40
by @faddabanan
Ni duk sai naji ma Abujan ta fitar mun a kai, matar da na gani ɗazun kawai nake tunani shin wacece? Bayanta na gani sai ɗan kaɗan daga gefen fuskarta amma ji nake yi na santa, to a ina? Kawai naji yawon da Ya Khalifa ya fiddo mu domin ni ya isheni, don haka na ce masa mu koma gida kawai don kaina ya fara ciwo. Abba dai na jin mu bai tanka ba sai ma kishingiɗa da yayi tare da ƙara yin bayan da kujerar motar da yake zaune a kai.
Mun isa gida a lokacin da su Auntie suke shirin fita, mun riski su Ya Saif sun ƙaraso su ma. Muna zaune saman dining table muna cin abinci sai ga Ya Khalil hanunsa ɗauke da katin dinner party ɗin abokinsa, wai yana gayyatar kowa na gidan. Abba ne ya fara dariya ya ce "Anya abokinka ya san yawan mu da zai ce yana gayyatar mu? Ai sai mu cike masa hall ɗin taf da 'yan gidan nan!"
Ya Khalil ya ce "The more the merrier, kuma he should be glad we are attending his party. Kai ma ga shi jinkirin da aka samu na tafiyar ya zama sanadin da za ka halarci bikin?"
Ya Khalifa ya yi ɗan gyaran murya kaɗan ya ce "Ni gaskiya zai yi wuya na samu zuwa, i have tons of workload to clear wallahi."
Ni kuma na ce ban taho da kaya irin na zuwa biki ba, don haka ni ma ba zan samu zuwa ba.
Ya Khalil ya ɗaure fuska ya katse zancen mu da cewa "Kai kun ga, ba wani ƙorafi da zan karɓa. Na je na gama cikawa bawan Allah baki kan cewa dukkanku za ku halarta sai kowa ya fara ba ni excuse? Are you for real? Zama muka yi da shi fa na lissafa ku aka ba ni katin kowa." Ya dire mana kati guda uku akan teburin cin abincin ya wuce ya bar mu.
Hakan ya sa washegari da Ya Khalifa ya dawo daga wurin aiki sai ga shi da riguna dogaye 'yan kanti sun sha stones guda uku, nawa, Auntie da kuma Fatima. Yana shigowa ana kiran magriba, kallo ɗaya za ka yi masa kasan ba ƙaramin gajiya ya kwaso ba. Don rigunan ma aiko mana da su ya yi domin mu fara shiryawa.
Ƙarfe tara muka bar gidan zuwa wurin dinner ɗin, kowa da lokacin da ya bar gidan tare da abokin tafiyarsa, kamar koyaushe ni da Ya Friend da Abba ne tafiyar mu ta zo ɗaya. Mun isa mun iske har har ango da amarya sun iso ma. Abba kam tunda ya ƙyalla ido ya hango budurwar Ya Khalil ya dinga yi wa Yayan sigina amma sai Ya Khalil ɗin ya yi kamar bai gan shi ba. Kai Abba da tsokana, wai duk ɓoyon Ya Khalil yau dai sun ganta kuma a ɓagas.
A lokacin da ake kiran sunayen masu zama a kujeru da aka ware domin ƙawayen amarya da abokan ango tare da plus one ɗin su ne, hankalina ya ɗaukantu ga wasu couple da aka kira. Na ƙura masu ido amma hankalina ya fi karkata ga macen musamma da naji an ambaceta da Barrister Rufaida Abdallah. Ai shakka babu sam! Wannan Rufaida ce! Ta zama siririya ta ƙara haske ta yi matuƙar canzawa, irin canjin da ba don nice ba da ƙyar a yi saurin gane ta.
Tun daga wannan lokacin ba wani abu da ake yi a ɗakin taron da ya ja hankalina sama da kallon Rufaida. Neman yanda zan yi mata magana nake yi, so nake ta ɗan kaɗaice ba wai a cikin jama'a ba. Lokacin da aka fara yi wa su amarya liƙi sai na hango tana komawa wurin zamanta ita kaɗai ta baro abokin tafiyar na ta wurinsu ango, ina kuma hangowa har yanzu liƙin yake yi.
Kai tsaye ina sassarfa na doshi wurinta, ban yi wata-wata ba na dafa kafaɗarta tare da ambatar sunanta kasancewar ta bayanta na ƙaraso wurin da take ɗin. Ta juyo ta kalleni kamar mai yin nazarina, fuskarta babu alamar wani emotions haka kuma babu sanayya, kafin ta ce "Yes? Lafiya? Why are you forming familiarity? Did i know you from somewhere?" Ta ƙarasa maganar tana ɗaga girarta guda ɗaya.
Nayi ƙaramin murmushi kawai, ba na haufin cewa ta gane ni amma sai na amsa da cewa Halima ce.
Sai kuma fuskarta ta yaye labulen da tayi mata ɗazun, domin yanzu shan mur ne ya lulluɓe fuskar. Ta karkata sosai yanda za ta ji daɗin yi mun kallon sama da ƙasa sannan ta ce "Lallai na yarda ba ki da kunya wallahi, kai infact wurin da kunya tayi ke kam ba ki san hanyar ba ma bare ki bi ku haɗu. Ni wallahi na zata idan ko a ina ki ka ganni ba za ki nuna kin sanni ba bare har ki samu audacity ɗin zuwa da yi mun magana. Malama (ta ƙarawa ƙwayar idonta girma) tun muna shaida juna ki ɓace mun da gani Halima. Ina so ki sani kin rayu ne a wani ɓangaren rayuwata da ya daɗe da wucewa, na kuma roƙe ki don Allah ki yi zaman ki a can don ba ni da buƙatar ki yanzu ko a wani lokaci daban." Abun mamaki kiɗan da ake yi a wajen bai hana ni jin komai da ya faɗa ba. Ba ta ba ni sararin magana ba domin a fusace ta miƙe tsaye bayan ta kammala caka mun maganganun nan, ta fisgi jakarta ta doshi wurin wanda na gansu tare a wurin bikin.
Kafin na ankara sai hango ta nayi ta nufi ƙofar fita. Da gudu na ƙaraso wurin zamanmu, Ya Khalifa ne kaɗai zaune a lokacin yana shan lemu yana daddana wayar shi, ban ga Abba tare da shi ba. A hanzarce na ce "Ba ni makullin mota Ya Khalifa, don Allah yi sauriiiiiiiiiiiiiiiiiiiii." Gani na a ruɗe sai ya sa ya kasa tambayar komai sai lalubo makullin da ya yi tare da miƙa mun. Warcewa nayi tare da ɗauko wayata da ke zube a gabansa na fice daga hall ɗin cikin sauri-sauri gudu-gudu.
Ina fitowa na hango danjar mota guda ɗaya tana ƙoƙarin barin wurin, ba ma sai na tsaya tababa ba, tabbas Rufaida ce. Wannab karon kam da gudu na isa wurin da Ya Khalifa ya yi parking motar, cikin ikon Allah babu motar da ta tare ta shi, don haka a gaggauce na tayar da motar na faraa bin bayan Rufaida duk da cewa ta fara yi min nisa zuwa yanzu. Na samu sararin bin ta na aƙalla minti takwas kafin ta yi nasarar ɓace mun gabaɗaya. Abin takaici a gare ni bai wuce rashin lura da hanyoyin da na biyo ba, saboda gabaɗaya hankalina na kanta gudun kar ta ɓace mun. Yanzu dai na ɓata ban san ta yanda zan yi na koma wurin bikin nan ba, dole na ja na samu wurin na yi parking.
Ƙarar da wayata take yi ne ya ja hankalina zuwa gareta, kafin na ɗaga har kiran ya yanke. Allon wayar kuma ya nuna na yi missing calls ashirin da takwas kenan. Mamakin yanda aka yi ban ji kiran ba ko sau ɗaya sai yanzu ya kama ni. Kira ne daga Ya Friend, Abba da Safiyya (Auntie), kafin na yi yunƙurin kiran ɗaya daga cikinsu har kiran Ya Khalifa ya ƙara shigowa.
Cike da fargaba ya fara tambaya ta wurin da nake. Jin nace ban san a ina nake ba sai Ya ce na sauka daga motar na zazzaga ko zan ga wani wuri irin shago, restaurant ko wani abu da idan an faɗa za'a iya gane ina ne tunda na ce ni banga wasu da zan iya tambayar ko ina ne wurin da nake ba.
Ranar dai sai wurin ƙarfe sha biyun dare suka gano ni, ashe ba ƙaramin nisa da wurin taron na yi ba, na san da a cikin nutsuwata nake da ba zan iya gudu da motar irin wanda nayi lokacin da nake bin Rufaida ba. Ganin nawa ya sauƙaƙa ne saboda wasu bayin Allah da na gamu da su, su suka tsaya tare da ni har su Abba suka ƙaraso.
Abba ne ya karɓi tuƙin wannan karon, shi kuma Ya Khalifa na tambaya ta me ye ya faru da har na zo wurin da ban sani ba. Na taƙaita maganar da cewa wata da na daɗe ban gani ba ne na biyo sai kuma ta ɓace mun. Abba dai bai ce komai ba.
A gida ma sai da na gama shirin kwanciya bacci sai ga wayar Abba, dole na sanya hijab saman kayan baccin nawa na fito falo wurin da ya ce yana jira na. Shiru gidan ko'ina da alama kowa ya kwanta ko kuma ya shige ɗakin kwanan shi.
Da na fito ma ban jira ya fara magana ba saboda na san dalilin kiran, na ce "Kasan ɗazu wa na bi da mota? Rufaida ce fa! Ka tuna ta? Ƙanwar Ya Buhari."
Cikin ɗan mamaki ya ce "A wurin bikin ki ka ganta?"
Muk ɗan yi maganar sama-sama, ganin cewa i'm okay sai bai wani ja maganar ba ya ce to mu je mu kwanta. Bayan ya daɗa jaddada min cewa "Idan Allah ya nufaci za ku haɗu, to tabbas za ku haɗu. Kar ki ringa damun ki da abubuwan da ba ki da iko akansu."
Washegari a latti na tashi daga bacci, rana ta riga ta fito lokacin da nayi sallar asuba. Ina kuma idar da sallah na ƙara mayar da kaina na kwanta, sai da aka sakko daga sallar juma'a sannan Auntie ta tashe ni.
Lokacin da nayi wanka na fito falo domin cin abinci saboda wata mahaukaciyar yinwa da ta koro ni, nan na iske kafatanin matasan gidan zaune a falo, da alama tun da suka dawo daga masallaci suka zuɓe anan suna ta hira suna raha a tsakaninsu. A cikin hirar ne na jiyo gobe da yamma ne jirginsu Abba, shi da Ya khalil za su tafi Lagos tare, a yayinda da Abba zai bar ƙasar gabaɗaya da misalin ƙarfe sha ɗayan dare. Suna ta tsokanarsa yana mayarwa, dama in dai baki ne to ba'a kada Abba a nan.
Har yamma gabaɗayanmu muna zaune a falon, a faɗar Ya Ishaƙ wai send off ake yi wa Abba. Ya Khalifa ma da zai fita babu yanda bai yi ba nayi masa rakiya amma na ƙi. Fatima da take gefe ta ce "Ya Khalifa na ce na zo na raka ka ai ka ƙi. Ita fa wannan ka bar ta, ga ni take yi tana bin ka za ta dawo ta ga babu Abban ya tafi."
***************
Wayyo ni Halimatu, yau ce ranar da Abba zai tafi. Tun ƙarfe biyu duk mun gama shiryawa za mu yi masa rakiya zuwa airport ɗin Abuja. Wannan rakiyar har da Hajiya amma tana motarsu Ya Saif da Ya Khalil. Safiyya suna cikin motar Ya Ishaƙ. Motar Daddy kuma akwai mamansu Ya Khalifa Ammi, da su Falila (ƙannensa). Kamar koyaushe ni da Abba muna motar Ya Khalifa.
Uku da mintina muka isa filin jirgin sama na Nmandi, huɗu na cika kuma su Abba da Ya Khalil suka tashi zuwa birnin Ikko. Ni kam har da guntun hawaye na yi. Kai sabo dai abu ne mai wahala gaskiya.
Tunda muka fara shigowa cikin gari kowa ya yi nasa wuri, ina nufin mu da muka je rakiya, irin kawai a haɗu a gida ɗin nan.
Muna tafiya ina ta kalle-kalle yanayin garin, ji nake kamar kar mu koma gidan yanzu don da gaske kewar Abba nake yi sosai da sosai. Muna bisa wani titi da ban zan iya cewa ina ba ne saboda ba sanin gari nayi ba na hangi wasu yara a mota, sun tsattsaya a bayan mota suna kallon motocin da ke biye da motarsu suna dariya. Haka kawai na samu kaina da shagalta da kallonsu saboda kamar na san su, lokacin da idona ya sauka kan matuƙin motar kuwa, a take gaba na ya faɗi. Kafin na gama gane me ke faruwa sai gani nayi sun yi kwana a yayinda mu kuma muka miƙe. Cikin ɗagawar murya ina dafe da ƙirjina na ce "Don Allah Ya Khalifa mu bi bayan motar can da ta shiga kwanar can, don Allah, don Allah, don Allah. Ka yi sauri Ya Khalifa kar su ɓace mana Ya ilahi. Pleaseeeeeeee." Ina magana ina waige.
Sai da muka ƙarya ƙa'idar tuƙi sannan muka samu sararin shiga kwanar da suka shiga, cikin ikon Allah sai ya zamo ba wani sauri suke yi ba shi yasa muka iya gano su. Ba mu kai ga cimma su ba na ga ya tsaya gaban gate ɗin wani gida ya yi horn, yana shiga ciki muna ƙarasowa don har ma an rufe gate ɗin da aka buɗe masa bayan ya shiga.
Ya Khalifa ya tsaya daidai gate ɗin yana jiran ya ga me zan yi, sai kawai na danna horn ɗin motar, shiru. Na ƙara dannawa nan ma babu alamar za'a taɓa gate ɗin bare a buɗe. Don haka sai na sa hannuna na danne horn ɗin na ƙi ɗage hannuna, sai ga maigadin ya leƙo yana wani yatsune fuska yana kuma buƙatar son sanin dalilin ƙarar da na cika masu kunne da shi. Na shaida masa wanda ya shiga gidan nan yanzu na biyo.
Duk abin nan da ake yi, Ya Khalifa na zaune uffan bai ce ba har ma na mance tare nake da shi, ta wani ɓangaren miskilin mutum ya yi a rayuwa. Da naga maigadin na neman ɓata mun lokaci da rainin wayonsa sai kawai na sauko daga cikin motar na doshi gate ɗin gaba-gaɗi ba tare da wata fargaba ba. Da alama mamaki ne ya riƙe maigadin ko kuma level of audacity ɗina yake son ya ga zuwa ina ne, don kafin ya ankara har na fusgo ƙofar shiga ta jikin gate ɗin ina ƙoƙarin danna kaina ciki. A guje ya ƙaraso yana ƙoƙarin hana ni amma na ƙi hanuwa sai hakan ya tayar da hayaniya tsakanin mu. Hayaniyar ce ta jawo hankalin waɗanda sike harabar gidan zuwa gare mu. Wanda na biyo ne ya tsaya yana kallona cike da mamaki kafin ya ce da maigadin ya bar ni na shigo, ya yi maganar ne daga can wurin rumfar parking ɗin motoci. Ganin an ba shi umarni sai ya bar ni na shiga a yayinda ya buɗewa Ya Khalifa ƙofar gate ya shigo.