AKWAI SO

The Man Power

by @azizat

            *AKWAI SO*

                    Chapter Six                                 

   BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

                   KANO, 2015

                 

               The Man Power

"To, ni ban taɓa ganin yarinya haka ba, zaman Lagos ai ba hauka bane"

Maami ke yiwa Aisha gulmar Hanan.

Tun da ta zo daga kunna kiɗa sai zaman ɗaki sau ɗaya da Maami ta shiga ta mata magana akan ta saki jikinta a gidan cewa ta yi 'to'. Sai dai Adama ta shiga ɗaki ta kai mata abinci ta gyara mata ɗaki. Babu abin da ta ke. Gaisuwa kuwa daga sannu Hajiya shikenan.

"To yanzu dai Maami tun wuri in kin san ba za ki iya juran zama da ita ba gara ki fito ki nuna mata tsarin zaman gidanki. Sannan ma ba makaranta ya kawota ba. Ba za ta je ta fara registration ba"

"Dana tambayeta cewa ta yi ta yi registration ɗin online. Kin san abubuwan ku sai ku 'yan Makaranta"

Aisha ta ce "ai ko ta biya kuɗi online akwai Departmental registration da za ta je ta yi da kanta a cikin makaranta"

"To zan mata magana"

Suka ƙarƙare hiran nasu da maganar EDD ɗin Aisha da ya kusa. Asibiti sun ce nan da kwana tara za ta haihu.

***

Hanan ke zaune a ɗaki gaba ɗaya ta damu da bayanin da Mommyn ta yi mata. Ita ta ina za ta fara da wannan baƙi guntun mutumin, ga uwa tumbi kamar mai cikin wata takwas.

Bata taɓa dating babban mutum ba. Sannan tana son handsome guys saboda sake jiki ta ke da su ta yi abinda dukkansu za su ji daɗi. Shi yasa ta manta da asalin Korede Direban Daddynta ta manne masa.

"Hanan, kina jina?"

"Ina jin ki Mommy" ta faɗa tana tura baki.

"Bamu da lokaci ki yi abinda ya kawo ki mu samu mafita kafin Daddynki ya gano gaskiya"

"To ai Mommy ba ya zama a garin. Ni fa tun dana zo ban taɓa ganinsa ba"

"Use your head Hanan, ki nemi numbarsa and ki yiwa Hajiya Sakina biyayya ba zata zarge ki ba"

"To na ji"

Miƙewa Hanan ta yi ta ɗaure gashin wig ɗinta da wani ribbon sannan ta ɗau wani gyale ta fito falo. Ganin babu kowa sai ta wuce kitchen. Ta wani ɗaki ta ji maganar Hajiya ta je ƙofar wajen ta buɗe.

"Sannu da aiki, Hajiya"

"Barka da safiya, Hanan"

lissafin kaya ta ke ita da Adama a store ɗin.

"Hajiya, ko akwai abin da zan miki?" Daga yadda ta yi maganar ka san ba aikin za ta yi ba

Maami ta kalli faracuntan nan zaƙo-zaƙo, yau kuma yellow ne ba ja ba. Ta yi saurin cewa "Babu, ki je ki huta kawai"

Har za ta fita sai kuma ta ce " Hajiya, Mommy ta ce na yiwa Alhaji godiya tuntuni amma na ga kamar baya zama ko za ki bani numbarsa na kira shi na masa godiya"

"Lah! Ba komai barin gama abinda na ke. Ai kafin ya tafi ya so ku gaisa ma bai dawo da wuri bane a ranan"

Hanan ta ce Thank you sannan ta fita.

Da Maami ta gama abinda ta ke sai ta fito ta shiga ɗakin Hanan da waya a hannunta. Ganin hanan ɗin zaune daga ita sai jan bra da denim bum short sai ta kau da kanta ta fara kira mata numbar.

Da Hanan ta ɗau numbar sai ta ce

"Zan faɗa masa za ki kira shi, amma ki ce masa 'yar Alhaji Sambo ce zai gane"

"Thanks, Hajiya"

Har Maami ta juya sai kuma ta dawo ta ce "Idan za ki je School da safe ki yiwa Driver magana zai riƙa kai ki idan zai kai Nazif makaranta"

Hanan ta fara rarraba idanu. Ta yi saurin waskewa da faɗin "ba a fara lectures bane amma da an fara zan masa magana"

"To, Allah ya taimaka"

Maami na fita Hanan ta sauke ajiyar zuciya. Dole ne ta samu kan Alhaji kafin asirinta ya tonu, wannan matar akwaita da bin diddigi.

Ta yi saurin saving numbar Alhaji Habibu sannan ta danna masa kira. Ba a ɗauka ba hakan ya sa ta ji jikinta ya yi sanyi. Anya plan ɗin Mommy zai yiwu kuwa?. Ta shiga whatsapp sai ta ga ba numbar da ya ke whatsapp Maami ta bata ba.

Ta ajiye masa missed calls biyar bai ɗaga ba.

Haka ta wuni a ɗaki tana ta jiran kiran Alhaji, amma shiru.

Can da yamma sai ta fito ta shiga kitchen wajen Maami.

"Hajiya, ina ga Alhaji baya picking new number, I've being calling him baya ɗauka"

"Aff! Na manta ban faɗa masa bane. Amma da mun gama girki zan faɗa masa"

Ta kalli abinda suke ta ce "da mi zan taya ku aiki"

"No, ki barshi. Aikin gidan ma nawa ne. Na fi son girki da kaina shi yasa kike ganina a kitchen. Ki je kawai"

Tana fita Maami ta ce Allah ya kiyaye ta bari a taɓa mata abinda za ta ci da wannan faracun mayun nan.

Ashe Adama ta ji abinda ta faɗa sai ta fara dariya.

"Ke bana son iskanci" Maami ta dakawa Adaman tsawa.

***

Ƙarfe goman dare sai ga kiran Alhaji Habibu. Hanan na ɗaukan wayar ta ji ya ce "Habibu Wakili speaking"

Maƙe muryarta ta yi ta ce "mai girma Minister"

Daga ɓangarensa ya ce "na tabbata sadda na yi Minister ba ki da wayo"

"Wayyo, Alhaji. Ni fa ba yarinya ba ce" ta faɗa da wani sexy voice.

"Ke ce Hanan ko?" Ya chanja zancen dan baya so ya buɗe wata ƙofar da wani abu zai shiga tsakaninsu. Na farko saboda ita 'yar tsohon maƙocinsa ce. Na biyu kuma ya san Hajiya Sakina da riƙe amana, za ta saka ido akan yarinyar sosai dan haka ba zai samu dama akanta tana kusa da Sakinatu ba.

"Alhaji bana jinka ko za mu koma Whatsapp mu yi magana"

"Ina ga..."

"Ohh! Kar ka ce min NO pleasssssse" Ta saki wani nishi wannan ya tada hankalinsa. Nan ya kashe wayar ya tura mata Whatsapp numbarsa da ya ke bawa 'yanmatansa. Ko ba komai zai iya ganinta ta Whatsapp.

***

ABUJA, 2015.

Alhaji Habibu Wakili yana zaune a ɗakinsa yana danna waya ya ji ƙaran taɓa ƙofa hakan yasa shi saurin kashe wayar dake hannunsa ya ajiyeta gefe ya miƙe da sauri.

Silk pyjamas ja ne a jikin matar. Ta saka baƙin net da ya rufe blonde wig ɗinta. Faracunta sun sha jan nail polish.

"Darling, Barka da dare" ta faɗa lokacin da ta ƙariso ɗakin.

Murmushi Alhaji ya yi ya ce mata barka da dare sannan ya ɗaure towel ya shiga banɗaki.

Tana gani ya shiga banɗaki ta yi saurin hawa gado ta ɗauko wayarsa da ke haske ta saka pin ɗinsa da bai san ta sani ba ta buɗe wayar. Kamar munafuka ta fara dube-duben abubuwan da ke wayar. Wa ya kira yau?. Da wa yai chatting? Sannan mi suka tattauna da Risikat Abimbola. Ganin bata ga komai ba sai ta ɗau ɗayan wayar da ke kashe ta kunna. Wayar dai ya ce mata wayar aiki ce da ke ƙunshe da sirrrikan businesses ɗinsa da duk wasu harkokin siyasarsa shiyasa ya saka mata tsaro sosai koda za ta faɗa hannun abokan adawa. Kusan rabin gaskiyar kenan amma musabbabin tsaro sosai a wayar saboda harkokinsa da mata da baya son Baraka ta sani ne.

A cikin matan Alhaji Habibu guda uku. Baraka ita ce mai shegen bincike da bin diddigin duk wani abunda ya ke yi.

Uwargidansa, Hajiya Sakina babu ruwanta da abinda bai shafeta ba. Ya yarda da ita, dan zai iya barin wayarsa a buɗe ba za ta ɗauka ta masa bincike ba.

Ita kuma Abimbola kaifi ɗaya ce. Ta gaya masa dokokinta bata son hayaniya, idan yana wajenta bata son distraction, ya yi duk abinda zai yi ya gama kafin ya shigo gidanta sannan babban abinda ta faɗa masa shine kar ya yadda ya shigo mata da wani cuta cikin gida dan duk ranan da ya kwaso wani ciwo a neme-nemensa kashe shi za ta yi. Shi ya sa tarkacen condom da wasu magungunan ƙarfi ya ke barinsu a gidanta dan kota shiga ɗakinsa ta gani bata magana.

Hajiya Baraka ganin ta kasa buɗe ɗaya wayar da kuma jin motsin kashe ruwa sai ta ajiye wayar ta kwanta akan gado ta yi likimo.

Alhaji ya fito yana goge jikinsa da towel, ya san halin matartasa amma duk bincikenta ba za ta taɓa gano yadda ake buɗe ɗaya wayarsa ba. Matakan tsaro na buɗe wayar ba kala ɗaya bane kuma suna cacchanjawa duk bayan awa ishirin da huɗu.

Ya gama tsane jikinsa ya saka rigar bacci, ya fesa turare, sannan ya hau saman gado ya kwanta gefen Baraka. Yana cikin tunanin yarinyar nan Hanan Baraka ta mirgino ta kwanta jikinsa. Da muryar bacci ta ce "ka sha man power ɗinka?"

Yai shiru bai kulata ba.

Baraka ce ke da wannan rashin kunyar. Bata shayin yaɓa masa magana musamman dan ta san weak point ɗinsa.

"You better drink ooo, Ina son action yau"

Haushin maganarta ya ji yai wani sauri ya yaye bargo ya kamo bakinta ya shiga kissing ɗinta da ƙarfi. Ya sa hannu ɗaya ya kwance igiyar robe ɗinta ya fara wasa da ƙirjinta da sauri-sauri kamar mayunwacin Zaki.

"Please, kar ka tsinke min nipple, ni bana son gra-gra, take it easy" ta faɗa tana ɗan buɗe ƙafafunta.

Yana shiga jikinta ya fara wani gurnani yana ta ƙoƙarin bugata da iya ƙarfin da nauyin jikinsa ya bashi. Yadda ya ke nishi da gurnani ka ce ya yi awa shida yana aikin ƙarfi ne.

Yai saurin fita daga ciki tun kafin Baraka ta fahimci abin ya kwanta. Amma tuntuni ta fahimci hakan.

Ɗan komawa gefe yai yana kaɗa mazantakarsa ko za ta tashi amma babu alamar za ta motsa nan kusa. Ya fi minti biyar yana kaɗawa babu abinda ya chanja. A shekarun baya kafin jikinsa ya saba da magunguna yana iya taɓuka daidai ƙarfinsa amma yanzu da jikinsa ya saba da shaye-shayen magungunan ƙarfi, sai ya zamana idan babu su ɗin shi ba namijin da zai iya burge mace bane.

"Dama ba abinda ka sha ka wani fara kamar abin kirki"

Ta jawo duvet ta rufe jikinta tana sake ƙaramin tsaki.

Alhaji Habibu ya tsaya cak da abinda ya ke yi. Ga tarin dukiya Allah ya bashi. Amma ga abinda Allah bai bashi dayawa ba a hannunsa. Koda yake Allah ya bashi dai dai halittar da ta dace da shi ne, amma saboda kalma ɗaya tak sai ya kasa sarrafa abinda ya ke da shi ɗin ya kuma convincing kansa da cewa sai da magungunan ƙarfi zai iya gamsar da mace.

A garin Onitcha ne mafarin komai. Lokacin da ya ke bautar ƙasa a shekarar 1987. Shi da wata corper da suke aiki tare. 'Yar Bendel ce, ta cika ta ko'ina irin matan da ya ke so. Farkonsa kenan, kuma a tsorace ya ke dan bai taɓa yi ba.

Sai dai lokacin da ya tuɓe a gabanta sai ta ke ce masa "Ha! This one too small ooo" shikenan duk wani confidence ɗinsa ya tafi.

Jiki a sanyaye ya maida kayansa ya fasa yin komai.

Daga nan tunaninsa ya chanja. Da ya dawo Kano sai ya fara bin masu maganin gargajiya yana neman maganin ƙara girman Azzaƙari. Har wajen masu shayi yana neman ganye ko wani jiƙo da zai ƙara girman mazantakarsa.

A shekarar 1989 da ya je Lagos sai ya biya wata Karuwa dan ya gwada ƙarfin magungunan da yai ta ɗirka tsawon shekaru biyu. A kanta ya fara. Ba zai taɓa manta kamaninta ba. Sunanta Suzzy, ƙwararriyar Karuwa ce dan haka bayan sun gama da ya biyata kuɗi sai ya ce ta faɗa masa gaskiyar ƙoƙarinsa.

Amsarta yai daidai da abinda 'yar Bendel ta faɗa masa, amma sai ta haɗa da cewa idan zai riƙa jimawa akan mace to za ta ji daɗinsa. Daga nan ya yi amanna da maganin ƙarfin maza. Wani lokaci ya kan dace, wani lokaci kuma ya haɗu da 'yan damfara su bashi na bogi idan ya sha sai ya ji shiru.

Lokacin da ya auri Sakina a 1990, ya riga ya gama gane iya ƙarfinsa idan bai sha komai ba, da kuma idan ya sha maganin ƙarfi.

Amma dogaronsa da magungunan da kuma girma ya sa yanzu idan bai sha magani ba baya ma iya taɓuka komai. Ainihin natural ƙarfinsa ya ragu sosai fiye da shekarun samartakarsa.

Yana jin Baraka tana minshari sai ya tashi ya shiga banɗaki yai wanka, da ya fito sai ya jawo drawer da ke gefen gado ya fito da wata ƙaramar kwalba ya buɗe ya kwankwaɗe dukka abinda ke cikinsa. Idanunsa ne suka rikiɗa suka koma jaa.

Babu macen da ta isa ta masa kallon ƙasƙanci. Shi namiji ne. Cikakken namiji.

Idanunsa tar a buɗe har awa ɗaya bayan ya sha maganin, da abin ya fara tasiri a jikinsa sai mazantakar halittarsa ta miƙe, yai saurin mirginawa gefen Baraka da ta jima da bacci. Babu macen da ta isa ta masa kallon ƙasƙanci. Shi namiji ne. Cikakken namiji...