MUMINA KO AZZALUMA

Shafi na 6

by @sadisakhna

⚫ *MUMINAH DA AZZALUMA*⚫




⚫ _SADISAKHNA_⚫





⚫ *BOOK 1*⚫




⚫ _PART 6_⚫




Wajajen misalin ƙarfe 4:00pm yashigo gidan ya dawo daga aiki. Bai shiga sashen su hajiya ummee ba sashensa ya wuce,kasancewar Surayyah tace masa ya dawo tanason suyi magana.

Yana shiga ƙamshin turare yaji ya kaure falon,amma bana turaren wuta ba wanda yake so. Na air freshner ne,saidai shima yayi daɗi ba laifi yafi babu.

Idonsa sauƙa yayi akan dining inda aka jera kulolin abinci,a ransa hamdala yake Allah yasa surayyansa ta dawo cikin hankalin ta.

Fitowa tayi daga ɗakinta tasaka atampa,saidai ɗinkin zamani akayiwa kayan matsatstse,amma yayi mata kyau sosai ya amshi jikinta.

Da murmushin ta ta ƙariso inda yake ta karbi brief case ɗin hannunsa. Shima sakar mata yayi inda yabita zuwa ɗakinnasa,har yanzu baya ganinta a yanda take kaman da,amma dai dama dama akan kwanakin bayan.

Rigar saman ta rage masa,tana ƙoƙarin cire ta cikin ya riqe mata hannu,haka kawai yaji baya sha'awar cire kayannasa a gabanta,dan ganin yake shifa kaman wata daban ba matarsa ba. Haɗe fuska tayi ganin duk abinda takeyi masa bata gwaninta,ganin hakanne yasa yakamo hannunta tareda yin magana cikin sanyin sauti.

"Am sorry dear ina sauri ne kije ki haɗamin abinci kafin nazo yunwa nakeji sosai"

Ɗan murmushi tayi tareda ɗaga masa kai tafita daga ɗakin,alamun ta yarda da abinda yace ko kuma yanayin muryar tasa tayi tasiri a kanta.

Bayan ta fita binta yayi da kallo tareda sauƙe ajiyar zuciya,gabaɗaya bayason ganin ya kebe tareda ita. Bayan da hakan shine abinda yafi komai sakashi nishaɗi. Kwata kwata sai yaji yakasa samun nutsuwa,musamman dayaga yanda take binsa da wani mayen kallo na sha'awa.

"Ya Allah mai yake damuna ne tsakani na da matata,ya Allah idan har akwai wani dayake boye wanda yakamata nasani gameda ita Allah ka bayyanamin shi,ya Allah ka dawomin da ita kamar yanda take a da"

Ruwa ya watsa sannan yasaka wasu kaya marasa nauyi ya fito falon.

Tana zaune a falo idonta akan tv,kulolin suna rufe kaman yanda ya gansu ɗazu bata buɗe ba.

Zama yayi kusada ita tareda cewa.

"Barkanki da gida,mai kika dafamin ne yau ɗin naga wannan shiri da akayi dominni?"

Ɗan murmushi tayi tareda yin fari da ido sannan tace.

"Sirrine saidai muje mu gani tare nida kai"

"Ohh kenan ƴan aiki ne sukayi yauma?"

"Ahah ba ƴan aiki bane yau sukayi,yau basu ma shigo part ɗinnan ba."

Bai sake cewa komai ba gudun kar ya ja magana,tashi yayi zuwa wajen dinning ɗin.

Itama biyoshi tayi a baya ta buɗe ɗaya flask ɗin wanda yake shine babba.

Shinkafa ce amma anyi steaming ɗinta da vegitables da kuma curry,tayi kala shar gwanin kyau da bada sha'awa. Saurin runtse ido Surayyah tayi jin wani mungun yawu daya taru a bakinta marar daɗin ji. A haka ta ɗauki cokali tafara zuba masa abincin a plate har saida yace ya isa tukunna.

Ɗaya flask ɗin ƙaramin shima ta buɗe,miya ce a ciki tasha nama na ƙaramar dabba,shima sai kamshin curry ne yake tashi. Subahanallahi wannan karon kam ji tayi kaman jiri zai ɗibeta saboda ƙamshin curryn daya haɗe wajen.

Ganin tatsaya sororo batada niyyar yin magana yasa Ahmad janye plate ɗin daga gabanta ya zuba salat ya fara ci.

"Uhmm yayi daɗi sosai amma bake kikayi abincinnan ba ko,don wannan ba irin kalar girkin ki bane"

Jin yana magana bata kulashi ba yasa ya ɗago ya kalleta,suna haɗa ido kaman jira yake taji wani amai da bata shirya masa ba yana shirin fitowa.

Tagudu tayi hanyar kitchen domin yafi mata kusa,a wajen sink ɗin wanke wanke tasake shi tafarayi. Tun tanayi shayin da tasha yana fitowa har yazamo babu komai sai ƙaƙarin kawai.

Ganin abin yaƙi ci yaƙi cinyewa yasa ahmad yabiyo bayanta,a bakin kitchen ɗin ya tsaya yana kallonta harta gama ta zuba ruwa.

Juyowa tayi suka haɗa ido saikuma ta ɗauke nata idon.

"Miye yake damunki,ko kinci wani abu ne ya bata miki ciki?"

"Ahah i don't think so. Kawai ina buɗe flask din abincin can naji zuciyata ta tashi. Ina zuwa bari naje na duba wani abu"

Wuceshi tayi tanufi ɗakinta da sauri.

A bangaren ahmad kuwa bai koma wajen abincin ba a kujera ya zauna ya kunna aljazeera.

Surayyah ce tafito daga ɗakinnata da wani abu a hannu,tana zuwa ta ajiyewa Ahmad a kan cinyarsa. Abin gwajin cikine na fitsari.

Ɗauka yayi ya duba inda yabada red line guda biyu dara dara.

Zaro ido yayi daya fahimci abinda hakan yake nufi.

"What are you pregnant? Me hakan kenan yake nufi"

"Kaman ya ahmad,bakayi farinciki ba dasu Farhan zasu samu ƙani ko ƙanwa ko ƙannai."

"No yaushe hakan ta faru naga......."

"Me kakeso kacene Ahmad,ba naka bane komai,abinnaka har yakai kayimin wannan ƙazafin har yakai ka ƙi amsar gudan jininka. Yaushe ka tsaneni haka?"

Cikin ɗaga murya take faɗin hakan saikuma ta fashe da kuka. Hanyar ɗakinta ta nufah da sauri kaman zata tashi sama.

Jikin Ahmad ne yayi sanyi,duk yana jinta wani iri a zuciyarsa amma yasan cikin jikinta bazai wuce nasa ba. Shi na wai yana nufin cikin jikinta ba nasa bane,kawai abinne yazo masa a bazata,sam sam bai shirya ƙarayin zuri'ah da ita ba da wannan sabin halayyar tata. Sai yaji inama lokacin da tace zata cire implant ɗinta tanason haihuwa bai biyeta ba. Glass ɗinsa dayake gefe ya ɗauka yasaka tareda sake kallon PT ɗin,gani yake kaman bai kalla daidai ba.


Tana shiga ɗakin tagoge hawayen tareda yin wani murmushi.

"Ta ƙare maka Ahmad amjad"

Wayarta ta ɗauka ta danna ƙiran zeezah,bata daɗe tana ringing ba ta ɗauka.

"Hello mrs Amjad ya akayi ne?"

"Am pregnant zeezah,ni kaina bansani ba sai ɗazu,gabaɗaya har yanzu bangama yarda ba. Shima naga da alama bayyi farinciki da samun cikin ba. I think zan xubarshi idan har zai batamin plan"

"What!!! Pregnant ohhh god oooo,nima ji nake kaman wasa kike. Kutt mai ma kikecewa ki zubar kuma? Ke dallah banza wannan wani sabuwar babbar dama ce nasakashi a cikin kejinki. Ko bakiyi tunanin hakan ba"

"Waye banzar kinfara rainani fah"

"Sorry oga surry kawai naji ƙwaƙwalwar taki tafara sanyine,wannan mutuminnaki yana son susuta ki,to amma cikinshi ne,naga kwanannan gabaɗaya ƙauracemiki yake"

"Kiji ki dawani zance,to kafin ya ƙauracemin fah. Sannan kema da kika sanni har kike wannan zargin. I think kinsan halina duk tsiyata bana hulɗa da maza"

"Ehh hakane kam,kenan a ranar kika samu cikin"

"Ehh inaga hakanne"

"Wayyo Allah i can't wait to see this tafashashshiyar drama"

"Mtsww kanki ba ɗaya ba yanzu dai sai anjima."

Tana kashe wayar zama tayi a bakin gadon tana shafa cikin tana murmushi.

"Zeezah kenan lallai har yanzu kema baki sanni ba,a tunanin ki zan zubar da cikinnan ne. Duk wannan yunƙurin danakeyi na jawo hankalin sa duk dan na samu wannan cikinne. Bansani ba ashe Allah yagama taimakona yabani tuntuni. Yanzu aiki zai fara wannan yaran sune makamina na yaƙar muradina a gidannan"

Tana gama faɗin hakan ta ƙara ɗaukar wayarta.

Dr.Najeeb naga ta ƙira,daga can ya ɗauka.

"Hello ran gimbiya ya daɗe ya......."

"Kaga ba wannan ba ina zuwa yanzu zakayimin gwaje gwaje akwai abinda nakeson comfirming"

"Okay okay to shikenan sai kinzo gimbiyata"

Kashe wayar tayi tareda jan tsuka,bata ma gama jin abinda yake faɗa.

"Maye kawai"

Ta faɗa tana wurga wayar tsakiyar gado.





Amin magana ta wannan layin 

***

Sadi-sakhna ce.