The Wedding Night
by @azizat
*AKWAI SO*
Chapter Five
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
KANO, 1990
The wedding night.
An ɗaura aurena a ranan Asabat ishirin ga watan October 1990 (20-10-1990). Aure ne da aka yi na gani na faɗa dan kuwa Habibu ya yi rawan gani a lefe da kuma kuɗin aure da sadakin da ya kawo. Duk da auren namu an yi shi ne a ƙanƙanin lokaci amma Habibu ya fitar dani kunya. Tare aka haɗa bikinmu da su Altine 'ya'yan Baba Ja'afaru amma duk da a gidansa aka yi taron biki hakan bai hana mutane sun gane akwai banbanci tsakanina da 'yanuwana ba.
Inna ce uwar Amarya. Kuma har ga Allah ta tsaya sosai akan bikina. Duk abinda uwa za ta yiwa 'yarta Inna ta mini a lokacin bikina. Ba ta bari na yi maraicin Ummana ba a ranan. Baaba Ladi ma ta taka rawa a bikina.
Da za a kaini ni da Inna muka sha kuka. Ita tana kukan rabuwa ni kuma ina kukan iyayena da ba su raye a ranan da za su fi kowa farin ciki da aurena.
Haka aka kaini gidan Habibu Tireda ina kuka.
Babu abin dana sani gameda SO sai abinda na ke karantawa a novels. Babu abinda na sani game da alaƙar mata da mijinta sai abinda na karanta a litattafan soyayya na Turawa.
Shi yasa lokacin da Habibu ya shigo ya fara janye mayafina ban san ya zan amsa masa ba. Mace an santa da kunya dan haka na yi shiru ina jin warin gumi da ya haɗu da turaren da ya fesa. Bana tunanin ya sake wanka tun wankan fita ɗaurin aure, dan kayan da ya saka aka ɗaura mana aure shine a jikinsa har yanzu. Kayan ne a jikinsa lokacin da yaya Musa ya sa aka kirawo Boda Luku mai hoto ya mana hoto ni da shi. Ko lokacin da ya matsa kusa dani aka ɗaukemu hoton irin warin gumi da turaren da na ji kenan.
Na rintse ido lokacin da mijina Habibu ya kai bakinsa kusa da bakina yana shirin kissing ɗina. Bakinsa warin namijin goro ya ke. Kamar akwai abinda ya sha kafin ya shigo ɗakin. Ban amsa masa ba duk da na taɓa karanta yadda ake kiss a litattafan da nake karantawa. Na kwanta shiru ina shanye duk wani zafi da nake ji ta ƙasana da kuma warin gumi da Habibu mijina ya ke yi.
Shikenan na zama mace kamar yadda su Inna ke faɗa. Na yi tunani, da ɗin ni ba mace bace sai da na yi aure? sai da na yi tarayya da Habibu?.
Lokacin da Habibu ya kwanta gefena yana nishi sai na ƙurawa ceiling ɗin ɗakinmu idanu. A zahiri duhu na ke gan, amma a zuciyata ina ƙiyasta layuka nawa ne a jikin ceiling ɗin, layi 8, 10,16 ko 20? Na kasa banbancewa.
Na sani daga yanzu dole na saba da zuwan Habibu. Wataƙila a haka zan saba da warin gumi da turarensa iya shekarun da za mu yi tare a doron ƙasa.
Na jima ban yi bacci ba. Na jima ina tunanin yadda gobe za ta kasance. Ko akwai so, ko babu...
Washegari dana tashi zan cire zanin gado dan na wanke sai na ji warin yawun bacci a jikin pillow guda ɗaya. Na girgiza kai na cire rigar pillown na kai banɗaki na wanke su duka. Duk wani datti na wanke, dattin gumi, dattin yawun bacci, dattin komai...
Daga gidansu Habibu aka kawo mana abin kari. Ya haɗo da kayan shayi muka karya tare. Lokacin da zai fita sai ya ce min ƙannensa za su zo, sannan da yamma za mu je na gaishe da mahaifiyarsa. Ce masa na yi 'to' ina tunanin abin da zan riƙa kiransa da shi.
Duk sunan dana kawo a raina sai na ji bai dace da shi ba. Bai dace da zamantakewarmu ba. Tun dana taso 'Alhaji' iyayena mata ke kiran Babanmu. Ban sani ba ko tun kan ya je Hajjin haka suke kiransa. Kai, duk ranan da na je gidanmu sai na tambayi Inna me take kiran Baba a farkon aurensu, musamman shekaru takwas ɗin farko da take ita kaɗai babu kishiya.
Da ƙannensa suka zo na ji yaya Habibu suke kiransa sai nima na fara kiransa da hakan.
Wasa-wasa kwanaki suka fara tafiya har na yi wata a gidan Habibu tireda. A lokacin ne kuma na fara wani mugun laulayi, kullum sai na yi amai sau biyar ko fiye. Na koma babu abinda zan ci da zai zauna a cikina. Ana cewa Amare na ƙiba idan suka yi aure amma ni watanni ukun farko na aurenmu wani mummunan rama na yi.
Sai da cikina ya kai wata huɗu sannan na fara samun sauƙi. A lokacinne kuma na yiwa Habibu maganar NCE saboda yaya Yusuf ya ce an fara siyar da form.
Tashin farko ya ce ba zan haɗa karatu da renon ciki ba na bari sai na haihu tukun tunda cikin na wahalar dani. Haka na haƙura ina addua'r Allah ya saukeni lafiya.
*
Bani da matsala a zaman aurenmu idan akwai matsalar da ke damuna kullum bai wuce pillow da ke jiƙewa da yawun bacci ba dan kullum sai na wanke rigar pillow. Ni na san hakan na da nasaba da jiƙon da Habibu ke sha duk dare idan zai kusanceni. Ban taɓa tambayarsa jiƙon na menene ba. Ban taɓa kuma ce masa bakinsa na wani irin wari idan ya sha jiƙon ba. Haka ban taɓa maida masa kiss ɗinsa ba, har ya ɗau hakan a matsayin ban iya kiss bane.
"Ki saki jiki dani ki dena jin kunya, Sakinatu. Shi ya sa matan kudu suka fi ku wayewa" haka ya faɗa min watarana da ya nemi bakina na danne leɓena.
Idan akwai abin da ke burgeni da mijina to bai wuce jajircewansa akan neman kuɗi da kuma kula da iyayensa ba. Kusan duk gidansu da shi suka dogara. Shi yasa ma duk abinda ya ke samu akansu ya fi ƙarewa. Matan Babansa huɗu, kuma su 27 ya haifa. Habibu shine ɗa na uku, na biyu a cikin maza. Mahaifiyarsu da suke kira Gwaggoji ita ce uwargida, kuma ita ke da 'ya'ya tara.
Babansu Malam Muhammadu Wakili mahauci ne amma sai shegen maƙo. Ance idan yana neman mace a waje kashe mata kuɗi yake kamar ba gobe, amma da zaran ya aurota shikenan.
Dukka 'yan gidan suna da billen mahauta, zane ɗaya da ya taho tun daga gefen hancinsu har wajen kumatu. Habibu yana da shi. Tun daren da ya fara zuwa zance na lura da zanen.
Habibu Tireda kamar yadda aka fi kiransa mutum ne mai naci akan abinda ya saka a gaba. Tun yana shekara bakwai da ya gane mahaifinsu ba ta kansu ya ke ba ya fara zuwa shagon Nura mai gyaran keke yana koyon yadda ake gyara. A shekara goma ya ɗan tara jari ya fara siyar da kayan tireda a cikin tray yana ajiyewa a gefen Maman Chinedu mai markaɗe. A hankali ya dinga samun riba har ya koma kasa kayansa a ɗan ƙaramin table saboda jarinsa ya fi ƙarfin tray.
Da kuɗin da ya ke samu ya ke biyawa kansa kuɗin makaranta. Lokacin da ya shiga sakandare kaf anguwa babu wanda bai san Habibu tireda ba. Har a gida ana aikanmu wajensa mu sayo gishiri ko Omo.
Lokacin da ya gama sakandare ne ya samu ya ɗan kafa rumfa ya cigaba da siyar da kaya. Bayan shekara uku ya samu kuɗi ya shiga jami'ar Bayero. Zai je makaranta ya dawo ya zauna a shagonsa ya cigaba da siyar da kaya. Daga nan kafin ya ƙare Jami'a ya samu shago a kantin kwari, yanzu haka har Lagos ya ke zuwa saro kaya. Duk da yanzu ba kayan tireda ya ke siyarwa ba amma har yanzu da sunan Habibu Tireda aka fi saninsa.
Yana yawan faɗa mini cewa zai yi kuɗi sosai ta yadda ni da 'ya'yana da mahaifiyarsa ba za mu wahala ba. Idan ya faɗi hakan sai na ji ya ƙara burgeni saboda jajircewansa.
***
A watan July 1991 na haifi ɗana Mujahid. Wata ranan Jummu'ah lokacin Habibu ya tafi saro kaya a Lagos. Ana saura kwana biyu suna ya iso. Ce masa na yi yayana Muhammadu ya masa huɗuba da Muhammad Mujahid saboda sunan dana ke so kenan. Bamu taɓa zancen sunan da za a sakawa abinda zan haifa ba har na haihu. Amma ni na jima da sawa a raina cewa idan namiji ne Muhammad za a saka masa. Ba kuma dan Muhammad ɗin sunan Baban mijina bane, sai dan sunan Babana ne. Muhammad Sabo shine cikakken sunan Baba duk da dai dukka 'yan gidanmu da Sabo muke amfani a makaranta. Idan da mace na haifa Maryama zan saka mata duk da sunan uwar mijina Fatsima ne.
Mujahid kowa ke kiransa saboda dangin mijina gani suke mai sunan sirikina aka sa wa yaron.
Mujahid na kaiwa wata biyu na sake tunawa Habibu zancen makaranta amma ya yi biris da maganar. Kaman ma so yake ya manta da alƙawarin da ya min kafin na amince da aurensa. Har ce masa na yi idan ba shi da kuɗi ne zan siyar da filin gadona na biya kuɗin makaranta amma yace ba haka bane. Wai ba ya so na yi ɗawainiyar reno da makaranta ne. Ban sake tada zancen ba har Mujahid ya kai wata bakwai sai gani da wani cikin. Gaba ɗaya wannan cikin ya dagula mini lissafi. A lissafina idan na yaye Mujahid zan takurawa Habibu koda hakan zai sa na kai ƙaransa wajen yayuna ne akan ya barni na koma makaranta amma sai ga ciki.
Yadda cikin Mujahid yai min shigar sauri haka wannan ma ya zo min babu shiri. A haka na tattara maganar karatu na ajiye saboda duk watanni huɗun farko na cikina na yi su cikin laulayi ne mai tsanani kamar yadda na yi a cikin Mujahid.
Wani lokaci da aka kwantar dani a Asibiti kwanana uku ana ƙara min ruwa saboda bana iya cin komai kuma kullum sai na yi amai Gwaggoji da ta zo dubani sai ta dinga faɗa wai na cika raki. Daga samun ciki sai kwanciyar Asibiti salon kawai na saka ɗanta kashe kuɗi babu gaira babu dalili.
Gwaggoji bata sona. Tun a watan farko na aurenmu da ƙannen Habibu suka zo suka ga ina soya kaji suka kai mata gulma ta ke sakani a gaba da cewa wai dan na taso a gidan arziƙi shine na ke son ɗanta ya kashe duka kuɗinsa a siya min kayan ciye-ciye.
Ban taɓa tanka mata ba. Uwarmiji uwa ce, irin tarbiyyan da aka min kenan. Ba ita kaɗai bama duka kishiyoyinta idan na je gidan ina girmama su.
Saboda yadda ta sa min ido haka kawai sai ta turo min ƙannen Habibun mata ta ce su zo su duba mi nake ci. Haka za su zo tun safe su wuni har dare kafin au tafi.
Mijina yana ƙoƙari sosai wajen kyautata mini, musamman ta ɓangaren abincin da nake ci. Babu abin dana nema na rasa ta wajen wannan. Ko baya gari akwai wanda ke kawo mini naman kaza ko ƙwan zabi duk sati.
Wani lokaci ko na masa magana sai yace gara in saba da cin daɗi dan shi Habibu Wakili sai yayi arziƙin da abincin da iyalinsa za su ci ba za su taɓa nema su rasa ba.
Da aka sallameni a Asibiti dole na yaye Mujahid na kai shi wajen Inna. Na cigaba da renon ciki. Ana saura wata ɗaya na haihu Allah ya yiwa babbar yayarsu mijina rasuwa.
Lokacin dana haihu aka samu mace sai mijina yai mata mai suna Aisha. Da ke da Laraba aka fi kiranta sai ya bar mata suna Aisha ba a saƙaya ba muke kiranta da Aishan kawai.
Lokacin da na haifi Aisha sai na fara tunanin yadda za a yi na samu tazarar haihuwa saboda wannan karan na samu na koma makaranta. Dana sake yiwa Habibu magana sai ya ce wai maganar gida ne a gabansa ba maganan karatuna ba. Haka na sake haƙura har muka tare a gidan da ya siya a chan Gyaɗi-Gyaɗi. Gida ne mai ɗakuna uku dan haka zamu sake sosai da yarana biyu. Ban yaye Aisha ba sai ga cikin Nana Fatima. Haka maganar komawa karatuna ya bi ruwa...