Ba Ni Da Masaniyya

01

by @faddabanan


Assalamu Alaikum my people. Allah ya yi dawowarmu sabon littafi kamar yanda muka alƙawarta a baya.

Zan kuma fara da yin ta'aziyya a gare mu 'yan Fadda-banan group game da rasuwar ɗaya daga cikinmu, Firdausi Mukhtar. Sannan ga Sakina Bunza game da rasuwar mijinta. Allah ya jiƙansu bakiɗaya da ragowan 'yan uwa da iyaye da muka rasa. Allah ya kyautata namu zuwan.

Sai kuma saƙon gaisuwa ga Umm kulthum da Maman Aslam. Na sani ba kwa gajiya da tiri-tirina, lols, Allah ya saka maku da mafificin alkhairi.

Kamar koyaushe, idan an ga na bauɗe, a taimaka a haska min hanya. Mu na zama 'yan uwan amana ne if we look out for each other.


Muna farawa da sunan Allah.


*******************

A daidai kan layin gidan zan je mai adaidaita sahu (keke napep) ya ja ya tsaya, yana ƙara tabbatar min da cewar shi fa ba zai shiga lungu ba. Sai dai na sauka na ƙarasa cikin layin da ƙafafuwana. Na kalli dalleliyar ranar da take haskawa cike da zafi kai ka ɗauka gasa ta fito a wannan ranar, sannan na kalli agogon wayata da ya nuna ƙarfe ɗaya da minti sha biyu, a take na ji raina ya ɓaci. Da a ce ina tare da bututun kunne (earpiece) da tabbas sa wa zan yi a wayata na saurari shirin da nake ta sauri dominsa a radiyo, na kuma zauna cikin keke napep ɗin domin na ga iya ƙarshen rigimarsa! Domin duk wani zafin kai da tururin kai da yake ji da shi, na dame shi na shanye. Na ƙara kallon agogon na ja tsaki mai matuƙar ƙara na ce "Wannan ai rainin hankali ne, don ba haka muka yi da kai ba."

Ko waigowa bai yi ba ya ce "Sai dai fa ki yi haƙuri kawai, lungun nan ba zan iya shiga ba bayan yanzun nan na gama wanke babur ɗina."

Na laluba purse ɗina tare da zaro hamsin na dangwara masa ina faɗin "Yanda ba ka shigar da ni ciki ba, haka kai ma ba za ka samu cikakken kuɗin da muka yi da kai ba." Na fito daga ciki ina tsaki.

Shi kuma ya tayar da babur ɗin yana cewa "Na ji ɗin, don dai naira ashirin? Ki riƙe na bar maki." Ya wuce ya bar ni ina gasuwa a cikin rana.

A hanzarce na shiga lungun domin isa gidan ƙawata Sakina Musa. Tafiyar minti biyu ce ta iso da ni gidan. A tsaitsaye na gaisa da kishiyoyinta tare da faɗawa ɗakinta ina cewa "Yi sauri Sakina ki ba ni Radio don Allah! Saura mintina da ba su fi goma ba a kammala shirin nan. Yi sauri! Yi sauri!"

Ta jawo Radio tana cewa "Kai Zara, wannan neman radiyo kamar saukar aradu?"

Ganin kamar tana ɓata min lokaci sai kawai na ƙarasa kusa da ita na fisga tare da kamo tashar da nake nema, na nutsu na fara saurare. Na farko ba shirin kaɗe-kaɗen ba ne ya dame ni, sarrafa harshen mai gabatar da shirin nake so, turancinsa daɗi yake yi min, ga uwa uba muryarsa. Duka abu ukun nan sun ba da ma'ana. Sau ɗaya yake gabatar da shirin a sati daidai wannan lokacin. Na kan ji dama ina da damar da zan yi magana da shi kai tsaye, ba domin komai sai don gaisuwa, sannan ya san da zamana da kuma ƙaunar shirinsa da nake yi. Iya haka ya wadatar da ni. Ban kuma magana ba har sai da yayi sallama na ƙare shirin. Ina ta jin babu daɗi ban samu shirin tun daga farko ba. Sakina kuma ta fita waje saboda ɗanta Walid da ya fara kuka lokacin da nake jin shirin, don kar ya hana ni sauraro.

Sakina Musa tare muka yi aji ɗaya da ita a firamare har da islamiyya. Da za mu shiga sakandare sai ni aka kai ni FGC Bakori, Katsina, a yayinda ita kuma ta wuce GGSS Kura da ke nan Kano. Tana aji biyar aka cire ta aka yi mata aure, yanzu haka yaranta biyu, Maijidda da ake kira da Jiddo sai wanda take goyo watau Walid. Ni kuma a daidai wannan lokacin ina Kwalejin share fagen shiga jami'a watau CAS, Kano.

Na ɗaga murya na ce "Dallah Malama na gama, sai ki dawo ɗakin ko?"

Ta shigo ɗauke da flask ɗin abinci tana cewa "Al-masifatu, ga ni ai. Abinci nake ɗauko maki."

Na ce "Bari kawai. Wani ɗan rainin wayon ɗan sahu na gamu da shi, wai shi ba ya shiga lungu. Sa'a ya ci ina sauri saboda program ɗin nan shi ya sa na sauka, amma da sai dai yayi ta yawo da ni ko kuma mu ci gaba da zama a napep ɗin, ƙila ma mu ɓige da hira bayan uwaka-ubanka."

Ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Kaɗan da aikinki Hajiyata! Ga ki a haka sak kalar masu haƙuri daga waje, amma daga ciki...hmm! Masifatu kenan. Ki fara cin abincin, Baby (ɗiyar mijinta) ta je nemo maki ruwan sanyi da zoɓo don zafin garin nan sai Alhamdulillah kawai."

Na fara cin abincin a yayinda ta ci gaba da cewa "Ni kam Zara me ye a cikin shirin nan da yake gigitaki har haka ne?"

Na ɗago na kalleta na ce "Chaɓ! Yanzu saboda Allah ba ki ji sanyayyar muryarsa ba? Ita ce ke tafiya da turancin."

Ta yi dariya ta ce "Daɗina da ke zuzuta abu. Ni ba wani sabon abu da na ji, kawai na ji murya irin ta kowa amma dai ba muryar babban mutum ba ce, shi ke nan."

"Ai ke dama ba a abin arziƙi da ke, ga ƙarin ba komai kike ganewa ba. Kin san wani abu? Yawancin masu daɗin murya ba su da kyau, ni kuma ga ni da son abu mai kyau alhali ni kaina laba'asa ce." Ta yi dariya kawai muk ci gaba da hirarmu.

***************


Yamma liƙis na shigo gidanmu. Na fara addu'a Allah ya sa Umma ba ta tsakar gida jin har an fara kiran magriba, yanzun nan za ta fara faɗan daɗewata. Muryarta na jiyo kuwa tana cewa "Watau Zara sai yanzu kike dawowa gidan nan ko? Wai wani irin kunnen ƙashi gare ki ne?"

Na zumɓuro baki na ce "Kai Umma don Allah, ina gidan Sakina fa kuma kafin a yi magriba na baro gidan Wallahi."

Ta girgiza kai abinta ta shige ɓangarensu da Alhajinmu ba tare da ta amsa ni ba.

Na ajiye jakata a tsakar gidan sannan nayi alwala tare da wucewa ɗakina, a falon na wuce Minal da Yaya Muna suna sallah.

Lokacin da muka zazzauna a falonmu muna cin abincin dare ne, Minal ta ce "Yaya Zara ɗazu ba ki ji program ɗinki ba, saura kaɗan na yi maki recording sai kuma na sha'afa."

Na amsa "To yanzu mene na tuna min? Ai kayan haushi ne ma, amma dai na samu ƙarshe tunda da ma an ce da babu gwamma babu daɗi."

Yaya Muna ta ja tsaki ta ce "Mayya da ke kawai, daɗinta bai san da ke ba ma."

**************


Mu biyar Ummanmu ta haifa. Yaya Bello shi ne na farko, ko shekara ba a yi da bikinsa ba. Sai Yaya Maimuna da muke kira da Yaya Muna, a satin nan ta kammala bautar ƙasa, shirin aurenta ake yi. Sai ni Zarah, biye da ni kuma Minal ce, ajinta uku a ƙaramar sakandare. Sai autan Umma Abdulƙadir ana ce masa AK.

Alhajinmu tsohon ɗan boko ne amma fa ba ya wasa ko kaɗan wajen batun tarbiyyarmu. Faɗa gare shi sosai, hakan ya sanya kowa yake ta-ka-tsan-tsan da shi a gidan gabaɗaya. Umma kuwa ma'aikaciyar jinya ce a asibitin Kwararru na Murtala da ke Kano. Tana da sauƙin kai sannan tana da faɗa idan aka yi abin da bai gamsheta ba.

Ni Zara na kasance ba za ka kalle ni kallo ɗaya ka kira ni kyakkyawa ba. Wankan tarwaɗa nake sannan ina da jikin ƙiba. Da ƙirjina da ƙuguna girma ɗaya ake sa min a wurin ɗinki, amma da yake ta tsakiyar bai kaisu girma ba, sai hakan ya ba ni cikakkiyar sura ta sosai. Ni doguwa ce a cikin mata. Sannan abin da ya fi ɗaukar hankalin jama'a zuwa gare ni bai wuce idanuwana ba. Wani shape gare su da girmansu ya bayyana shi sosai. Hancina kam irin namu ne na 'yan Afrika sannan ina da cikakkun laɓɓa.

Tun bayan kammala sakandare da nayi ba abin da na tsana kamar irin wani ya ce yana sona. Kana faɗa tashi ɗaya nake tsanar wanda ya faɗa don ko kallon ɓangaren da yake ba na yi bare magana ta sake haɗa mu. Na fi ƙarfi ga abokai maza.

Duk lokacin da ba mu da lectures a CAS, mukan kasance a rumfar Coke Joint da ke makarantar domin shan lemo da snacks, amma fa ƙarfin zaman namu saboda mu sha hira da abokanmu ne.

Akwai wata sara da abokanmu su Alious suke yi muddin aka zauna a Coca-Cola joint ɗin nan, tun ban fahimta ba har na gane. Ba su da aiki sai kallon 'yan matan da ke shawagi ta ɓangaren. Idan ka ji an ce full-light suna nufin mai wanda suka hango tana nesa, watau wanda ake faɗawa zai iya juyawa sosai ya ganta. Idan kuma dim-light aka ce tana kusa kenan, sai ka juya cikin hikima. Tun kuma da muka gane har da mu ake juyawa domin ganinsu ɗin.

Na kasance masoyiyar karatun litattafan Hausa ce, kusan duk wani littafi da ya fito sai na karanta shi. Akwai wata mata a unguwarmu da take bayar da hayar littafi, har ajiye min sabo take yi saboda ta san ina da saurin karatu, don zan iya kaiwa har ƙarfe ukun dare ina fama. Alhajinmu tuntuni ya so hana ni karance-karance nan amma sai na ɓuya na sha karatuna. Zuwa yanzu kam ya haƙura, ko da nayi kuskure ya ga littafin sai ya ɗauke ido kamar bai gani ba.

Duk da cewa muna wani lokaci da burinmu kawai mu san mene ne a cikin aure, watau wannan rayuwar sirrin ta ma'aurata. Hakan ya sa duk wata ƙawarmu da aka aurar, mu ne kan gaba wurin zuwa washegarin kai ta domin jin me ya wakana darenta na farko a gidanta. Muna sane da cewar hakan ba abu ba ne mai kyau, tunda sau nawa ana faɗa a islamiyya ba a bayyana sirri irin wannan, amma daga mu ƙawayenmu har amaryar sai mun yi hirar.

Abu ɗaya ne yake tsaya min a rai a irin wannan hirarrakin. Tun daga bakin ƙawayenmu da aka aurar zuwa abin da nake karantawa a litattafan Hausa ko na kira su da hadisan 'yan Kano kamar yanda Katsinawa ke kiransu lokacin da nake sakandare a can, bai wuce na cewar daren farkon nan yaƙi ne ba. Wannan kalmar zafin da nake ji daga bakuna mabanbanta yana ɗaga min hankali, ga ni da ɗan banzan son jikina. Wannan ya wanzar min da tsoro a zuciyata game da tarayya ta aure ba da wasa ba.

Direbanmu Malam Habu ne ke kai mu makaranta ya ɗauko mu. Amma idan unguwa za mu je ba dole sai shi ne zai kai mu ba. Umma ta kan ce mu fita mu nemi abin hawa mu hau, domin rayuwa juyi-juyi ce, kar ta zo ta juya, ya zama ba mu saba ba mu sha wahala.