Taƙaitaccen Tunani

44

by @faddabanan

Wurin Mommy na fara isa tare da shaida mata dawowa ta sannan na wuce sashena. Da wanka na fara sannan na yi sallar magriba tare da ishan da na ji an fara kira daidai lokacin. Duk wannan abubuwan nayi su ne a lokacin da a ƙarƙashin zuciyata mamakin ganin Ya Buhari a Abuja nake a daidai wannan lokacin. Ko dai wani aikin ya zo domin nasan aikin banki babu ɗaga ƙafa.

 

Sai da na shirya tsaf sannan na kai wa Mommy kayan tsarabar biki mai yawa, kafin na dawo ɗakina na fara warware kayan da na dawo da su, ina tattara waɗanda ban yi amfani da su ba ina sakawa cikin durowar kayana sai gefe kuma ina tara masu datti.

 

Ban ji lokacin da aka buɗe ƙofa ba sai motsin mutum kawai na ji a kusa da ni. Da yake hankalina gabaɗaya yana kan aikin da na ke ba ƙaramin firgici ne ya shige ni ba har ina sakin gogaggun kayan wankin hannuna ƙasa. Ko da wasa kai ko a mafarki ban taɓa tunanin zai shigo har ɗakin baccina ba. Yo zuwan shi ɗaya ne ma fa Abujan tun bayan aurenmu, wanda ni dai na saka shi a ido. Na cije, na daure, na dake tare da tsugunawa na tattaro kayan da suka zube a hannuna na tafi durowar kayan ina jera su kaman shigowarsa ɗakina bai affecting ɗina in whatever way ba!

 

Shi ya fara magana "Sannunki da zuwa" daga jin yanda ya yi maganar nasan gatse yake yi mun sai ban amsa ba kuma ban ƙara baro gaban durowar ba balle na dawo zuwa wurin gadona inda nake ware kayan kenan. Na juyo ina fuskantarsa amma ban yarda na kalli fuskarsa ba sai ma ƙafafuwana da na zubawa ido.

 

A hankali na yi magana, saboda a yanda na san shi a baya ba ya son yana faɗa yana magana ka yi masa shiru ka ƙi amsawa, hakan fusata shi yake ƙara yi. Na ce "Ina yini Yaya? Ya hanya?"

 

Kamar ban yi magana ba ya ci gaba "Watau wuyanki ya riƙa ko Sadiya? Na ɗauka na ce maki kar ki je bikin nan? Watau ke ga ki mara kunya ki ka kama hanya ki ka tafi. Sannan tsabar kin raina ni sai ki rasa ta wurin da za ki sanar mun sai ta hanyar text message ko? Watau na yi duk abinda nake ganin zan yi, you defied my order and even have the guts to tell me you did exactly what i ordered you not to. Sannu Hajiya."

 

Duk yanda na so na yi magana maƙogwarona rufewa ya yi ruf. Ba ihu yake yi mun ba lokacin da ya ke faɗa, amma muryar shi is dangerously low kuma hakan ya ja mun bugun zuciya fat-fat. Ya cigaba da magana "Da alama duk waɗannan abubuwan da ki ke yi saboda aure ba shi da daraja a idonki balle mu gani a mu'amalar ki. Don na tabbatar da kin san ƙima da darajar aure da ba za ki ɗauki ƙafa kin san kina matar aure ki biyo wani ƙato tun daga Kaduna har Abuja ba, shi ba mijinki ko Yayanki ba sannan ba muharraminki ba." 

 

Jin shiru ban amsa ba har lokacin ya ɗan ɗaga murya a tsawace ya ce "Ba da ke nake ba?"

 

In taƙaita maku dai daren nan na sha faɗa, wallahi ni har mamaki na yi akan ban san ya ɓaci da faɗa har ya kai haka ba. Kuma da na buɗe baki zan yi masa bayani ko amsa maganarsa sai hawaye ya hana ko kalma ɗaya fita daga bakina. Har ya gama faɗanshi ya fice zuwa ɗakinsa (na ci sa'a yau an shiga) ya bar ni da tulin kaya a gaba na. Ina kuka ina jera kayan, idan ma kukan ya ci ƙarfina sai na zauna a ƙasa na sha kukana sannan na miƙe na ƙarasa kawar da kayan. Ga gajiya, ga ɓacin rai ga shi gobe zan je makaranta, makarantar da yau ban gama gane kanta ba ma.

 

Tunda na tashi sallar asuba ban koma bacci ba duk kuwa da yanda nake ji a jikina. Na shiga kicin na haɗa masa kalaci mai kyau (Mommy ta yi ƙoƙari wurin koyon girkinmu gaskiya ba laifi, balle yanzu ga komai a wadace a gabana, wasu girke-girken ma sai yanzu nake tuno su).

 

Na yi shirin makaranta sannan na sa ɗaya daga hijaban da siya a Kano har ƙasa sannan a gurguje na je ɓangaren Mommy na gaisheta sannan direban ya tafi kai ni makaranta.

 

Lokacin da na dawo yamma liƙis duk a zatona ba zan dawo na iske Ya Buhari a gidan ba, amma ina shigowa domin shaidawa Mommy na dawo (kamar yanda muka saba tun daa can) kafin na wuce sashena sai na gan shi tare da ita a zaune suna magana, daga gani mai mahimmanci ce, shi ne yake yi mata bayani ita kuma tana saurara.

 

Da daddare kuma yana falona ni kuma ina kicin ina ƙoƙarin rage aikin abinda zan girka da safe tunda yana nan har lokacin, domin da ni kaɗai ce zan iya shan tea da bread na tafi ko na je ɓangaren komai na ɗiba abincin na tafi da shi makaranta kawai tunda tana da mai yi mata girki. Ina daga kicin na ji shi yana yin wayar da take soya mun zuciya, bana jiyo me yake faɗa sosai amma ina jiyo irin dariyar nishaɗin da take sa shi yi. Da na fito zan wuce ɗakina ne na iske yana ce mata da alama abinda ya zo yi zai ɗauki lokaci don yana jin zai iya ƙare satin gabaɗaya a nan, bai san ma ta ya ya zan yi coping without her ba, ko za ta taho gobe idan ya so sai su koma tare kawai? 

 

Ni dai ikon Allah ne ya kai ni ɗakina. Akwai cin fuska da ta kai wannan saboda Allah? Kamar fa an faɗawa kishiyarki ba ki da wani amfani ga mijinku ne a zahirin zance. Akwai wani abinda zai ja mun raini a wurinta sama da haka? Habawa! Shi yasa babu mamaki ta ke nuna ban isheta kallo ba saboda ta san da ni da bango ba mu da wani bambamci a wurin mijinmu.

 

Na yi kuka a ɗakina bayan na rufe, har ban san iya tsawon lokacin da na kai ba. Na dinga roƙon Allah ya sassauta mun irin wannan bala'in kishin Ya Buhari da nake fama da shi. Idan kuma Allah ya san zamana da shi ba alkhairi ba ne ya kawo mana hanyar rabuwa a ma fi sauƙaƙƙiyar hanya.

 

Da safe da yake ba da sassafe zan je school ba, kawai na shirya masa abincin na bari kan tebur na koma ɗaki na kwanta. Baccin da ban yi ba jiya da daddare shine ya ɗauke ni yanzun a ɗaki. Ƙarshe dai makarantar da ban je ba kenan.

 

Tun isowar matarsa kuma sai dai na hange shi, cin abincin daren nan na ɓangaren Mommy na daga cikin abinda na tsana a rayuwata. Matarsa fa sam ba ta san idon suruka ba. 

 

Ranar Alhamis na yanke shawarar ba zan je na ci abinci ba, Mommy har ɗaki ta biyo ni kuma maimakon ta lallaɓani sai ma balbaleni da faɗa da tayi. Faɗa take yi akan ta ga ba wani hoɓɓasa da nake yi game da aurena, kawai na saki komai na sa ido. A ina na taɓa ganin sa ido yana aiki?

 

Ni ban gane me Mommy take nufi da zancenta ba sam. Bawan Allahn nan ko kallona ba ya yi, to me zan yi masa saboda Allah? Kuma ba wani zuwa gari yake yi ba kullum daga aiki dai matarsa ya sani. Daga ranar ban ƙara fashin zuwa cin abinci ba amma ba wani abu da ya sauya a gare ni. Na fi kowa addu'ar su koma wurin da suka fito saboda ko na samu sauƙin faɗuwar gaba, ɓacin rai da gane-ganen abin da zai ɗaga mun hankali.

 

Tun bayan tafiyar na tattara hankalina zuwa ga makaranta. Mommy ta haukatani da shan fruits yanzu, dama tun asali ita ma'abociyar shan su ce amma sai ta ƙara mun. Tun ba su dame ni ba har ba na iya zama ban sha shi ba, haka farfesu. Takanas take dafa mun sai dai na zo na ɗauka ko ta aika mun sashena.

 

 

     BAYAN WASU WATANNI 

 

Wata kusan biyar kenan, kuma a ciki sau ɗaya jal na yi katarin sake haɗuwa da Ya Buhari a gidan, shi ma ina shigowa gidan ko minti biyar ban yi ba aka tafi kai shi zai hau jirgi zuwa Lagos. 

 

Yau kuma ta kasance ranar da na kammala jarabawar zango farko na jarabawar da nake yi, na dawo na iske gidan a cike da motoci, ban ma ba wa kaina wahalar yin horn domin a buɗe mun na shiga ciki ba don babu hanyar wucewa. Parking na yi can gefe na shigo gidan a matuƙar gajiye ina mamakin a ina muka samu waɗannan baƙin haka? Har na bar gidan nan mu kaɗai ne da Mommy. Motar Rufaida da wasi tsirarrun motoci da na gani a cikin harabar gidan sai ya ba ni damuwa na fara azamar shiga ciki gidan don sanin me ke faruwa.

 

Sashen Mommy tunda na doso shi hayaniya ce kawai take ta shi amma irin ta hira da dararraki. Gab da zan shiga falo naji an zo da gudu an rungumeni, Hanifa da Hanif ne. Na rungume su a zuciyata nace har su Anty Aysha suna nan kenan?

 

Ina shiga na fara gaisar da mutanen da na iske ina kallon su. Abun mamaki yau a falon nan har 'yan uwan Daddy na gani watau su Kawu Sagir sannan ga Ya Buhari a cikinsu amma yana wani nishaɗi da jin daɗi da har sai da zuciyata ta yi rawa don na manta rabon da naga farin ciki irin haka a fuskarsa, ni gani nake kaman ma idanuwansa kyalli suke yi. Rabon da bawan Allahn nan ya kalleni ba zan iya cewa tun yaushe ba ne, amma he really look me in the eyes and smile. Ji na yi kowa na falon ya ɓacewa ganina, shi kaɗai ne focus ɗina, wallahi a cikin kaina ji nayi kamar babu kowa a falon sai ni da shi ko kuma irin kamar kowa ya ɓace ɗin nan. Abu ɗaya ne ya maido ni cikin hankalina watau irin yanda Rufaida ta rungumeni, gaskiya ina jin da gudu ta zo domin ji nayi kaman ta ɗan tura ni kaɗan.

 

Sai ƙwaƙwalwata ta ɗauki sakwanni sannan na gane me take faɗa min, cewa ta yi 'yar uwa ki taya mu murna, bayan waɗannan shekarun da sha yau dai Allah ya yi an saki gabaɗaya kayayyakin Daddy da aka kama na kamfanoninsa. Allah ya karɓi addu'ar mu ya yanke mana iya haka.

 

Mommy kam cewa tayi na je nayi wanka na ci abinci na huta, saboda tun safe bana gida. Ga shi ma lokacin an fara kiran sallah. Sai da na baro can na taho sashena sannan na lura ashe yau ko matarsa ban lura ko tana wurin ba ko a'ah.

 

Bayan na isha na je ɓangaren Mommy don sanin ko akwai abinda zan taimaka da shi saboda gida da ya ke cike da mutane. Na iske Rufaida da mijinta za su tafi, haka ma su Anty Aysha za su wuce masaukinsu na cikin gidan (ɓangarensu ɗaya da su Ya Buhari amma ƙananan sashe ne da kowanne guri ƙofar shi daban) ta bar mana su Hanifa anan ta ɗauki Daddy ta wuce da shi saboda ƙuiya yake yi.

 

Ban ga 'yan uwan Daddy ba amma na ji Mommy na cewa a je guest room (can hanyar gate) a kai masu ruwa mara sanyi, ina jin sun buƙace shi ne.

 

Ban ɓata lokaci ba na ɗauki su Hanif muka wuce sashena na kunna mana carton muna kallo muna shan yoghurt da na nemo a fridge ɗina, kowa da robar na sa a hannunsa.

 

Wurin ƙarfe tara Mommy ta aiko a ɗauko su wai zasu yi shirin bacci. Na bi bayan ɗan aiken domin roƙonta akan ta bar su mu kwana don Hanifa ma har ta ɗan fara bacci. Amma sai cewa ta yi "Ni kam Sadiya ban san lokacin da za ki yi hankali ba, oh ni! Yaushe rabon da ki ka ga mijinki? Yanzu kuma da yake gari shine za ki kai masa 'yan kwana? Hala dai zamanki a haka ba ya damun ki ko?" Ban jira ta ƙara cewa komai ba don na ga kaman yau sakin layin za ta yi na ce "To bari a kawo su." Na fice da sauri.

 

Tare muka koma da mai taho da su, ni kuma na kimtsa wurin na kashe TV na wuce ɗakina na kwanta. Ko minti talatin ban yi da kwanciya ba na ga kiran Ya Buhari ta waya ta.

 

A falo na iske shi yana kallo, bai kalleni ba wannan karon. Kawai ya buƙaci na haɗo masa fruit salad ne. Na riga na saba da fruits saboda Mommy don haka ko da yaushe bana rabo da su, don kai tsaye na je na haɗa masa. Ban kuma tambaye shi wane iri yake so ba kai tsaye mai madara na yi masa bayan na ga kankana da ayaba ne yayi mun saura a firij ɗin.

 

Tun kuma faɗan da Mommy ta yi mun kwanaki na daina bar masa waje idan na kawo masa abinci, can gefe nake zama na jira ya gama na kawar kafin na ba shi wajen. Yanzu ma haka na yi, zama na yi na haɗa gwiwata na sa kaina a samanta ina kallon TV amma bana gane me ake yi.

 

Zuciyata ta dinga tunzura ni akan na yi masa murnar abinda ya faru tunda na shigo ɗazun ai ba magana muka yi ba. Ina son yi ina tsoron gwasalewarsa, kaɗan da aikinsa. Maganar ce ta fito ban shirya ba, don haka a tsorace na yi masa murna na kuma yi shirin jin ya gwale ni amma ikon Allah wai Ya Buhari ne ya zauna yau yana mun bayanin abubuwan da suka wanzu a baya game da irin wahalar da suka shiga sakamakon kama kayan nan da aka yi. Maganar ta gaskiya jarumi ne Ya Buhari, daga labarin da ya ba ni na gane shi ya ɗaukewa ragowan 'yan gidan damuwarsu shi kaɗai. Sannan ya tsaya tsayin daka da kawunansu suka kasa samun sararin wawure abinda ya yi masu saura ciki har da gidan nan na Abuja da a faɗarsa Daddy ya siya babu daɗewa ya rasu. Matsalolin rasuwar Daddy sun sa shi ya yi girman da ya wuce shekarunsa. Shi yake ba ni labari amma ni nake yi hawaye.

 

Ganin ina hawaye ya sauko ƙasa tare da jawo ni kusa da shi muka zauna tare da jingina da kujera. Ya ce "Ashe dai har yanzu Sadiya ruwa-ruwa ce, har na tuna lokacin da ki ka kuka saboda su Kawu Sagir sun takura mun." Yana dariya.

 

Wani sanyi ya ratsani jin sautin dariyarsa, ban san a shagwaɓe na yi magana ba sai da maganar ta fito "Ni ban yi kuka ba, yanzu ma ai ba kuka nake yi ba."

 

"To na ji. Ruwa ne ya shiga idon ki ko?"

 

"Ni babu komai......"

 

Ya katse ni "To mu ga ido don na yi alƙalanci da kaina."

 

Na goge idona na ce ga shi. Ya ce kin yi algus malama. Sannan ya ƙarasa ba ni labarin zirga-zirgar da ya dinga yi a watannin bayan nan duk akan zancen kayan ne, kuma sun samu taimako ne daga ɓangaren mijin Rufaida...

 

A haka dai labari ya sauya zuwa abinda na cire rai a kan sa a tsakanina da Ya Buhari. Ni dai ban taɓa shiga tashin hankali irin wannan ba, ban san ko tashin hankalin ne ya sa ni wahala a hannunsa ko a'a daɗewar da nayi rabona da abun ne ko kuma yanayin halittar Ya Buhari da Yallaɓai ce ba ɗaya ba ni dai ban sani ba.

 

Washegari da sassafe ya bar Abuja don farkawa nayi na iske ba ya nan. Rashin sanin madafa ya hanani kiransa a waya na ji ya ya hanya saboda ai ban faɗa mun zai yi tafiya ba. Ina ga tare da Kawu Sagir suka tafi domin ban gansu ba lokacin da na fito ba.

 

Na shiga ruɗani, jiya ya kasance da ni a matsayin matarsa duk a zatona ya huce komai ya wuce shi kenan amma ko a rubuce bai bar mun saƙon cewa ya tafi ba. Ni ɗin ma Rufaida ce ta faɗa cewa ya je kwaso kayan kamfanin ne domin kai su Kano da sauran shirye-shirye. Har zuwa dare da kowa ya watse zuwa wurin da ya fito bai kira wayata ba duk kuwa da naji suna waya shi da Anty Aysha ɗazu da rana kafin su tafi. Yaƙe kawai nake ta yi kamar ban damu ba. Ni Halimatu wace irin rayuwa na shigar da kaina ya Allah?!