FreeArewaPen original
Ba Ni Da Masaniyya
- 1views
- 70chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 01
Assalamu Alaikum my people. Allah ya yi dawowarmu sabon littafi kamar yanda muka alƙawarta a baya.Zan kuma fara da yin ta'aziyya a gare mu 'yan Fadda-banan group game da rasuwar ɗaya daga cikinmu, Firdausi Mukhtar. Sannan ga Sakina Bunza game da rasuwar mijinta. Allah ya jiƙansu bakiɗaya da ragowan 'yan uwa da iyaye da muka rasa. Allah ya kyautata namu zuwan.Sai kuma saƙon gaisuwa ga Umm kulthum da Maman Aslam. Na sani ba kwa gajiya da tiri-tirina, lols, Allah ya saka maku da mafificin alkhairi.Kamar koyaushe, idan an ga na bauɗe, a taimaka a haska min hanya. Mu na zama 'yan uwan amana ne if we look out for each other.Muna farawa da sunan Allah.*******************A daidai kan layin gidan zan je mai adaidaita sahu (keke napep) ya ja ya tsaya, yana ƙara tabbatar min da cewar shi fa ba zai shiga lungu ba. Sai dai na sauka na ƙarasa cikin layin da ƙafafuwana. Na kalli dalleliyar ranar da tak...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.