45
by @faddabanan
Akwai certain mutane a rayuwa da a ce kullum za ka gode masu saboda kawai suna raye ko da basu ɗaga yatsa domin su taimaka maka ba, godiyar ba za ta taɓa isa ba saboda yawan kirki da halin kirki da Allah ya wadata su da shi. MAMAN ASLAM you are indeed one. Allah ya sauƙaƙa maki rayuwarki da ta iyalinki har ƙarshen duniya, ya ba ki abinda ki ke nema na alkhairi. Sannan gaisuwa ga Minal, Aslam da babana Faruƙ, yarana masoya shayi kamar ni nan 😂, Allah ya yi maku albarka.
Faddabanan Family i hail ooo! I love you to the moon and back! Sai dai a yi mun afuwa ban fara typing da wuri ba bare na jero sunayen active members, but just know i appreciate you all, i enjoy all the comments, jokes, checking on each other and i want you to know ban ɗauke ku for granted ba, i super enjoy your company! Kar a manta dai idan an ga na sauka daga titi a ɗan taɓo kafaɗata don kar na yi cikin daji ban lura ba...lol. Kowanne gyara is most welcome.
Abun farin ciki da ya samu members ɗin mu tun daga aure da haihuwa, muna yi maku fatan alkhairi, Allah ya sa albarka. Ameen. Marasa lafiya ko masu marasa lafiya muna addu'a Allah ya basu lafiya, ya sa kaffarar jiki ne. Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.
**********************
Wasa-wasa har sati ya ƙare babu kira ko wata magana daga gare shi. Hakan ya sa na rame saboda ko ruwa mantawa nake yi na sha balle abinci, tashin hankali ya sani gaba ban san a wane mizani nake ba a wurinsa ba. Don da wannan shirun da ya yi mun gara ya yi magana ko fargabar za ta sake ni idan na san mazauni na. Ga shi babu makaranta balle na ɗan samu abinda zai ɗauke mun hankali ko da ɗan kaɗan ne.
Ranar talata ina kwance a kan kujera a sashen Mommy da daddare, idona yana kan TV amma babu abinda nake fuskanta domin tunani nake yi. Nasan Mommy waya take yi amma ita ma bana jin me take cewa tunda hankalina ba ya kusa da ni balle ƙwaƙwalwata ta fassara mun abinda take faɗa.
Jin ta ambaci sunana ne ya sa hankalina ya dawo gare ta, naji tana cewa "Eh Halimatu ba? Ina ga dai ƙila zazzaɓi take yi a tsaye, gabaɗaya ta zabge kwana biyun nan kuma ba ta da aiki sai kwanciya. Na ba ta wayar?" Sai ta saurara kafin ta sake cewa "Oh okay, ya fi ma." Ta yi sallama ta katse wayar.
Sai lokacin na ɗago kaina na kalleta ina faɗin ni Mommy na faɗa maki lafiyata ƙalau fa. Tana gyara ɗan kwalinta ta ce "Ke ni raba ni da maganar lafiya ƙalau ɗin nan ta ki. Ina kallon ki ɗazun ki gama tuttura abinci a plate sannan ki ka mayar da shi kicin. Kuma ya ce mun ɗazun da safe da kuka yi magana ba ki faɗa masa ba."
Na ce "Wa?" Saboda nasan ni ban yi waya da wani yau ba.
Ta harareni kaɗan ta ce "Mijinki mana"
Na yi ajiyar zuciya ina gyara kwanciyata na ce "Ai dama na faɗa maki ba wani abu ba ne, shi ma ban faɗa masa ba saboda babu amfanin ɗaga masa hankali babu dalili."
Ta ce "Na ji Madam lafiya lau, yanzu dai tashi ki tafi ɓangarenki, ya ce zai kira ki nan da minti talatin."
Har sha ɗayan dare babu alamarsa, kuma in dai daga bakina Mommy za ta ji ba ya kirana to tabbas ba za ta ji ba, i'll play along. Idan ya faɗa mata ya kira ni, to ya kira ɗin kawai. Da yake halin ɗan adam ne mantuwa kafin sati biyu fargabar ta ragu duk da ba ta tafi ba saboda har yanzu a lingering issue abun yake domin ba'a kawar da shi ba.
Satin da muka gama hutu naji ana maganar Mommy za ta tafi medical checkup, kaman kowacce shekara sai ta je tun bayan accident ɗin nan, dama ga shi kwana biyu tana ƙorafin bayanta ya na damunta. Shirin tafiyar ne ma ya kawo Rufaida gidan, ashe koyaushe tare suke zuwa, duk da cewa yanzu haka Rufaida ciki ne da ita.
Watau duk yanda na zaci Ya Buhari ya wuce nan akan Mommy da 'yan uwansa. Duk a zatona talauci na bala'i suka shiga bayan rasuwar Daddy, ashe abinda ya tattaro da Daddy ya bari, Rufaida take ba ni labari, ya siyar da na siyarwa, ya kuma juyar da wasu abubuwan na shigowar kuɗi, sannan ya tattare kuɗaɗen gabadaya akan Mommy da Rufaida kaɗai. Ita Anty Aysha ya ce tana da mai kula da ita, shi kuma aikin bankin da ya samu a Jos da shi yake hidimarsa shi yasa ya tsuke kansa. Wani tausayinsa ya tsirga mun a zuciya, watau ya gwammace ya yi irin waccan rayuwar don kawai ya yalwata Mommy da Rufaida. Ko ba'a ce komai ba kana ganin gidan Abuja kasan ya fi ƙarfi talaka wallahi. Kawai dai idan ka haɗa rayuwarsu da ta baya to tabbas za ka ce sun samu karayar arziki amma ba wai talauci ba.
Ranar da za su tafi babu wurin da na je, ina tare da Mommy kamar zan yi kuka ganin ni kaɗai za'a bari sai masu aiki. A haka ma gidan ya yi mana girma balle kuma ba ta nan gabaɗaya na kwanaki? Ya Buharin ma ya zo yana gari tun jiya da daddare amma har yau ɗin da azahar ta yi ban ji ɗuriyarsa ba balle na gan shi. Amma na ga ranta ya daɗe ta shigo ta gaishe da Mommy, ni kuma na yi dabara na wuce banɗakin Mommy kamar zan yi wani abu a ciki.
Lokacin da na fito Mommy ta zuba mun ido kuma na san maganar da za tayi don haka na yi saurin katse ta da cewa "Mommy don Allah don't say anything."
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Well, not now. Amma idan na dawo dole nayi magana kar ku maida ni uwar banza."
Ban amsa abin da ta ce ba, sai na taso na rungumeta na ce "Ni dai kawai ki je ki dawo lafiya shine addu'a ta, ko kullum bulala za ki dinga mun gara na dinga ganin ki."
Ta yi dariya domin ƙara mun ƙarfin gwiwa saboda ta lura tafiyarsu da suka yi hatsari a cikinta ne yake dawo min nake a matuƙar tsorace da tafiyar ta ta. Ta ce "Ki ce na siyo bulalin dukan doki daga can kawai." Ni dariyar ma kasa mayar mata na yi.
Da yamma Rufaida da mijinta suka zo ɗaukar Mommy, ya ce zai tafi tare da su saboda Ya Buhari yanzu ba zai yiyu ya bar gari ba yana ƙoƙarin tayar da kamfanin Daddy na Kano. Sannan ga ƙarin matarsa na da ciki. Ina matuƙar sha'awar soyayya Rufaida da mijinta wallahi, kowanne a cikinsu ƙoƙarinsa bai wuce na ya farantawa ɗan uwansa ba, haka wanda aka farantawa ƙoƙari yake ya rama shi ma. They are so selflessly inlove with each other.
Sai kuma a lokacin ne na yi katarin ganinsa a harabar gidan shi da matarsa, za su yi rakiya zuwa airport. Ni dai ban san lokacin da na fara kuka ba, komai ya dagule min. Mommy ta dinga rarrashina tana cewa "To da wannan kukan da ki ke yi Halimatu ai gara ki yi mun addu'ar zuwa da dawowa lafiya ai. Taho mu tafi airport ɗin sai ku dawo tare da su Buhari." Da sauri na girgiza kaina akan ba zan je ba sannan na daure na saketa don kar na ɓata masu lokaci. Na rungume Rufaida ina ce mata ki dame ni da waya don Allah da zarar kun sauka, ki yi ta bani rahoto. Ta janye jikinta cikin ɗaga murya ta ce "Yes Ma!" Na fara dariya da hawaye a idona na juya na koma cikin gida don ba zan iya kallon tafiyarsu ba.
Har safiya ban ji komai ba kuma hakan ne ya sa na ɗan saki jikina, saboda lafiya ce ke ɓuya. Sai wurin ɗaya yau nake da lectures don haka tun goma da rabi na gama shiri domin so nake na fita da wuri, maybe fita wajen zai rage mun kewar da nake yi. Makullin mota ta na sashen Mommy tun shekaran jiya da ta bayar a gyaro mun na manta su a can. Na yi murmushi da na tuna ranar tana cewa ki tabbata kin ɗauki makullanki kar ki zo kina tashina da sassafe saboda za ki fita tun bakwai.
Kai tsaye can na dosa tunda nasan ba ta rufe ba, kawai kayayyakinta masu mahimmanci na taya ta kwashewa muka sa su a ɗayan ɗaki aka rufe. Ko ka yarda da mai aiki sai ka ɗauke abinda zai iya jan hankalin su.
A hankali na yi sallama na shiga falon don a zatona babu kowa ciki, amma sai na yi mugun gamo. Ya Buhari ne zaune saman kujera, na shigo a daidai lokacin da matarsa take gota shi shi kuma ya miƙo hannu ya riƙota yana cewa "Ina za ki? Zo nan ki ba ni labarin abubuwan....." Ban jiyo me ya ƙarasa faɗa ba amma ya jawota tare da ɗorata saman cinyarsa, kuma maganar shi ta yanke mun ne saboda cusa kansa da yayi tsakanin wuyanta. Ba su ji sallama ta sam ba.
Da na shigo na ɗauka naji sanyin AC amma yanzu wani mashahurin zafi ne ya ke ɓulani ta ko'ina, kamar na cire mayafina da rigata na zubar nake ji. Cike da ƙarfin hali na yi sallama da ƙarfi yanda za su iya jiyowa sama da dariyar da take ƙyalƙyalawa daga abinda yake yi mata da su kaɗai suka sani. Duhu ya fara taso mun ta wurin idona ina ƙoƙarin kawar da shi na daure na ɗaga ƙafata ina cewa a zuciyata "Allah ka rufa mun asiri na fita daga wurin nan da ƙimata cikakkiya, Allah ka rufa mun asiri na daure kar na yi wani abinda zasu gane abinda suke ciki ya dame ni." Na wuce su zuwa wurin console na tsakanin falo da ɗakin kwanan Mommy watau wurin da na zuba makullin kenan, sannan a hankali kamar babu damuwa a tare da ni na ce 'Ina kwana' ban kuma damu da ko sun amsa gaisuwar ba ko a'a.
Cikin ikon Allah sai ga shi na fito har na buɗe mota na shiga na tayar, sai na fito daga gidan sannan na yi parking ta ƙarshen layin domin na samu nutsuwa. Jikina rawa kawai yake yi sai da na kai mintina kusan goma sannan na ji na fara jin iska tana shiga ta duk da cewa na kunna AC ɗin motar tun fitowa ta daga gidan. Sai kuma a lokacin ne na ji damshi bisa fuskata alamun kuka nake. Sai da na ƙara kusan minti ashirin karfin na samu irin nutsuwar da nake buƙata, sannan na kuma na roƙi Allah ya kawo mun mafita. Na san ya sa ni a cikin halin da nake ciki ne don ya san zan iya ɗauka.
Gabaɗaya yinin ranar na yi a cikin matsanancin baƙin ciki da kishi ne, bini-bini sai na faki idon jama'a na goge idona saboda hawayen da suka ƙi tsaya mun tunda har wannan lokacin su nake hangowa a cikin idon zuciyata da na zahiri. Kuma fa ko da wasa bai kalle ni ba. Kai jama'a!
Ko da na koma gidan ma salin'alin na wuce ɓangarena don ba ni fatan na gansu daga shi har ita. Na kulle kaina sannan na fara neman abinda zan ci, ina jin kukan da na sha yau kwashe mun ciki ya yi don bala'in yunwar da na kwaso har jikina rawa yake yi.
Sai kuma a lokacin ne Rufaida ta kira ni, har tana ba ni haƙuri da sai yanzu suka settling sosai. Wannan ne ya ƙarasa kwantar mun da hankali tare da ba ni nutsuwa duk gabaɗaya ranar. Alhamdulillah ala kulli haal.
Har suka tafi ban ƙara sa ɗaya daga cikinsu a idona ba. Sai yanzu na daɗa gane cewa zuwan da yake yi ɗakina aikin Mommy ne, tunda ga shi ba ta nan ya yi kwana biyu amma ko nema na bai yi ba.
Ruƙayya ta zo Abuja takanas gani na, Ya Saif ne ya kawo ta, yana kuma sauke ta ya tafi. Har yau na kasa faɗawa Rukky irin zaman da muke yi da Ya Buhari, haka kawai nake ji bai kamata kowane mahaluki ya ji batun nan ba. Rukky ta canza ta yi ɓul-ɓul da ita, don ma tana da ciki. Har ina tsokanar ta cewa da shi tayi tuntuɓe a ƙofar ɗakinta ranar da muka kai ta da alama tana ta dariya. Ya Khalifa gaisuwa ya aiko mun da shi bai zo ba.
Ranar da Mommy za ta dawo kam gidan ma a cike yake don su Anty Aysha ma har sun kwana suna jiran dawowarsu. Ni kuma ina kitchen tare da masu aiki duk wani abin kusa da baki da na san Mommy ko Rufaida na so ba wanda ban tanadar masu ba, rabona da farin ciki irin na ranar har na manta.
Tunda suka duro muke zaune a sassanta muna ta hayaniya, ita ma anyi da ita ta kwanta ta huta ta ce ta sha bacci a jirgi. Sai can yamma sannan na ɓallo na yo sashena.
Turus na tsaya a bakin ƙofar falon bayan na buɗe, Ya Buhari ne ya jingina da kujera ya sa tafin hannunsa ya rufe fuskarsa. Ɗazun ya zo da rana lokacin muna ɗakin Mommy ina dannawa Rufaida ƙafarta wai sun yi mata tsami, don haka ban gan shi ba.
Kuma a sanin da na yi masa wannan zaman alamu ne na abu na damunsa, da alama ya gudo nan ne domin gujewar hayaniyar mu. Na mayar da ƙofar na rufe sannan na taka a hankali na sauke duka labulayen ɗakin domin ya yi duhu, na kashe wutar sannan na kunna TV tare da kashe maganar TV ɗin gabaɗaya, yanda nasan yake buƙata idan yana brainstorming na neman maslaha a cikin matsala. Sannan na koma kicin na ɗora tea a fancy tea pot na saka duka kayan ƙamshi sannan na zuba sukari ya yi zaƙi ba wai don yana da shan zaƙi ba ne, a'a, amma a irin wannan lokacin nasan yana son abu mai zaƙin. A hankali na ɗauko na kawo na ajiye a tebur ƙarami na kusa da kujerar da yake zaune kafin na wuce ɗakina tare da rufo ƙofar a hankali don kar na dame shi.
Sai bayan isha na fito falo, na iske tea ɗin ya wuce rabin tea pot ɗin don haka na sake zuba wani ruwan tare da sake dafa wani tunda nasan zuwa yanzu spices ɗin cikin shayin sun ƙara tsumuwa a ciki. Shi kuma Ya Buhari ba ya ɗakin ban san ina ya je ba, har ma ya kunna fitulun da na kashe masa. Sai na kasa komawa cikin gida kawai na kwanta a falon abu na.
Ban san bacci ya ɗauke ni ba sai da na ji an ja ƙafata a hankali sannan na buɗe ido da sauri, yana shirin zama a kujera da ke nesa da ni ya ce "Ki je ɗaki ki kwanta mana."
Na miƙe tsaye amma ba ɗakin na wuce ba kicin na je, na ɗauko tea ɗin da na sake dafawa sai na haɗo da snacks, a cikin waɗanda muka yi wa su Mommy ne na kawo masa sannan na samu wuri na zauna a ƙasa saboda na ga kaman ya warware ba irin ɗazun ba. Ban yi magana ba sai kuma na yi sa'a movie ɗin da ake yi a talabijin ya ja hankalina sosai, don yanzu na tsani kallon na soyayya.
Gyaran murya kaɗan ya yi hakan ya sa na juyo da sauri wurinsa don na ɗauka ko ƙwarewa ya yi, sai kuma na ce "ko na kawo ruwa?"
Ya girgiza kai ya ce "Thanks for all of this" ya faɗa yana nuna abinda ke gabansa tare da buɗa hannayensa kamar yana nuna falon gabaɗaya.
Wani irin daɗi ya tsirga zuciyata amma ban nuna ba, sai na ce "Do you want to talk about it?" Ya kalle ni kamar bai gane me nake nufi ba don haka sai na ƙara da cewa "The thing that's bothering you."
Ya ce "Ah! Zancen kamfanin nan ne fa. Abubuwa sun yi mun yawa ni kaɗai, ga shi mutane babu amana ban san wanda zan yarda da shi ko a'a ba. Sannan a wurin aiki na ɗauki leave without pay su kuma sun fara damu na akan na koma ko na ajiye aikin, dama abokin Daddy ne ma ya sa baki a ka bani da farko. Kullum ɗin duniya sai na tuna Daddy, ba ma kaman kwanakin nan. With him komai da sauƙi yake zuwa."
Na ɗan yi shiru sai kuma na ce "Ina wannan Mr. Victor ɗin nan? Wanda Daddy yake yawan bar maku aiki tare idan zai yi tafiya lokacin can?"
Ya kalle ni kallo na sosai kafin ya ce "Abinda na yanke shawarar yi kenan ɗazun, watau nemansa. An ce yana Port Harcourt, har ma an ba ni lambarsa. Ina ga gobe da safe zan kira shi."
Na yi sauri na juyo na kalle shi "Ina fatan ba maganar za ka yi masa ta waya ba ko?" Kafin ya yi magana na katse masa hanzari na ce "Kawai ka je ka same shi har can, shine za ka samu high chance na convincing ɗinsa na ya biyo ka ya taimaka maka for the take off ko da bai zauna ya yi aiki da kai ba. I take that he works in a far better place than a start up company ko?" Irin kallon da yake mun sai da na yi murmushi na juyar da kaina. Bai ƙara magana ba sai shi ma ya taya ni kallon abinda nake kalla, da aka gama na yi masa sai da safe tare da kwashe kayan ya gama ci na wuce ɗakina. Na kuma tashi da safe na iske ya bar Abuja da sassafe.
BAYAN WATA UKU
Abubuwa da yawa sun faru ciki har da kammaluwar zancen kamfanin Ya Buhari. Tun zuwan da ya yi bai ƙara zama da ni mun yi magana ko minti biyar ba, ban ce waya ba domin ba ya kiran waya ta har zuwa wannan lokacin. Ban da da safe na iske ragowan tea a kicin da sai na ce mafarkin abinda ya faru na yi. Duk da har yanzu ban san ina ya sa gaba ba, amma na ɗan samu sauƙin damuwata.
Zuwa wannan lokacin kuma ya ajiye aikinsa na Jos ya ɗauki matarsa sun koma gidanmu (ko gidansu zan ce) na Kano. Bai cika zuwa Abuja ba ban kuma san a wane hali yake ciki ba.
Ranar talata Rufaida ta haihu, ɗiya mace. Kasancewar muna hutu a school tunda aka yi waya aka ce ta haihu (sun ƙi faɗa mana da suka kai ta asibiti don kar a ɗagawa Mommy hankali wai), na ɗaga jaka akan zan je can. Amma Mommy ta ce mu dakata a dafa mata abu a tafi da shi, sai kuma ta yi kara ta ce naje yau gobe sai mu koma tare. Rufaida kam har da tsokana ta wai daga ni har uwargidana mun ƙi haihuwa, ga shi kuma Ya Buhari da son yaran jama'a. Ban biye mata ba, amma a zuciyata cewa na yi uwargida ta ƙi haihuwa dai (kai jama'a, ashe kishi har yanzu bai bar ni na faɗa maku sunanta ba ko? Khadija aka ce sunanta), ni da hanyar haihuwar ma sau ɗaya aka bi da ni kuma dukkan alamu sun nuna tsautsayi ne.
Gudun ma kar ta ja maganar sai na shiga kicin zan gasa mata naman da za ta ci. Tun ina aikin na fara jin jiri da tashin zuciya. Haka na dinga sa ka kaina ta waje ina gudun iskar kicin ɗin har na samu na gama na kai mata, na kuma hau kan gadonta na kwanta domin tare jirin. Tana buɗe kwanon lokacin da ta zauna za ta ci ban san lokacin da na miƙe tsaye ba sannan da gudu na doshi banɗakinta. Har yamma amai nake yi a gidan Rufaida ga shi na kasa cin abinci sai jikina ya saki.
Waya suka yi suka sanar da Mommy domin ba zan iya tuƙa mota na koma gida ba a wannan halin ba, na ki matsawa daga kusa da banɗakin saboda yanda nake ta fama yin aman akai-akai. Dole asibiti aka kai ni daga gidan Rufaida.
Mun koma wurin Mommy da sakamakon ciki na wata uku da satittika. Na ƙara tsorata da lamarin Allah ni Halimatu, watau rabo ne kawai ya ja ya tara da ni a ranar da ya ke nishaɗin sakin kayan kamfani da aka yi kenan.
A satin ya baro ɗimbin aikin shi ya zo ganina bayan Mommy ta sanar da shi. Ba ƙaramin mamaki hakan ya ba ni ba saboda ban taɓa zaton akwai abinda zai sa na samu sassauci daga gare shi ba. Da da ban san ina da ciki ba kusan lafiya ƙalau nake yi sabgogina, amma tunda na sani shikenan ko abinci ba na iya ci sai ƙarin ruwa ake ta yi mun, hannuna har kumbura sai da ya yi. Haka ya zo ya yi ta tausaya mun yana mun sannu.
Tun daga lokacin akai-akai ya ke zuwa Abuja duba ni. Lokacin da Rukky ta haihu cewa ya yi na yi haƙuri kar na je duk da cewa yanzu ciwon nawa ya ragu sosai. Ban ja ba na ba ta haƙurina zauna a gidana kawai.
Ban san ko cikin ne ko kuma sauyi aka samu ba, duk wannan zuwan da ya koma yi ba ya zuwa ya tafi bai karɓi haƙƙinsa a wurina ba. Ni yanzu ban gane ba, shin dubiyar ya ke zuwa ko kuma abinda ya ke kawo shi kenan. Sai na lura kaman yana matuƙar son ya ga ina maida martani ko taking charge, ai kuwa na sauke ta ido nake yin exactly that sannan ciki ya sa bala'in son hakan nake yi. Ba ma hira har zuwa wannan lokacin, idan ka ga muna magana to wata matsala ce ta tashi yake faɗa mun. Kuma cikin ikon Allah kullum bana rasa abun taimakawa a matsalar imma shawara, rarrashi ko na faɗi wani abin da idonsa zai buɗe ya san ina zai dosa.
Lokacin da na yi nauyi sai ga Abba tsulum a Abuja kamar an wullo shi, bai faɗa mun zai zo ba sai kawai maigadi ya aiko. Jikina na rawa, ina son ganin Abba ina tsoron Ya Buhari don haka waya na ɗaga na kira shi na shaida masa ga Abba ya zo. Sai ya ce shi ma bai fi awa ɗaya ya ƙaraso Abuja ba. A sashen Mommy na sauke shi. Mai hali ba ya fasa halin shi, sai tsokanata yake yi wai ga Sadiya da ciki. Anan Ya Buharin ya iske mu kuma ban ga alamar ya nuna damuwarsa ba ko a fuska don haka sai na ji nutsuwa ta saukar mun ta sosai.
*****************
Lamura tsakanina da Ya Buhari suna kan hanyar gyaruwa, kuma na yi sa'a Allah ya sa ina iya lura da abubuwan da yake so komin ƙanƙantar su ina kuma iya bakin ƙoƙarina domin in dai jira nake ya faɗa da bakinsa to ashe babu abinda zan gane. Ban san abinda gaba za ta bayar ba amma a wurin da muke yanzu na samu kwanciyar hankali ina kuma fatan nan da wani lokaci mai zuwa za mu koma kaman baya ko fiye da haka. Kuma har wannan lokacin ban daina addu'a game da hakan ba.
Samun cikina sai ya zamo kaman na buɗe mana hakan a cikin gidan domin na ji an ce Khadija ma cikin ne da ita. Ni na samu mace ita ma bayan watanni ta haifo mai sunan Daddy.
Maa shaa Allahu la ƙuwwata illah billah
Ƙarshen littafin TAƘAITACCEN TUNANI kenan.
Mu haɗu a littafi na gaba BA NI DA MASANIYA in shaa Allah, kuma kamar yanda na faɗa a KOWA DA ƘADDARARSA zai zama paid ne in shaa Allah, little token ooo. Lol.
Faddanku na godiya, Allah ya yi mana albarka da zuriyyarmu gabaɗaya. Ameen Ya Rabb.