ZAWAJUL MUWADDA

Chapter 14

by @saratalkasum88

*ZAWAJUL MUWADDA*





_Sarat Alƙasum (Mom Nusy)_



*PAID BOOK ONLY N500*



*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION*



_My sister karki bari ayi tafiyar nan babu ke, domin salon na daban ne ya bamban da sauran littafan Maman Nusaiba da kika karanta a baya. A turo da kuɗin ta wannan account ɗin, account number 0003187186, Name account, khadija Salisu, Name Bank, Ja'iz Bank. Sai a yi screen shot a turo ta wannan whatsapp number +966577675904 ko da ƙarin bayani ake nema wannan number za ta bi sai kun zo_


*LAST FREE FAGES*



*SHAFI NA* 1️⃣4️⃣


Da wani kalar yanayi wanda ba ta taɓa jin ta shiga irin shi ba ta ɗago, wani irin abu take ji yana mamaye zuciyarta ta kasa ɗauke kanta daga kallon da take mishi, ba ta ankara ba sai ji ta yi ana share mata hawaye ta yi firgigit sai ta ganta daf da shi, numfashinsu na gauraya da juna hakan ya sa ta yi saurin lumshe ido sauran hawayen suka samu samar gangarowa.

“Didi me ya faru ?” Ya faɗa a sanyaye.

Girgiza mishi kai ta yi ta ja dogon numfashi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren jikinsa, sai da ya sake magana sannan ta ji bakinta zai iya furta magana, “Babu komai Uncle kawai dai naji daɗin ganin ka ne.”

Murmushin gefen baki ya yi ya juyo suka haɗa ido da Dr Abubakar, miƙewa ya yi yana danna waya ya ce “Friend ni zan wuce zan hau napep ina da aiki a asibiti za mu yi waya.”

Kafin ma ya ce wani abu sai jin shi ya yi a waje yana yi wa Baban Ummi sallama, jinjina kai ya yi ya kamo hannunta ya nuna mata ta matso kusa da shi ta zauna. Ba muso ta tashi ta zauna a gefen shi tana wasa da 'yan yatsun hannunta cike da jin kunya, wai yau ita ce zaune da namiji a kujera ɗaya? Ƴar dariya ta yi domin abin ya ba ta mamaki da al'ajabi, kallon ta ya yi ya ce “Didi za mu tafi na sayo miki kayan school a can kasuwar da kike zuwa.”

Zaro ido ta yi domin maganar ta zo mata a bazata, rausayar da kai ta yi ta ce “Uncle ni dai karka manta da ni idan ka tafi America, muna gani a waya idan ka saba da mutum da ya tafi wata ƙasar sai ya manta da kai.” Ta ƙarasa maganar hawaye masu zafi suka fara zarya kan kuncinta. A ruɗe ya ɗago da fuskarta cikin yanayin damuwa na ganin hawayenta, zuciyarsa na azalzalar shi yana jin kamar ya maida ta cikinsa su tafi tare, rasa abin da zai mata ya yi sai ya janyo ta ya rungume yana shafa bayanta.

Lamo ta yi a jikinsa tana jin yadda zuciyarsa ke mugun bugawa da sauri har sai da abin ya ba ta tsoro, a hankali ta ɗago ta kalle shi ya sa hannu ya goge mata hawayen, “Uncle ba ka da lafiya ne?” Ta yi magana tana nuna mishi saitin zuciyarsa. Lumshe ido ya yi ya ce “No ina lafiya, ki tashi ki je ki faɗa wa Mama sai mu tafi lokaci na tafiya kinga zan hau jirgin zuwa Legos.”

A hankali ta zare jikinta daga nashi ta koma gefe kanta a ƙasa ta ce “Uncle dama garinku Legos ne?”

Shuru ta ji bai ba ta amsa ba ta ɗago ta ga ita yake kallo, shagwaɓe fuska ta yi ta turo baki gaba tana faɗin “To ni dai nama na ɗaci gareshi kamar maɗaci.”

Murmushi ya yi ya ja hancinta ta buge hannunsa sai ga hawaye, dariya ta ba shi ya ce “Raguwa kawai ɗan taɓa hancin da na yi shi ne kika fara kuka?”

“To ai da zafi.” Ta faɗa tana juya mishi baya alamar ta yi fushi.

Haƙuri ya ba ta amma ta ƙi juyowa tana cewa “Hmm in da kai ne aka yi wa sai ka yi kuka sosai.”

Sai da ta ƙi haƙura ya ce ta rama sai su tafi, juyowa ta yi tana dariya ta ce “Na haƙura bari naje na faɗa wa Mama idan ta yarda mu tafi, idan ba ta yarda ba sai dai ka je kai ɗaya.”

To ya ce mata ta fita da sauri tana kiran Maman Ummi, da kallo ya bi ta yana mamakin yadda ko'ina na jikinta yake tafiya da shi. Ba ta jima ba ta dawo tare da Safwan ta ce “Mama ta ce kar mu jima da mun je mu dawo.”

Tashi ya yi ya yi gaba suka bi bayan shi, Maman Ummi ta fito ta ce “Ku tafi da Abbansu mana.”

David dai ya gane ɗar-ɗar suke yi da shi shi ya sa, jinjina kai ya yi ya ce “Mama ki kwantar da hankali naki babu abin da zai faru, yadda na ɗauke su haka zan dawo da su lafiya.”

A sanyaye ta kalli Baban Ummi ta mishi alama da su koma ciki, sai da ya shige ta juyo ta ce “Na yarda da kai ranka ya daɗe kana da kirki, nasan babu abin da zai faru da su da yardar Allah, amma ka ga tafiya da babba ya fi duk abin za a yi a gaban shi ne saboda gudun maganar yan unguwa, amma babu komai ku tafi.”

Godiya ya mata ya kama hanun Safwan da Sidra suka wuce Ummi ta ce ba za ta bi su ba sai sun dawo, murmushi ya yi ya buɗe musu mota suka shiga ya su suka wuce..


Ba su yi nisa sosai ba ya ji motar tana wani irin kuka, a hanzarce ya yi packing a gefe hanya ya fito ya buɗe, dudduba ta ya fara yi nan ya gano man ne babu. Bayan motar ya buɗe domin ya ɗauki man amma ya ga wayam ba komai, duddubawa ya yi gefen shi gaba da baya ya ga babu wani gidan mai da yake kusa da su, dafe kai ya yi ya lalibo number Sayyid ransa a dagule ya danna mishi kira. Yana ɗauka ya ce “Sayyid ya aka yi na aje mai mai yawa a cikin motar nan amma yanzu na duba na ga babu? Kuma ga shi man ya ƙare ina tsaka da tafiya.”

Sautin dariyarsa ya ji ransa ya ɓaci sai ya katse kiran yana jan tsaki, galam ɗin man ya ɗauka ya zo saitin su Sidra ya ce “Didi ku zauna zan ɗan duba nan gaba kaɗan na gani ko zan samu mai sayar da mai na sayo, kar ku je ko'ina fa.”

Murmushi ta mishi ta amsa da to sannan ya tafi, ganin ya yi nisa sai ta buɗe ta fito ita da Safwan tana kallon hanyar ta ta zuwa Kwari, Safwan ya ce “Anty gaskiya motarsa akwai daɗi har da sanyi.”

Dariya ta yi ta ce “To kai dama ba ka taɓa hawa mota ba?”

Gaba kaɗan ya yi ya samu waje ya zauna itama ta zauna suka fara hira..


Ɗan'ado ne tare da tawagar shi daga can gefen su Sidra suna ta chakewa, ɗaya daga cikinsu ne ya hango su Sidra ya yi ashar yana layi ya ce “Kai oga ga fa can yarinyar da muke nema ita da ƙanenta a zaune gindin wata mota.”

Zabga mishi mari Ɗan'ado ya yi suka tafi luu a tare suka zube ƙasa, da kyar Ɗan'ado ya tashi saboda duk cikinsu ya fi kowa chakewa. Damƙar shi ya yi ya ce “Kasan dai ba na son eh rainin hankali, waye zai ba ta mota?”

Dariya ya yi ya nuna mishi da hannu, murza ido ya yi yana ƙoƙarin tsayawa da ƙafafuwansa, ita ce dai ya gani hakan ya sa ya sheƙe da dariya ya ce “Kai Horo ɗan zabga mini mari masu ƙarfi mana.” Ya faɗa yana isowa gaban Horo da ke zaune gefe ya soke addarsa a ƙasa yana kallon su shi bai sha komai ba. Tashi tsaye ya yi yana hura hanci dama yana jin haushin Ogan nasu da ya ci zalinsu jiya, sai da ya taƙarƙare ya zabga mishi mari, kafin ya ɗago ya sake mishi wani a ɗayan kumatun. Ɗan'ado da ya ji mari ya shige shi sai ga shi ya wartsake yana faɗin “Kan bala'i! Amma Horo ka iya mari.”

Dariya ya yi ya koma ya zauna shi kuma ya lalibo wani shirami wanda ya saka wannan leda da Suwaiba ta ba shi, kullum da ita yake yawo saboda gudun saɓani a cewar shi su haɗu da Sidra kuma ba shi da abin da zai mata. Buɗewa ya yi ya fito da ledar ya dubi Horo ya ce “Maza ku je ku kamo mini ita a kaita wancan kangon da muka saba zama, yau ina so zan huta na sarara da ita idan na gama kuma sai ku zo.”

Dariya suka sa kowa yana marisa Horo ne kaɗai a daidai suka nufe ta, suna tsallaka hanya wasu suka biyo ta bayan motar wasu kuma ta gaban motar dan kar ma ta subce musu.

Sidra na zaune sai ganin maza ta yi a kanta a tsaye ɗaya daga cikinsu na ƙoƙarin faɗowa kanta, a firgice ta miƙe tana rawar jiki ta kama Safwan ta riƙe tana kallon su.

“Ke fice mu tafi kafin na miki ɗaukan amarya.”

Cewar na hannun damar Ɗan'ado yana nuna mata hanya.

Ganin suna layi sai ta ja da baya ta ƙara rike hannun Safwan ta ji ta yi karo da wani abu, a mugun firgice ta juyo nan ma ta ga wasu mazan ne guda biyu, hanya suka nuna mata suna ba ta umarnin ta wuce su tafi, sai a lokacin ta tuna da David ya ce karsu kuskura su fito waje, baki na rawa ta ce. “Don Allah me na muku?”

Dariya suka sa suna nuna ta da hannu, cikin azama ta shamamce su hangaza biyun da ke gaban ta ta kwasa a guje suka bi hanyar da David ya bi, rufa mata baya suka yi wasu na faduwa wasu kuma suka tsaya suna haki kamar sun jima suna gudu..

Sai da suka yi nisa da su ta juya ta ga ba sa bin ta ta juyo tana huci, sosai zuciyarta ke bugawa da mugun gudu har sai da ta sa hannu ta dafe ƙirji, buɗe idon da za ta yi ta ga ƙafafuwansa a kusan nata ta ɗago da sauri, ganin shi ne ta ruƙo hannunsa tana nuna mishi bayan su.

Da mamaki yake kallon ta amma bai ce mata komai ba ya kama ta Safwan ya riƙe hannunta suka dawo.

Ko da suka dawo ba su gs kowa ba a wajen ta kalli inda suka zauna da mamaki, man ya zuba zuciyarsa sam ta kasa nutsuwa har ya gama ya rufe motar, buɗe musu ya yi suka shiga..


Tun da suka hau kan titi ya ga wata jar mota na biye da su duk inda suka bi, da hannu ɗaya ya ɗauko glass ɗinsa ya manna can jikin hannun glass ɗin ya danna, wani blue ɗin haske ne ɗan kaɗan ya baiyana. Wata ƴar farar barima ya ɗauka ya maƙala a kunne itama ta kawo haske, jinjina kai ya yi ya ɗauki wayarsa sai ya rage gudu yana tafiya a hankali, still dai ya ga motar na biye da shi.

“Mati ka faɗa wa jakunan yaranka bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne, Mikiya ce a gaban su ba zomo ba, zan iya yin komai domin kiyaye lafiyar abar ƙaunata. Idan kuma ka ƙi ji za ka gani da idanuwanka zan yi abin da na saba yi, ka sanni farin sani Mati.” Ya faɗa cikin wani irin voice wanda ya fito da asalin fusatar da take zuciyarsa.


Dariya na cikin wayar ya yi ya ce “Mikiya ai ni yanzu tun da aka mana tsakani na daina bibiyar duk abin da ya shafe ka, amma fa ka sani maza bisa kanka ni ba sa'anka ba ne sai dai na yi da Mr Obinna shi ne daidai da ni, sannan da kake maganar wai za ka yi abin da ka saba ina jira na ga me za ka yi. Na ga kana son saka ɗiyar mutane a cikin musiba, yarena ƴar jahata kuma ƴar garina dole na ɗauki mataki a kanka, idan kuma ka yi taurin kai ka nuna ba za ka rabu da ita ba to zan sheƙe ta na kashe banza. Na kara da ubanka ma bai ji daɗi ba ballantana kai ɗan ƙaramin alhaki, very soon zan shafe tarihinka daga kai har wannan twin brother ɗin naka sai mu ga ta tsiya, sannan ka tuna ajiyarka da ke America Kalma ɗaya tak zan faɗa a tarwatsa wannan ajiyar da ba ka son kowa ya ji, zan kuma fasa kwai mai mugun wari da ɗoyi wanda zai hana ka bacci, ba kai kaɗai ba har da ubanka sai warin ya sa zuciyarsa ta buga ya mutu a take, idan kuma kana ganin har yanzu ni sa'anka ne ka koma gida ka tambayi Obinna waye Mati ? Sannan ka faɗa masa na ce zan fasa kwai, idan har ba ka ga tashin hankali a idanuwansa ba na maka alƙawari zan ba ka dukkan abin da yake naka ne a wajena.”


Wani iri David ya ji kalaman Mati suka saka shi, wasiwasi ya fara yana tambayar kansa to meye tsakanin Dad da Mati? Tsaki ya ja domin ya san waye Amti ciki da waje, zai iya komai domin ya cimma burinsa hakan ya sa ya saki murmushin da shi kaɗai ya bar wa kansa sani.

Juyawa ya yi ya ga duk sun yi bacci hakan ya mishi daɗi dan ba ya son su ji abin da yake faɗa, duk da kuwa yasan wani yaren ba fahimta za su yi ba.

“Idan ka kara da Dad ka yi nasara a kansa to ka sani ni ba shi ba ne, ka kiyayi ranar da za ka ganni eyes to eyes a gaban ka, ina me tabbatar maka zan yi aika-aika wa rayuwarka matuƙar ka ce za ka taɓa lafiyar masoyiyata ko kuma familyna, idan kuma ka ga za ka iya to ga guri nan ka taɓa lafiyar Didi ka ga aiki da cikawa, da fatan ba ka manta waɗannan kyawawa yaran naka mafi soyuwa a zuciyarka suna can America ba ko?”


Saurin katse shi Mati ya ce “Kar...”

Katse kiran ya yi yana murmushi ya ci gaba da tafiya, yana gaf da shiga kasuwar ya sake kallon bayan shi ta madubi sai ya ga sun daina bin shi, ƴar dariya ya yi yana jinjina kai..

Suna isa ya tashe su ya fito ya buɗe musu suka fito, kantin wani ɗan garinsu ya nufa in da ya tarbe shi cikin farin cikin ganin shi.

“Oga David yau kaine a shagon namuwo?” Ya faɗa yana kallon Sidra da ta manne a jikinsa gara ma Safwan shi gaba ya yi ya shige cikin kantin wajen kayan wasa.

Murmushi ya yi ya ba shi hannu duka gaisa, bayanin abubuwan da yake buƙata ya mishi shi kuma ya kira yaransa duk suka ɗauko mishi, bayan ya gama sa mishi a leda ya kasa haƙuri ya ce “Oga David Who is she?”

Haɗe fuska ya yi sai ga Safwan ya dawo riƙe da kwallo da wani ɗan jirgin wasa da takalmi fuskarsa cike da annuri ya zube su a gaban David, da murnar shi ya ce “Uncle don Allah ka saya mini wannan kayan wasan ina sonshi, Baba ya ce zai kawo mini daga Benin amma har yau bai dawo ba.”

Shafa kansa ya yi ya ce “Karka damu duk abin da kake so zan saya maka, ka je ka ɗauko harda kayan sawa da takalma da komai da kake so.”

Tsallen murna ya yi ya rungume David ya ce “To Uncle dama ba ni da takalmi da kayan sawa duka kala huɗu ne sai na school, Uncle in ɗauko har jakar makaranta?”

Jinjina mishi kai ya yi ya tafi da sauri. Mai kantin ya ce wa ɗaya daga cikinsu ya bi shi ya ɗauko mishi duk abin da ya nuna yana so..

Bayan ya tafi David ya canja harshe zuwa yarensu na yarabawa, in da yake sanar da abokin nasa matsayin Sidra a gareshi. Zaaro ido ya yi David ya jinjina mishi kai alamar tabbarwa sannan ya ɗora da cewa “Zan bar komai a hannunka lokaci zuwa lokaci kake bincika mini lafiyarta, tana zuwa har nan talla da ta zo ka lura da ita. Bayani sosai ya mishi da duk wani abu da ya tsara wa rayuwar Sidra, sosai ya ji daɗi.

Bayan sun gama komai ya biya kuɗin suka tafi.


Sai da ya kaisu har Ƙofar gida ya fito musu da kayan, Safwan da gudu ya faɗa gidan yana kiran ƙanen Ummi. Sosai Maman Ummi ta yi mamakin kayan da ya sayo wa Sidra har da na Ummi, haka ta leƙa ta mishi godiya suna tsaye da Sidra.

Narke mishi ta yi kamar za ta bi shi take ji, da kyar ya rarrashe ta ya tabbatar mata da za su yi waya da zarar ya sauka, tana kuka ta ƙara riƙe hannunsa gani take kamar in ya tafi ba zai sake dawowa ba.


“Uncle ni dai idan ka je karka manta da mu, bayan su Mama ban taɓa jin na damu da wani ba sai kai, jikina yana ba ni kamar za ka gujeni ko ka ce ma ba ka sanni ba idan ka haɗu da yan matan can farare masu kyau.” Ta ƙarasa maganar tana sakin samun kuka marar sauti.

Hannunta ya kama ya buɗe mota suka shiga baya, zuciyarsa na mishi wani irin nauyi ya ɗago fuskarta, ji yake kamar shima ya yi kukan ko zai samu sauƙin abin da yake ji, ajiyar zuciya ya sauke ya share mata hawayen murya a shaƙe ya ce “Didin Uncle kin san yadda nake kinji a zuciyata? Ke ɗin ta daban ce a cikin mata Didi, I love you so much, ba zan taɓa manta ki ba har abada matuƙar ina numfashi, idan na samu yadda nake so zan dawo bayan one months na ganki, zan nema miki gurbin karatu a can America kinga kin dawo kusa da ni ko?”

Shuru ta yi tana nanata kalmar I love you a zuciyarta, duk da ba yau ba ta fara jin an ce ana sonta amma tashi kalmar sai ta ji ta har ƙasan zuciyarta. Hannunta da ke cikin nasa ya ɗan murza a hankali ya ce “Didi.”

Ɗago kai ta yi suka haɗa ido ta yi saurin sunkuyar da nata, yau sai ta ji ta ƙara jin kunyar shi fiye da kowacce rana.

“Didi do you love me?”

Fuska ta rufe tana murmushi hakan ya sa yin dariyar farin ciki, amma dai ransa ba daɗi. Haka ya samu dai ya lallaɓa ya raka ta har baƙin ƙofa ta ce ba za ta tafi ba sai dai shi ya fara tafiya, murmushi ya yi ya shiga mota yana ɗaga mata hannu itama ɗaga mishi sai da ta ga ya ɓace wa ganin ta sannan ta koma ciki.


Ko da ya shiga kama hanya daret Airport ya nufa gabaɗaya ransa a jagule, ba ya son tafiya ya barta a wannan yanayin amma babu yadda zai iya tafiyar ta zame mishi dole, wayarsa ce ta ɗauki ringing ya duba ya ga Mariam ce, da kamar ba zai ɗauka ba sai ya tuna da sakon jiya da dare ya yi saurin yin picking. Bai ce komai sai jin sautin kukan ta ya yi a daidai lokacin da ya ƙaraso airport, sai da ya gama packing sannan ya nisa gabaɗaya duk gwiwarsa ta sage, da wani irin yanayi mai ɗauke da damuwowi ya ce “Mariam what's wrong?”

Daina kukan ta yi yana ji tana sauke ajiyar zuciya sai kallon lokaci yake saura minti ashirin jirginsu ya sauka.

“Yaushe za ka dawo?”

Nannanuyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce “Gaskiya zan jima kafin na diro Nigeria, ba zan samu damar zuwa wajen aurenmu ba sai dai ku yi bikinku sai ki hayo jirgi ki zo nan.”

Sake sakin sabon kuka ta yi tana faɗin “Why my love? Auren namu ne ba za ka zo ba ayi komai da kai? Gaskiya ni ban yarda ba wannan ai zubar da kima ne a idon jama'a sai su ɗauka ma ba ka sona auren dole ne za a maka da ni, ban san me ya same ka ba kwanan nan idan na tambaye ka idan har ba ka sona please ka sanar da ni babu takura zan haƙura da kai, ni na fi son na auri wanda nake so kuma yake sona domin mu zauna lafiya, amma kai na kasa gane inda ka dosa sai kake yin abu kamar ina takura maka. Ka faɗa mini idan ba ka son aure zan haƙura da kai, kuma ni zan faɗa musu ba kai nake ba ka ga su Mom ba za su ga lefinka ba. Ita wadda kake so ɗin ka san dai is not easy ta karɓi soyayyarka ko?”

Lumshe ido ya yi yana jin babu daɗi, tabbas gaskiya ta faɗa amma dai ba zai bari a samu matsala ba game da auren su, sannan yana da yaƙini Didinsa tana matuƙar sonshi tun da ta nuna damuwarta a kan tafiyar da zai yi, baya ya yi ya jingina da kujera ya ce “Sweetheart don't worry please, na faɗa miki ina matuƙar sonki kuma aure za mu yi ki haifa mana yara masu kama da ke, tun da dole sai kun yi taro zan kutsa na zo a kan lokaci da an gama sai mu dawo tare hakan ya miki?”

Sautin murmushin ta ya ji hakan ya sa ya ji sanyi a ransa ko ba komai ita ɗin jininsa ce ƙanwarsa, fita ya yi daga motar ya ce “To yanzu zan wuce idan mun sauka Legos ba zan je gida ba wucewa zan yi, idan na je za mu yi waya sai ki faɗa mini duk abin da kike so mu yi a bikin.”

Yana ji ta yi tsallan murna tana dariya ta ce “Thank you very much My bloody, sai ka sauka love you.”

Murmushi ya yi ya ce “Love you too Sweetheart bye.” Ya kashe kiran yana bin hanyar shiga cikin airport ɗin.

Sai da ya shiga jirgi ya zauna sannan ya yi wa Abubakar text message ya zo ya ɗauki mota ya mayar da ita gida, sannan ya ƙara jaddada mishi da ranar Monday ya tabbatar ya kai Sidra da Safwan sabuwar School ɗin da ya saka su, ya kuma dinga ziyartar su akai-akai. Sai da jirgin ya tashi suka fara tafiya a sararin samaniya ya kalli ƙasa daga tagar jirgin, ji yake duk wani farin cikinsa ya bar shi a Kano..



Ranar Sidra wuni suka yi ana gwada kaya ita da su Ummi, sai da yamma ta haɗa kayan ta aje a nan ta ce ba za su kai gida ba a aje musu shi har na school ɗin, Maman Ummi ta adana kayan ta zuba musu abinci cikin leda dan kar Inna ta gani ta ce su ɓoye in sun shiga ɗaki su ci suka amsa da to.



Ko da suka je gidan sun samu gidan wayam ba kowa, Sidra ta leƙa ɗakin Inna ta ga a ƙulle ta duba ko'ina ta ga ba sa nan sai ta ja Safwan suka shige ɗaki. Har bayan isha'i ba su dawo ba sai abin ya ba wa Sidra tsoro suka fito tsakar gida suka zauna, suna nan zaune har kusan shaɗaya sai ga Inna ta shigo gidan tana surutai, Sidra ta miƙe tsaye tana kallon Inna da murmushi kan fuskarta ta ce “Inna sannu da zuwa, wai ina kika je babu kowa har Suwaiba ma ba ta dawo ba, ga shi ban ga kayan tallar ba sai muka zauna.”

Ba ta bata amsa ba sai da ta buɗe ɗaki ta fiddo tabarma ta shinfiɗa sannan ta kalle su tana dariya ta ce “Kayya yaran nan! Ai biki na tafi can ƙanwar Aminiya ta haihu shi ne muka tafi, yanzun ma gajiya na yi na ce ni na taho kawai ku zo ga shinkafa da miya mai daɗi ku ci, wannan har da safe ma zan ɗumama mana mu ci ba sai kin yi mana girki ba.”

Wani sanyi Sidra ta ji yau dai ba a hantare su ba suka zauna a gaban ta, faranti mai girma ta sa Safwan ya ɗauko ta zuba ta ce su sa su ci har ita, mamaki ya ƙara kashe Sidra amma ta kawar kar ta yi abin da 'yan kirkin na Inna za su tafi marassa mutumci su zo. Bayan sun gama ta ce su je su kwanta Sidra ta ce “Inna ki tashe ni da wuri kafin ki gama komai kin ce gobe da safe koko da ƙosai za ki mini na fidda.”

“A'a ɗiyar nan ai na hutar da ke ba zan iya yi ba da safe, gobe tare za mu tafi gidan sunan idan muka wuni sai mu dawo.”

Baki Sidra ta saki kamar wata sakarya tana bin Inna da kallo har ta shige ɗaki, kama hannun Safwan ta yi suka shiga ɗakinsu. Ba su jima ba zafi ya hana su kwanciya ta fiddo musu tabarma suka, kwanta a waje..



Kamar yadda Inna ta faɗa ƙarfe tara na bugawa ta sa Sidra ta yi wanka har da hoda ta ce ta shafa, ita dai Sidra lamarin na Inna gani take ko dai aljannu ne masu tausayi suka shiga jikin Inna? Haka ta sa hoda kaɗan ta sa kwalli duk da ba a cikin nutsuwa take ba amma ta yi kyau sosai, ta saka dinkinta na Sallah ta sa hijabi Inna ta ce ta sa mayafi sai dai kuma ya yi dauɗa, haka ta ɗauko mata na Suwaiba sabo dal ta ce “Sa wannan kinga cikin mutane za mu shiga ba na so a ganki da datti sai naji kunya.”

Murmushi Sidra ta yi ta amsa ta ce su fita kofar gida ga ta nan fita suka amsa da to, sai da ta kira Saude tana ɗauka ta ce “Aminiya gamu nan za mu fito fa karki ɓata mana lokaci.”

Dariya Saude ta yi ta ce “Haba dai ai ni zan jira ku mu haɗe a bakin hanya.”

To Inna ta ce sannan ta fito.


Tafiya suka yi mai ɗan nisa Sidra ta ga ba hanyar gidan Saude ba ce ta ce “Inna gidan mai haihuwar za mu je?”

“Eh mana can za mu tafi.”

Daga haka ba ta sake cewa komai tana riƙe da hannun Safwan, Unguwar sabuwa ce babu mutane sosai Sidra tana ta kallon wajen domin ba ta taɓa zuwa ba. Ƙaran motoci suka sa Inna ta juyo da sauri sai gani ta yi mota biyu baƙaƙe sun baɗe su da ƙura, kasa ganin gaban ta ta yi tana faɗin “Safwan, Sidra ku kawo hannunku wannan irin ɗiyan masu kuɗin nan ne da suke wulaƙanta mutane a hanya.” Ta faɗa tana miƙa musu hannu.

Ihun Sidra ta ji da Safwan suna kiran sunanta “Waiyo Inna an riƙe mu ana ja, Innaaaa!”

Suka kira sunan da ƙarfi daga haka ta ji ɗif ba kowa, ita kanta bibbiyu ta fara gani.

Sai da ƙurarta lafa ta dudduba ta ga babu su sai ledar da ta ba wa Sidra ta gani t

Da takalmansu har da mayafin da ta ba ta, wata irin kururuwa Inna ta yi tana salati tana faɗin “Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Jama'a an sace mini yarana ku taimake ni ɗiyan amana ne.”

Mutanen unguwa wasu duk suka fito daga gidajensu aka yo kan Inna ta firgice sai kuka take tana nuna musu takalman su Sidra, wata mata ta tashe ta ta ce su tafi police station su sanar da su. A rude Inna ta miƙe tana sumbatu da kyar matar ta ja ta suka tafi.....






*To fa wasa farin girki! shin su waye suka ɗauki Sidra da Safwan? Wani hali David zai shiga idan ya ji labari? Wani hali mahaifin su Sidra zai shiga idan ya ji an ɗauke yaransa? Wata amsa Inna za ta ba wa Baban su Sidra idan ya dawo?*


_Duka wannan amsoshin sai ku biyo Anty Sarat domin jim yadda za ta kaya. Karku manta littafi only N500 ne hajiyata karki bari ayi tafiyar nan babu ke.._


*Za ku turo kuɗinku ta wannan account ɗin account number 0003187186, name account, khadija Salisu, Name Bank, Ja'iz Bank. Sai ya yo screen shot a turo ta wannan whatsapp ɗin +966577675904*




_Maman Nusaiba ce_