Shafi na 3
by @sadisakhna
*MUMINAH DA AZZALUMA*⚫
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 3_⚫
Kukan Farhan ne ya tasheta daga bacci,wanda yake ta ihu kaman ana zare masa rai. Mitstsike idonta tayi kaman bata so ta zaro ƙafarta daga kan gadon.
Bacci ne a idonta sosai saboda abinda Ahmad yayi mata jiya,amma tasan bata isa tayi ba tunda yau ɗin weekend ne,gashi Hajiya mama bata nan mahaifiyar Ahmad kakarsu ballantana ta turasu wajenta.Ita kuma Hajiya ummee tana zuwa makaranta koyarwa ta islamiyya.
Buɗe ƙofar da tayine yayi daidai da shigowar Farhana tana dariya,wacce Farhan yake binta a baya zai kamata da robot na wasan yara a hannunsa bashida kai.
Duka duka yaran basu wuce shekara uku da rabi ba,amma kasancewar kuɗi ya zauna da kuma kula,zaka iya cewa sunyi shekara biyar. Duk da cewa twin ne amma basa kama sosai saidai na jini,domin Farhan yafi kama da Ahmad,yayinda ita kuma Farhana take kama da mahaifiyar tasu Surayyah.
Saurin riƙeta tayi ta hanata shigewa ta gefenta zuwa cikin ɗakin,dariyar da takeyi ta haɗiye tana kallon mahaifiyar tasu wanda itama ita take kallo.
"Zo nan menene ya haɗaku mai kika masa?"
Tsuke baki tayi tareda yin inda inda kaman mai in'ina,hakanne yabawa Farhan damar faɗin abinda tayi masa.
"Ba itane ba ta cire min kan spider man ɗina,kuma ni ban cire mata kan barbie ɗinta ba,wlh sai na rama nima bazan yadda ba"
Ƙarisa maganar yayi yana kaiwa Farhana duka,wanda Surayyah tayi saurin hanashi.
"Ohhh waiku kullum kuna cikin faɗane kam,babu dama idan mutum yana tareda ku ya huta? Ina Nini ɗin taku tayi,data barku kuke ta yawo a gida kuna damun mutane?"
"Uhm ta tafi part ɗin su Maman sultan(Hajiya Hunaiza) kaiwa kayan Sultan na makaranta"
"Okay naji maza ku kama hanya ku bar wajennan,kuje wajen daddynku yana sashensa ku tayashi fira. Idan kuka sake dawomin nan kuna faɗa sai nayi punishing ɗinku,kunjini?"
Yanda ta ɗaga murya tana magana ne yasa Farhana tabe ɗan bakinta zatayi kuka,dan dama ita sakaliya ce duk da tanada tsokana.
Furzar da iska tayi daga bakinta alamar tana cikin damuwa tareda rusunawa ta kama kafaɗunta.
"Ohhh common my lily miye kuma na kukan ehh,kawai nace kuje wajen daddy yana ƙiranku kafin ninin ku ta dawo kinji,jiya ya siyo muku chacolate,ko bazaki sha ba?"
sakin fuskar tayi da sauri tareda ɗaga kai alamar zata sha.
"Yawwa kuje maza ku karba"
Hakan da tayi yayi tasiri don da sauri suka juya zuwa sashen mahaifinnasu wanda yake kallon nata babban falone ya raba.
Bayan sun bar wajen juya ido tayi tareda yin magana wanda ita kaɗai tasan mai ta faɗa sai kuma mahaliccinta.
Duk abinda suke Ahmad yana kallonsu daga back yard ɗinsa,da cup na tea a hannunsa wanda yake kurba a hankali. Ganin tahowar yaran zuwa sashensa yasa ya girgiza kai tareda yin murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo.
"Hmmm i don't know what the hell is happen,amma tabbas da abinda yake faruwa"
Wayarsa ce tayi ƙara wanda hakan yasashi saurin ɗagawa,da alama dama ƙiran yake jira.
"Hello Saleem ina jinka mai kake cewa ne"
Ɗaga ɗaya bangaren mai wayar yasake maimaitawa.
"Ahmad Ni inaga ka daina wannan zargin akan matarka bashida kyau ko kaɗan,duk wani bincike danayi da kuma gwaje gwajen dakasaka ayi dukka abu ɗaya yake nunawa. Kwananann ni bansan mai yake damunka ba,idan ancemin wani zargi matarsa irin wanda kakeyi a yanzu to bazan taba kawowa kaine ba Ahmad,duk wanda ya sanka koda na mintuna ne to yasan yanda kakeson matarka kake mutunta ta kuma kake yabonta,amma for god sake wai kaine kake zarginta a yanzu?,kan abinda bakada masaniya akai,kawai wai haka zuciyarka ta baka. Yaushe zuciyarka tayi tasiri akan ka da har take son rabaka da wacce a baya ita ta nuna tana so. Yakamata kabar wannan abun tun ni dakai kaɗai muka sani,kada ka manta ko badan komai ba saboda ƴaƴanku da yanzu suke tasowa,sannan kafi kowa sanin gidansu ita da kuma inda ta fito,iyayenta ba ƙananan mutane ne ba,kaman yanda kakeda ƙarfin iko kasam itama tanada shi,bazasu yarda da wannan abin daka tsiro kake shirin ɗorawa ƴar su ba. Sannan kuma........"
"Enough Saleem enough enough please,don Allah ka dakata haka ya isheka haka"
Saurin kashe wayar yayi tareda zama akan kujerar da take gefensa,domin ji yayi gabaɗaya ƙafafunsa sun gagara ɗaukarsa. Zare glass ɗin idonsa yayi ya ajiyeshi akan tebur ɗin kana ya ɗora hannunsa akan goshinsa.
"Wayyo Allah na mai yake damuna ne haka,na kasa ƙaryata zuciyata saboda nasan tanada gaskiya,yayinda kuma na kasa yarda da ita saboda duk duniya idan da mai shaidar Surayyah kan bahaka bane to nine. Meyasa haka meyasa,miyasa meyasa sai ni"
Sambatu ya cigaba dayi tun yana yi a hankali har ya zamto yanayi da ƙarfi kaman mai magana da wani,cin ƙarfinsa abin yayi wanda hakan har yasaka shi zufar da ƙwallah. Ƙarar bugun ƙofar wajen dayake ne ya dawo dashi cikim hayyacinsa,saurin goge fuskarsa yayi tareda nufar ƙofar,yasan su Farhana ne,sai a lokacin ma ya tuna ashe ya ga lokacinda Surayyah ta turosu izuwa sashennasa.
Farhana ce ta fara shigowa,idonta ya sauƙe akan nasa.
"Abba mai yasamu idonka naga yayi ja?"
Dariya yayi tareda girgiza kai,halinta iri ɗaya dana surayyansa a baya,babu inda ta barta wajen kula da abinda yake tareda ita komai ƙanƙantarsa,banda yanzu da gabaɗaya ta sauya masa. Shauƙin so da kuma ƙiyayyane suka bayyana cikin zuciyarsa a lokaci guda,saurin kawar dasu yayi dukka,dayaga suna barazanar zautar dashi,bai taba ganin wanda emotion biyu mabanbanta ke ziyartarsa kaman shi ɗin ba a halin yanzu.
"Ahah sweety ƙwaro ne ya faɗamin a ido yanxu,mai kika yiwa bro ɗinki naji yana kuka da safennan,uhm uwar surutu"
Ya faɗa yana lakace mata kumatu.
Kamar dama jira take tashiga tsaramasa abinda ya faru,shikuwa Farhan tunda yakama ƙofar shigowa wajen bayan an buɗe musu bai ƙariso ba bai kuma koma ba.
Hannu Ahmad ya miƙa masa akan yazo.
"Sorry my boy ka daina fushin mana haka,zan siyo maka wani spider man ɗin babba wanda yafi wannan kaji,zo ka gaisa da daddy koh"
Sai a lokacin ya ƙariso wajen mahaifinnasu tareda sakin fuskarsa.
Rungumesu yayi dukkansu a jikinsa yana jan ajiyar zuciya,kana kallonsu kamar wanda ƴaƴa suka rasa mamarsu shikuma ya rasa matarsa.
"Abba yau kama mammy taƙi bari mu zauna a wajenta ta koremu,jiyama har dukan Farhan tayi daya zubar mata da madara,gashi sai tayi ta zuwa anguwa,kullum in mun dawo a makaranta sai mu samu batanan,ta daina yi mana homework da labarai kaman da. Mukam ka kaimu Wajen ummee bazamu zauna anan ba. Nini ma ta tafi wajen Sultan Har yanzu bata dawo ba,gashi yunwa mukeji"
Runtse idonsa yayi yana sauraron ƙorafin ƴaƴannnasa,ashe bashi kaɗai bane har yara ma sun fahimci hakan,to amma meyasa kowa ya faɗawa sai yaƙi yarda dashi,ƙarshe ma saidai yaga laifinsa?
Jin ƙorafinnasu bazai ƙareba yasa katsesu tareda ɗauke musu hankali da wani abun,duk da yasan gaskiya suke faɗa amma bayason hakan ya zauna a ransu harma yayi tasiri,shi kansa babba abin yana damunsa inaga kuma su yara.
Kitchen yashiga bayan yabarsu a falo domin haɗa musu abinda zasu ci, shi dama ma'abocin sha'awar yin girkine idan yanada lokaci,musamman ma yanzu da bayacin abinci a gidan.
Jallof ɗin taliya yayi musu da sardine,bayan sunci yayi musu wanka suka bar gidan. Don yanzu ko ran weekend ne baya sha'awar zama a gidan, idan yasan itama tana nan.
Safa da marwa tafarayi a cikin ɗakin,ganin tana ta ƙiran wata lamba amma har yanxu ba'a ɗauka ba.
Tsuka taja kaman zata zuqe iskar datake wajen gabaɗaya kana tace.
"Iskancin banza nifah wannan abun ya isheni haka,ace koyaushe daga wannan matsalar sai wannan,shi kaɗai guda ɗaya amma nakasa gamawa da babinsa,ayi mutum da zuciya kamar ta Samudawa sam sam taƙiyin laushi. Ni wlh nagaji da wannan halayyar tasa,Nayi zaton tsantsar soyayyar sa akaina yakeyi ba hali ba,amma na kula bani yakeyiwa soyayyar ba halinne. Kenan koda jinya na kamu dashi haka zai tsallake yayi tasa rayuwar idan yaga ya daina ganin abinda yake so? Lallai maza halinsu da nuna kulawarsu ba abin yarda bane"
Duk maganar tanayinta ne tana kallon kanta a madubi,bata ma san ƙiran da take yashiga ba.
"Hello surry yane kike ta zubamin ƙira kaman na kashe miki miji,"
Mai magana a ɗaya bangaren tafaɗa da muryar duniyanci tana ƙarisawa da wata ƴar iskar dariya.
"Mtsw bazaki gane ba Zeezah maganarki fah gaskiya ce,wannan mutumin bani yakeso ba,wancan halin yakeso,sam ko inda yake yaƙi yarda naje bare wani abun yashiga tsakanina dashi"
"Haaaa ai dama na faɗamiki,maza ai sun gama da mata,yafiso kullum yasamu mace tamkar karya da asurka sai yanda yajata tukunna zatayi,to ke ki koma yanda yakeso ɗin mana"
"What no no i can't do this bullshit kuma,wai a ina kikene nakejin hayaniya,akwai maganar da zamuyi"
"Ohh ni wai ina wani sabon club ne wlh da aka buɗe,bakiga wajen ba ya tsaru ya haɗu matuƙa,gashi nayi gamo da wani zazzafan gaye ohhhhhh rayuwar shaƙatawa fah tayi. Ko zaki fitone kema ki rage ƴar iskar guguwar da guy ɗinnaki ya zuba miki"
"Ni ba wannan ba maganar kawai zamuyi kuma ina so muyi cikin gaggawa,turomin address nazo na sameki,kina nan dai da biye biyen mazan kinnan,kinsan bazan iya wannan zubda class ɗin ba."
"Uhm gashi kuma Amjad ya juya miki baya ba,ina zan iya nayi tabin mutum yana garani,ga wannan saidai suyi ta binka kana ɗaga kai."
"Dan yaga ina sonsa ne shiyasa yakemin yanda yaga dama,amma soon zan ɗinke zuciyata zai kuwa san dawa yake buga wasa, domin son danake masa baikai son danake yiwa dukiyarsa ba. Ina sone na bishi a hankali amma shi baya ganewa"
"Wai harna tausaya masa,Allah sarki Amjad young billioneer bai san da wacce irin macijiya yake tare ba. Na turo miki kizo ina jiranki,wata wine na samu mai cajin kai,nasan zatayi miki daɗi sai kinzo kawai"
Ta ƙarisa maganar tana janta irin na wanda yafara lulawa duniyar gajimare.
Hmmmm omo wlh karku bari nayi labarinnan babu ku,akwai tafasa da tafashe tafashe ina faɗa muku hmmm😀😀😀
Amin magana ta wannan layin
***
Sadi-sakhna ce.