Chapter 1
***
*BA DON MACE BA...*
✍️ *BY FATIMA FANTAH*
*BA DON MACE BA... LITTAFIN KUƊI NE A KAN ₦1000. GA MAI BUƘATA YA TURA KUƊINSA TA WANNAN ASUSUN 0421863702 FATIMA MUHAMMADU GT BANK. SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR ***. ALLAH YA BA DA IKON SIYA DA BIYA. AMEEN.*
*GARGAƊI*
*Ban yarda wani ko wata ko wasu gungun al'umma su juya mini labari ta kowace irin siga ba, sai da rubutaccen izinina. BA DON MACE BA... Mallakina ne.*
*JAN HANKALI*
*Ba Don Mace Ba... Ƙirƙirarren labari ne, idan ya yi daidai da rayuwar wani ko wata a cikin al'umma, to akasi ne cikin rashin sani.*
*Yadda muka fara lafiya Allah ya sa mu gama lafiya, Allah ya tsare hannuna da rubuta abinda zai cutar da wani ko wata a cikin al'ummar musulmi.*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*_Ciwon 'ya mace, na 'ya mace ne. Shi ne zancen hikima da ya yi mini tasiri tun daga yarintata har zuwa lokacin da juyayyar ƙaddarata ta canza fasalin tunanina, ta karantar da ni sabon darasin da na fahimici cewa wata 'ya macen takan zamo silar zubar hawayen 'yar uwarta mace._*
*SH 1*
AGEGE, LAGOS NIGERIA
10:46pm
Tsaye nike na jingina hannayena duka biyu jikin bango, tamkar ana soka mini allurai dubu nake jin tsira a kowane sashe na jikina, idanuwana suna juyawa numfashina na kaiwa da komawa tsakanin huhu zuwa bututun mafitar numfashina. Bakina ya kasa furta kowace irin kalma sai dai neman ɗaukin Ubangiji da nake a cikin zuciyata.
Tamkar an kwaɗa mini guduma na ji wani abu ya bigi ƙoƙon kaina, zallar azaba ta ratsa daga cikin kan har zuwa tafin ƙafata. Runtse idanuwana na yi, "Ya Allah kar ka kashe ni ba tare da gaskiyar lamarin rayuwata ya bayyana gare ni ba…"
Tsirar alluran ta kara yawa cikin jikina, wani irin juyi jaririn da rayuwarsa ta dogara da ni ya yi tamkar shi ma yana jin kwatankwacin abinda nake ji, jikina ya ƙara karkarwa hannuna da nake jinsa tamkar an liƙa shi da cingam a jikin bango na jawo da matsanancin ƙarfi, cikin kiɗima nasa hannun na tallabe cikin da nake kintacen watanninsa za su kai biyar.
"Ya Ubangiji na roƙe ka da yaren da babu mai jinsa sai kai, babu masanin sa sai kai ɗaya, ka raya ni na haifi abinda ke cikina, ya Allah kar ka ɗauki raina da na ɗana har sai ya sadu da mahaifinsa..."
Wata tsirar ta sake taso mini, kamar an ɓalle wani kangi a cikin hancina, na ji wani abu ya yaye ya bar ni da shi wasarere, hakan ya tilasta mini furzar da numfashina ta baki, wani ruwa mai ɗumi ya biyo ta cikin hancin hakan ya tabbatar mini jini ne. Da ƙyar na duƙar da kaina domin bawa jinin damar ɗiga a kan ƙasa.
Sunayen Allah kawai nake ambata a cikin tsokar da ke manne da ƙirjina. Na kasa motsa ko da ƙaramin yatsana, na yi shiru ina sauraren azabar da ke ratsa jini da ɓargon jikina.
Kaɗan-kaɗan na ji ta fara raguwa, jinin da ke ɗigowa daga hancina ya tsaya, juyin da cikin jikina ke yi ya ragu. Numfashi mai karfi na furzar na ja ƙafata a hankali, jin ta matsa daga inda take ya sa na ji wata guntuwar nutsuwa ta dirar mani, hannuna na janye daga jikin bangon na ja ɗayar ƙafar domin isa wajen tabarmata, sai dai ban yi nasarar kai wa gare ta ba nauyin jikina ya buwayi ƙafafuwana hakan ya sa na faɗi ƙasa daɓas tsakiyar madaidaicin kangon ɗakin.
Take ƙuguna da sauran jikina suka amsa, a wahalce na dafa hannuwana na ja ƙuguna na jingina da bango. Hawayen da ke sintiri kan dandamalin fuskata suka ƙaru, takaici da tuƙuƙin baƙin cikin da ba ni da maganinsa suka ƙara toroƙo cikin zuciyata, rufe idanuwana na yi cikin raɗaɗi da ƙuna, sannan na soma karanta. Ayatul kursiyyu da ƙul'a'uzai domin samun sawaba. Cigaba da maimaita addu'ar da duk ƙwaƙwalwar kaina ta taskace na yi har na samu sauƙi da ƙarfin da na iya jan gangar jikina zuwa wajen tabarmar, ina isa gare ta na kwanta ina mayar da numfashin wahala.
★
4:37am.
A hankali na soma motsawa, 'La'ilaha Illah Anta Subhanaka Inni Kuntu Minazzalimeen,' na ambata cikin zuciyata. Tashi na yi zaune, babu wadatar haske cikin ɗakin kasantuwar fitilar Obasanjo ya gaza da na kunna ta disashe, miƙewa na yi cikin rashin ƙarfin jiki na janye mayanin labulen taga da ya yi mini katanga da hasken farin wata da ya mamaye sararin samaniya, ina yaye labulen haske ya ratso cikin ɗakin. Baya na yi na lalubo butata da ke cike da ruwa, a hankali nake takawa har na fito waje zuwa inda ban ɗaki yake.
Ban jima cikin ban dakin ba na fito, sai da na fara wanke jinin da ke hancina sannan na yi alwala na koma ɗaki. Kasantuwar asuba ta kawo jiki hakan ya sa na gabatar da shafa'i da wutiri da raka'atanil fajr. Zama na yi na mintuna kaɗan ina zikirin ya hayyu ya kayyumu birahmatika astagisu aka tayar da sallar asuba, miƙewa na yi na gabatar da tawa sallar, bayan na idar na jingina da bango ina azkar har zuwa wayewar safiya.
Karfe bakwai daidai na shafa addu'ata, abayar da ke jikina na yaye na yi sama da yangwalalliyar rigata, na yi ƙuri ina kallon cikina, hannu na ɗora kansa na yi shuru ina sauraron motsinsa. "Barka da safiya abun ƙauna, ina fata kana lafiya. Jiya mun sha wuya ko? Ka yi haƙuri, duniya gidan jarabawa ne, kuma rauninmu shi ke tayar da ƙarfinmu, wata rana wannan wahalar za ta zama labari. Ka yi haƙuri ka ji, Amminka na gaishe ka..." Shuru na yi tamkar yana jin zancen da nake cikin zuciyata. "Kai ma kana gaishe ta ko?" Murmushi ya suɓuce mini na sake shafa cikina, sauke hannun na yi na karanta Lahaula da sauran addu'o'in kariya na tofa na shafe cikin gaba ɗaya.
Gyara zaman rigata na yi tare da hijabina sannan miƙe na ɗauki jakata. Buɗe jakar na yi, babu komai cikinta daga ƙaramin littafin rubutu da biro sai takardar naira dubu ɗaya da wasu 'yan canji. "Ba za su ishe ni na ci abincin yinin yau ba." Na ayyana a raina ina kaɗa kai.
Kai tsaye waje na fita na zira takalmin silifas sannan na jawo ƙofar ɗakina na rufe.
A cikin Unguwar Agege da ke birnin Legos gidan da na rakuɓa ina gudanar da wahalalliyar rayuwata yake. Gidan wani tsoho ne yana rayuwa shi da ɗansa da kuma 'yarsa. Yarinyar idan ta fita ba ta cika dawowa ba sai can cikin dare, da gari ya waye kuma kafin ta tashi daga barci na fita kasuwata.
Ba komai ba ne kasuwata ba face bara a babban titin Agege. Bara ita ce ci na, ita ce sha na, ita ce suturata a tsayin watanni uku da na yi ina yin ta, da ita nake komai na ƙaddararriyar rayuwata.
Shi kuma ɗan nasa mai suna Ayuba yaro ne mai nutsuwa da hankali, tamkar ba uwa ɗaya ta haife shi da 'yar uwarsa Saratu ba. Shi ya taimaka mani da kangon ɗakin da ba a ƙarasa aikin gininsa ba. Kodayake kusan duka gidan haka yake ba kammalallen gida ba ne, huntun bulo ne ba filasta da fulo.
Kasantuwar Ayuba ya san ba na magana, hakan ya sa ya ɗaga mini hannu cikin girmamawa. Jinjina kai na yi tare da mayar masa da martanin gaisuwar da ya yi mini. "Allah ya kiyaye ya ba da sa'a." Sake ɗaga hannu na yi alamun, ameen sannan na fice daga gidan.
IPAJA ROAD
AGEGE CENTER MOSQUE
Wurin cike yake da tarin masu bara, mafiya yawan su kuma, mata ne da yara maza daga cikinsu ɗaiɗaiku ne. A gajiye na isa wurin duk da babu nisa mai yawa tsakaninsa da gidan da nake. Jefi-jefi masu bayar da sadaka suna wucewa, sai dai ni ban samu komai ba kasantuwar ba na iya kokowa wurin karɓa. Har ƙarfe goma na safiya ta kawo jiki ina zaune gefe ina kallon masu bayar da sadakar da masu karɓa.
Wata mota mai matuƙar kyau ta yi parking daidai wurin da muke, zuba mata idanu na yi ina ƙare mata kallo. Cikin sauri da gudu irin na ƙwaƙwalwa wani tunani ya yi walƙiya cikin ƙwaƙwalwar kaina. 'Marcedes Benz' na ayyana a raina. Guje-guje da hanzarin masu karɓar sadaka a gurin motar ya dawo da ni hayyacina.
Tamkar na miƙe na karɓi tawa sadakar na ji, sai dai kokowar karɓar kuɗin da mutanen ke yi ta wuce yadda nake iya kare kaina daga gare ta. Daga inda nake ban motsa ba na zuba musu idanuwa ina ta aikin kallonsu, gani na yi ya miƙo kuɗin da ban iya kintacen nawa ba ne ya damƙa hannun ɗaya daga cikinsu. Kamar fari suka yi gefe suna rigima wajen raba su. Sam ban raɓi inda suke ba, na yi zaune ina jiran ta inda nawa rabon zai ɓullo.
"Baiwar Allah." Shi ne abinda kunnuwana suka zuƙo mini nesa kaɗan da ni. Kaina na mai da wurin da nake kintacen sautin muryar. Gaba ɗaya an sauke gilashin motar, kyakkyawan saurayi na yi tozali da shi gefen mazaunin direba, kallo ɗaya za ka yi masa ka san kuɗi sun zauna a fatar jikinsa. Da hannu ya yi mini alamun nazo. Miƙewa na yi da ƙyar saboda nauyin ciki tare da raunin da ke dabaibaye da jikina.
"Ke ma bara kike?" Ya tambaye ni lokacin da nake isa wajen shi. Jinjina kai na yi alamun eh.
Kaɗa kai ya yi cikin nuna damuwa. "Amma baiwar Allah ba ki da miji ne? You're too young and you're pregnant?" Baya na yi alamun tafiya domin ba surutunsa ya kawo ni ba, karɓar abinda zai taimake ni da shi ya kawo ni.
"Hey..." Ya faɗa. Juyawa na yi ina kallonsa, kuɗi ya miƙo mini. "Well." Ya faɗa yana ƙura mini idanuwa cike da al'ajabi. "Ko ma me ye, bai kamata a irin yanayin da nake ganinki a ce kina gurin nan ba..."
Gaba na yi na koma inda nake zaune, lissafa kuɗin da ya ba ni na yi. Kilo sha biyu ne na nairar Nijeriya. Uku daidai na raba su, dubu takwas na saka a jakata, sannan na miƙe na ba wa ɗaya daga cikin matan sauran dubu huɗun. Agogo na duba, ƙarfe goma da mintuna kaɗan, hamdala na yi a zuciyata, sannan na tafi shago na sayi abinda zan buƙata da nake tunanin zai min wuni biyu. Gaba na yi ina taku a hankali har na isa cikin lungun gidanmu, wurin Innani na biya na karɓi ƙosai da kunu sannan na wuce gida.
★★★★★
New G.R.A Modoji
Katsina State Nigeria.
Tsaye suke cikin farfajiyar wani katafaren gida. Cikin murya mai cike da kissa da kisisina ta furta. "My Boo..."
Murmushi ya sakar mata tare da faɗin, "My Shona." Langaɓar da kai ta yi a shagwaɓe ta ce, "Ji nake kamar kar ka tafi Sweetheart."
"Shona, dole na tafi mana, idan ban tafi ba wa zai nemo mana kuɗin?"
"My Boo... We're now a millionaires, saura ƙiris ma mu zama billonaires, ko My Boo?," ta ƙarasa zancen tana rungume shi. Jinjina kansa kawai ya yi ba tare da ya furta komai ba.
"Nawan, Allah ya kiyaye. Sai ka dawo," Buɗe motar ya yi ya shige, a hankali ya silala ya fice daga cikin gidan.
Da sassarfa ta shige cikin falon gidan, juya kai ta yi ta kalli wani sashe cikin ƙayataccen falon, harara ta watsa ma wurin sai kuma ta saki dariya ta faɗa kan daya daga cikin kujerun da suke zagaye da falon. Numfashi ta sauke ta jawo wayarta. Kira ta danna ringing biyu ta yi aka dauka.
"Hello Mom."
"Na’am diyata, 'yar albarka," ta amsa daga gefe.
"My mom in fada maki tafiyarmu Vienna ta matso, few days suka rage, yanzu haka ma ya tafi wurin meeting Kano."
Wacce ta kira da Mom ta ce, "Ɗiyata ina fata ku je lafiya ku dawo lafiya, ni abinda nake so ko hajjin bana a yi ta da ni."
"Mom ba ki da matsala, ko ni nan zan biya miki da kaina. Ba ma haka ba Mom, ai kafin lokacin hajji sai na cika miki account ɗinki da kuɗi lokacin da za mu tafi har wasu sai kin biya ma wa"
"Ina alfahari da ke ɗiyata." Uwar ta faɗa cikin shewa.
"Kin san wani abu Mom? Gaba ɗaya fa Sweetheart ya ƙarasa mance wannan matar tasa, haka Ummansa ba ya tuna komai fa game da 'yan iskan family ɗinnan nasa. Yanzu ni kaɗai nake da AbuƊalib sai yadda na yi da shi." Dariya suka yi gaba daya.
Sai da suka yi mai isar su sannan Uwar ta ce, "To abinda zan fada maki dai ki mai da hankali ki tara abinda kika tara, ba kin ce can Binina."
"Vienna fa Mom."
"Oho, ko ma mene ne dai ku kuka sani. Ina ce can ma kudin zai samu ba, to ki kokari har gida ya siya miki, ba iya kudin za ki ta karɓa ba, ki samu ki samu har da Kadarori."
"An gama My Mom," ta fada tana wata dariyar. Hira suka cigaba da yi kafin daga bisani ta kashe wayar.
Ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ɗora, cikin isa da ƙasaita ta ce, "Laure! Laure." A hanzarce yarinyar ta ƙaraso tana faɗin ranki ya daɗe ga ni. Ɗan yamutsa fuska ta yi a banzace ta ce, "Ki mai da hankali ki ƙara gyara gidan nan, don na ji wani wurin yana ɗan tashi. Sannan a yi min ɗanwake, yau danwake nake son ci."
"To hajiya an gama," ta fada tare da mikewa tsaye da sauri ta fara abinda aka umarce ta.
★
Tuƙi yake a hankali ya har ya hau babban titin da zai fitar da shi daga Katsina wanda zai ɗauke shi ɗoɗar ya kai shi har birnin Kanon Dabo.
Kallon titi yake yi ƙwaƙwalwarsa cike da tunani, tamkar akwai inda ya kamata ya je kafin ya wuce, tamkar akwai abinda ya kamata ya yi kafin ya hau hanyar, tamkar akwai wanda ya kamata ya gani kafin ya je meeting ɗin. Zuciyarsa ta buga da ƙarfi, rufe ido ya yi ya buɗe wani abu mai kama da mamayar duhun dare ya soma lullube masa zuciya, numfashi ya furzar da ƙarfi ya cigaba da tafiya a hankali.
"Manzon Allah S. Ya ce, "Idan za ku yi tafiya ku sayi hanya. Yin sadaka kenan Joonam, kar ka wuce ƙofar welcome to Katsina ba ka yi sadaka ba Yaya."
Da sauri ya taka birki, gefe ya yi da sauri ya tsaya cikk, maganar yawo take a cikin tasmaharar tunaninsa. Hannu ya sa ya bigi sitiriyan motar, 'What's wrong with me? Ina fama da hallucination ne wai?... Noo... But i want see a Doctor immediately. Bara na isa Kano..."
Kansa ya ɗora kan sitiyari kamar idanunsa za su zubar da ƙwallah. Sai da ya mayar da numfashi sosai, sannan ya ja dogon tsaki, dubu biyar ya fiddo ya riƙe a hannunsa, motar ya tada ya cigaba da tafiya. Almajirin da yake hange kaɗan har ganinsa ya so yamutsa tunaninsa ya miƙa wa kuɗin.
"Allah ya kiyaye Allah ya sa a sauka lafiya."
Almajirin ya faɗa. Kallonsa ya yi ba tare da ya iya amsawa ba, dogon tsaki ya ja, domin suna ɗaya daga cikin kalaman da ke mashi gizo suna kai farmaki wa nutsuwarsa. Cikin rashin sanin makamar tunaninsa ya mayar da hankalin kan hanya ya cigaba da tuƙi cikin kwarewa domin isa Kanon dabo.
*TAKU MAI ƘAUNAR GANIN FARIN CIKINKU A KOYAUSHE, FATIMA MUHAMMAD SANI AKA FANTAH. NAKE MUKU FATAN ALKHAIRI KU KASANCE CIKIN ƘOSHIN LAFIYA.*
*KI MALLAKI NAKI A KAN ₦1000 KACAL.*
*CONTACT ME @*** IF YOU'RE INTERESTED*
*KU DANNA BLUE LINK DA KE ƘASA KU YI FOLLOWING WHAT'S APP CHANNEL ƊINA DOMIN SAMUN DUKKAN SHAFUKAN ƊANƊANO.*
***
*DON'T FORGET TO LIKE👍 COMMENT💬 SHARE🔀*