ZAWAJUL MUWADDA

Chapter 9

by @saratalkasum88

*ZAWAJUL MUWADDA*





Daga alƙalamin


_Sarat Alƙasum (Mom Nusaiba)_



_(Labarin Sidra)_



*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*



*بسم الله الرحمن الرحيم*



*PAID BOOK ONLY N500*

_Za ku turo kuɗinku ta wannan account ɗin. Account number 0003187186, Name account, khadija Salisu, Name Bank, Ja'iz Bank. Sai ayi screen screen shot a turo ta wannan whatsapp number +966577675904, idan ana neman ƙarin bayani wannan number da na bayar za a yi magana kai tsaye_



*SHAFI NA* 9️⃣



Tun Sidra na ƙoƙarin kare kanta har ta kai matakin da ba za ta iya ɗaga ko da ƴar tsayarta ba, sosai ta ci duka Inna na gefe ta haye gado tana ƙara zuga Suwaiba.

Sai da gaji dan kanta da dukan sannan ta tashi a kanta ta daka mata tsawar da ta nemo ƙarfin tashi daga kwancen ba arziki ta zauna, wani irin zafi gadon bayanta ke mata gefen bakinta ya fashe jini na zuba ta rarrafa da kyar ta fita a ɗakin tana wani irin kuka mai ciwo, shin ita sai yaushe ne za ta ji daɗin rayuwa a gidansu? Yaushe ne Inna za ta daina saka Suwaiba ta mata duka ba tare da ta aikata musu komai ba?

Da kyar ta dafa bango ta miƙe tsaye tana runtse ido Suwaiba ta leƙo ta ce “Idan kika yi minti biyar a banɗakin nan sai na zo na ƙarya miki hannu.”

Da ɗan sauran kuzarin da ya rage mata ta tattaka ta nufi banɗaki, kasancewar ana zafi ruwan da ta aje a buta a ƙofar banɗaki wanda ta yi shirin yin wanka da shi dan ta tafi Islamiya sai kuma ta ga lokaci ya ƙure sai ta bar ruwan a nan shi ne ta ɗauka ta isa ciki. Doguwar rigar jikinta ta cire ta durƙusa ta dinga kwara ruwan a gadon bayanta ta fi jin zafi da ciwo a baya sama da sassa jikinta, hannu ta kai ta shafa fuskarta ta ji shatin yatsun Inna ya mata ruɗu-ruɗu ta sake sa wani sabon kukan kamar za ta shiɗe, sai da ta ga ruwan ya ƙare sannan ta miƙe sai a lokacin ta ji zafin ya ɗan ragu ta mayar da kayan jikinta ta fito zuwa ɗaki, vSuwaiba na tsaye a tsakar gida riƙe da bulala tana lissafin lokaci.

Can cikin kayansu ta binciko ta janyo wata leda baƙa ta buɗe jiki na ɓari, dubu biyu ta zaro a cikin dubu ashirin ɗin da Abubakar ya ba ta ranar da suka haɗu a kasuwa shi ne ta ɓoye su dan kar Inna ta gani ta kwace, a jikin ɗankwalinta ta ƙulle ta mayar da hijabin ta fito tana sunkuyar da kai Suwaiba ta daka mata tsawa tana nuna mata gyaɗa da goro har da su Maggi da sauran kayan miya a cikin babban bakati fari shi kuma goron a tire an rufe shi da garara, wani iri ta ji ganin uban kayan da za ta ɗauka amma saboda babu yadda ta iya sai ta sunkuyar ta jinjina za ta ɗauka sai ta kasa, Inna da ke ɗaki ta leƙo ta ce “Ke ɗora mata kar ta zubar mini da kayan kuɗi yau a gidan nan zuciya ta ɗebe ni in sumar da ita.”

Bikita-bikita Suwaiba ta wuce ta ɗauki kayan ta ɗora mata a ka ta ɗauko goron ta ɗora mata a samar gyaɗar tana zagin ta, babu gammo sai ta ji zafi ta ce “Inna don Allah ki ce ta sa mini gammo kar kayan su faɗo su fashe.”

Tashi Inna ta yi ta fito ta ɗauko zanin Suwaiba da ke kan igiya ta naɗa ta ce da Suwaiba “Ke ɗaga mini na saka mata ko ta fita da wuri.”

Riƙe ƙugu Suwaiba ta yi cike da tsiwa ta ce “Tsakani da Allah ni dai kar a ɗaukar mini zani a yi gammo da shi, shi ne fa zan sa yanzu idan na yi wanka na tafi gidan su ƙawata ni dai a aje min abuna.”

Kwafa Inna ta yi ta aje mata zanin ta wuce ɗakin su Sidra tsoro ya kama ta tana addu'ar kar ta bincika mata jakarsu ta ga kuɗin da ta ɓoye yau ta rasa mai ceton ta a hannun Inna.

Ba ta jima ba sai ga ta ta fito da zanin Sidra wanda ta cire yau tana naɗawa ta iso ta ce ta ɗaga mata kayan, tana mita tana faɗin magana ta ɗaga mata aka sa mata, sai da Inna ta tabbatar ya zauna sannan ta matsa ita kuma ta fita.


Har ta kusa fita daga gidan ta ƙwala mata kira ta juyo ta dawo, da hanzari ta shiga ɗaki ta fito da garwashi a kasko ta kunce wani ɗaurin magani a leda ta zuba ta ce ta zo ta tsaya a gaban kaskon, ba muso ta ƙaraso ta tsaya hayaƙin na shiga jikinta Inna na ƙara kora shi wajen ta sai faɗi take “Tsaya da kyau ya shiga jikinki maganin kasuwa ne Aminiya ta amso min daga wajen wani malami saboda na dinga turara miki da kin fita za ki sayar ki dawo gida a kan lokaci, saboda ni na gaji da aikin gida shara da wake-wake da abinci, amma idan kika sayar da wuri in kika dawo sai ki yi ko da abinci da wankin ne sauran ni sai in yi in na ga zan iya, idan kuma ba zan iya ba sai na bar miki duka dan ni ba jakar gidanku ba ce na gaji da yi muku abinci kuna ci, sannan malamin ya ce in an ce ki kai cikin gida za a saya sai ki ce ke ba za ki shiga ba, shegiya arziƙi yana bina kina guje mini shi to ba na son iskanci soya namanki za a in kai cikin gidan mutane talla? Idan kina so mu zauna lafiya ki yi duk abin da nake so ni kuma babu abin da ba zan miki ba har dinkuna zan ke miki ba sai a Sallah ba.” Ta ƙarashe maganar da taushin murya.


Sidra da hayaƙi ya turniƙe ta ta ja da baya tana tari ta ce “Inna ya isa haka ni zan tafi, kuma zan yi duk abin da kika ce.” Ta faɗa a sanyaye.


“Yawwa ɗiyar kirki ashe dai yanzu kin fara hankali, to maza je ki Allah ya ba da sa'a kin ci abincin rana?” Ta yi maganar tana washe baki.

Sororo Sidra ta yi tana kallon Inna cike da mamakin tambayar, wai yau ita ce Inna ke tambaya ta ci abinci? Ko dai mafarki ne take? Sai da Inna ta sake tambayar ta sannan ta kalle ta da sauri ta ce “A'a Inna ban ci ba sai kunun da muka sha da safe.”


Naira hamsin ta kunto a haɓar zaninta ta miƙa mata tana faɗin “Yawwa to ga shi Hamsin ce ki ci abinci har na dare dan ba zan iya girki ba gidan Aminiya zan je sai bayan isha'i zan dawo.”

Ita dai abin ganin shi take banbarakwai namiji da suna Hajara bayan an gama mata dukan tsiya shi ne yanzu har ake ba ta kuɗin abinci abin da ba a taɓa yi mata ba tun da mamanta ta rasu? Ajiyar zuciya ta sauke ta amshi kuɗin ta yi godiya ta wuce tana ta mamaki wani sashe na zuciyarta na faɗa mata ko dai Innar aljanu gareta? Murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi tana goge hawayen da suka zubo mata ta ƙarasa fitowa..


A ƙofar gida ta haɗu da wani matashin saurayi ɗan gayu yana tsaye a jikin motarsa baƙa ya harɗe hannaye idanuwansa a kan kofar gidansu, baki ta riƙe sai kuma ta sake kallon shi tana tuna in da ta san wannan fuskar sai kuma ta basar ta zo za ta wuce shi sai ta ji ya mata magana.


“Yan mata ji mana, na ce ko Suby tana nan?”


Jiyowa ta yi sai yanzu ta gane shi ta mishi wani irin kallo sannan ta ce “Eh tana nan mana ina za ta je?”


Murmushi ya yi ya iso gaban ta ya sa hannu ya ɗauki ɗaurin gyaɗa ya ce “Nawa-nawa?”


“ɗari-ɗari.”


Gyaɗar ya juya sai ya sake ɗauko ɗaya ya sa hannu a aljihu ya zaro ɗari biyar ya miƙa mata sannan ya ce “To ga shi ki riƙe har canjin na bar miki, amma ke ƙanwar Suby baby ce ko?”

Gyaɗa mishi kai kawai ta yi ba ta ce komai ba, wani irin kallo uake bin ta da shi sannan ya ce “Gaskiya ke kyakkyawa ce sosai ga ki fara ƴar dumaduma, ba ƙarya fa ki haɗu baby.”


Takaici ne ya rufe Sidra ta juyo za ta ba shi amsa sai ga Suwaiba ta fito cikin shigarta ta riga da wando jins rigar ko rufe cikinta ba ta yi ba, Sidra ta girgiza kai ta juya ta wuce tana jin Suwaiba na tambayar saurayin nata me ya sa ya tsayar da ita ya ce gyaɗa ya saya, har ta ɗan yi nisa da su bai daina kallon ta ba yana sakin murmushi yadda take tafiya abin sai ya ƙayatar da shi, Suwaiba na ta zuba mishi shagwaɓa kanta a ƙasa ta ji bai rarrashe ta ba kamar yadda ya saba, hakan ya sa ta ɗago da nufin ta ce mishi ta fasa binshi wajen party sai ta ga idanuwansa a kan ƙanwarta, wani irin janyo rigarsa ta yi ta ce “Ƙanwar tawa kake kallo bayan gani a gaban ka?”


Lumshe ido ya yi yana shafa sumarsa zuciyarsa sai ƙara ƙawata mishi surar Sidra take da yadda za ta dace da shi in suka jera, ajiyar zuciya ya sauke ya wani sha Kunu ya ce “Gaskiya na yi fartu Suby ƙanwarki nake so, ba kuma so na in ɗauke ta in kaita hotel mu Kwana ba a'a soyayya ta aure, tun ba yau ba na kamu da son ta haɗuwa ta da ita ta farko a hanya wajen wani abokina za ta sayi ruwa.”


Idanu Subaiwa ta zaro cike da tashin hankali tana kallon saurayin nata, a kiɗime ta ce “B.. Ba.. Ban gane me kake nufi ba babe?”

Hura mara iskar bakinsa ya yi ya miƙa mata ledar hannunsa ya ce “Abin da kunnenki ya ji waccan yarinyar ita nake son na aura, domin ita ce kalar macen da nake fatan ta zama matata na mata duk abin da take so, ke daga yau ma mu rabu na daina fita da ke tun da ƙanwarki zan aura sai an jima idan kuma za ki biyo ni mu je mu ɗan yi cilin ɗin ƙarshe to zo mu tafi, idan kuma ba ki so shi kenan dama ina da 'yan matan da zan tarba.” Yana gama maganarsa ya shige motarsa ya ja hayaƙi ya lulluɓe.



Tamkar Soja a fagen fareti haka Suwaiba ta ƙame idanuwanta a kan inda ya aje motar, ƙaran motar ne ya dawo da ita haiyacinta ta ɗora hannu a ka za ta sa kuka sai kuma ta fasa ta nufi gida a guje, hankalinta in ya yi dubu to yau ya tashi saboda duk samarin da take tarawa suke zuwa party da su babu wanda ya kai KB kashe mata kuɗi duk abin da take so shi yake mata, shi ne namijin da ta ci alwashin zaman aure da shi domin ta fantama ya kaita kasashen turai, sai ga shi ya ce ƙanwarta yake so ba ita ba..


A gigice ta faɗo ɗaki Inna ta firgita za ta ɓoye tana faɗin “Waiyo mun shiga uku me kika janyo mana Suwaiba?”


Zubewa ta yi a gaban Inna ta fashe da kuka ta ce “Inna ki taimake ni zan mutu KB zai rabu da ni.”


Cikin rashin fahimta Inna ta ruƙo ta tana faɗin “Waye kuma wani KB?”


“Saurayina wanda yake ba ni saƙo in kawo miki har yake saya mini kaya, wannan wanda ya saya mini iPhone shi ne yanzu ya zo yana jirana na fito wannan maiyar ta fita ya ganta, shi ne fa ya ce ai shi dama ita yake so tun haɗuwar su ta farko a kasuwa.” Nan dai ta kwashe labarin komai ta sanar da ita tana kuka wiwi, Inna ta kwashi salati tana tafa hannu ta ce “To shi in ban da masifa me ya gani a jikin waccan yarinyar ƴar ƙarama? To Wallahi ba za ta saɓu ba dole ma ya bar maganar Sidra, in dai ina raye ba ta isa ta fiki jin daɗin rayuwa ba zan yi maganin abin, yi shuru kin ji ƴar lele tashi ki gyara fuskarki ki tafi gidan ƙawar taki ni zan ji da komai, duk garin nan babu in da za a fara zuwa neman auren ta in ba nan ba, to zan ga ta yadda zai aure ta.” Ta faɗa tana ƙara rarrashin Suwaiba tare da mamakin me KB ya gani a tattare da Sidra wanda Suwaiba ba ta shi?

Da kyar ta shayo kanta ta wanke kwalliyar da ta yi ta sake wata sannan suka fita a tare ita ta yi gidan ƙawarta Inna ta nufi gidan Saude..


A bakin ƙofar shagon Audu ta tsaya tana kallon shi yana sallamar customers, gabaɗaya hankalinsa a kan ta yake sai sauri yake dan ya gama ya fito. Bayan ya gama ya fito yana faɗin “A a wai ƙanwata ke ba kya gajiya da talla ne? Ɗazu fa kusan La'asar kika tafi gida kuma yanzu ma ki fito?”

Dariya ta yi tana gaishe shi ya amsa sannan ta ce “To Yaya Audu ya zan yi in ban yi tallar ba? Babu inda ake barina na fita sai talla.”

Fuskantar ta ya yi ya haɗe fuska ya ce “Ƙanwata kina nufin ki ce yanzu zuwa school da Islamiyar ma waccan matar ta hana ki zuwa? To wai tsaya ma ina Baba yaje?”

Girgiza kai ta yi ta ɗago suka haɗa ido karaf ya ga kumatunta sun kumbura, matsowa ya yi kusa da ita ya kai hannu ya shafi kuncin yana faɗin “Lalalala ƙanwata waye ya mare ki haka har shatin yatsunsa suka fito miki a fuska ga shi nan ma ta kumbura?”


Shuru ta yi ba ta ce mishi komai ba sai ya fusata ya daka mata tsawar da ta sa ta miƙewa tsaye ya nuna mata in da ta tashi, “Dawo ki zauna uban waye ya mare ki ki faɗa mini?”

Ganin yadda ya birkice yana tambayar ta baki na rawa ta faɗa mishi dukan da Suwaiba ta mata, wani irin huci Audu yake ya dafe bancin da ƙarfi ran maza ya ɓaci, hannunta ya kamo ya dudduba ya ce “Tashi maza mu je asibiti a duba ki.”


A tsorace ta kalle shi ta ce “A'a ni dai ba na jin komai ka bari fuskar ma za ta huce.” Ta faɗa tana ƙoƙarin mayar da hawayen da suke shirin zubo mata.

Kankance idanu ya yi cike da masifa ya ce “Kin san Allah in ba ki tashi ba.”

Da sauri ta miƙe tsaye ya damƙi hannunta tana son kwacewa amma ta kasa, sakin ta ya yi ya amshe kayan tallar nata ya saka a shagon sannan ya kulle ya sake kuma ruƙon hannun ya soma jan ta.


Sidra dai ta rasa bakin magana yau Audu ya ba ta tsoro matuƙa, ganin ya ki sakin mata hannu ta ce “Yaya Audu to ka cika ni mana ba kyau fa ka riƙe hannuna.”

A fusace ya juyo ya ce “Na sani ai.”

Gum ta yi da bakinta tana bin shi tamkar rakumi da akala, ya tare musu adaidaita suka hau ya faɗa mishi in da za su.

A ƙofar wata kyamis suka tsaya ya ce mai adaidaita ya tsaya ya maida su ya amsa da to, suna isa aka zaunar da ita, da yake mace ce a kyamis ɗin sai da ta sa Audu ya fita waje ta sa Sidra ta cire kayan jikinta ta duba ko'ina na jikinta a gadon bayanta ne shatin bulala ya fito wajen har ya saɓe fata, bayan ta gama mata ta fiddo cream da magunguna ta aje sannan Audu ya shigo.

Ƙarin bayani ta nema ya faɗa mata ta nuna mishi maganin da za su saya da adaɗin kuɗin, a take ya ciro ya ba ta dubu bakwai ya amsa suka fito mai adaidaita a nan yana jiran su ya ɗauke su ya mayar da su.


Kayan tallar ya ba ta da farko ya ce ta tafi gida amma ta kafe fir ta ce ya bari ta je ta sayar, idan har ta je gida haka za a mata dukan da ya fi wannan yawa, ba dan ya so ba ya aje maganin ya barta ta tafi..



Inna na zuwa gidan Saude ta kwashe labarin abin da Suwaiba ta faɗa mata ta sanar da ita, kwafa Saude ta yi ta ce “Lokaci fa ya yi Binta da za ki yada ɗanyan mangwaro ki huta da ƙuda, na ba ki shawara tun wuri kafin wannan ranar ta zo amma kin ƙi bi kina wani nuƙu-nuƙu yanzu ga shi kin fara ganin abin da nake faɗa miki ko?”

Cike da yarda da maganar Saude Inna ta gyada kai ta ce “Wallahi sai yanzu na yarda da magamarki aminiya ga shi har ta fara yi wa Suwaiba kwacan saurayi, haka ɗan ƙanwata Iluwa ya dage kai da fata sai an aura mishi ita bayan mamansa ta ce mishi ya nemi Suwaiba tun da ya kama aiki amma fir ya ƙi yaron nan da yake shegiyar dangin mayu ce ta lashe mishi kuruwa, gaskiya yanzu na aminta zan yi abin da kika faɗa ko mun sakata mu wala ni da ɗiyata a gida, yo ina dalili ina mafari kullum da kalar masifar da za mu gani a kan wannan ƙoɗaɗɗiyar yarinyar.”

Wani kalar murmushi Saude ta yi ta shige ɗaki ba ta jima ba ta fito da wata takarda ta miƙa wa Inna, juya takardar Inna ta yi tana yi wa Saude kallon ƙarin bayani. Turo ɗankwali gaba Saude ta yi ta ce “Idan kin yarda za ki yi wannan abin to zan kira wannan number na ce komai ya kammala, dama tun tuni mun gama magana yardarki kawai nake buƙata ki ga aiki da cikawa.”

Baki Inna ta riƙe ta ɗaga kai sama alamar tunani hakan ya sa Saude ta ɓata rai ta ce “To meye kuma na tunani? Kinga in ba ki shirya ba na mayar da wannan takarda na aje, amma ki sani idan har kika bari wannan damar ta subce miki babu ruwana, ai da ni ce ke tun shekaru biyu baya zan gama da wannan matsalar.”

Haka dai ta dinga janyo ra'ayin Inna har Inna ta amince suka tafa sannan suka ɗore sabuwar hira suna yi suan shewa.








_Maman Nusaiba ce_