Shafi na 1
by @sadisakhna
⚫ *MUMINAH DA AZZALUMA*⚫
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Da sunan ALLAH muke farawa mai rahama a duniya mai jin ƙai a lahira.
Ayimin afuwa kasancewar na ɗauki wani Loto(lokaci) ba'aji ɗuriyata ba,saikuma na bayyana da wani sabon littafin mai sabon salo da kuma sabon labari. Ah kunsan in mutum ya ɗauki wani lokaci yakanji abu ya fita masa rai,amma maƙasudin ajiye labarinnawa na JODAH shine na samu haɗarin rasa takardun baya,to waiwaya wa nasake rubutawa daga farko sai ya faskara,musamman dana ci karo da wannan labarin a cikin kwanyar kaina,sai kuma naga kaman zaifi armashi da bada citta haɗi da tafiya da ra'ayin ku masu karatu. Wannan ƙunsasshun dalilai suna sukayi tasirin sauya akalar alƙiblar alƙalaminnawa zuwa kan wannan labarin mai suna MUMINAH DA AZZALUMA. dafatan zaku gama aikinku ku zauna bisa kujera ko gado mai laushi ku bani haɗin kai mu antaya cikin Wannan labari mu ragargazoshi muga mai ya ƙunsa a ciki.......nice dai takun SADI-SAKHNA mutuniyar makaranta kamar kullum. zamu fara da littafi na farko kamar koyaushe a kyauta ne,domin na bawa mai karatu babbar damar tantance tantamar sa na shin zai bimu ne ko kuma zai yada zango anan.Sannan daga baya mu ɗunguma littafi na biyu wanda shikuma tafiyar sa saida masu sulalla za'a yishi,naira na gugan naira har naira 400 kacal to in kun shirya zamu fara shiga cikin labari. Allah yabamu sa'a yayi mana gamdakatar,ya fiddamu cikin wannan damuna lafiya sannan yabamu iri mai amfani ameeeen.......
⚫ _PART 1_⚫
Katafaren ginine daya ƙawatu da fasaha irin ta zamani,iya filin da ginin ya mamaye yayi bake bake a wajen ma a tsakiyar garin abuja ya isa ya faɗamaka cewar mamallakin ginin kuɗi dai ba wani abun ba sun zauna a cikin aljihunsa.
Babban kampani ne daya ƙunshi abubuwa da dama a waje guda,akwai fannin wajen ƙera kujeru da kayan ɗaki na alfarma irinna ƙasashen ƙetare,fannin motoci fannin gwalagwalai da sauransu.
A gaban fuskar babban ginin an rubuta AMJAD EMPIRE da wani rubutu mai kamada launin lu'u lu'u. Amjad empire shine headquater na dukka kampanonin da suke ƙarƙashin mai wannan suna. Bayan wannan akwai wasu ƙananun kampanin a sauran jahohin da suke ƙasar ta Nigeria. Sunan na Amjad ya samo asaline daga mamallakin wajen wato AHMAD JALALUDDEEN (AMJAD) ƙaramin matashi mai ji da tashen ƙudi da damawa a duniyar ta masu hannu da shuni, duk da cewar familynsu ma ba ƙananan mutane bane,amma kuɗin da Allah yabashi da baiwar juya taro zuwa sisi cikin fasahar zamani shiya taka rawar gani wajen bashi nasarar tara maƙudan kuɗaɗe da kuma taka babban matsayi a shekarun da basu wuce talatin da biyar ba. Ahmad Jalaluddeen shine sunansa na ainihi,amma mutane sun fi ƙiransa da Amjad,wannan dalilinne yasa duk wani abu nasa yake amsa ƙiran sunan. Mahifinsa Jalaluddeen Mahraz ɗan asalin ƙasar Chad kasuwancin fulawa ne yakawo mahifinsa Mahrazu ya taho dashi shida ƙanwarsa Hunaiza, ganin mahaifiyarsu ta rasu kuma ya kafu a Nigeria cikin birnin Kano yasa yaƙi ƙomawa ƙasar tasu ta chad,yacigaba da kasuwancinsa har ya buɗe gidajen buredi da gurare da dama,ya tara dukiyarsa daidai gwargwado inda ya ɗora ɗannasa Jalaluddeen akan Harkar,saidai shi ba irinna mahaifinnsa yayi ba,mai makon haka sai ya juya akalar kasuwancinnasa zuwa siyan alkama a wurare daban daban ya dungayin fulawar. A haka har ya dawo Abuja da zama bayan Rasuwar mahaifinnasa,ita kuma Hunaiza a can garin kano tayi aure ta tara nata iyalan.
Shima Alhaji Jalaluddeen tun a garin kanon yayi aure mahaifinsu yana raye da wata ƴar aminin mahaifinnasa wacce ya sauƙa wajensa zuwansa garin Saidai Aisha wacce yaransa ke ƙiranta da hajiya Ummee bata taba haihuwa ba,bayan itane ya ƙara auren Amina ,sukuma ba ƴan nan bane kasuwancin ne yakawosu daga garin gombe.
Haɗuwar fulanin gombe da kuma na Chad shine ya taka rawar gani wajen zunzurutun kyau da ƴaƴan Alhaji Jalaluddeen ɗin sukayi. Hajiya mama (Amina matar Alhaji Jalaluddeen itama tanada haƙuri irinna Hajiya ummee amma tanada faɗa in akayi abinda bai dace ba. Yayinda itakuma Hajiya ummee in kaji maganarta to an taba mata Ɗan ɗakinnata wato Ahmad. Ahmad shine na farko, tun yayensa Hajiya Mama ta badashi ga hajiya ummee, sai kuma ABDULHAKIM da ABDULKADIR wanda su ƴan biyune sai kuma NADIYA Da NIMRAH sukuma wa da ƙanwane,Nimrah itace autarsu itama ganin Hajiya Mama tana mata faɗa sabanin hajiya ummee yasa ta tattara kayanta ta nufi can. Dukkansu a cikin Estate guda suke rayuwa wacce Ahmad ya gina ya dawo da dukka familynsa ciki harda ma Babar su Hunaiza da iyalanta. Da kuma Mamar mahaifiyarsu wacce itama tana raye,saboda ya farantawa mahaifiyar tasa rai.
Hajiya Hunaiza tanada zafi da kuma son kanta da yaranta,sannan ga nuna isa da gadara akan dukiyar yayannata da ƴaƴansa,yayinda itama Deedee mamar Su Hajiya Mama mahaifiyar su Ahmad ita kuma takeda surutu da ƙin ganin taga gaskiya ta ƙyale.
Shi uban gayyar wato Ahmad nasa bangaren daban inda suke zaune da matarsa Surayyah da ƴaƴansu ƴan biyu Jalaluddeen da kuma Mai sunan Mamarta Maryam inda ake ƙiransu FARHAN da FARHANA shekararsu huɗu da aure ƴaƴansu kuma shekara uku.
A ƙarshen Hawa na goma na ginin anan Aka shimfiɗawa CEO na kampanin wato Ahmad Amjad wani katafaren office mai kama da Gidan alatu, Ba kowane zai gani yaƙira wajen da office kawai ba saboda girma da kuma tsarin da wajen yayi. Akan kujerar dake gaban babban table ɗin yake zaune hannunsa riƙe da ink biro yana ɗan kaɗashi akan Table ɗin. Takardune a gabansa da alama sign wasu Papers yakeyi ya tsaya,duk wanda yakalleshi duk kayan alatun daya tara,dan suit ɗin dake jikinsa ma abun kallone,amma kai tsaye zai gano tsagwaron damuwa da rashin kwanciyar hankali a cikin ƙwayar idanunsa.
Turo ƙofar glass ɗin akayi wani mutum ya shigo wanda shima bazai wuce Sa'anni da Ahmad ɗin ba. Saleem kenan PA ɗinsa hakazalika kuma Abokinsa ƙwara ɗaya tal kaman rai. Wasu takardun ya shigo dasu a hannunsa,yana isowa kan table ɗin ya ajiyesu kana ya zubawa Ahmad ido.
Shima ɗago da idanunwasa yayi wanda suka ɗan saka launin ja a cikinsu na alamar mutum baya samun nutsuwa da bacci.
"Shin sau nawa zance maka idan bangama wani aikin ba kada ka kawomin wani Saleem,wai yaushe na zama injine ni banasani ba."
Cikin sanyi da nutsuwa yake maganar amma shi a hakan wai faɗa yakeyi.
Saida yagama maganar ko nace faɗan kafin Saleem ya murmusa tareda jan kujerar gefensa ya zauna.
"Mutumin dayake cewa shige da ficen aiki yana kaɗan wai yau shine yake cewa aiki yayi masa yawa,Amjad wannan takardun fah dana kawo maka yau kwanansu uku ana jiran sign ɗinsu bakayi ba,tun ranar monday yakamata ace anyi,domin na contract ɗinmune da companyn Ƙarfe dake china. A da nasan ko awa bazasuyi ba da kawowa zaka gama dasu,amma yanzu kalli aikin dake gabanka tun wancan satin baka gama ba. Ba wannan bama Sectariyarka tace yau kwananka uku bakaje gida ba anan kake kwana. Amjad wai lafiyanka kuwa menene yake faruwa,kaida tun lokacin da kayi aure komin aiki zai kaimu 2 na dare kai 3 na dare ma sai ka tafi,bakinka ya dunga ambatar ka bar Surayyah ita kaɗai, kasha barin tafiya ƙasar waje ka haƙura da shi akan kayi nesa da ita lokacin da take da ciki,amma wai kaine ka kwana uku a office baka tafi gida ba,shin wanne irin faɗane ya haɗaku haka, gashi Surayyah batayi maka kama da wacce zata bata maka rai irin haka ba. Dan yanzunnan na haɗu da ita a bakin ƙofarka wai kace kada a barta ta shigo,har kuka tayi sannan ta juya ta tafi.
Ba wai inason shiga lamarin gidanka bane amma Amjad wannan fa babban lamarine da zai tabaka ya taba iyalanka harma ya taba Kasuwancinka"
Har yagama bayaninsa Ahmad bai tanka masa,saida ya tabbatar yagama kafin ya ɗauki envolope ya miƙa masa kana yace.
"Gashi akwai dukkan bayanan da ake buƙata da abubuwan daza'ayi amfani dasu,inaso kaje kayimin bincike akai"
Karba Saleem Yayi ya buɗe ya fito da takardun da kuma wani abu anyi sealing a leda. Bayan ya karanta zaro ido yayi tareda kallon Ahmad ɗin,wanda shi ko a jikinsa kamar bai san mai yagani ba.
"Are you serious Ahmad (tunda ya ƙirashi da ainihin sunansa to abin babbane) kana nufin abin har yakai kayi irin wannan binciken akanta,ban taba tunanin abinda kake faɗa gaskiya ne ba sai yanzu. To........."
"Look Saleem surutunka yashiga kwanyata har ya cikata,idan har bazaka iya yimin ba ka kawo zan bawa wani yayi min,Ina sonta amma a yanxu ko kusa zuciyata ta gaza aminta da ita,i love her but i can't trust her,so i don't have a choice daya wuce nayi bincike akanta........"
Littafin MUMINAH DA AZZALUMA kenan maiso zai iya biyan kuɗinsa tun yanzu kafin ayi nisa naira 400 ne.
Amin magana ta wannan layin
***
Sadi-sakhna ce.