HAJAR

{89..}

by @feenerhfeeche

6 MONTHS LATER


★Hajar na zaune room dinta cikin doguwar rigar Atampa wcca aka yiwa ɗinkin maternity, girman rigar ya rufe turtsetsen cikinta dake da wata bakwai, sosai cikin ya amsheta don bai muzanta mata kamanni ba sai ma wni kyau da ta ƙara, tayi wni irin haske mai kyau snn jikinta ya sake cika ta ko ina musamman ma ƙugunta, plate ne akan cinyarta mai ɗauke da dice fruits, a hankali take cakar fruits din da fork tana sha, saida ta gama shanyewa snn ta kalli agogo, ƙarfe sha ɗaya da rabi ta gani, tashi tayi daga gefen gadon da take, saida ta miƙe snn cikin nata ya sake bayyana, ta gyara rigarta da ta tattare ta nufi door da empty plate din da ta gama shan fruits, downstairs ta sauka walking gently, duk da girman da cikinta yayi bata jin nauyin jikinta, haka take sintirinta tsakanin sama da ƙasa kamar ycca ta saba kafin cikinta ya girma, ko ina na gidanta tsaf tsaf ƙamshi ya ratsa ko ina sbd azababben turaren da take bunka masa frequently, kitchen ta shiga ta wanke plate din kafin ta kife ta fito ta haura sama, room dinta ta wuce ta buɗe wardrobe ta ciro hijab da ya shiga da flowers din kayanta ta saka, wayarta ta saka a handbag ta ɗauki handbag din ta nufi door bayan ta saka flat shoe, ɓangarensa ta shiga da sallama, ya fito daga bedroom knn ta shigo, ta turo baki tace "Allah ka daɗe..", yayi murmushi yace "Afwan Momma princess", ƙarasowa yayi inda take ya riƙe hannunta ya jata zuwa kan Sofa, gefenta ya zauna yana kallonta yace "Ohh yarinyar Umma duk sanda za'a je wajen Umma tin asuba ake fara shiri", ta juya idanunta gami da turo lips dinta da suka sake ciza color dinsu, yace "Toh bari muyi daily routine namu kafin mu wuce ko..?", ta gyaɗa kai, tashi yayi ya shiga bedroom after few minutes ya fito da rechargeable Bp gauge, ya koma position dinsa ya zauna snn ya fara measuring Bp din nata, kullum ne sai ya duba cause yana sane da lokacin da jininta ya hau, farkon aurensu har ta zauna gidan Mami, Alhmdllh a kullum zai duba BP din nata yaga normal, ynxun ma dai normal din ya gani as usual, ya ɗage hijab dinta ya shiga shafa turtsetsen cikin nata yace "Hi Princess..", shafa cikin itama tayi tace "Hi Prince..", yayi chuckling yace "Princess give her a slight punch if she call you prince again..", tayi ƴar dariya tace "Ah am telling you is a boy", ya ja hancinta yace "ni kuma nace girl", ta ɗauke hannunsa daga cikinta ta gyara hijab dinta, sosai ake shan musu a tsakaninsu akan gender din unborn baby din nasu, shi yace girl ita kuma tace boy, To prolong the musu shiyasa ba'a duba gender din babyn ba a ciki wai idan yaxo ya raba gardama, shi kam yace idan baby boy ne zai bata presence, sai ƙarfe sha biyu saura suka fita compound, saida suka ɗauki hanyar gidan Umma yace "bamu siyawa Sabrah sweet ba..", tace "Ohh ai sauri muke sai next time kuma", yace "A'a fa we have to get her something", ai kam saida suka tsaya wani bakery suka sayi snacks snn suka cigaba da tafiya, Nurain yayi parking a ƙofar gidan Umma yace "Greet Umma well later in na dawo zan shigo mu gaisa", Hajar ta gyaɗa kai tace "Toh" da haka ta ɗauki ledar snacks din da handbag dinta, ya matso yayi pecking lips dinta yace "Take care..", tace "Sure Allah ya tsare Moon..", yayi nodding head yace "Ameen" sai kuma ya buɗe motar ya fita, zagayowa yayi side dinta ya buɗe mata ƙofa ta fito, tace "Moon i can do this", yace "No let me do it" da haka ya rufe murfin motar, tace "Thank you" da haka ta nufi ƙofar gidan walking slowly, saida ya tabbatar ta shige snn ya zaga ya shiga driver seat ya bar layin. Umma ta fito daga ɗan madaidaicin kitchen din gidan dake tsakar gida jin sallama, sakin baki tayi tana kallon Hajar da ta shigo, Hajar tayi murmushi tace "Ummanmu..", Umma ta kalleta from head to toe tace "La'ilaha Hajara..", Hajar ta ƙarasa ciki ta rumgumeta tace "Na'am..", Umma ta janyeta daga jikinta tana sake kallonta tace "Hajara kinyi nauyi bazaki zauna a gida ba ko..?", Hajar tace "Wata fa wajen biyu banzo ba", Umma tace "Toh ke ba kiga halin da kike ciki ba", Hajar tace "A'a Ni ba komai" da haka ta wuce ƙofar palour, Umma ta bita da kallo, Hajar na shiga palourn ta cire hijab dinta, Sabrah ta leƙo daga ɗakin Umma tace "Addah snnu da zuwa..", Hajar tace "yauwa... fito mna kike laɓewa a jikin labule", Sabrah tace "wanka nayi zansa kaya", Hajar tace "Okay", Umma ta shigo palourn ta zauna bayan ta ɗora sanwar rana, Hajar ta gaida Ummanta da ladabi, Umma ta amsa tana tmbyarta ya take, bayan wni lokaci Hajar tace "Yaya fa..?", Umma tace "Mu'azzam ya tafi Abuja wni aiki", Hajar ta waro ido tace "Abuja..?", Umma tace "Eh ai kinsan ynxu aikin nasa ba iya kano bane har wasu garuruwan suna zuwa aiki", Hajar ta gyaɗa kai tace "Toh Allah ya dawo dashi lfy", Umma tace "Ameen", Hajar tace "Nabilah ta tafi ne..?", Umma tace "Tin yaushe ai shekaran jiya ma Bappa yaxo aka ɗaura aurenta anan masallaci bayan sallar juma'a, bbu wni taro da akay sbd uwar baso take ba, haka akay komai lami bbu wni shagali sai kace ba auren budurwa ba, ƙannen mahaifinku mata suka miƙata gidan mijin", Hajar tace "Ynxu anyi auren Nabilah... Umma kinje gidan nata toh..?", Umma ta girgiza kai tace "A'a banje ba gsky sai nan gaba insha Allah zan dai daure naje idan tayi sati", Hajar tayi shiru ba tace komai ba tana wni tunani, toh ko ya labarinsu Maimuna da Sa'adatu, Allah yasa dai suma sunyi hankali kamar Nabilah, Sabrah ta fito bayan ta gama shiryawa suka gaisa da Yayarta, Hajar ta bata snacks da suka siya mata, sosai Sabrah ta dashare haƙora tace "ngd Addah", Hajar ta mata murmushi sai kuma ta kalli Umma tace "Umma dan Allah yau ma ki bani aron Sabrah na tafi da ita..", Umma ta girgiza kai tace "yaushe ta dawo daga gidan naki, daga ke har ita ku ka yaudareni dan sati ɗaya nace tayi ta dawo gida amma saida ku ka cinye sati uku..", Hajar ta marairaice murya tace "plxx Umma wnn karon baza mu ƙara ba..", Umma ta girgiza kai tace "A'a wai ance miki bayar da ɗa sauki ne dashi iyeh, ki bari idan kin haifa akace ki kawo sai kiji yacca akeji", Hajar tayi murmushi tana hasaso ycca take son unborn babynta tin kafin ma yaxo duniya, ta rasa a tsakanin ita da uban ɗan wane yafi son babyn, so da dama idan ta kissima yacca za tayi raising babyn bayan yazo duniya idan kuma taji yacca uban yake mararinsa sai taga kamar ya fita son babyn, toh dai mgnar Umma gsky ce don itama fa da alama rowar ƴaƴan nan za tayi, ko zata bayar toh fa tsaf Nurain zai hana. Ƙarfe uku da minti hamsin Umma taji ana sallama a soro, ta san ko waye don ta gane muryarsa, tashi tayi ta fita tsakar gida tana cewa "ka shigo mna Naseer sai kace wni baƙo..", Naseer ya shigo yana sake yin wata sallamar, Umma tace "saika tsaya a soro sai kace baƙo... Bismillah shigo ciki" da haka ta juya ta shiga palour, Naseer ya ajiye doyar da ya shigo da ita snn ya ƙarasa palour da ƙatuwar ledar hannunsa, ya zauna kan kujera yana shafa kansa, da sakakkiyar fuska Umma tace "Sannu da zuwa..", ya russuna yace "Umma barka da yamma", Umma ta amsa with care snn tace "ya hanya..?", yace "Alhmdllh ai kwana na uku da dawowa sbd auren Nabilah..", Umma tace "Eh fa hka ne, Allah ya sanya Alkhairy", yace "Ameen..", tashi Umma tayi ta shiga ɗakinta, ta kalli Hajar dake zaune kan darduma tana zaman tahiya tace "idan kin idar da sallar kixo ga Yayanki.." da haka ta juya ta fita, Hajar na idar da sallah ta miƙe ta fita palour, Naseer ya ɗaga kai ya ɗan kalleta sai kuma ya mata murmushi, Hajar ta samu guri ta zauna tace "Yaya ina yini", yace "lfy lou Hajar... ykk ygida...?", tace "lfy alhmdllh", yace "Masha Allah hka akeso", tayi shiru ba tace komai ba, Umma tace "kawo masa abinci da ruwa", Hajar tace "Toh" snn ta tashi ta fita, Umma ta maida dubanta ga Naseer tace "Allah yyi Albarka naga doya", ya shafa kansa yace "ba komai", tace "ya can wajen Huzaifa ba wata uku ya rage masa ba a karatun..?", yace "Eh ai ya gama ma... saidai yace bazai dawo ba don ya samu aiki mai kyau a can", Umma tace "Masha Allah shi kam ya fita da Sa'a wllh ace kana gama mkaranta ka samu aiki..", Naseer yace "Wllh kam ai da offer dinsa ya fito", Umma tace "Masha Allah..", ya janyo ledar da ya shigo da ita yace "ga wasu kayan ma", Umma ta ja ledar kusa da ita tace "Alhmdllh Naseer ai ka kusa gama haɗa lefen ma", ya waro ido yace "bafa a siyi kayan shafa ba", tace "Toh ai anyi mai wuyar tinda an haɗa sutura da takalma da jakunkuna, kayan Shafa ba masu wni whala bane..", ya shafa kai yace "gani nake kamar kayan basu da yawa", Umma ta riƙe baki tace "Lalala siff dita ai ta zama kantin kwari, kaya kam ka haɗasu ba kaɗan ba Naseer, bari Hajar ta kawo mka abinci kaci saina fiddo mka kaga yawansu..", yace "A'a kar a fiddo in na gansu zan iya shagala", Umma tace "Toh shknn, ai kayi mai wuyar ma wllh, ka gama gini tass har an sakawa gida padlock, a marrar nan ka samu gidan kanka ai ba ƙaramin luɗifi bane", a lokacin Hajar ta shigo masa da abinci a plate da kuma jug din zoɓo mai sanyi. Biyar da ƴan mintina Nurain ya kira Hajar a waya yace mata yaxo, Hajar ta fita palour don da za tayi wayar ɗaki ta shiga, har lokacin Naseer bai tafi ba don dman idan yxo yana jimawa sbd sai ya daɗe baizo ba, tini Hajar ta gayawa Umma cewa zai shigo su gaisa, Umma tace "Toh kawomin hijab dina", Hajar ta koma ɗaki ta kawowa Umma hijab dinta snn ta fito, bbu jimawa suka shigo tare da Nurain, Nurain ya gaida Umma da ladabi, Umma ta amsa da sakakkiyar fuska, bayan sun gaisa da Umma ya juya ya miƙawa Naseer hannu sukay musabaha, Nurain ko minti biyu bai ƙara ba ya yiwa Umma sallama ya fita, Umma tace "marmaza ki shirya ku tafi karki barsa yana jira", Hajar ta shiga ɗaki ta ɗakko handbag dinta ta fito, tace "Umma na tafi, idan Sabrah ta dawo Islamiyya zan kira", Umma tace "Allah ya kaiku gida lfy, saura kuma na sake ganin ƙafarki nan kusa", Hajar ta turo baki tace "next week ma zanzo..", Umma tace "karma ki kuskura na gaya miki", Hajar ta dubi Naseer tace "Yaya ka gaida gida", yace "Aha, Allah ya kaiku gida lfy", tace "Ameen" da haka ta nufi tsakar gida ta fita, cikin mota ta tarar dashi don haka ta buɗe front seat ta shiga, kallonta kawai yake har ta rufe ƙofa ta gyara zamanta, ta ɗan kallesa sai kuma ta buɗa lulu eyes dinta tace "how was your day My Moon..?", yace "Totally dull without you by my side", ya kamo hannunta ya kissing deeply yace "I missed you", tayi murmushi ta sarƙe yatsunta cikin nasa tace "Same", Ai kam hka ya fara driving ba tare da ya saki hannunta ba, saida suka hau saman titi yace "bari mu tsaya mu sayi chocolates ba..?", tace "Ai basu ƙare ba", yace "yeah it is better mu ajiye extra kar ya yanke mna Princess ta mna rigima", tayi ƴar dariya tace "Ohk", A wani mall suka tsaya, tana gaba yana biye da ita suka shiga cikin mall din, direct Aisle din Chocolate da Crunchy biscuits suka tsaya, ya bata basket yace ta ɗebi wnda take so zai duba wni abu, Hajar ta fara dubawa tana ɗebar abinda take so tana sakawa a basket, kukan baby ta jiyo daga jikin Aisle din da take, ai kam da sauri ta zagaya, wata mata ta gani durƙushe a ƙasa tana kwashe kayan da suke zube tana zubawa a basket, babyn da yake hannunta sai tsanyara kuka yake tana ɗan jijjigasa, Hajar ta isa inda take ta ajiye basket din hannunta, matar ta ɗago ta kalli Hajar, Hajar tace "ya Baby yake kuka" da haka ta sunkuya ta amshi babyn ta fara jijjigasa, ai kam tini yayi shiru, Mamansa ta ƙarasa kwashe kayan ta miƙe tana kallon Hajar tace "ngd", Hajar tayi murmushi tace "mention not" sai kuma ta ciro babyn daga shoulder dinta zata miƙawa Mamansa, ba ta miƙa mata ba ta tsaya tana kallon fuskar babyn wcca ta mata kama da fuskar wni mutum da ta sani a rayuwa, muryan namiji suka ji ance "Habibty are you done..?", Matar ta juya gun wanda yayi mgnar tace "Eh Habiby..", Hajar ta ringa kallonsa still tana riƙe da babyn har ya ƙaraso, shima kallon nata yake bbu ko ƙiftawa, Hajar ta saukar da kanta sai kuma ta ɗan russuna tace "Ya Sayyadi ina yini", ya ringa kallonta yace "Hajar Adam Gini..?", Hajar ta gyaɗa kai, Nura ya kalli kyakkyawar matarsa Maryam yace "Ɗalibata ce", Maryam ta kalli Hajar tace "Allah sarki sannu ko", Hajar tace "Ashe matar Ya Sayyadi na kawowa temako..", Maryam tayi murmushi tace "Ai kuwa dai", har Nurain zai wuce Aisle din da suke ciki sai kuma ya dawo sbd ya hango Hajar, ya shigo Aisle din walking majestically, saida ya kusa zuwa kusa dasu snn yace "Baby wife..", Hajar ta juya tana ganinsa tayi wni kyakkyawan murmushi tace "My Moon", shima murmushin ya mata kafin ya ƙaraso ya dafa shoulder dinta yace "what are you doing here..?", tace "Ya Sayyadin Islamiyyarmu da mukay sauka a hannunsa ne..", Nurain ya kalli Nura for the first time yace "Okay" sai kuma ya miƙa masa hannu sukay musabaha, briefly suka gaisa, Nurain ya kalli Hajar yace "let go wife..", tace "sure" da haka ta miƙawa Maryam baby boy din tace "Allah ya raya", Maryam ta amshi babyn tace "Ameen ngd", Hajar ta sunkuya zata ɗauki basket din da ta ajiye amma tini Nurain ya rigata, ya riƙe hannunta suka bar wajen, shopping din suka ƙarasa snn suka bar mall din. Haka rayuwar ta cigaba da garawa Couple din cikin jin daɗi da annashuwa suna rainon unborn dinsu tare, kuma har zuwa wnn lokacin ba a duba gender din babyn ba kuma suma basu dena musu ba, kowa yana kan bakarsa, shi yace baby girl ita kuma tace boy, a haka cikin Hajar ya shiga wata tara, saida ya shiga wata na tara ne snn ta fara jin nauyin jikinta, ba ta iya wnn hawa da saukar kamar da amma dai ta kan sauka downstairs twice a day. Yau da wuri Hajar ta kwanta cause tin safe take jin slight pain sai ynxu ta samu ya lafa mata shine ta kwanta, tana kwance kan gado shi kuma Nurain yana zaune kan couch yana aiki jikin laptop, wajen ƙarfe sha ɗaya Hajar ta farka, ba tasan lokacin da ta kwaye duvet din jikinta ba tana so ta miƙe zaune amma ta kasa, ji take kamar bayanta zai ɓalle, ta shafa both side dinta wai ko za taji present din mijinta, tana jin wayam ta buɗe idonta tarwal tace "Moon", da sauri Nurain ya taso ya isa gaban gadon, ya ɗagota yace "Mene ne..?", ta shiga yarfe hannu don ciwon gaba gaba yake, kawai girgiza kai take sideways ta kasa cewa komai, hasken ɗakin ya kunna sosai, Hajar ta muskuta tayi kneeling kan gado sai kuma ta kwallara wata ƙara tace "Nurain..!!", da sauri ya dawo ya zauna, ta riƙe hannunsa da iya ƙarfinta tace "ka ciremin wnn cikin.. Princess ce ko Prince ni dae bana so na bar maka", habawa ai tini Nurain ya fahimci cewa labor ne, ya tashi ya fita daga ɗakin yana jin yacca take kwala masa kira, bai wni jima ba ya dawo, gani yayi har ta kifo daga kan gadon, ya duƙa gabanta ya fara ƙoƙarin cire mata rigarsa dake jikinta, kawai daurewa yake don har ya fara rikicewa, ita kam Hajar kawai cewa take Nurain ka cire Princess din na bar maka, da kyar yayi jarumtar saka mata ƴar shawalwalar rigarta da ya ɗakko mata, ya mayar da ita kan gado yana jera mata sannu, ƙoƙarin hantsilowa take yayi saurin riƙeta, ta fashe da kuka tace "wayyo na shiga uku na lalace nace ka ciremin", da kyar ya samu ya cire hannunsa a nata ya fita, box din da ya shirya 2weeks ago mai ɗauke da duk wani abu na baby da mother sbd zuwa asibiti ya ɗauka ya fita, bai wani jima ba ya dawo bayan ya kai box din mota, da bibbiyu ya haura stairs, a ƙasa ya sameta malala ta sake sakkowa daga gadon, da ita da turtsetsen cikin nata ya haɗa ya ɗauka, ko gidan ma bai iya rufewa ba ya ajiyeta gaban mota ya kwantar da seat din, gida biyu hankalin Nurain ya rabu, ɗaya yana kan tuƙin da yake ɗayan kuma yana kan Hajar da take cikin raɗaɗin ciwo, da haka suka isa private hospital din Dr Mansoor, tini Midwives suka amshi abarsu aka wuce da ita labor room, Nurain ya ringa shawagi tsakanin ƙofar labor room din, After 20mins wata Midwife ta fito, Nurain yace "how is my wife..?", Midwife din tace "Sir please go in your wife need you..", bai ƙarasa jin ta bakinta ba ya buɗe ƙofar labor room din ya shiga.......✍️