00
by @maidambu41
SO DA CIWO❤️🩹
Masana ilimin soyayya sun tabbatar da so babu ruwan shi da halitta ko jinsi, babu ruwanshi da yare ko Kabila, so bai san wasa ba, sannan so bai san sabo ba! So Sa'a ce kuma alkhair ce. Sai dai har yau babu wanda ya san yadda so yake da ciwo. Musamman ka so wanda bai san da kai ba! Ba laifi ba ne idan an soka bisa kuskure sai dai kuskuren ka sadaukar da soyayyar da ka gama faffutukar gina shi! Wata duniyar da wata alkaryan! So da Ciwo! Musamman idan ya hadu da raunatattun zukata!
_Duk yadda zan bada labarin wahalar da na sha da Abu Zar tabbas ba zai yarda ba! Na same shi a lokacin da ban zata ba! Nayi kokarin mantar da shi zafi da raɗaɗin da yake ji! Kwatsam duniya da wasu mutanen cikinta su min iyaka da shi? Shin sau nawa aka tab"a saka ka kuka akan wanda kake so? Sau nawa aka tab'a disgaka? Idan har hakuri yana da riba tow me yasa lokacin da na tsinci dami a kala ace ban isa moranshi ba? Mai karatu ka bi labarina a nutse zaka fahimci duniyar da na rayu cikinsa ba iya jinyar zuciyarshi nayi ba sai da na kafa kaina da gwamnatina...._
Kura min idanu yayi kafin ya ce min. Murmushin gefen baki yayi, ya ce mata. "Ok we shall see what can happen next!" Yadda yake rarraba idanunsa a kaina yasa na kara sunkuyar da kai ina matse hannu. Murmushi yayi a karo na biyu ya ce. "Me kika dauke ni?" Ya nuna kanshi yana kallona. Yadda yayi min tambayar ya narka min da zuciya, bakina yana rawa na sunkuyar da kaina cikin wani irin kuka na ce. "Me zan gaya maka Hamma yadda ma dauke ka? Taya zan bude maka zuciyata?"
"Karya kike!" Yusrah Bukar ta banko kofar office dinsa. "Ina jinki Baby gaya min!" Ya fada cikin tattausar murya me kashe zuciyar duk wata y'a mace da ta hadu da shi. D'ago kai nayi ina kallonshi, hannunshi ya kai fuskana yana murmushi. "Ina jinki Auta, yau autancin kike ji? Ko na kira Hamma Jamal."
"Abu Zar! Wai me yasa kake shirin zubar da mutuncinka ne? Taya zaka kalli duniya da manyan Friends dinmu ka gaya musu kana Dating teenage poor village girl." "Mss Bukar ko zaki fita ne?" Ya fada idanunshi a kaina.
"Yarinyar nan dai ba sonka take ba, domin ina da evidance akan yadda take tare da wani, gashi nan Sharahbil gashi nan yadda ta gudu daga gidan Iyayenta ta biyo Uncle dinta, Dr Mansur wanda kake tsammanin likitanka ne turo ta yayi domin dukiyarka." Ta watsar da wasu takardu da hotunanmu da Sharahbil da suka zo tare da Raheemah. Dake kirjina nayi da yake barazanar fashewa nayi na d'ago ina kallonshi kafin na juya ga Yusrah. "Na ji duk abinda kika fada gaskiya ne, kuma Abu Zar ba shi bane karshen rayuwata, idan na rasa shi ina da wasu da zasu tsaya min, ki yi kokarin ture gwamnatin da na kafa ki kafa naki." Na juya ina kallonshi kafin na cire zoben da ya saka min na d'ago hannunshi na saka mishi. " Ka tuna da ni a duniyarka, na so ka kuma zan so ka har karshen rayuwata." Na juya na bar office din.
A bakin office din na ga mutane dayawa sun taru ashe suna tsaye a bakin kofar. Murmushi nayi musu ina me ratsa tsakiyarsu. "Mss Yola, wannan hukuncin bai dace ba, Sir Abu Zar." Murmushi nayi na ce mishi. "Ba kome!"
Na sani nayi laifi, amma kuma akan me rayuwata zata zama hujja akan abin da ya shafi soyayyata! Taya Yusrah ta ɗan Sharahbil? "Raheemah."
______
"Me kika gayawa Yusrah? Me yasa kike ƙoƙarin lalata min gobena? Tun muna yaran nake baki duk wani abin da na mallaka babu zuciya ne a kirjinki?" Na fada a zafaffe.
"Maama kina nufin saboda namiji zaki zo kina min ihu? Saboda wancan bayaraben zaki zo kina kuka da ihu? So gaskiya na gaya mata idan kina sona kamar da ki bar min shi sai a wuce wurin ke fa yar so ce, sannan da kike ihun akan shi kina tsammanin dangi zasu karbe shi je musamman Dr Umar Dattijo Yola?"
kallonta nayi cikin takaici da tashin hankali, ashe da can hauka nayi da sunan soyayya! Ashe da shirme nayi da son Yan uwantanka! Yanzu da nasan So da Ciwo.
"Heemah, shi ɗaya Allah ya bani a yanxu bani da wani da zan dafa." Cikin izgilanci ta ce min.."Ga Sharahbil nan sai ku gyara tsakaninku, idan kika duba Maama kome kin fini, Iyayenmu duk da abin da kika yi suna matukar sonki. Ki har min shima kina da farin jini zaki samu wanda ya fishi. Yadda tayi maganar karshe sai jikina yayi sanyi, tari tayi tana rike kirjinta. "Twins amma kuma na bar miki kome da na samu, wallahi na sha wahala kafin na samu kanshi ban tab'a sanin dadi da wuyar so ba, sai akan shi na bar miki kamar kasada nayi da rayuwata!"
Zaro idanu tayi tana faɗin. "Kenan ba zaki iya bar min namiji ba haba Maama an sauya min ke Maama keda na sani da kaunar duk abin da nake so, kome nake so zaki min Haba Maama shi kenan gara na mutu kawai." A duk lokacin da tayi irin wannan maganar ba karamin cutawa nake ba, ban bata amsa ba sai fita da nayi daga dakin na koma cikin gidanmu ɓangare Kakarmu, Mahaifiyar su Baffa Dada. Ina shiga tana gorza goronta. Na zube a gabanta ina kuka.
"Yau ma ta bukaci ki bar mata wancan kyakkyawar Yaron ko?" D'ago kai nayi ina wani irin kuka, na rasa yadda zan yi."Eh Dada!" "Me yasa ba zaki fada iyayenku ba?"
D'ago kai nayi ina kallonta. "Tausayinta nake ji!" "Zata kuwa kashe ki domin kuwa zuciyarta babu Allah idan har da gaske tana sonki yadda kike sonta ba zata tab'a kallon abin da kike da shi ba!"
Na sani Dadah gaskiya ta fada amma ban san yadda xan yi da Raheemah ba, domin nasan Allah ya daura min kaunarta da sonta, bana mata musu duk da nasan ni ce da laifi na sakewa Raheemah kome na rayuwata har na samu kaina a haka, amma nayi Imani da Allah Ni da Abu Zar Babu me rabu sai Allah, domin ina mishi wani fitinannen kauna ne da nasan shine ajalina. Taya zan bawar Aminayata yar uwata mutumin da nake so? Taya xan lamunci mishi rokon sakaina kashi? Kunsan irin azabar da na sha kafin ma same shi! Lallai ruwan da ya dake ka shine ruwa domin nasan so da ciwo, ina son shi haka ina son abuna, amma ba zan iya ba.
**
"Wallahi na gaya miki Boɗɗo ki jawa Ayuba kunne ya bar min Yarana, babu ruwanshi da Yarana, ina ruwansa!" "Kiyi hakuri Lantana p!" Ta fada tana kallon Ayuba da yake cin abinci hankalinsa kwance kamar bashi ba.
"Allah ya shirya ka!"
"Amin Ya Allah!" Ya furta can ƙasa yana mikewa.
"Innarmu! Tunda nake ban tab'a ganin fushinki ba. Har yau?" "Saboda Allah ya saka min yakana da hakuri akan duk abin da zaku yi, ai nasan ba don kome kayi magana ba sai don gyaran gobensu!"
****
"Wato Malam Salihu, ina kara baka hakuri Yaron nan Bello Allah ya mishi rasuwa a wani gobarar da ya tashi a gidan da suke kwana, sun kone kurmus!" "Timmmmm!" Suka ji zubewar wani magidanci da ya fito daga ban daki!" Koda suka isa kanshi haka suka yi tare tare aka nufi daki da shi .
Duk da a rude take amma kuma mutuwar Bello yazo mata bazata jikinta yana rawa ta kalli Malaminsu ita kanta sai ta rasa mijinta zata duba ko mutuwar danta zata tsaya a kai. Kamar ana turara ta shiga dakin, ta zauna tana kallon mijinta.
***
"Ya sunanka?" Binsu yake da idanun nashi cikin nutsuwa da rashin wayo. "Suna ya sunanka!" Abin da yake kara maimaita kenan.
***
"Assalamu alaikum!" Ta fada tana kafe shi da idanu. Sai da ya kalleta sama da ƙasa, ya ce mata. "Waalaikumunsalam!" Saboda sanin muhimmancin sallama ya amsa mata. "Abu Zar Akindele ko?" "Hmm!" Inda take bai kara kalla ba, ya cigaba da abinda yake. Mikewa yayi yana murmushi. Mika min tea cup yayi cikin gajiya ya ce. "Cupcake na gaji!" Ya fada yana kashe min idanu, a gaban Heemah wani irin kunya ce ta kama ni, duk na diririce. "Hmm sorry na jima!" Matsowa yayi gabana ya cire min abu a gefen kaina. "Muje ko!" Ya fada yana kallona, juyawa nayi na kalli Moon da Heemah. "Hmm drive zai zo daukar mu!" Murmushi yayi yana faɗin. "Muje!"
****
"Abhu, ba laifina ba ne iyayena ne amma ina sonka ita wancan yarinyar da bata sonka fansar da soyayyaarka tayi anya kasan ciwon da yake cikin so kuwa ba." Lumshe idanu yayi ya bude shi akan Yusra, kafin ya ce mata. "She have reasons for sacrifice my love to Yar uwarta, me yasa ke kika gaza fahimtar how i'm? Me yasa kika yi zabi dan uwanki akai na? Maama!" Ya fada yana murmushi sannan ya ce mata. "Kin ga ki tafi Yusrah ba zan kara asarar Cupcake ba, zaki iya tafiya."
"Abhu don Allah kada ka bita Naija please!" Murmushi yayi ya saka kai ya bar parlour ya nufi cikin gidansu. Yana shiga ya samu Professor a zaune yana rike da magazine. "My boy ya dai?" Gyara zama yayi yana kallon Madam Aleesha da take rike da goran ruwa ta mika mishi. "Son ya batun Rahmatullah?" Gyara zama yayi kanshi a sunkuye ya ce musu. "Dad ina son zuwa can ne?" Kusan shekara uku tunda aka fasa auren shi bai kara yarda yayi maganar mace ba, amma yau ya ce zai je gare ta duk da kuwa yaji labarin Rahmatullah amma bai kawo a ranshi yarinyar ce har lokacin ba. "Abu Zar kana ganin babu matsala ko naje da kaina ne!" Murmushi yayi cikin sanyin halinsa ya ce mishi. "Dad am not little boy, ka bani damar zuwa da kaina idan yakin yafi karfina zan sanar maka!"
"Imamu yarka ta turo min kabila gidana, bayan cin zarafina da tayi bai isa ba sai ta kawo min kabila? Bayan cin mutuncina da tayi sai ta kawo min Bayarabe? Ni Umar Dattijo Yola na ce ban amince ba, Haruna Junaid Mairo Zulaiha ku tabbatar ban yarda Rahmatullah ta kara kula Yaron nan ba, kada na kara ganin shi a kofar gidan yaron da kana ganin shi ka ga arne wato Abidah da ke da Hassana abin da kuka shirya kenan? Ku kawo min wanda zai ci zarafina bayan ta ƙi auren zumunci shine zata kawo min arne tubabbe wanda bai da addini? Dubi yadda yaron ban ya tufke gashi kasan yahudawa suka haife shi. Ke Rahama wallahi zanci zarafinki!"
Duk wannan abin da ake kaina na tsakanin cinyoyina ina rusa kuka. "Alhaji dai ayi ta kai zuciya nesa, yanzu an daina auren dole, wadanda aka yi na zumuncin har yau babu zaman lafiya a duba lamarin a bar mata abin da take so!" "Furerah ni kike gayawa magana? Ni kike zubarwa da mutuncin a gaban jama'a?" "Allah ya huci zuciyarka Alhaji ban ga ranar da auren zumuncin yayi ba, tace bata so a bata wanda take so meye laifinta to."
Yadda Datti ya fusata kamar zai daki Dadah yada na kara tsananta kukana, bana tab'a jin ance sunyi koda sa'in'sa da shi ba yau akaina suna fada a kaina. "Kayi hakuri Alhaji in sha Allah ranar juma'a za a daura auren Rahmah da duk wanda kake so!"
"Wallahi idan kuka daura mata aure da wanda bata so sai na bar gidan nan. Abidah da Hassana tunda ba zaku iya magana ba, tow na ga wanda ya isa daura mata aure da wnada bata so, idan kuwa kuna son gamawa da duniya lafiya." Inji Dadah
A fusace Dattijo ya ce mata. "Wallahi da Rahmah ta auri Bayahude gara ki bar min gidana na rantse da Allah ai kema auren zumunta muka yi akan me yasa baki bijirewa Iyayenmu ba sai ita zaki saka ta bijire min, Raheemah ta gaya min kome kece kike zuga Rahmah!"
"Eh saboda baku san kome ba," ta kalli Raheemah ta ce mata. "Allah sai ya sakawa yar batalikan nan, kin lalata tsakaninta da iyayenta Haruna kayi asarar haihuwa, ban miki baki ba amma in sha Allah dai kin yi danasanin abin da kika aikata......
Not love triangle, entangled love ne,.a tsakanin waɗanda mata ukun wacece take nasara.......
----------------
"
_______________
Ahalin Prof AbdulGaffar Akindele Rafiq sun rasa dansu Rafiq
-----------
Haka ma Ahalin Malam Malam Habibu sun rasa dansu Bello
------- shin Bello yana raye ko waya mutu?
#Ramlat A Manga
Mai_Dambu