Shafi na 7
by @sadisakhna
⚫ *MUMINAH DA AZZALUMA*⚫
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
Mashaallah ƴan uwa barkanmu da yamma yakkuke ya ayyuka. Nariga na bada uzurina ga wanda suka sani na jina shuru banyi posting ba. Yarinya ta ce babu lafiya gabaɗaya ta kaɗemin hankali dan haka kuyimin uzuri don Allah. Amma cikin ikon Allah ta warware alhamdulillah da sauƙi........ohhh iyaye mata a gaisheku,wato duk wanda baya duba da rayuwar mata a cikin gidajensu ballantana ya tausaya musu harma ya jinjinamusu da sauransa. Gaisuwa da jinjina gareku iyaye mata na gida masu albarka. Allah ya raya mana ƴaƴan mu da imani,sannan yabamu ikon kulada amanonin da suke hannunmu. Ni tawa guda ɗayace ta dameni ji nayi komai yafitamin kai. Saina tuna akwai wacce tananan da huɗu ko biyar kowanne saita juya ta bashi lokacinta,ga gidan,ga maigidan,ga awakin gidan,ga kajin gidan....kowa jiranta yakeyi ohhh🥺🤕. Allah ya kyauta
,yaƙarawa mazajenmu tausayinmu kawai.
Wanann shafi sukutum sadaukarwa ga IYAYE MATA. Allah yasakamuku bisaga ƙoƙarinku
⚫ _PART 7_⚫
"Hajiya ummee"
"Na'am"
Ta amsa tareda ɗaga ido ta kalli Nimrah wacce ta tashi zaune daga kan kujerar da take. Itama hajiya mama wacce take zaune zuba mata ido tayi hakama Zainab.
Ɗauke kanta tayi tamayar kan Hajiya ummee tareda cewa.
"Wlh ummee gaskiyar Yah Ahmad ne Aunty Surayyah ta sauya sosai,wai fah ashe masu aiki take sakawa su na yimasa girki yanzu,dayace bazaici bane shine tace wai na yi masa. Kunga kayan data saka kuwa,hmmm wlh ko turai iyakaci bingil bingil fah sannan warin........."
"Ke ke ke ya isheki haka banason munafurci,wato Nimrah kina nan da Gulmarki koh,ina ruwanki mata da gidanta,dan ta ƙiraki kinyi masa girki wani abune,idan batada lafiya fah. Shine kinje kin gano zaki zo kina fesawa ko,wato kullum ina rabaki da irin wannan halin bakyaji.
Shima ai inajin labarin abinda yakeyi,wai shi tana nuna masa hali ba yanda ya saba gani ba. Shikenan kullum ake kwana a gado. Kokuma dan yasha mangwaro yazama ƙwallo sai akace ya yasar. To wannan halin sakarcin ba a nan gidan ba. Yacigaba dayi duk lokacin da muka haɗu zaiga yanda zanyi dashi"
Hajiya Mama ce tafara faɗa,ta inda take shiga ba tanan take fita ba. Hajiya ummee kuwa murmushi kawai tayi batace ƙala ba.
"Hmmm mama kenan wlh kema dan bakiga yanda ta koma bane,da saita baki mamaki,kuma indai yanda nagani ne to abin a tausayawa yah Ahmad ne"
"Tausayi yaci ƙaniyarsa shida tausayin. Dan yaga yana abu ba'ayi masa magana shine yaketa yi koh. Sanin kansa ne iyayen yarinyar nan ba ƙana nan mutane bane. Duk lokacin da abinda yakeyi yaje kunnnensu ba abin kunya zai jawo mana ba. Waye zai yarda a dunga yiwa ɗiyarsa haka,har wani yace shi bai yarda da itaba. Yasan bai yarda da itan ba yaje ya auro ta hadda zuri'ah"
"Mama wlh ki daina wannan faɗan bayan bakisan mai take faruwa ba"
"Ke in baki tashi kin bar wajennan ba kema sai naci malafar ubanki,ƴar kare da surutu sai kace rediyon fulani"
Filon dayake gefenta ta wurgeta shi,hakan yasa ta tashi ta fita daga falon da gudu tana dariya.
"Mamar yara wannan faɗan dai da alama ita dai Nimrah ta tsokanoshi ne amma ba da ita ake ba damu ake"
"Hmmm addah kenan ki barni dashi naga ke lallabashi kikeyi,haka kawai mata tana nuna maka ɗabi'u masu daɗi kana jin daɗi kana yabonta,saidan kuma kaga ba yanda ka saba gani ba saika fara nuna mata baƙin hali. Gashi itama wannan ganin yanayi harta fara ɗebowa tana fesarwa. Su mata ai sun gaji sauyawa daga lokaci zuwa lokaci. Idan kuma juna biyu ne da ita fah takeyin hakan. Shikenan sai yace baisan zance ba. Ina halin dattaku anan. Kanason zama da mata kuma bazaka jure ƙalubalenta ba"
Ta daɗe tana faɗan saida tayi dan son ranta kafin tayi shuru.
"Ka ƙirani amma tun ɗazu kaƙi cemin komai,sai saƙe saƙen zuci kakeyi. Mai yake faruwane naga abinnaka yanzu yafi ƙarfin magana saidai addu'a"
"Saleem cikine da ita fah?"
"Wacece mai cikin,wai Surayyah?"
Ɗaga kai yayi batareda buɗar baki yabashi amsa ba.
"To menene don tanada cikin,wannan ne haihuwarta karon farko dazaka ji abin kaman sabo?"
"Hmmm bazaka gane bane saleem,wai ni kowa baya ganin ya take ne saini kaɗai nake gani. Dukkan ku bakwa ganin sauyawarta ne. Nafaɗa muku akwai abinda yake tattareda Surayyah wanda ba daidai bane,amma babu wanda zai yarda dani. Har ila yau bangama da wancan ba kuma ace wai cikine da ita a yanda take nan zata ƙara rainamin yaro inaa bazai yiyu ba."
"Bazai yiyu ba kaman ya,kaifah kace tariga ta samu cikin,to me zakayi mata"
"Idan zata yarda Saleem zubda cikinnan za'ayi,ko nawane ta faɗa zan bata idan har zata zubda shi wlh"
"Innalillahi wa inna ilahi raji'un,kai gaskiya ahmad ba ƙalau kake ba zancen gaskiya,dolene naje na samu baba na faɗamasa halinda ake ciki,wai yau cikin dayake jikin Surayyah kake shirin zubarwa,kaida har kyautar kujerar makka ka bawa nurse ɗin datayi mata gwajin cikin su farhan"
"Hmmm wai fah kallon marar hankali kukemin ko Saleem? Inama zan buɗe zuciyata na nunamuku yanda nakeji,inaga da zaku yarda dani. Kwanciya danayi da ita tasamu cikinnan har yau kuma bazan manta ranar ba ji nake kaman na tabka wani babban zunubi a rayuwata da bazan iya gogeshi ba. A da abin baya damuna sosai amma ganin sakamakon daya biyo baya ya ɗagamin hankali ba kaɗan ba. Inama zan koma baya na goge wannan lokacin,inama zan buɗi ido naga bata cikin rayuwata,da saina fi kowa farinciki a rayuwata"
Sororo Saleem ya tsaya yayi yana sauraransa,gabaɗaya maganganun gani yake kamar ba daga bakin ahmad ɗin suke fitowa ba. Ohh idan kana raye a duniya kana numfashi to zaka ga komai ma.
"Ni yanzu kafi ƙarfina bansan mai zance dakai ba,kawai a matsayina na abokinka taimako ɗaya zanyi maka shine zan dunga yimaka addu'a a kullum idan nayi sallah,akan Allah ya yayemaka duhun daya lullubeka,domin ba ƙalau kake ba"
Yana gama faɗin hakan ya tashi daga office ɗin yafita cikeda damuwa.
Ya rufe ƙofa kenan sukayi ido huɗu da Surayyah wacce ta shigo office na farko inda sakatariya take.
Tun kafin Saleem yayi mata magana ta jefa masa gaisuwa,hannunta da wata farar takarda mai kaman envolope.
Wucewa tayi zata shiga office ɗin ahmad ɗin,maganar sakatariyar ce ya tsaida ita. Wacce take sake tuna mata gargaɗin da Ahmad yayi mata akan kada ta sake shigowa nan ɗin.
Wani kallon ina zuwa kanki tayi mata kafin tashige cikin office ɗin,duk abinda yafaru Saleem yana kallonsu har ta wuce shima yayi ɗan guntun murmushi yabar wajen.
"Mai ya kawoki nan,ba nace komai kike buƙata ki bari na dawo ba?"
"Haba Ahmad amma ai ka bari na zauna koh?"
Tayi maganar da murmushi akan fuskarta,jan kujera tayi ta zauna,saida ta lila na ɗan sakanni kafin ta ajiye masa takardar a gabansa.
"Daga asibiti nake nayi gwaji da duk abinda ake buƙatar mai ciki tayi, ina ɗauke da ciki na tsawon wata uku,what will suprise you ƴan biyu ne saidai ba kaman su farhana ba su dukka mazane"
Ɗagowa yayi da sauri ya kalleta,twins kuma wai maza he can't imagine.
Komawa yayi a hankali ya jingina da jikin kujerar tasa,jin cewar ƴan biyune kuma maza sai yaji kamar ya fasa furta kuɗirin dayayi niyya,saidai kuma inaaa zuciyarsa taƙi aminta sam da lamarin.
"Nasan bawai albishir na cikin kikazo kiyimin ba,maganar danayi jiyane ya kawo ki,nawa kike buƙata ki zubar dashi?"
Wani murmushin ƴan duniya Surayyah tayi kafin taja dogon numfashi.
"Ahmad kenan,kaman yanda kake iƙirarin na sauya kaima kanka ka sauya,nayi tunanin dana faɗamaka mai yake cikina zaka sauya ƙudurin dayake ranka,amma sainaga koda akan fuskarka babu alamun kaji daɗin zancena. So tunda wannan hanyar ka zaba shikenan sai mu bita. Yanzu na riga nasan you no longer love me,since you can't accept my blood anymore".
Maganganunnata gabaɗaya sun isheshi,kawai so yake tafaɗi mai take so.
"Kowanne jinjiri ɗaya daidai yake da company ɗaya da suke ƙarƙashin wannan ginin. Idan har zaka bani companynka guda biyu da suke kaduna AMJAD GOLDEN TOWER da kuma AMJAD VIP PALOUR. To a shirye nake dana zubar dasu,idan kuma ba haka ba to bazan zubar ba,kuma halayya yanzu ma tafara sauyawa daga gareni"
Bayan yagama jin bayanan nata murmushi yayi tareda murza biron dayake hannunsa.
"Go and keep your belly safe,zanyi tanadin tarbarsu a matsayina na ubansu,amma soyayyata kaman yanda taki tazare a zuciyata haka suma tasu tazare daga zuciyata. Abinda kika buƙata bazai samuba"
Kallonsa take da mamaki ganin ko ja in ja basuyi ba har yafasa yin deal ɗin. Bayan waɗannan companyn bakomai ne a wajensa ba don ya rabu dasu. Karon farko da fito da ƙudurinta fili amma batayi nasara ba,to daga ina mistake ɗin yake?.
Amin magana ta wannan layin
***
Sadi-sakhna ce.