Taƙaitaccen Tunani

42

by @faddabanan

Ko da na koma gida ban wani ɗaga hankalina ba, don ko a jikina ban ji wata alama ta zan yi aure a kusa ba balle nan da sati biyu. Sai kuma na rungumi shawarar Ruƙayya ta dagewa da addu'o'i don na rage bacci kullum cikin dare ina sallah da neman taimakon Ubangiji a bisa lamarin. Ɗan tashin hankalin da na fara fama da shi ma yanzu duk ya tafi, kuma ko da kuskure ban ƙara yi wa Inna maganar ba sai ma sabgar gaba na da na kama. Na san kuma warwarewa ta tana tsorata Inna kawai ba ta son nuna min ne, ba mamaki tsoro take ji ko wani abun nake shiryawa. A haka muke har satin ya ƙare wani ya kama. Duk da cewa Abba ba ya ƙasar amma yana sane da abinda ke faruwa da ni ta hanyar waya.

*****************

Tun ranar Alhamis baƙi ke taruwa a gidanmu duk da dai ba wani mashahurin taro Inna ke shirin yi ba. Gwaggo Hafsatu ce ta sani gaba aka yi mun gyaran jikin da bai wuce na kwana uku ba. Ruƙayya suka haɗa da raka ni gidan ƙunshi da gyaran gashi, komai suka ce a yi da to kawai nake amsawa na yi. Ni kaina mamaki nake ba wa kaina na rashin damuwata akan abinda ake yi, ji nake yi kamar pranking ɗina kawai suke son yi so i'm trying to maintain my 'steeze'. Ni da Rukky kam mun mayar da abun wasa da tsokanar juna, ta yi ƙoƙarin ta gayyato wasu ƙawayenmu na makaranta na ce kar ta soma. Mu sa wa su Inna ido kawai mu kallo ikon Allah. Wannan biki kamar na 'yar tsana?

 

A haka dai aka yi Kamu tare da Yini sai kuma walima bayan an ɗaura auren ranar asabar. Ni ɗaurin ne ma ya sa na gasgata zancen auren. Rukky kam sai kira na matar ɓoyayye take yi muna ƙyalƙyala dariya.

 

Duk aka gama biki kowa ya watse ba'a kaini gidana ba kamar yanda al'adar biki take. Ni kuma na sa a raina in dai ni ce zan tambayi Inna akan wannan batun to kuwa ba zan taɓa sani ba. Har ranar litinin ban ga alamar za'a kai ni wani wuri ba. Dama kuma tunda aka fara biki muna ɗakina ni da Ruƙayya, ban yarda na shiga sabgar kowa ba sannan kana shigo mun ɗaki nake neman yanda za ka fice. Ba kowanne baƙo a gidan zuwa wannan lokacin ban da Gwaggon Zaria, ita ranar Alhamis na ji tana cewa za ta tafi, don haka nake ta yi mata tuni akan ta tunawa Baban Zaria batun neman admission ɗina da Jamb ɗin da nayi yanda zan ajiye diploma ɗin kawai.

 

Ranar talata da daddare Baba ya sa aka kira ni. Faɗa akan biyayyar aure cikin murya mai nutsuwa ya yi mun, kuma sai a lokacin ne jikina ya amsa lamari, gabana ya hau faɗuwa ina hawaye saboda ya yi maganganu masu ratsa zuciya. Ko da na koma ɗakina kasa bacci nayi na haɗe kaina da gwiwata ina tunane-tunane marasa kan gado da alƙibla, a haka na kai har wurin asuba ban yi bacci sai kuma ganin daren ya zo gangara sai na cike shi da nafilfili na sallah ina nemawa kaina albarka da alherin auren nawa.

 

Da safe kam har Inna ta gama haɗe mun jakunkunan kayayyakin sawa na, sai kuma kayan kitchen da na gani a gidan nan, duka an zuba a Hilux. Mu koma muka shiga ƙaramar mota kuma kai tsaye airport aka wuce da mu, watau ni, Gwaggon Zaria sai kuma Rukky. Ni da Rukky mamaki ma ya hana mu magana sai kawai muka zubawa sarautar Allah ido. Wanda ya kai mu airport ɗin ya yi mana komai har zuwa lokacin da muka tafi domin shiga jirgin, shi da Gwaggo kawai suke magana a yayin da ni da Rukky muke ta mu maganar can a gefe.

 

Muna sauka a filin jirgin saman wurin da muka je na fara ɗan mamakin wurin da na gan mu, amma dai na ja bakina na tsuke ban ce uffan ba ina jira na ga ina diramar za ta ƙare. Muka samu waje muka zauna saboda Gwaggo ta ce za'a zo ɗaukar mu ne. Shirun da na yi ina tunani sannan ga gajiya da rashin bacci sai bacci ya fara fusgata sai kawai na rufe ido tare da kifa kaina saman hannun da na ɗora bisa hannun kujerar da nake zaune.

 

Rukky ce ta girgiza ni tana faɗin na tashi ga shi an zo ɗaukar mu. Gwaggo kuma ta hau ja mun mayafin ƙaton gyalen da aka ba ni na rufe jikina da shi tun daga Kano har sai da ta rufe mun kaina. Sai kuma a riƙe hannuna zuwa wurin motar da aka zo ɗaukar mu har ma na jiyo wata zaƙaƙura tana buɗa a cikin jama'a.

 

Ban san a ina Rukky take ba don ban ji duriyarta ba, don haka bacci ne ma ya ɗaukeni a hanya. Guɗa da na ji ce ta tasheni ashe mun iso, har kuma lokacin ban buɗe kaina ba. Amma ina jiyowa ana ta yi wa Gwaggo sannu da zuwa ana kuma ta gaishe-gaishe. A haka aka mana jagora zuwa masaukinmu.

 

Da na ji hayaniya ta yi ta sauƙi sai na ɗan janye mayafin kaina, duk sun fice sai mu kaɗai don haka na yi amfani da damar na ƙarewa ɗakin kallo. Ganin bangane komau ba sai na taɓe bakina na miƙe domin yin alwala da gabatar da sallar azahar. A gefe guda an jera kulolin abinci kala kala, sai na tuna ɗazu da suke fita na ji wata na cewa a bar baƙi sun huta su ci abinci tukunna.

 

Can yamma kuma sai ga kayana sun iso, Rukky ba ta wani ɓata lokaci ba ta hau jera nun sun a wardrobe. Wurin da aka sauke mu shine part ɗina da zan zauna, an zuba komai na amfani har kitchen don ko kayan kitchen ɗin da aka taho da su daga Kano babu wurinsu a ɗakin girkin nawa.

 

Bayan an yi magrib muna zazzaune a ɗakin, ni da Rukky dariyar Ya Saif muke yi akan ya ƙi yarda na yi aure wai. Sai lokacin ma na tuna ban faɗawa Abba na tare ba don haka na fara laluben wurin da ana ajiye wayata domin kiran shi.

 

Kiran layin Abban ya yi daidai da buɗe ƙofar ɗakin da muke ana sallama, muryar da na ji an yi sallama da ita ya sa na ƙurawa ƙofar ido ina jiran na ga waye. Mommy ce ta shigo da fara'arta, da sauri na tashi na rungume ta na ce "Sannu da zuwa Mommyna, ashe kin san nayi aure?"

 

Tana dariya ta ce "Ai dole na sani, auren 'ya ta guda?"

 

Bayan sun gaisa da su Rukky ne nake tambayar ta ina Rufaida, shi ne ta ce "Rana ɗaya aka ɗaura maku aure da ita ai, bayan kin kwana biyu sai a samu mai yi maki rakiya gidanta."

 

Sai da ta gama hirarta da su Gwaggo ta mike za ta tafi sannan ta kalle ni ta ce "Halimatu sai fa kin yi haƙuri, mijin naki ba ya gari gaba ɗaya lokacin ɗaurin aurenku, ai kin ga bai halarta ba ko? Ɗazu ma ya kira waya wai ya...." Ban san ya aka yi ba sai kawai na tsinci muryata na faɗin "Waye mijin nawa?"

 

Mommy ta tsaya tana kallona kamar ba ta gane maganar da nake yi ba, ta ce "Me ki ka ce?" Na ƙara maimaitawa.

 

Ta juya ta kalli Gwaggo tana murmushi ta ce "Kar dai ba ku sanar mata cewa Buhari ne mijin na ta ba?" 

 

Sai da gaba na ya wulla ya hautsina sannan ya fara dukan tara-tara, gumin da na ba na gani ya fara tsattsafo min. Wallahi na daɗe ban samu kaina a cikin tashin hankali irin na wannan lokacin ba. Mommy ta zuba mun ido sannan ta ce "Halimatu da damuwa ne?" Da sauri na girgiza mata kai alamar a'a. Ta yi mana sai da safe ta tafi. Ni da Rukky mun zama so shocked! Abincin da ta zo da shi lokacin shigowarta wallahi ko kallonsu ban ƙara ba saboda na san ina cikin masifa. Mutumin da ya tsane ni? Zan ga ta ya ya za'a yi zaman auren nan kuwa!

 

Gwaggo kam abincinta ta ci ba ta ko bi ta kanmu ni da Rukky da ke zaune muna jimami har wannan lokacin ba, tana sallar isha kuma ta koma ɗayan ɗakin da zummar kwanciya, ta yi mana sai da safe ta kwanta abin ta. Sai kuma a lokacin na samu sararin fitar da abinda ke raina ga Rukky domin ina matuƙar tsoron zaman da za mu yi. Na fi kowa sanin ya fi kowa na gidan tsanata, ban ma san ta ya ya har ta kai ga ɗaura mana aure ba ba cin ga abokinsa Faruƙ. Duk ba na wannan ba, ya fi kowa sanin extent ɗin halin da nasa kaina a ciki can baya. Gaba na har lokacin faɗuwa yake yi. Rukky shawara ɗaya take jadadda mun akan na dage da addu'a da kuma biyayyar aure sannan sai na zama jaruma ta haƙuri dangane da lamuransa kafin na yi nasara. 

 

Ta kuma nuna min ba mu san me ye nufin Allah ba, tunda wa ya taɓa tunanin zan riga ta aure? In ban da Faruƙ ai ba ni da wani tsayayye, shi ma sai mu daɗe ba mu haɗu ba. Kuma har lokacin da aka sa ka bikinta ba mu hango nawa a kusa da na ta ba bare har mu yarda zan riga ta.

****************

 

Kashegari da safe da muka yi waya da su Ya Khalifa, saboda Ya Saif na son ya zo ya ga Rukky kafin su koma Kano, ga shi ni ban san ina ba ne, shine na roƙi Ya Khalifa ya kawo su tunda shi ne ya san gidan. A falon Mommy aka sauke su kamar yanda ta bayar da umarni. Sun yi mun Allah sanya alheri. Ni ranar ma tashi nayi sak mara lafiya, ba ni da kuzari ko ɗan ƙanƙani.

 

Zuwa ƙarfe huɗu na yammacin ranar dukkanin wasu baƙi sun watse a ranar, ciki kuwa har da Rukky da Gwaggo. Gwaggo kam cewa ta yi a mota za su koma ba sai sun hau jirgi ba, don haka hilux ɗin da aka kawo kitchen ɗina da za'a mayar suka shige abin su kawai sai kawai.

 

Tunda suka tafi nake ɓangarena ina kwance abun duniya ya dame ni, sallah kaɗai ke ɗaga ni har ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.

 

Washegari da safe bayan na yi wanka sai na fito na wuce sashen Mommy. A tare muka yi abincin karin kumallo muna ta hira, ina ba ta labarin abubuwan da suka wanzu bayanta ita ma tana ba ni labarin wasu abubuwan. A lokacin ne nasan Anty Aysha a Kaduna take da zamaa halin yanzu sannan yaran da na gani 'yan biyun nan watau Hanif da Hanifa yaranta ne, sai kuma ƙaninsu mai sunan Daddy don da Daddy suke kiran shi.

 

Sannan ta zama serious sosai ta fara mun faɗan riƙe aurena da mahimmanci tana kuma buƙatar kar na kunya ta ta akan al'amarin aurena. Ta ce na dage na zama jaruma mai juriya sannan kar na sake na ba da ƙafar da za'a yi ƙorafi game da ni, kawai na yi iya bakin ƙoƙarina, to in shaa Allah ba ni da damuwa.

 

Ban kuma yi ƙasa a gwiwa ba na faɗa mata batun karatuna a Zaria, ta ce babu damuwa kafin hutunmu ya ƙare za'a tsara yanda zuwana makarantar zai kasance.

 

Ranar da na cika kwana goma sai ga Rufaida ta zo da yamma gida, ita ta tuƙo kanta. Gaishe da Mommy kawai ta yi ta taho ɓangarena. Mun daɗe muna hirar cike gurbi watau labaran abubuwan da suka faru da ɗaya bai sani ba. Kuma a cikin hirar ne naji cewa ashe Ya Buharin ma ya yi aure tun shekara uku da suka wuce, tare suke da matar a Jos. A daidai wannan lokacin na daɗa shiga firgicin zama na da shi, don Allah me yasa su Inna suka sa ni cikin tashin hankali irin wannan? Ita dai Rufaida haƙuri ta ba ni da cewa kuma na daure ko ma me ye zai faru, wata rana komai zai zama labari. Hakan ya sa nasan da wuya idan da yardar shi aka yi auren nan. Rana zafi inuwa ƙuna!

 

Na gaza daurewa har sai da na tambaye ta yanda aka yi aka ɗaura auren mu da shi, gara na san gaskiya na kuma san yanda zan shirya.

 

Ta ce "Tun ranar da ki ka bar gidanmu bayan kin suma sai Mommy ta damu a nemo ki, kin tafi ba mu yi musayar lamba ba duk mun ɗauka za ki sake dawowa tunda kin ga gidan amma shiru. Lokacin da Anty Aysha za su koma KD sai kawai muka tafi tare da su muka je har Kano gidanku neman ki. Inna kaɗai muka samu a gidan, ba ƙaramin mamakin ganin mu ta yi ba barin ma Mommy, tayi ta kuka. Ta kuma shaida mana kina Zaria gidan ƙanwarta kina makaranta ne a can bayan Mommy ta neme ki. Ta tambayi Inna ko kin yi aure ne? Da ta ce mata a'a sai kawai katsahan muka ji ta ce idan babu damuwa tana son ta sake nemawar Ya Buhari auren ki a karo na biyu. Inna kawai ta jinjina lamarin ne akan ya kamata a ji ra'ayin Buhari tukunna don ta ɓangarensu babu matsala amma Mommy ta dage babu damuwa. Daga nan kawai sai ta ce sati mai zuwa za su aiko da kayan al'ada na iyaye da su sa rana. Ko da muka dawo Kaduna waya kawai ta kira Ya Buhari ta faɗa masa ta nemar masa aure kuma tana son a haɗa da nawa bikin tunda ya kusa, wallahi ko musu bai yi mata ba amma tun lokacin zuwa yau bai leƙo Abujan ba kuma bai ce uffan ba. Kin san wannan daɗewar da tayi asibiti ba shi ba, ko a cikinmu so yake ya ji mun ce 'to' akan koma menene ta buƙata daga gare mu balle kuma akan shi." Haka na yini jikina a mace ina jimami.

 

Tun ƙarfe takwas na rufe ƙofar sashena na kwanta na rasa me ke mun daɗi. Can wurin ƙarfe tara da rabi na ji ana ƙwanƙwasa ƙofata, da sauri na tashi na je buɗewa don jin ko me Mommy take buƙata a daren nan. Gabana sai da ya faɗi! Ya Buhari me tsaye fuskarsa a bala'in murtuke, bai jira komai ba ya sako kai ciki, ban da na yi sauri na matsa da tsaf zai bangaje ni ma. Kai tsaye kujera ya dosa ya zauna tare da karkacewa yana zaro wayarsa daga aljihunsa. Ga ni nayi tsayuwata a bakin ƙofa ba za ta kai ni ko'ina ba shi yasa na rufe ƙofar na wuce kitchen na ɗauko masa lemu da ruwa da kofi bisa tray na kawo gabansa na dire tare da faɗin sannu da zuwa. Bai amsa mun ba, hannunsa ɗauke remote yana canza tashoshin TV ɗin da tunda aka kawo ni nake cikin tashin hankali ban kunna ba. Ban daddara ba na sake gaishe shi sai dai an ci sa'a ya amsa ciki-ciki da nuna alamar an dame shi fa don haka sai na miƙe zan wuce ɗakina tunda daman tuni na gama shirin bacci kafin zuwansa.

 

Ban ƙarasa ƙofar ba naji ya kira ni da 'ke, dawo nan', na dawo na zauna a ƙasa ina saurarensa. Ko kallona bai yi ba ya fara magana da cewa "Buƙatarki ta biya tunda kin sa Mommy ta ruguza min tsarina na zama da mace ɗaya. Amma ina son ki sani ba'a ɓari a kwashe daidai, sannan kin yi matuƙar sa'a ni ba ɗan siyasa ba ne don haka gara ma ki sani ba ki da sauran ƙima a idona, ba zan yaudari kaina ko ke ba na nuna maki akasin haka ba. Ina mai tabbatar maki wannan jikin (ya nuna kansa) ba zai taɓa haɗuwa da naki ba, atoh, gara ma ki san wani irin aure ki ke ciki. Kina da damar da za ki nemi saki, ina mai yi maki alƙawarin duk ranar da ki ka nema sakin a take zan ba ki ki ƙara gaba. Kuma wallahi kin ji na rantse (ya ɗaga ido ya kalle ni) idan ki ka kuskura ki ka haɗa ni da Mommy sai kin gane babu komai a cikin shayi ban da ruwa, don kar ma ki ce ban ja maki kunne ba. Now! Leave my sight! Get out!"