14
by @autarmanya
*SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*14*
Ya lumshe idanunsa yana fesar da Numfashi ƙasa ƙasa Sautin Kukan Ya Minau na ratsa dodon Kunnen shi, Kafin ya ɗago da idanun nashi ya dire kallon shi akan Innah wadda tai tagumi tare da zubawa Ya Minau Ido takaici da tarin damuwa ne bayyane a saman fuskarta.
Tsaki Aunty Nafi taja tana cewa.
"Haba Yaya gaskiya a sake tunani danni kam banga alfanun wannan aure ba, kowa ni ɗa namiji yana fatan samun macen ƙwarai wadda ta fito daga gidan martaba amman wannan kam mahaifiyar yarinyar nan ba ƴar mafuta bace"
Cikin damuwa Innah ta dubi Ya Minau tana cewa.
"To yaya zamuyi wannan ƴar, Babanku ya kafe akan ayi auren nan ni kaina ba so nake ba sabida Maryam ba ƙaunata take ba to abin ne yafi ƙarfina dole na tattara na zubawa sarautar Allah ido duk abin da Allah yayi akai daidai ne"
Faridah ma mita take Aunty Hajjo kam ta kasa magana sai faman Jijjiga ƙafa take duk irin wahalar da suka sha wajan haɗa lefen nan amman wannan cin zarafin ne zai biyo baya.
In kujerar daya ke kai tai motsi to Saadik yayi motsi acikin maganar su, sai dai zuciyar shi ƙunci ne tare da tarin damuwa haka ya cigaba da wanke takalmin shi ya kaɗe ruwan ciki ya jingine a jikin bango ya miƙe yabar Musu tsakar Gidan to shi mai zai ce, bayan duk Babane yaja musu da bai karɓi tayin ubanta ba da wannan tozarcin bai faru a gare suba.
Ɗaki yaje ya shirya cikin Jc jajaye wandon iya gwiwar shi sai farar safar ƙafa sai farin takalmin Ball ya fito bai ma shiga gidan ba ya wuce filin ball cikin son kau da damuwar daya bar ƴan uwan shi suka fara buga ƙwallo.
Da ƙyar innah ta rarrashi ya minau sabida dama itace babba amman tafi ƴan uwan sanyin zuciya da rauni har magariba suna gida suna jira shigowar Baba ganin bai shigo ba har bayan sallar yasa suka tattara suka wuce gidajen su duk rai babu daɗi.
Sai bayan sallar isha'i baba ya shigo gida sam innah batai masa maganar ba har sai da yaci abinci ya zauna a tsakar gida yana sauraron labarai a Radio.
Innah ta aje masa kofin Furar data damo masa.
Ya dube ta tare da cewa.
"Hafsatu mai yake damunki ne? gaba ɗaya tinda na shigo gidan nan na fuskanci yanayin ki ba daɗi"
Innah ta rausayar da kanta gefe cike da zurfin ciki tare da danne abin da ke cin ƙasan ranta tace.
"Babu komai Babansu ga furar nan ko sai anjima zaka sha?"
Baba ya fuskance ta.
"Haba Hafsatu bafa yau na sanki ba, wallahi shiyasa inna ga Sadauki ya ɓoyen abin da ke damun shi nakan ce barewa batai gudu ɗanta yayi rarrafe ba, yanzu dai faɗa mini mai ke damun ki?"
Ya faɗa yana maida hankalin shi kaco kam izuwa gareta.
"To inda hali Babansu ina neman alfarma da abar batun haɗa sadauki da wannan yarinya ƴar wajan Amadu wallahi abin babu arziƙi sam kai kaga cin zarafin da maryam taiwa yaran nan yau haba talauci hauka ne shima baya so nima bana so dama dannewa nake kuma nike tausar shi akan auren"
Ta faɗa tana haɗe fuska.
Baba yayi dariya.
"Ikon Allah wato ku dai mata bakwa rabo da cece kuce, To yanzu so kike na zama ƙaramin Mutum ɗan uwana ya bani kyauta nace bana so kome?"
Innah ta kuma haɗe fuska cikin rashin sukuni tace.
"Tinda abin ba daraja ba martaba a haƙura kawai"
Baba ya kama haɓa.
"Haba Hafsatu shifa shaiɗan baya son ƙulla alheri gaba ɗaya bamu san mai ke tattare da wannan aure nasu ba"
Cikin zafin da bai santa da shi ba tace,,,
"Meye acikin auren in ba ta shin hankali ba........
Da sauri yace.
"Kefa uwa ce Hafsatu kada kiwa auren nan mugun baki"
Lokacin hawaye ya fara sauka daga saman fuskar Innah abin da yayi matiƙar ɗagawa Baba hankali kenan cikin kuka! tace.
"Shekaru Kusan Arba'in muna tare da kai Muhammadu baka taɓa saka doka na karya maka ba baka taɓa zuwa da abu na musa maka ba amman don Allah ka janye auren Sadauki da wannan yarinya tinda shima ba sonta yake yi ba kawai biyayya ce yake yi maka"
A ɗan fusace Baba yace.
"Sabida bakya ƙaunar Jinina Haɗin zumuncin ne bakya so shikenan zan gani tsakanin ni da ke waye zaifi rinjaye akan wannan lamari"
Da sauri tace.
"Kai ne zakai rinjaye"
Ta faɗa tana goge hawayenta.
Lokacin Saadik ya shigo gidan wanda sauran ƙarashen maganar ta sauka a cikin kunnen shi.
Ya nemi guri a bakin Ƙofar Kitchen ya zauna ya tsirawa Innah ido wanda idan idon nashi bai masa gizo ba hawaye yake gani a saman fuskar Mahaifiyar tashi.
Baba miƙewa yayi cikin fushi yama fice daga gidan gaba ɗaya.
A hankali Innah ta ɗago tana cewa.
"Kaga ni ko sadauki wallahi bana son auren nan bana so bana so!
Kalmar data firgita Saadik ta hargitsa masa zuciyar shi kenan.
Hannun shi biyu ya saka ya rufe fuskar shi yana jan numfashi gaba ɗaya Jikinsa rawa yake hankalin shi yayi mugun tashi.
Ya kai minti goma a haka kafin ya ɗago manyan idanunshi waɗanda suka sauya launi zuwa jajir ya zubawa Innah yana fesar da Huci zazzafa.
Muryar shi a raunane ya ce mata.
"Haƙiƙa innah nafiki tsanar wannan aure wallahi innah nima bana son shi bana ƙaunar shi ban san meye yasa Baba ya kafe ba"
Sauran maganar ta maƙale masa sabida Jin muryar Baba akan shi.
"Idan ka auri Rabi'atu ka saka wuƙa ka yankanta Abubakar Saadik! daga nan zan san kai cikakken maƙiyinta ne kuma zanyi maganin ku daga kai har uwar taka tinda naga abin babu arziƙi"
Gaba ɗaya Baba ya birkice musu kamar ba shiba faɗa yake ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba seda yayi wa Innah da Saadik kaca kaca sannan ya sa kai ya shige ɗaki.
Innah ta zabga tagumi shiko Saadik ta shi yayi yana rangaji yabar tsakar gidan.
Ya shiga cikin yanayi marar daɗi ranar sai bacci ɓarawo a idanunshi amman duk juyi fushin mahaifin shi da ɓacin ran mahaifiyar shi akan auren yake haskowa.
Shi baba idanunshi ya rufe ne akan haɗin zumunci ita kuma innah cin zarafin da akaiwa ƴaƴanta ke cin ranta har taji ta tsani auren.
Zaɓin wa zaibi?
Daya gaji da juyi, sai ya miƙe ya shiga toilet ya ɗaura alwala ya shiga jera sallah yana faɗawa ALLAH damuwar shi yaji daɗin zuciyar shi yaci kashi casa'in da tara na daga cikin damuwar shi ta kau dalilin daya sa har ya sami bacci mai nauyi wanda ya kusan makara a sallar asubahi agurguje yayi wanka yayi alwala ya fita masallaci yana idar da raka'atul fijir liman ya tada Iƙamar sallah ya maida ajiyar zuciya Allah ya taimakeshi ya samu raka'atul fijir ɗin, ba a tada ba hakan yabi sahun sallar bayan sun idar ya zauna yayi azkar sannan ya fito cikin gida ya shiga ya gaida Baba wanda ya amsa mai gaisuwar da ƙyar sannan ya ƙarasa wajan Innah dake damun koko a kitchen ya tsugunna ya gaishe da ita.
Yana saka hannu yana tura mata wutar ɗumamen tuwon data ɗora.
Cikin kwantar da murya yace.
"Don Allah don Annabi Innah ki bar sanya damuwar auren nan aranki nina barwa Allah komai kuma wallahi tinda na barwa Allah in har auren nan babu alkairi rushewa zai yi"
Innah ta maida ajiyar zuciya.
"Sadauki haƙiƙa cin zarafin da maryam taiwa yarannan ya ɗagan hankali da shi na kwana ga ɓacin ran mahaifinka amman tinda ka ambaci Allah magana ta ƙare nima zan cigaba da addu'a akai"
Ya lumshe idon shi dayay masa nauyi ya warasu akanta yana cin tsananin damuwar daya gani a tare da ita.
A hankali yake kwantar mata da hankali harta sake.
Don ya ƙara kwantar da hankalinta yasha kokon yaci ɗumamen tuwon da farar safiyar duk da bai kari a wannan lokacin.
Sannan yayi mata sallama ya tafi ɗaki agurguje ya shirya ya fita kasuwar ƙofar ruwa.
Don kai kaya.
***********
Momi ta sheƙe da dariya tana cewa.
"Tsinannu gayyar tsiya ai nice maganin ku"
Ko kallon kayan batai ba ta barsu a wurin.
Ita kam adaah bata ma san wainar da ake toyawa ba tana can ɗakinta tana kukan takaici.
Abbah da magariba ya shigo gida yadda yaga kayan ne ya bashi tabbacin masu kawo kayan basu sami tarbar arziƙi ba.
Aiko tindaga parlour yake kiran Momi ranar taga tijara domin cewa yayi akan auren zai iya sakinta.
Data ga ba haza shine tahau bashi haƙuri.
Ranar Abbah yayi kwanan takaici washe gari wajan ƙarfe goma ya dira agidan Baba.
Lokacin Baba yana ƙoƙarin fita kasuwa Abba ya ƙaraso haka suka juya cikin gidan haƙuri Abba ya dinga bawa Baba duk da bai da tabbas na abin da Momi taiwa masu kawo lefen amman ya tabbata bata shuka abin kirki ba musamman daya kira Iyah mahaifiyarta tace sam Momi bata faɗa musu maganar kawo kayan lefen ba.
Baba ya dubi Abba yace.
"Amadu wannan ban haƙuri da kake kamar nace maka Sadauki ba zai auri adawiyya ba ka kwantar da hankalin ka akan wannan lamari komai zai tafi yadda bakai zato ba cikin alheri"
Cikin sanyin Jiki Abba yace.
"Hankali na ya tashi da lamarin Maryam haƙiƙa banyi dace da mace ta gari ba, gaba ɗaya Halin Rabi'ah na uwarta ne, In har ta auri bare ba zasu zauna lafiya ba Ina ji ajikina auren rabi'ah kamar wani nauyi ne da zan sauke kafin fitar Numfashi na"
Da sauri baba yace.
"Ka bar faɗin haka amadu ni ban da kamar ka, duk shirme suke itama hafsatu ta damu ko wacce bata son auren mu toshe kunnuwan mu alheri muka nufa kuma shi zai ƙullu Sadauki yayanta ne koba aure shi mai tsaya mata ne da ikon Allah"
Da ire iren wannan Baba ya samu hankalin ɗan uwanshi ya kwanta koda suka fito innah da ƙyar taiwa Abbah sallama muryarta a shaƙe ranar anci sa'a domin a motar Abba suka fita Abba ya aje baba a kasuwa shi ma ya wuce tasa.
Iyaye mazan sun toshe kunnuwan su daga cece kucen matansu domin ita ma innah ta riƙe wuta sosai akan lamarin musamman da Anty nafi ƙanwarta ke ƙara rura mata wutar ƙin auren sai dai Baba da yake yafi ƙarfin gidan shi tara ƴaƴanshi yayi kaf yace bai lamunta wani ya ƙara sukar auren ba da wannan aka samu sauƙi.
Shiko Abba komai na shawarar biki baya tinkarar momi Iyah yake faɗawa hatta kayan lefen ma ya ɗebe su ya kai gidan iyah sabida haka koda biki yayi saura kwanaki bakwai iya ta sayi goron rabo ta saka Mariya ta kakkai gidan danginta sabida ganin take taken matan yasa Baba yace wa Abba ya tsaida ranar biki domin ko Saadik ɗin ma baba bai faɗawa ba, sai da Bikin yayi saura kwanaki bakwai.
Baba ya kira saadik ɗin ya shaida masa duk yadda saadik yaso baba ya ɗaga masa ƙafa amman baba yaƙi yace ko bukka ce ya saka matar shi.
Da damuwa saadik ke shaidawa Innah wadda sam baba bai shawara da ita ba, cewa tai kada ya ɗaga hankalin shi abin da Allah ya hore mishi yayi ita kam ba taro zatai ba tinda abin yazo a ƙure iya ƴan uwanta kaɗai zata faɗawa.
Gaba ɗaya saadik ya shiga busy gidan daya kama suka shiga gyara shida su Nura ƙanin Nura yayi paint a gidan wanda Falo ne guda ɗaya sai ɗaki aciki sai banɗaki da Kitchen duk a falon.
Ɗan ƙarami ne gidan irin na zaman mutum ɗaya.
Bai sami nutsuwa ba sai ana saura kwana biyu daurin aure su Nura ne suka bugo katin ɗaurin aure suka shiga rabo Babawo yayi musu ɗinki shaddar ɗaurin aure duk su huɗun.
Ana gobe ɗaurin aure Iya ta saka Abbas ya kaita gidan Momi wadda ta saki jikinta sam batai zaton da bikin bama sabida Abbah baya bibiyar ta akan lamarin shiyasa ta saki jiki akan aikin malam yaci maganar aure ta mutu zasu yi son ransu ita da lubna shiyasa suke ta ƙulla yanda za'ai Mahir ya turo manyan shi.
Ƙaramin hauka momi ta shiga yi sanda iya ke sanar da ita tazo tafiya da Rabi'ane sabida gobe za'a daura aure a wuce da ita gidanta.
Momi kuka Adaah kuka sai da Abba yayi jan ido sannan Adaah tabi iya domin ko kayanta ma bata haɗa ba, Abba yace a kai mata su daga baya.
Komai na momi ya tsaya cak sai faman zage zage take kuma tace ba zata taka ƙafarta gidan bikin ba Hajiya lubna tafi momi shiga tashin hankali data ji maganar amman data tina zagon ƙasan datai sai taji bata damu da auren ba tasan dole adaah zata fito ɗanta ya aure ta, domin ba burin ta auren adaah ba burinta dukiya.SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma 9022260850 Opay bank, Shaidar Biyan kuɗi zuwa ***, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.