MUMINA KO AZZALUMA

Shafi na 5

by @sadisakhna

⚫ *MUMINAH DA AZZALUMA*⚫




⚫ _SADISAKHNA_⚫





⚫ *BOOK 1*⚫




⚫ _PART 5_⚫




Yafi awa a tsaye da alama wani abu yake jira,domin lokaci zuwa lokaci yake duba agogon dayake babban falon.

Jin ƙarar tsayawar motane yasashi saurin leƙa windown.

Fitowa tayi daga cikin motar da abayar data fita da ita a jikinta,cikin taku na nutsuwa ta tura handle ɗin falon tashigo. Turuss tayi ganin da wanda ta haɗa ido daga shigowarta. Saurin basarwa tayi tareda sakin ƙaramin murmushi.

"Ohh honey ka dawo kenan"

Tana faɗin hakan bata jira mai zaice ba ta wuce shi zuwa ɗakinta,muryarsa ta tsinkayo ya ƙira sunanta,hakan yasaka ta tsayawa cak tareda juyowa.

"Amm magana kakeyi"

"Ahah ba magana nakeyi ba ihu nake,shin daga ina kike,?yaushe kika fita? sannan da iznin wa har kika kai wannan lokacin a waje?"

"Wannan tambayoyin fah Dear,yaushe ka farayimin kulle da har kakemin waɗannan tambayoyin"

"Ohh ina tambayarki kike tambayata,yaushe kika fara ɗaukar aure a abin wasanki,sannan yaushe rayuwar damuke ciki tafara buɗemiki ido kiyi abinda kikaga dama. A matsayina na mijinki ko bazan hanaki ba i think inada haƙƙin nasan ina kikaje kana kuma yaushe zaki dawo. Na dawo gidannan Tun ƙarfe 4:00 na yamma,mai zan ci? Yara sun dawo daga makaranta mai zasuci mai akayi musu a makaranta mai zasuci mai suke buƙata ? Shin ƙalau suke? Duk waɗannan basu dameki ba daga shigowarki kawai ɗakinki zaki wuce"

"Yara yara yara.......!! Kullum maganarka yara,ni banida nawa ƴan cinne dazansha iska? Sannan da kake maganar haƙƙi yaushe rabonka kai da ka sauƙe naka haƙƙi,ko nikaɗaice mai haƙƙi akai kai? Batun abinci sau nawa kakeson na ajiye maka abincin na kuma roƙeka domin kaci?"

Kallon ta yakeda mamaki ganin yanda take maida masa martanin maganarsa,shin ina bada haƙurin dayazama halinta ko itace da gaskiya ko ba ita ba.

Lumshe idonsa yayi tareda furzar da wata iska ya wuce ɗakinsa kana ya turo ƙofar da sauri.

Saroro Surayyah tayi tana kallon inda yabi da kallo,saikuma ta tsinci dukkan jikinta dayin sanyi,ganin fushin dayayi bata taba ganin yayi kamarsa ba.

"Ke nura wai ina nuran tayi ne"

Hajiya Deedee ta faɗa tana lelleƙawa daga inda take zaune akan kujerar falonnata.

Nimrah ce tafito daga wani corridor tana kumbura kamar kububuwa,hararar Deedee take kaman idonta zai faɗi ƙasa sannan tace.

"Wai Deedee sau nawa zance ki daina cemin nura ne,nura sai kace wata na namiji,in bazaki iya faɗin Nimrah ba ni ki ƙirani da ainihin suna na,habaaa ni nagaji da wannan sunan wlh,sai kinsa watarana wasu sunji su dinga ƙirana dashi ko"

"To ko kefa ni dama nafison ƙiranki da sunanki Indo (Aisha) miye kuma wani Nura,a garin iyayi duk kun sakawa kanku sunayen ifiritai ƙarfi da yaji"

"Kinji ko kinji ko ina,wai in bazaki faɗi abu daidai ba ki ja bakinki mana kiyi shuru,tukunnama miye yasa kike zunduma min wannan ƙiranne,kina daga zaune kin hakimce. Karma kice na matsa miki ƙafa ganan Saratu zata miki,danni karatun jarrabawa zanje nayi"

"To naji uwar ƙorafi da surutu,dama shi kika iya ai sai danne dannen waya,gashi nan nace kiyimin masa kin tashi kin tsula mata mai kaman ɗanwake,aradu idan ciwona ya tashi aka tambaya cewa zance kece sila"

Ta ƙarisa maganar tana tauna masar kaman tana tauna kashi.

Zaro ido Nimrah tayi sororo tana ƙarewa Deedee kallo,kai tsaye zaka hango tsagwaron baƙin ciki na furucin deedeen.

"Tabb lallai ma tsohuwar nan,haka kawai saiki tsiri cewar ayimiki abincin da mutum ko ido huɗu bai tabayi dashi ba saidai a waya,amma haka mutum zai dage yayi miki. Fisabilillahi ina na taba ganin wata Masar Hatsi,amma haka nayi browsing nayi miki,shine zakice wai tayi mai,idan ba bazan sake yimiki abinci mai aikin ki ta dunga miki,ni na tafima bazan sake zuwa sashennaki ba"

Tana buga ƙafa kaman zatayi kuka take maganar.

"Ah ah Nimrah Deedee kika saka a gaba haka kina mata wannan wankin babban bargon saboda bakida mutunci?"

"Hajiya mama ce tafaɗa wacce shigowarta kenan falon"

"Faɗa mata dai da bakizo bama inaga dokeni zatayi,dannace tayi masa yayi mai ina faɗamata shine takemin wannan tujarar,marar kunya kawai"

"Deedee eeee!!,yanzu Deedee haka akayi ?"

Nimrah tafaɗa har idonta yana ƙwalla.

"Ohh ƙarya zatayimiki kenan wuce kije wai aunty Surayyah tana nemanki zaki tayata girki,idan ina kamaki kinayi mata wannan rashin kunyar saina babballaki ingayamiki"

Shigewa Nimrah tayi tana kumbura magana take ƙasa ƙasa wai ta daina yiwa Deedee labarai daga yau. 

Kai tsaye sashen Ahmad ta wuce,har sannan bakinta bai daina sababi na abinda Deedee tayi mata.

Tura ƙofar tayi tareda yin sallama,amma shuru babu amsa,shiga tayi cikin falon tana ƙaremasa kallo. Gashi dai anyi shara amma ganinsa take wani iri kaman ba yanda tasaba ganinsa kullum ba.

Tunani ta tafi yi a lokacin baya sanda take zuwa,tana shigowa zata jiyo ƙamshin girki dakuma su farhana suna falo zaune da kayan wasansu. Suna haɗa ido da Aunty Surayyah zata sake mata murmushi su gaisa. In ta gama abinci haka zata zubawa Ahmad su zauna tana bashi a baki yana ci ana hira har yagama,bayan ya kammala ta tashi da sauri ta ɗauko jakarsa. Sunayiwa juna kalamai da cewar basason rabuwa a haka zata rakashi har jikin motarsa. Bazata shigo ciki ba har sai taga yabar farfajiyar gidannasu tukunna.

Daga nan saita tayata su gyara gidan su saka kayan ƙamshi ,sunayi suna hira. Aunty Surayyah abar so ce ga kowa.

Nimrah ta ƙarisa tunanin tana dariya idan ta tunata da kuma ɗabi'unta.

To miye kuma nake begenta kaman wacce ta mutu,tana nan fah. Wata zuciyar tace da ita haka.

"Lafiya kika tsurawa falon kallo kina murmushi,kin gagara ƙarisowa?"

Surayyah ce tayi maganar wacce take tsaye daga ita sai kayan bacci masu gajeren wando.

Nimrah tayi mamakin shigar tata,kuma har tsawon wannan lokacin ƙarfe 10:00pm da kayan bacci a jikinta?.

A haka dai ta basar ta gaishe da ita,itama amsawa tayi a daƙile kaman bataso.

Ƙarisowa cikin falon Nimrah tayi ta zauna,rabonta da shigowa part ɗin tayi wata ɗaya da ɗoriya,ko shiyasa take kallonsa tamkar sabon abu,yakoma tamkar matacce daga rayayyen data sanshi.

"Am dama abinci zakiyimin,yace bazaici na masu aiki ba,to i think zaici naki tunda ke ƙanwarsa ce,amma kafin ɗora min ruwan zafi zansha tea"

Tana gama maganar da ƙariso cikin falon ta zauna tareda ɗaukar remote ta sauya tashar da takeyi zuwa nigerin film.

Itadai Nimrah duk abinda takeyi sakin baki tayi tatsaya tana kallonta,gani take ko a mafarki wannan abun bazayyi wu ba ballantana a zahiri,amma gashi ba mafarki takeyi ba kuma yana yiyuwa. Anya kuwa wacce take gabantan Aunty Surayyah ce,kuma gashi ita ɗince ba wata ba. Lallai karka shedi ɗan adam.

Tashi tayi ta wuce ta gabanta zuwa kitchen ɗin.

Komai yana muhallinsa tabbacin yau ba'a dafa komai ba a kitchen ɗin. To me maigidan yaci kafin ya fita.

"Allah sarki Yah Ahmad har na tausaya masa,sauyawar mace lokaci guda haka nan. Ni in hancina ba ƙarya yayimin ba warin shisha ma fah naji tanayi koh? Wai hmmm Allah ya kiyaye,waye zayyi tunanin Aunty Surayyah zata sauya ɗabi'unta haka"

Da haka dai Nimrah ta gama yimata abincin ta jejjera sannan ta gyara kitchen ɗin ta fita. Lokacin ita kuma tashiga wanka,bata ma bari sun haɗu ba.





Amin magana ta wannan layin 

***

Sadi-sakhna ce.