{91..}
★Sosai Hajar ta saɓe tayi luƙui abinta ita da baby, gata ta ko wace kusurwa ake gwada mata, mijinta ya mata haka zalika ma yan uwansa, ga nata ƴan uwan suma, ƴan uwan Umma ma da suke nan kano duk saida suka zo, yau kwananta huɗu da haihuwa, yau ma Ummanta taxo tare da Iya da Wasilah da kuma Nabilah, Nabilah na riƙe da babyn tace "Masha Allah... Allah ya raya", Anty tace "Ameen", Wasilah tace "Ni kam na sha zasu bamu itane mu tafi da ita tinda dai hka al'adar haihuwar fari take..", Anty tayi ajiyar zuciya tace "Toh dai gashi nan din ma bbu abinda ta rasa na uwa, wllh suna kamantawa", Iya tace "yoh wne kamantawa kuma.. kawai su bamu ɗiyarmu mu wuce da ita gsky..", Umma duk tana jin su ba tace kanzil ba, Anty tace "Ni kam banga aibun hkan ba wllh, duk so ne fa yasa suka riƙeta..", Iya ta gyaɗa kai tace "sai dai hkan, amma dai gsky ya kamata a duba uwar ƴa", Umma dai ba tace komai ba hakama Nabilah dake riƙe da baby, ƙofa aka buɗe Noor ta shigo da fara'arta, da ladabi ta gaishe da mutanen ɗakin, ta ƙarasa wajen Hajar tace "Hajar..", Hajar tayi murmushi tace "kun dawo..?", Noor ta amshi babyn daga hannun Nabilah ta zauna gefen Hajar tace "Azalzalansa nayi muka taho, hka kurum ayi suna bbu ni..", Noor ta shafa cheek din babyn tace "Masha Allah so cute" sai kuma ta rumgumeta tace "Hajar ki bar min ita..", Hajar tayi murmushi kawai, Noor ta rage murya sosai tace "Hajar ya kika ji a labor room..?", Hajar tayi wni murmushi tace "words can't express the pain na rantse, kawai dai na ganni a gidan glass", Noor ta kyalkyale da dariya tace "Na shiga uku..", kawai hango kanta take nan da wata biyar, Mami ce ta shigo ta samu waje ta zauna suka gaisa dasu Umma bayan gaisawar da sukay ɗaxu, Sakeena ce ta shigo ma'aikata gidan mata biye da ita da kayayyaki, boxes ne aka lubge da kaya masu yawa a tsakar ɗakin, su Umma dai suka bi kayan da kallo bbu wnda yace wani abu, tini Mami ta musu bayani cewa kayan barka ne, kaya iya kaya aka zubawa Hajar da Babynta masu uban tsada, bbu abinda babu na kayan baby, har da set din danƙareren gold aka sakowa Hajar cikin kayanta, itama baby an saka mata ɗan kunnen gold guda biyu masu kyau. Daren ranar Nurain ya shigo kamar yacca ya saba, babyn sa ce rumgume a hannunsa yana kallonta, Hajar tace "Papa bear..", ya kalleta yace "Uhmm Mamah bear..", tace "daman Noor ce tace tana son na bar mata baby, ni kuma i can't say no to her nace tazo ta ɗauka..", tini Nurain ya haɗe gira yace "She must be crazy, my princess is not a toy..", Hajar tayi murmushi don tasan za'a kwata, wnn yarinya mai rabata da ubanta a ynxu ai sai Allah, wayar Nurain ce ta fara vibrate, ya karkata yace "Mamah bear help me with my phone..", Hajar ta zura hannu cikin aljihunsa tana cewa "ka ajiye wnn princess din mna", yace "A'a saidai kar a ɗaga wayar", tana ciro wayar yace "Who..?", ta kalli screen din tace "Punk..", yace "Ohk", tace "In ɗaga..?", yace "Sure Farooq ne", picking tayi snn ta kara masa a kunne, ita dai kallon mamaki take masa, toh wai don an ɗauki baby shine baza ayi amfani da hands ba, ko dai nasa salon ɗaukar yaran ne hka, suna gama wayar yace "Farooq zai shigo..", tace "Okay", ta tashi ta ɗauki zumbulelen hijab dinta ta saka, sai a snn ya ajiye babyn kan gado ya tashi ya fita, bbu jimawa ya dawo tare da Farooq, Farooq ya samu guri ya zauna kan kujera, gaisawa sukay da Hajar snn ya mata barka, ita dai kanta na ƙasa ta amsa a taƙaice, Nurain na zaune position din da ya tashi ya rumgume baby, Hajar ta ɗan saci kallonsa ganin bai bawa Farooq ita ba, Farooq yayi gyaran murya yace "Dude..", Nurain ya kallesa da gefen ido yace "why..?", Farooq ya murtuke fuska yace "The Baby..", Nurain yace "ka makara duk wnda bai zo ba 2days ago to ba ganin baby", Farooq yace "i was not in town you know..", Nurain ya miƙe da babyn a hannunsa yace "really" sai kuma ya miƙa masa ita, ashe Farooq bai iya ɗaukar jarirai ba gwara ma Nurain, ai kam ya riƙe babyn a hnkali don gani yake idan ya riƙeta da kyau zai iya ɓallata, babyn ta ɗan karkace a hannun Farooq, habawa ai da sauri Nurain ya taro abarsa sai kuma ya amsheta, Farooq yayi dariya sosai yace "riƙe abunka..", Nurain ya koma ya zauna yace "ko baka faɗa ba", Farooq yayi slight smirk bai ce komai ba, few minutes after that Farooq ya ɗauki wayarsa yayi dialing numbern da yayi saving da Baby with love emoji, kara wayar yayi a kunne yace "Baby where are you..?", daga ɗaya ɓangaren da muryar mace aka ce "Ohh Darling muna gaisawa ne da Mami..", yace "Ohk you have to be fast kar Ummi tace munyi dare..", tace "Alright am coming.." da haka ta katse kiran, few minutes aka buɗe ƙofar ɗakin, da sallama ta shigo kafin ta ƙaraso ciki, tinda ta shigo Farooq yake kallonta, ita dai sau ɗaya ta kalli position dinsa ta ɗauke kai, sosai tayi bowing tace "Yaya ina yini..", Nurain ya ɗan kalleta yace "lfy lou Khausar... how are you doing...?", tace "fine Alhmdllh" sai kuma ta kalli Hajar tayi murmushi tace "Ina yini Maman baby", Hajar ta mayar mata da murmushin tace "mun yini lfy", Khausar tayi murmushi tace "lfy alhmdllh.." da haka ta ajiye medium ledar hannunta ta amshi babyn a hannun Nurain, bbu jimawa Khausar ta kwantar da babyn ta ɗauki ledar da ta ajiye ta miƙawa Hajar tace "Allah ya rayata", Hajar ta amshi ledar tace "Ameen thank you", sosai Hajar tayi mamakin yacca Khausar ta sauya mata, ba tin yau ta fahimci hkan ba, ynxu suna gaisawa cikin mutunci bbu wni ɗagawa, Khausar tace "Yaya saida safe" da haka ta nufi door, Farooq ya tashi ya ciro note din ƴan ɗari biyar biyar ya ajiyewa Hajar snn ya fita. bayan tafiyarsu Farooq Nurain ya kamo hannun Hajar yace "you need anything Love..?", ta gyaɗa kai, yace "Name it Baby wife..", ta kwantar da kanta a shoulder dinsa tana turo baki tace "Seafood", yace "Ohk", ta ɗaga kanta tana kallonsa, yayi kissing lips dinta lightly yace "let me buy it for you", ya duƙa yayi pecking cheeks din baby kafin ya fita, bayan fitarsa da few minutes Hajar taga babyn ta fara saƙa da hannunta alamar ta tashi, ɗaukarta tayi ta fara breastfeeding dinta, tana gama breastfeeding dinta ta sakata a kafaɗa, after few minutes ta kwantar da ita don har ta koma bacci. Ranar suna gida cika yayi maƙil da ƴan uwa da abokan arziki na both side, yarinya taci suna Nanerh Khadijah amma ana kiranta Nanerh sbd sunan Mami ne, gsky an zuba shagali mai lasisi, Hajar har ta gaji da kyau sai shiga take tana fita cikin sabbin ƴan ubansun kayan da aka ɗinka mata, kyau mai sanyi tayi don bata kwaɓa kwalliya ba, komai nata natural ta barshi, kitso kawai akai mata sai jan ƙunshi, sosai Hajar taji daɗin zuwan Oum Sulthan da sauran neighbors dinta. Daren ranar sunan ne Nurain ya shiga part din Maminsa da take kiransa, a bedroom dinta ya tarar da ita, Mami tace "What is your next plan after the naming ceremony..?", ya shafa kansa yace "Nothing Mother..", Mami tace "Okay, sai Hajar ta tafi gida ta ƙarasa 40days dinta", habawa ai tini Nurain ya zubawa Mami idanu, shi da yake so a basa matarsa da ƴarsa su tafi gida ya yaji ana mganar 40days, Mami tace "kasan dai hkan al'ada ne ko, kuma nasan suma iyayenta kawai kawaici sukay mna ta zauna a nan na sati guda, bana so a shiga huruminsu da yawa, itama nasan tana so taje wajen mahaifiyarta..", Nurain dai ya kasa cewa komai don ji yake kamar ana zare masa spine, Mami tace "Any problem with that...?, idan fa kace baka so toh ba zata ba", ya girgiza kai, Mami tace "ba kace min zaka tafi China ba ko ka fasa ne..?", ya girgiza kai yace "A'a zan je", Mami tace "Ohk... shknn ma kaga kayi tafiyarka lfy bbu wni burden ita kuma taje gidansu ko?", ya gyaɗa kai yace "Toh shknn our Mami... yaushe zata tafin..?", Mami tace "ko gobe sai a kaita", yace "Toh". Nurain na barin wajen Mami direct ɗakin da Hajar take ya wuce, ta fito daga wanka knn ya shigo, rabonsa da ita tin safe a palour da akay musu hoto da baby dinsu, yace "where is our princess..?", tace "An tafi da ita wajen Hajiya za'a mata wanka", ya sauke ajiyar zuciya yace "yau an bata whala ko..?", Hajar tayi ƴar dariya tace "whala kuma..?", yace "Eh mna, nasan an ta ɗaukarta ne, duk yawan mutanen nan sai suce sai sun ɗauki baby", tace "A'a fa Hajiya ce tasa aka goya ta so duk wnda zai ganta saidai ya ganta a baya", Nurain ya sauke ajiyar zuciya yace "better", ƙarasawa yayi inda take, tayi sauri ta saka kayan baccinta riga da wando, saida ta gama sa kayan snn ya gaya mata mgnar zuwa gidan Umma, sosai yaga farin ciki ya bayyana bisa fuskarta, ya riƙe hannunta gami da sarƙe yatsunta da nasa, ƙoƙarin kwace hannunta ta ringa yi amma yaƙi ya saketa, ta marairaice tace "wani fa zai iya shigowa", yace "wnda ya shigo shi yaga duhu, kowa yasan am with my wife" da haka ya riƙo ƙugunta ya janyota jikinsa ya bata wni kiss a lips, ta zaro ido sai kuma ta fara turasa, ya ɗago hannunta da ya sarƙe da nasa yayi kissing, murya ƙasan maƙoshi yace "i will miss you", suka ringa kallon eye balls din juna, yaja hancinta yace "Silly girl..", ba ta san lokacin da wni murmushi ya kufce mata ba, kawai ta faɗa ƙirjinsa ta kwantar ta kanta gami da lumshe ido tana shaƙar pure scent dinsa. Haka kuwa akay washe gari Anty Zulaihah da Sakeena suka raka Hajar da baby Nanerh har gidan Umma, Umma never expected that don haka a fili ta nuna farin cikinta, Hajar ma dai taji daɗi sosai saidai tasan za tayi kewar mijinta. Duk wadanda basu samu sunje barka da suna ba nan gidan Umma suka biyo Hajar, Sosai Hajar take jin daɗin zama a wajen Ummanta, ga Sabrah anyi ƴa kullum ta goye Nanerh har yarinyar ta saba da baya, gashi mimin Uwa ya amsheta sai narka ƙiba take don yacca tazo ƙatuwa haka ta ɗora, kullum Nurain sai yaxo da yamma ko da daddare, a haka Hajar ta cika sati biyu da a gidan Umma, yau ma dai ta shirya tsaf tana jiran Nurain da yace zaizo, sai ƙarfe 8 na dare ya ƙaraso, ya shigo suka gaisa da Umma kafin ya wuce ɗakin soro wnda yake matsayin sitting room kuma ɗakin Mu'azzam, Hajar ta shiga ɗaki ta amso Nanerh wacca take hannun Sabrah tana mata wasa, Hajar tace "har ynxu dai babyn naki bata isa fara dariya ba ai Anty Sabrah", Sabrah tace "idonta biyu shiyasa nake mata wasa kar tayi kuka", Hajar ta wuce ɗakin soro, shiga tayi tace "Sannu da zuwa My Moon", yace "you're welcome Baby wife", ta ƙarasa ciki, Nurain ya amshi Nanerh yana kallonta, a kullum yarinyar ƙara girma take da kyau, ya jima yana kallonta kafin ya ɗauki wayarsa dake hannun kujera, ya kalli Hajar yace "Come", ta taso ta zauna kusa da shi, kunna wayar yayi snn ya kunna data ya shiga wni page, yayi ƴan danne danne snn ya miƙa mata yace "which one do you like?"........✍️