi tai zafi ji take kamar Ranta zai fita dan ɓacin rai bata taɓa ganin mace mai izza da wulaƙanci da rashin sanin darajar mutum irin matar nan ba.


Sai a titi suka haɗu da junan su Ya minau mai rauni tuni ta soma kuka.

Umar ya samo musu ɗan sahu suka hau duk cikin su babu wanda ya iya magana, har suka ƙarasa Gida.


Yanayin da suka shigo gidan kaɗai shiya fahimtar da innah abin da ke zuciyoyin su.


Saadik yana zaune saman kujera ƴar tsugunno yana wanke takalmin training ɗinshi.


Farida randa ta nufa tana shan ruwa.

Su kuma suka zauna saman tabarma.

Kukan ya Minau ne ya cika kunnuwan su.

"Don Allah Innah ki cewa Baba yabar batun auren Saadik da Ƴar gidan Baba Amadu haba talauci hauka ne duk wahalar da muka sha ganin munyi komai cikin tsari abin ya kasa yiwuwa matar nan takan akwatinan da muka kai ta dinga bi tana takawa bayan cin mutunci da muzancin data mana.........SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank, ko kuma 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa ***, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.