AKWAI SO

The Wedding Picture

by @azizat

             *AKWAI SO*

                    Chapter one

             

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

                   KANO, 2015

                 The Wedding Picture


HAJIYA SAKINA, mace mai shekara 42 a duniya ke zaune akan ɗan ƙaramin stool tana kallon fiskarta a madubi. Kwallin da ta gama sakawa ne ta ke ganin kamar ya ɗan zazzago a gefen idonta na hagu. Ƙibar da ta haɗa tun haihuwar autanta Nazif shekaru goma da suka wuce shi zai sa ka ga kamar ta haura hamsin. Ƙaton tumbin da ta ajiye tun bayan haihuwar autan nata har yau ƙara girma ya ke ya ƙi raguwa, tun tana biye-biyen siyen slimming tea har ta gaji ta haƙura da chanjawar da haihuwa ya janyo mata.

Ƙarar alarm ɗin wayarta ne ya ankarar da ita lokaci ya yi da za ta tafi turakar mijinta. Koda ya ke hira ce kawai za ta masa na abubuwan da suka faru a lokacin da ya ke tare da sauran matansa guda biyu da ke Abuja. Zuwa awa ɗaya ko awa biyu za ta masa sallama ta dawo ɗakinta ta kwanta.

Kamar kullum ta kan yi ƙoƙarin tsaftace jikinta sannan ta yi kwalliya ta fesa turaruka masu ƙamshi idan za ta je wajen mijinta. Wannan al'adarta ce tun farkon aurensu har zuwa yau. Kwalliyartata dai baya wuce 'yar kwalli, hoda, sai jan janbaki, sune kwalliyarta a kullum, sai kuma ƙanshi da bata rabuwa da shi a koda yaushe.

Hajiya Sakina ko Maami kamar yadda 'ya'yanta ke kiranta Allah ya azurtata da haihuwar 'ya'ya shida a cikin shekaru ashirin da huɗu da aure. Ta auri Alhaji Habibu Wakili tana shekara 17 a duniya. Tun yana ƙaramin ɗan tireda har zuwa yanzu da Allah ya buɗa masa arziƙi.

Jin ƙarar Alarm ɗin ƙarfe goma da minti biyar na dare da ya buga ya sa Hajiya Sakina ta gaggauta shafa jan janbaki a ƙananun lips ɗinta sannan ta miƙe ta fesa turare kaɗan a jikinta.

Rufo ƙofarta ta yi a hankali sannan ta wuce ɓangaren mijinta.

Gidan nasu madaidaicin gida ne da Alhaji Habibu ya siya a shekarunsu na goma da aure, lokacin ita kaɗai ce matarsa bai fara tunanin tara mata ba. Ɗakuna biyar ne a gidan da falo biyu. Falo haɗe da master bedroom shine sashen Alhaji. Sai cikin gidan kuma falo da ɗakuna huɗu da kitchen, da store. Ɗaki ɗaya na Hajiya Sakina ne, sai ɗakuna biyu na yaranta, sai ɗakin baƙi. A wannan gidan suka rayu har shekara goma shahuɗu. A gidan ta aurar da 'ya'yanta biyu mata, Aisha da Nana Fatima.

***

Alhaji Habibu Wakili yana kishingiɗe akan gado yana chatting fiskarsa ɗauke da murmushi saboda abinda aka turo masa.

"Kai yarinyar nan ja'ira ce" ya faɗa a bayyane yana matse ƙafarsa.

A Instagram ya ga hotunanta. A take kuwa ya tura mata DM da private account ɗinsa. Tun da ya tura mata dubu ɗari biyu ta tabbatar da gaske shi ɗin ne Alhaji Habibu Wakili ta sake da shi ta fara tura masa abubuwan da suke birkita masa hankali. Ba a Abuja take ba shi yasa bai samu sun haɗu tun wata biyu da ya fara cin karo da ita a Instagram ba. Ya mata alƙawarin zai biya mata kuɗin jirgi ta zo Abuja su yi weekend amma ta ƙi. Yanzu haka saboda ita ya shigo Kano tun laraba maimakon ranan Jummu'ah da ya saba shigowa. Gobe Alhamis da ita zai wuni gashi tun yanzu ta fara birkita shi, ina ga sun haɗu.

Sallamar Hajiya Sakina ne ya katse shi yai saurin ajiye wayar yana kallon Uwargidan tasa yana amsa sallamarta tareda ƙoƙarin miƙewa ya zauna ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya dan kar ta gane tashin da ya yi.

"Uwargida ran gida" ya faɗa yana murmushi

"Barka da dare, Alhaji" Maami ta faɗa tana zama a kujerar da ke ɗakin.

Sai da suka gaisa sosai, ta masa ya gajiyar hanya sannan ta tambaye shi ko ta kawo masa shayi, ya ce mata baya buƙatar komai.

"Barin kawo maka ruwa" ta faɗa tana miƙewa jan leshin da ta sa sai ɗaukan ido yake.

Tana fita falonsa yai saurin ɗauko wayarsa yana ƙoƙarin

bawa Babynsa haƙuri akan ta bashi minti talatin yana zuwa.

Har Hajiya Sakina ta dawo ɗakin ta ajiye ruwa da kunun Aya mai sanyi Alhaji yana faman danna wayarsa.

Tunani ta yi ko da ɗaya daga cikin matansa da ke Abuja ya ke chatting. Koma wacece a cikinsu ba huruminta bane.

Matan Alhaji Habibu biyu suna Abuja. Ita kaɗai ce ya barta a Kano. Sau ɗaya ya ke zuwa mata a wata sai kuma idan biki ko wani harkan kasuwanci ya kawo shi Kanon.

Shekaransu goma shaɗaya da aure ya auri Baraka, lokacin ta gama jami'a tana bautar ƙasa. Baraka ta yi karatu wannan dalili kaɗai ya isa ya ce mata zai tafi da ita Abuja lokacin da Alhaji Habibu ya shiga harkar siyasa ya tare a Abuja. An ce mata ƙaton gida ya siya a Abujan. Bata taɓa zuwa ba. Ta yi tunanin zai ɗauketa lokacin da komai ya kammala Baraka ta tare sai bai kawo mata maganar ba, itama sai ta yi shiru da cewa zaman Abuja ba nata bane.

Duk wanda ya san Alhaji Habibu Wakili wanda yai Minister a zamanin Obasanjo 2003 zuwa 2007 to zai san shine da matarsa Hajiya Baraka Habibu Wakili kamar yadda ta kakaɓa sunan mijinta a sunanta. Ba kasafai mutane suke tuna cewa akwai uwargidan Alhaji Habibu Wakili mai suna SAKINA SABO SHEHU ba. Har Alhaji Wakili ya gama tashensa a siyasa Maami bata taɓa canja sunanta zuwa na mijinta ba.

"Hajiya kika ce akwai yarinyar da za ta zo zama da ke?" Alhaji ya katse shirun nasu. Lokacin da ya ke Abuja ta kira shi a waya ta ke faɗa masa akwai wata 'yar ƙawarta da za ta zo ta zauna da su, yarinyar ta samu admission a BUK kuma Babanta ba ya so ta yi zaman hostel.

Maami ta yi murmushi ta ce "Alhaji ka tuna Hajiya Maimuna, Maman su Salim da muka taɓa zama da su lokacin muna Gyaɗi-Gyaɗi?"

Alhaji ya ɗan ɗago ido daga kan wayarsa da ya ke dannawa ya ce "matar Alhaji Sambo?"

"Ita dai, ka san Lagos suka koma ai. To 'yarta Hanan ce za ta zo"

"Hanan?" Ya faɗa yana ƙoƙarin tuno yaran Alhaji Sambon da ya sani.

Maami ta yi saurin ƙatse shi da cewa "Lokacin da suka koma Lagos aka haifeta. Ka san yaransu uku duka maza ne kafin su bar Kano"

"Haka ko" Alhaji ya faɗa yana maida hankalinsa kan chatting da ya ke yi.

"Ba matsala zamanta a nan ko?"

Ba tareda ya ɗago ya kalleta ba ya ce "Allah ya kawota lafiya, sai ta zauna a ɗakin Maryam, kin ga kin sami abokiyar hira kafin Maryam ta dawo".

"Nagode, Alhaji. Allah ya ƙara daraja"

Alhaji Habibu ya amsa da Amin.

Shiru ne ya ratsa ɗakin. Alhaji sai murmushi ya ke abinda ya ke kallo a wayar ke ƙayatar da shi.

Maami ta sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Hirar tasu ta ƙare kenan.

Ta ɗan yi gyaran murya ta ce "Alhaji kana dai ji daga wajen su Nana da mijinta ko"

"Fatima da Mijinta suna lafiya. Bai fi sati biyu da suka wuce ba ma ita da mijinta suka kawo mana ziyara har gida"

"Madalla! Allah ya basu zaman lafiya"

"Amin" Alhaji ya amsa a taƙaice. Babu wani ƙarin bayani gameda 'yartata da mijinta. Wata uku da suka wuce aka yi auren Nana Fatima ta tare a Abuja, a Abujan ta haɗu da mijinta dan a can ta ke karatu. Lokacin auren ma Alhaji ya so ya ci mata fiska wai a Abuja za a yi bikin. Sai da Mujahid da Aisha suka saka baki kafin aka dawo da bikin Kano.

Itama Fatiman da ke zaman Abuja ya koya mata zaman ƙarya har da cewa ta fi son a yi bikin a Abuja ba a Kano ba, wai gidan Abuja ya fi girma.

Bata sani ba ko dalilin an yi bikin a Kano ne ya sa har yanzu ta ƙi ta zo Kano. Mijinta kwanaki da ya shigo Kano ya zo har gida ya gaishe da Maami kuma ta ji daɗin hakan.

Ganin dai hankalin Alhaji akan waya ya ke ya sa Hajiya ta miƙe tsaye ta tattara tray ɗin da ta kawo ko kallon abinda ta kawo dama Alhajin bai yi ba.

"Sai da safe, Alhaji"

"sai da safe, Hajiya"

Har ta kai ƙofa ta ji ya ce "gobe zan fita da sassafe, akwai wasu ayyuka da zan je na duba zan iya kaiwa can dare kafin na dawo"

Hajiya Sakina ta ce "Allah ya kaimu goben"

"Mu kwana lafiya"

A can ƙasan maƙoshi ta amsa masa da Amin.

Lokacin da ta shigo babban falo sauke ajiyar zuciya ta yi. Idanunta suka sauka kan wani ƙaton hoton frame na aurensu. Shi kaɗai ne hoton da ta ke da shi na aurensu wanda ta ɗauka ita da Alhaji Habibu. Ƙaramin hoto ne da har ya ma fara koɗewa saboda ajiya, sai kuma shekaru huɗu da suka wuce a lokacin Anniversary ɗin cika shekara ishirin da aurensu babban ɗanta Mujahid ya je aka enlarging hoton aka masa frame. Shi da kansa ya saka hoton a falon.

Ko miye zai kawo nan da wata biyu idan ta cika shekara ishirin da biyar da aure sai Allah!.

Mujahid da Abida ne iyayen celebration ɗin birthdays ko anniversary. Ita sai ta manta da abu ma sai ka gansu da cake wai suna celebrating ɗin wani abu nata. A lokacin da ta cika shekara 40 a duniya ma ƙaton cake Mujahid ya kawo. Ita kuma Abida ta baking nata cake ɗin a gida. Alhaji baya nan amma duka yaran sun zo, aka sha hotuna bayan nan kuma suka tafi restaurant cin Abinci. Ba za ta taɓa mantawa da wannan ranan ba. Har hawaye ta yi saboda farin ciki.

Hawayen da ya ke shirin gangaro ma Hajiya Sakina ya sa ta yi saurin kashe wutan falon ta wuce ɗakinta. 

Cire leshin jikinta ta yi ta shiga banɗaki ta yi alwala ta fito ta saka doguwar rigan bacci. Ɗan sosa kanta da ta yi ya tuna mata cewa ya kamata gobe ta je a yi mata kitso, satin kitson kanta na biyu kenan, ya fara tsufa.

A hankali bacci ya tafi da ita...

©AzizatHamza2024