The Guest
by @azizat
*AKWAI SO*❤
Chapter Three
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
KANO, 2015
The Guest
"Adama!" Maami da ke kitchen ta ƙwalo sunan mai aikinta.
"Na'aaaam, Hajiya" Adama ta amsa daga can cikin ɗaki.
"Wai ba ki gama gyaran bane?"
"Yanzu zan gamaaaa"
Maami ta girgiza kai. Ba a taɓa kawo mata 'yar aiki 'yar ƙauye irin wannan ba. Ta yi wata shida da su amma har yanzu Hajiya Sakina bata iya sake mata aikin gidan saboda duk abinda ka sakata sai an samu matsala.
Har Maami ta ƙare soya dankali da ƙwai ta haɗo shayi ta kawo dining Adama bata fito daga ɗakin Abida ba.
Maami ta zauna ta fara shan shayinta da ya ji kanamfari, lemon grass da citta da sauran kayan yaji. Saboda ƙibarta ta jima da dena amfani da madara.
Tana karyawa sai ga kiran Hajiya Maimuna. Hajiya ta ɗau kiran tareda sallama suka gaisa. Hajiyar ta ce mata yanzu jirginsu Hanan ya tashi. Maami ta ce Allah ya kawota lafiya.
"Hajiya, na gama gyaran" Adama ta faɗa tana kallon plate ɗin dake gaban Maami.
"Wai yaushe za ki koyi yin aiki da jikinki ne kam Adama?. Ki dinga kazar-kazar kin ji. Ba wai a saka ki aiki ɗaya ki wuni ba ki gama ba"
"Zan gyara, Hajiya"
"Ki je kitchen ki ɗauko abinci ki karya"
Adama ta wuce da sauri. A iya zamanta da Hajiyar in dai wajen abinci ne tana cin daɗi dan abincin da kowa ke ci a gidan shi take ci. Wata Ummanta Naja'atu ce da ta taɓa aiki da Hajiyar ta kawota gidan bayan ta gudo daga gidan da ta fara aikatau, saboda muguntar matar da 'ya'yanta. Hajiya ta karɓeta da hannu biyu amma da sharaɗin ba zata riƙa kwana ba, dan dokar aiki da Hajiya kenan.
Lokacin da Maami ta gama karyawa sai ta ɗauki plate ɗin da mug da ta sha shayi ta kai kitchen ta saka a sink zata fara wankewa Adama ta shigo da sauri ta ce "Hajiya, barin wanke kwanon"
"Barshi, ki je ki ƙarisa cin abincin ki" dama kallon da Adamar ke yi a falo ne ya hanata gama cin abincin da wuri.
Maami ta maida komai wajensa ta goge wajen da ruwa ya taɓa sannan ta fito.
Ɗakin Maryam Abida ta shiga dan ta ga gyaran da Adaman ta yi. Ta ce mata ta matsar da kayan Abida gefe saboda idan Hanan ta zo ta samu gefen da za ta saka kayanta a closet ɗin, amma Adama bata yi ba. Maami ta girgiza kai. Idan ta kira Adama ta ce za ta mata masifa ma, ɓata bakinta kawai za ta yi. Ita shiyasa bata son 'yan aiki yara. Ba dan Naja'atu ba babu abinda zai sa ta karɓi 'yar shekara shahuɗu aiki.
Da kanta ta shiga arranging kayan Abidan saboda a samu space. Wani rigan Nana Fatima da ta gani ne ya sa ta tunanin Allah ya sa lafiya ta ke da mijinta. Kullum sai Aisha ta kirata sun gaisa duk ƙarshen wata kuma za ta zo gida su wuni tare. Yanzu nema da ta yi nauyi bata zuwa. A 2013 da aka yi auren Aishan ta samu ciki amma sai ta yi ɓarinsa a wata na huɗu. Sai wannan da ta samu yanzu yana wata na takwas.
Da Maami ta gama arranging space ɗin sai ta fita ta sa Adama ta kirawo mata driver ta ce masa anjima zai je Airport ya taho da baƙuwarsu.
Ɗakinta ta wuce ta watsa ruwa sannan ta fito ta saka doguwar riga. Yanzu ɗinkin doguwar riga ko Abaya ta fi sakawa, dan ta fi son saka abinda za ta jita a sake ba tareda kuma ya nuna girman tumbinta.
Ta riga ta haƙura da shan slimming tea dan basa mata aiki. Wanda ta siya last da ya sakata gudawa sai da ta kwanta a Asibiti kwana ɗaya ana ƙara mata ruwa. Tun daga nan ta tattare komai ta watsar. Kwanaki waist trimmer da ta ga ana tallatawa a Instagram ta siya ta ke ɗaure cikin da shi, amma bayan kwana biyu da ta gagara numfashi bayan ta sa sai ta watsar. Ga su can har guda biyu a ƙasan akwati bata sake waiwayansu ba.
Ta so siyan abun motsa jiki, sai shima ta zo ta watsar da batun exercise ɗin, dan tunda su Khalil da Abida suka sakata a gaba da cewa ta riƙa fita gudu duk safiya ta watsar da komai ta zauna da ƙibarta haka. Dan kam ba za ta iya fita gudu ba.
Kusan ƙarfe ɗaya na rana Maami na ɗaki tana shirin shiga banɗaki ta yi alwala Adama ta ƙwala mata kira
"Hajiya, ga baƙuwarki ta iso"
Maami ta fasa shiga banɗakin ta fito falo ta zauna tana jiran shigowar Hanan. Adama ce ta fara shigowa falon da akwatuna guda biyu sannan sai ga Hanan ɗin ta shigo tana cin chewing gum.
Maami ta ƙare mata kallo. Farinta na bleaching ne dan har wani orange-orange ta zama. Sai kuma dogon gashin da ta saka har gadon baya wanda ya ke juyawa idan Hanan ɗin ta juya kai. Gyalen material ɗin da ke jikinta a kafaɗarta na dama ya samu zama. Duk ba wannan bama, abinda Maami ta ƙi jini ne ta gani a jikin Hanan ɗin. Zara-zaran fake nails jajaye ne a hannunta. Yadda Maami ta tsani ganin zaƙo-zaƙon farcen da mata ke sawa ko gashin wig bata tsana kamar haka ba. Ita a tunaninta babu mai hankali da zai saka dogayen faracu kuma ya ce zai zauna da tsafta. Wallahi ko abu ka bata ta ga faracunka da datti in dai na ci ne ba za ta ci ba. Cewa ta ke daga farce ake gane ƙazantar mutum.
"Sannu, Hajiya"
"Sannu, Hanan. Ya su Mamanki?"
"She's fine, ta ce na gaishe ki"
"To ina amsawa" Maami ta kalli Adama da ta tsaya riƙe da hannun akwati ta ce ta kai Hanan ɗaki.
"Idan kin huta sai Adama ta kawo miki abinci, sannu da zuwa" daga faɗin haka Maami ta wuce ɗakinta. Sai da ta kira Hajiya Maimuna ta ce mata Hanan ta iso Hajiyar ta mata godiya sannan ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala. Ta fito ta shimfiɗa sallaya za ta tada sallah ta fara jin ƙaran kiɗa daga ɗakin Abida. Speaker aka kunna dan da ace waya ce ba za ta ji kiɗan da ƙarfi har ɗakinta ba. Khalil ne da mai wannan jujun saka kiɗa a gidan shima kuma tun da ya tafi Malaysia karatu ta samu nitsuwa.
Ta tada kabbara ta fara sallah. Da ta gama ta zauna ta ɗan yi azkar sannan ta ɗaga hannu ta fara yiwa duka 'ya'yanta addu'a. Tana cikin addu'ar wayarta ya fara ringing. Sai da ta gama ta jawo wayarta daga kan gado ta ga missed called biyu na Anty Hafsah matar Yaya Ibrahim.
"Assalamu Alaikum"
Daga ɓangaren Anty Hafsah ta ce " Anty Sakina, Lace ɗin nan yadi uku kika yanka ba yadi huɗu ba fa"
"To ai Hafsah yadi uku kika ce"
"Ba ki dai ji da kyau ba, yadi huɗu na ce"
"To ki yi haƙuri zan sa driver ya kawo miki sauran yadi ɗayan"
"Amma fa ba zan biya ciko ba tunda dai ke kika faɗi kuɗin da kanki"
Maami ta yi murmushi ta ce "Maman Sultan kenan, tsaf zan fanci kuɗina a wajen mijinki gara ma ki turo min cikona"
"Ni dai ina jira" ta kashe wayar.
Maami ta ajiye wayar itama tana miƙewa tsaye. Idan ka haɗa business da 'yan'uwa sai a hankali. Yanzu haka akwai matan yayunta dayawa da ta ke bi kuɗi har yanzu shiru.
Gara ma Yaya Ibrahim da Yaya Muhammadu idan ta bi ta wajensu kuɗi na fitowa, amma sauran kam ce mata suke ta karɓi kuɗinta a wajen matan ba za su biya musu ba.
Store ɗin kayanta ta shiga ta yanko yadin kayan ta saka a leda ko sticker na sunan business ɗinta bata saka ba. Adama ta bawa ta ce ta ba wa driver ya kai gidan Maman Sultan a Nasarawa.
***
Alhaji Habibu Wakili bai shigo gida ba sai ƙarfe shabiyu na dare. A gajiye ya dawo ya shiga ɓangarensa. Yana shiga ɗaki ya kwanta yijif a gado yana numfashi. Yau saura kaɗan numfashinsa ya ɗauke tsabar daɗi. Yarinyar nan ta kai shi ƙololuwar daɗi a yau ɗinnan. Maganin da Baba Buzu Maigadinsa na Abuja ya ke bashi ba ƙaramin aiki ya ke masa ba. Idan ya sha wannan jiƙon ya kan iya awa ɗaya har awa ɗaya da rabi yana gurzan mace. Wannan karan ma sai da ya bawa yarinyar nan mamaki dan kafin su haɗu ta gama ce masa ba zai iya komai a shekarunsa ba. A shekarunsa hamsin da biyu jinsa ya ke kamar ɗan shekara talatin. Ba macen da ba zai iya karawa da ita ba.
Ko wanka bai yi ba saboda gajiya a haka ya fara bacci har da minshari.
Da Asuba da ya tashi ji yai inama a can guest house ɗin kawai ya kwana. Amma yarinyar ce ta ƙi zama su kwana. Ƙarfe shaɗaya na dare ya sauketa a inda ta ke zama kafin ya wuco gida.
Yai miƙa yana shafa guntun gemunsa ya shiga banɗaki yai wanka sannan yai Alwala ya fito. Jallabiya ya saka ya fito ya wuce masallaci.
Da ya dawo daga masallaci a falo ya zauna ya fito da wasu documents yana duba wa.
Maami ce ta shigo ta gaida shi sannan ta tambaye shi ko a yi breakfast da shi ya ce a yi dan yana jin yunwa. Fita ta yi ta kunna gas ta fara prepping abin da za ta masa sannan ta shiga ɗakin Nazif ta tashe shi dan ya fara shirin makaranta.
Makarar da ta yi da Asuba ne ma ya sa bata fito ta tashe shi ya je masallaci ba. Ta dai tashe shi ya yi sallar Asuba ƙarfe shida saura.
Ta fito daga ɗakin Nazif ta wuce ɗakin Alhaji ta fara gyarawa.
Rigar da ya cire jiya ta ke so ta kai washing machine. Ta fara duba aljihun rigar ko akwai kuɗi ko wani abu ta cire, sai ta ji kamar kwalba a ciki. Ta ciro kwalbar tana tsammanin kwalbar turare ne amma hoton abin da aka zana a jiki ya tabbatar mata ba turare bane. Ire-iren kwalabe da ƙulle-ƙulle da ya ke sha duk dare tun yana Habibu Tiredansa ne. Ta sani, da wannan ya dogara. Shi yasa wani lokaci idan ya zo mata ta ke jin warin namijin goro ko saiwowi haka. Wani kokaci kuma har warin Agumun Yarabawa ta ke ji.
Ɗauke kwalbar ta yi ta ajiye masa a gefen turarukan da ya ke shafawa dan ya tabbatar ta gani. Ƙoƙari ta ke ta kore duk wani zargi da ke zuwa mata.
Zargin ita kaɗai ce matarsa a Kano.
Zargin jiya da ya ce zai jima, ta jira shi a falo har ƙarfe shabiyun dare kafin da ta ji shigowar motarsa sai ta wuce ɗakinta ta kwanta.
Zargin gajeran wandon da ya cire jiya yana wani ƙarni, sannan... Astagfirullah! A'u'zubillahi Minash Shaiɗanir Rajim. Ta kawar da sheɗanin da ke son birkita mata tunani.
Sai da ta gama komai har an kai Nazif makaranta sannan Adama ta iso. Maami ta ce ta je ta gyara babban falo, kitchen, da ɗakinta sannan ta kaiwa Hanan abinci ɗaki tun da yarinyar ta ƙi fitowa.
Da Alhaji ke karyawa kafin ya fita ya ke tambayarta ko baƙuwar ta iso Maami ta ce masa ta iso. Alhaji ya ce idan ya dawo da yamma sai ta kirata su gaisa. Maami ta ce ba matsala...
©AzizatHamza2024