HAJAR

{90..}

by @feenerhfeeche


Nurain na shiga labor room din ya tarar da Hajar kwance kan gado, ya ƙarasa gaban gadon ya shafa fuskarta, ta buɗe idonta a hankali, duk gumi ya tsattsafo mata a goshi tana ajiye numfashi a hankali, ya kamo hannunta yana murzawa with care yace "Sorry wife", hawaye ne suka fara sauko mata tace "Nurain bana son nan wajen ka kaini wajen Ummana", ya shafa kanta yace 'Sorry, Allah ya saukeki lfy wife", lumshe idonta tayi ba ta sake cewa komai ba, wata Nurse ce ta shigo instead of Midwife tace "Amm za'a mayar da ita ward tinda labor din ya tsaya..", Nurain ya dan yi jim duk da cewa yaji abinda Nurse din ta faɗa, yace "idan laborn ya dawo sai kuma a dawo da ita nan..?", Nurse din tace "Sure", ya girgiza kai don bai yarda ba duk da yasan cewa hka tsarin hospital yake, gsky ba za a wahalar masa da mata ba a ringa wni walagigi da ita, yace "A barta a nan din har zuwa ta haihu mna..", Nurse din ta rausayar da kai tace "Ohk" sai kuma ta juya ta fita, Nurain ya janyo kujera ya zauna ya sake kamo hannunta ya riƙe, a haka bacci ya ɗan kwashe Hajar, shi kam yana zaune tunkurkur yana gadi don dman ya saba, ya ciro wayarsa ya duba lokaci yaga 12:30 na dare, yana nan tare da matarsa, duk bayan 20 to 30mins sai Midwife ko Nurse sun shigo to check on Hajar, ƙarfe huɗu da rabi lokacin asuba ta kunno kai toh a lokacin ne Hajar ta farka, kuma kai tsaye naƙudar ta taho mata gadan gadan, An sha gumurzu iya gumurzu, daf da sallar asuba Hajar ta silloɓo ƙatuwar baby girl dinta bayan ta leƙa lahira, gidan glass kam saida ta shigesa sbd girman ƴar, a duk wnn gumurzun Nurain na room din don hannunsa ta yiwa mummunar riƙo da haihuwar tazo, tini aka gyarata ita da baby dinta aka mayar dasu Amenity ward, bayan fitar Nurse da Midwife din da suka kula da ita Nurain ya taka gaban gadon, ya ɗaga fuskarta da tayi jajur, pecking forehead dinta yayi, ya ɗago yana sake kallonta yace "Thank you so much wife", ita dai ba tace masa komai ba sai aukin lumshe ido, yayi pecking hannunta deeply yace "Thank you for making me a Father..", ya sake pecking hannun yace "Thank you for giving birth to my child..", a kasale ta masa murmushi sai kuma ta lumshe idonta, sai a lokacin Nurain ya ɗauki babyn tasa dake kwance kan gadon jarirai, ya ringa kallon fuskar babyn wcca tke baccinta peacefully, kumatunta a cike ɓul ɓul ga kuma nauyi tubarkallah sai kace ba first born ba, rumgumeta yayi sosai a jikinsa for a while, bai mayar da ita kan gadon jariran ba ya kwantar da ita kusa da Mother dinta wcca baccin whala ya kwasheta, sai a lokacin Nurain ya samu chance din kiran Mami, ai kam bugu ɗaya ta ɗaga tinda asuba tayi, Mami kam da taga kiransa saida gabanta ya faɗi, tini ya sanar mata abin alkhairy da ya faru, ta tmbyesa suna gida ko asibiti yace asibitin Dr Mansoor daga hka suka katse wayar, Saida ya kira Nurse ta tsaya a room din tare da Hajar da babyn sa snn ya wuce mosque dake kusa da hospital din don yin sallah. Ƙarfe shida da minti sha biyar na safe Mami ta iso asibitin tare da Sakeena wcca a harabar asibitin suka haɗu itama tazo, Mai aikin Mami ta shigo da basket din abinci, Nurain ya tashi daga kan kujerar da yake zaune yana kallon Hajar da baby dinsa da suke bacci har lokacin yace "Mami snnu da zuwa", Mami tace "yawwa" sai kuma ta matsa gaban gadon tana kallon fuskar Hajar, Sakeena ta ƙarasa shigowa ta ɗauki Babyn ta zauna gefen gado tana kallonta, sai kuma ta kalli Nurain tace "Mace ko namiji..?", yace "Baby girl..", Sakeena tace "Masha Allah, Ya ilahi wllh kamarku ɗaya brother..", Mami ta juyo ta kalli Nurain tace "Tin yaushe take bacci..?", yace "Tin Asuba", Mami tace "Ohk", saida Mami ta zauna a position din da Nurain ya bata snn Sakeena ta kawo mata Baby, Mami ta ringa kallon Babyn snn tace "Tubarkallah Masha Allah..", Babyn kamarta ɗaya da ubanta bbu abinda ta bari, har thick eyebrows dinsa saida ta kwaso saidai ita komai nata na mace ne, even complexion na ubanta ta ɗakko saidai ynxu akwai hasken jinjirantaka shiyasa tayi haske, Sakeena ta tsaya daga gefen Mami tana cigaba da kallon Babyn, the baby is so cute, gata ƙatuwa masha Allah, duk da cikar fuskarta da cheeks amma hancinta bai nutsu ba, hancin ya fito sosai gashi ɗan ɗos masha Allah, wani motsi babyn tayi ta yamutsa fuska har saida dimple din da take dashi ya bayyana kansa for the first time, Sakeena tace "Woah Masha Allah har da dimple...", Mami tayi murmushi tana jin son yarinyar, Nurain dai ganin gaba ɗaya hankalinsu na kan Babyn kamar ma sun manta dashi ya duƙa ya gaida Mami, Mami ta kallesa da murmushi kwance fuskarta ta amsa snn tace "An samu ƙaruwa.. Toh Allah ya raya mna ita bisa sunnar manzo..", ya shafa kansa bai amsa ba, Sakeena ce tace "Ameen", After 30mins Hajar ta farka, Sakeena ta haɗa mata shayi mai kauri ta kai mata, ganin taƙi shan shayin Mami tace "ko ba kya son wnn dear..?", Hajar ta ɗago idonta da suke a kumbure tace "A'a", Sakeena tace "ko ya miki zafi ayi diluting..?", Mami tace "A'a da zafin sai yafi.. try and take it even small daughter..", a hankali Hajar ta fara shan shayin, har saida taji ɗuminsa a cikinta da take jin tamkar an yashe mata ƴar hanji, Nurain ne ya shigo ya ajiye ledar da ya shigo da ita, sosai yaji daɗi ganin ta farka, ya matsa gaban gadon yana tmbyrta how she is feeling, Mami tace "kira likita ya dubata", yace "sure", ya nufi door ya fita, bai jima ba ya dawo tare da Nurse da Dr, both the Mother and the Baby were fine haka likitan ya faɗa, snn yace nan da 12 idan an sake tabbatar da lfyrsu za a sallamesu. Kafin ƙarfe takwas su Umma suka zo tare da Anty da Hafsah, tini Sakeena ta miƙawa Anty babyn bayan sun gaisa, Hajar ta gaida Umma da Anty, Umma dai kawai kallon ƴarta ta take, Hafsah ta koma kusa da Hajar ta zauna tace "Sannu sister..", Hajar tayi murmushi kawai, daga kan su Umma bbu wnda ya sake zuwa, don duk wnda ya kira yace zaizo Mami take cewa ya wuce can gidan suma gasu nan dawowa, Hajjaju Hajiya ma can gidan Mami tasa aka wuce da ita, kamar yacca Dr ya faɗa hakan kuwa akay, 12 aka sallamesu bayan an tabbatar bbu wni matsala, gidan Mami aka wuce da Hajar snn aka bata ɗaki guda, kafin kace me ɗakin ya cika sai zuwa ake ganin baby da duba Hajar, Umma dai bata biyosu gidan ba ta wuce gida duk da cewa tana son kasancewa da ƴarta, taso ace an bata ƴarta ta tafi gida da ita amma kuma kawaici yasa tayi shiru, ai suma taga yacca suke taraiyar Hajar din suna bata kula ta musamman, ai soyayya ce ta jawo har suka tafi da ita, Hajar na zaune kan gadon ɗakin, Anty kuma na zaune kan kujerar room din, Hajiya ce ta shigo tana dogara sandarta, Anty ta tashi daga inda take tace "Hajiya ga waje..", Hajiya ta zauna kan kujerar tace "yewwa" sai kuma ta kalli Hajar tace "Sannu Hajaru.. haihuwar fari ki haifo wnn narkekiyar ƴa ai dole a miki sannu", Hajar dai ta saukar da kanta ba tace komai ba, Sakeena ce ta shigo da Babyn a hannunta wcca take tsanyara kuka don ta farka ne, Hajiya tace "A'a lfy..?", Sakeena na jijjiga babyn tace "Tashi tayi ne Hajiya", Hajiya tace "miƙata ga uwarta ta bata Nono", Sakeena ta miƙawa Hajar Babyn, Hajar bata amshi Babyn ba tayi kamar bata san ana miƙo mata ba, amma kuma har cikin ƙahon zuciyarta take jin kukan yarinyar, Sakeena ta ajiye mata ita akan laps tace "feed her", Hajar ta saukar da idanunta tana kallon babyn, tinda taxo duniya sai ynxu ta kalleta da kyau, wni gurmi ne taji ya buɗe a zuciyarta wnda wnn shine karo na farko da ya buɗe, ta ringa kallon jinjirar dake wutsil wutsil a cinyarta tana ƙishin ƙishin, lokaci guda ta fara kuka, ɗaukarta tayi ta sakata a shoulder ta ringa shafa bayanta, still dai babyn bata dena kuka ba, Anty ta zauna kan gadon tana kallon Hajar da kyau tace "ki bata mna", Hajar ta saukar da kanta tace "Ni me zan bata", Hajiya ta caɓe zancen tace "ki bata Nono ko saita shiɗe ne..", firr Hajar ta kasa feeding babyn a gaban mutane, yama za ai tayi feeding gaban mutane, Sakeena tayi murmushi don ta gane manufar Hajar, itama haka tayi wnn wautar a haihuwarta na fari, Sakeena ta amshi babyn daga hannunta, feeder dinta na ruwan zam zam ta dauka ta zauna tana bata ruwan, daidai nan Mami ta shigo, Mami ta kalli Sakeena tace "ya take kuka har ynxu..?", Sakeena tace "Mami a siya mata formula first ynxu naga kamar ruwan mimin bai zo ba", Mami tace "Ohk bari na yiwa Nurain mgana ya kawo mata madaran..", Hajiya ta kalli Mami tace "yau naga jaraba, wace irin madara ana zaune ƙalou, jaririya da Nonon uwarta sai ace a siyo mata madarar kanti, ku bar ganinta ƙatuwa indai ku ka fara bata madara toh wllh duk saita tsiyaye, wnn kumatun da tazo dashi duk saiya zazzage wllh, kar a wni bata wata madara Nonon uwarta ne kawai zaisa jikinta ya cigaba da ɗorewa...", Mami ta saukar da murya tace "Hajiya ai ba madaran za'a bata ba, na wni lokacin ne kafin abincinta yaxo", Hajiya tace "Toh ta yaya zaizo bayan ba'a barta ta zuƙa ba, sai tana ja snn zaizo da wuri, snn kuma jegon zamani na shirme wai sai a bawa mai jego wni banzan shayi ina muka bar kunun kanwa", Mami tace "Toh sai a mata kunun kanwar..", Hajiya tace "Eh da yafi, jinjira sai tsanyara ihu take", da haka Mami ta fita zata saka a damawa Hajar kunun kanwar da Hajiya tace. bayan sallar la'asar Hajar ta fito daga bathroom Anty biye da ita, wanka Anty ta taimaka mata tayi da ruwan zafi snn kuma tayi deep sitz bath tinda bata samu tear ba, Hajar ta kalli babynta dake kan gado tana bacci, tin ɗaxu da aka bata madara take bacci abinta, Anty ta ciro mata kaya cikin box din kayansu, Hajar na gama saka kayan Anty ta shaƙe mata bowl da chicken pepper mai bitter leaf da Anty Zulaihah ta kawo mata, knocking door akay snn aka buɗe, Nurain ne ya shigo, ya ƙaraso cikin ɗakin snn suka gaisa da Anty, ido huɗu sukay da Hajar ya sakar mata murmushi, tayi sauri ta ɗauke idonta ta cigaba da shan pepper soup dinta, Anty ta buɗe ƙofa ta fita, tana fita Nurain ya matsa kusa da Hajar ya sunkuya yana kallonta, ta ɗan kallesa sai kuma ta turo baki tace "Why the look..?", yace "Mamah bear how are you doing..?", ta turo baki tace "bayan wnn princess din taka ta bani whala..", yayi ƴar dariya sai kuma ya zaga side din da babyn take ya ɗauketa, ai kam yana ɗagata ta wni tsanyare da kuka sai kace wcca aka kunna da remote, waro ido yayi snn ya mayar da ita ya ajiye, habawa ai tini Hajar ta taso saura ƙiris tayi fatali da pepper soup din, ɗaukar babyn tayi ta fara jijjigata, saida babyn tayi shiru snn ta zauna gefen gado ta ajiyeta a laps dinta tana kallonta, Nurain ya zauna kusa da ita yana kallon babyn shima, ya taɓa small soft lips din babyn yace "Finally dai Princess ce..", Hajar ta ɗan kallesa sai kuma tayi murmushi, koma dai mene ne ita tana son abarta.


★Ruqayyah na zaune tsakiyar gado ta haɗe kai da guiwa sai rusa uban kuka take, ɗakin nata cike yake da ƴan uwanta, Meema dake kusa da ita tace "haba Ruqayyah wai bazaki dena kukan nan ba, yau fa ranar murna da farin ciki ce a wajenki amma ki zauna kina kuka", Ruqayyah dai ba tace mata uffan ba ta cigaba da rusa kuka, tabbas murna ya kamata tayi a wnn rana amma kuma zuciyarta zafi take, Meema ta taɓe baki tace "Toh Allah ya kyauta" daga haka bata sake cewa komai ba, bbu jimawa Kulsoom elder sister din Ruqayyah ta shigo, sakin baki tayi tace "what is this, wai ba tayi wankan ba..?", Meema tace "yeah", Kulsoom ta zauna gefen Ruqayyah ta dafa shoulder dinta tace "Ruqayyah ki tashi kiyi wnka mna.. dangin Angon fa sunxo", wani tashin hankali ne ya sake baibaiye zuciyar Ruqayyah, Kulsoom ba ta bar ɗakin ba saida ta tabbatar Ruqayya ta shiga wanka, saida Ruqayyah ta kwashi lokaci mai yawa snn ta fito, tini Kulsoom ta kawo mata lafayar da zata saka da kuma kayan ciki, Meema ce ta taimaka mata wajen shiryawar, Ruqayyah ta saka hannunta da yaji zanen ƙunshi ta goge hawayen dake sauko mata, Haj Safiyya ce da ƙanwar Daddy suka shigo ɗakin tare, da haka suka fita da Ruqayyah da aka lulluɓe mata fuska da lafaya, wajen Momy aka kai Ruqayyah domin ta mata faɗa snn suyi bankwana, Momy ba ta iya cewa komai ba bayan fatan Alkhairy da tayi mata da zaman lfy a gidan mijinta, daga wajen Momy aka kai Ruqayyah Amarya wajen Daddy shima ya saka mata Albarka, wajen dattijan gidan aka kaita daga ƙarshe snn aka miƙata hannun dangin mijinta da suke jiran a basu ita, gursheƙen kuka kawai Ruqayyah take har aka fita da ita, aka sakata a motar da take matsayin ta Amarya suka bar gidan da convoy din motocin rakiyarta. Finally Ruqayyah tayi aurenta cikin aminci, a sabon asibitin da ta dawo aiki ne Allah ya haɗata da mijin aure, Mijin nata babban Likitan yara ne, tinda ta fara aiki a asibitin ya nuna interest akanta, farko dai sharesa ta ringa yi har zuwa wni lokaci ta ɗan fara kulasa, da haka har ta basa digit dinta da address din gidansu, soyayya mai tsafta Dr Sa'eed yake yiwa Ruqayyah, ita dai Ruqayyah kawai dai tana kulasa ne ba wai don zuciyarta naso ba, she wants to move on din, ranar da Daddy ya ganta tare da Dr Sa'eed ai kam a ranar ya masa mgana, da yake Dr Sa'eed ba da wasa yaxo ba da gske aurenta zai yi aikam tini ya turo magabatansa, aka saka lokacin auren ba mai tsaho ba cause Dr Sa'eed yace a shirye yake, har week din aure ya kama abin mamaki shine Ruqayyah ba taji tana son wnda zata aura ba, kwata kwata ta kasa buɗe zuciyarta ta bada ƙofa wni ya shigo, ga dai Dr Sa'eed din bashi da wni matsala ga kyan hali saidai kuma ba yaro bane don ya haura hamsin, snn kuma yanada matarsa har da manyan ƴaƴa ma, Ruqayyah dai tayi accepting dinsa ne sbd ta goge black spot din da tayi a wajen parent dinta, kuma don dole ma ta amshesa sbd bazata taɓa samun abinda take so ba, ya riga da ya mata nisa nisan da bazata iya kamosa ba, amma dai ta ɗauki hkan a matsayin darasi mai ƙarko da inganci na rayuwa, yeah some opportunities comes first in life, toh itama hkan ne, sau ɗaya damar auren wanda take so tazo mata amma tasa ƙafa tayi fatali da ita, wnn ya zame mata izina snn kuma ta dauki lesson har ma ta zama teacher, zata iya koyar da duk wcca taga ta dauki step irin nata don ta taimaka mata kar ta aikata abinda za tayi nadama a nan gaba......✍️