Ba Ni Da Masaniyya

02

by @faddabanan


Duk iya yanda nake tunanin na waye ashe wayerwar tawa ba ta kai ta zuwa party ba. Ɗaya daga cikin ƙawayenmu Khadija Uba ce saurayinta ya haɗa mata party na jin daɗi kawai domin ba na zagayowar ranar haihuwarta ba ne, kuma har Minjibir za a je don can ne wurin fatin. Dukkanmu babu wanda bai samu kati ba, watau ni da aminaina su Ni'ima da Hajjo amma sai na ƙi yarda na bi su. Tsoro nake ji kar mu tafi mu yi hatsari a hanya, don ko zan haɗiyi Alƙur'ani, Alhajinmu ba zai taɓa yarda cewa wannan lokacin ne zuwana na farko ba. Ban da faɗansa da nake mugun tsoro da gudu, ba na jin akwai abin da zai hana shi duka na.

Ranar Asabar muna zaune a common room da ke bayan cafeteria a makaranta, duk wadda za ta je partyn sanye take da abaya baƙa wadda kasan rigar ƙananan kaya ne a ciki da suka yi ɗam a jikinsu. Ƙarfe sha biyu motoci suka zo suka kwashe su. Ni'ima ta bi su, a yayinda ni da Hajjo muka yi zamanmu sai kuma ragowan da ba a gayyata ba.

Matsalata ɗaya ce kawai, ni Allah yayo ni da son sanin abin da bangane ba, i'm naturally curiosity and inquisitive in nature. Har bincike nake don son sanin mene ne abin da ya ja hankalina da ban san shi ba. Wannan halin nawa ya kan sanya ni yin abubuwan da ba a zaci zan iya ba, duk saboda son sanin me ke faruwa.

Duk yanda Hajjo ta yi da ni akan mu tafi gida bayan kammala lakca ɗinmu ta ranar Asabar ɗin nan tun ƙarfe biyu, ƙin yarda na yi na tafi. Malam Habu ma waya na yi masa cewar wani abu ya tsayar da ji a makaranta don haka ba sai ya zo ba, zan dawo da kaina. Abin da ya hana ni tafiya bai wuce jiran na ga dawowarsu Ni'ima ba, kawai so nake ta dawo ta ba ni labarin me ya wakana a Minjibir ɗin!

Zuwa yamma kuwa kusan gabaɗaya makarantar an rairaye, mu 'yan kaɗan da muka saura mun dawo harabar common room ɗin da bishiyoyin filawa suka zagaye mun zauna akan kujerun sumunti da ke kafe a wurin. Mitar Hajjo ce ma ta sa na haƙura da dakonsu don ban san karfe nawa za su dawo ba ganin yanzu har biyar da minti arba'in ta yi. Ina cikin gyara ɗaurin ɗankwalina domin tafiyar sai na ji motoci na fakawa a kusa da common room ɗin. Taka kujerar da nake kai nayi na leƙasu.

A durƙushe suke fitowa suna shigowa common room ɗin a guje gudun kar a gane su. Kusan gabaɗayansu ba sa tare da abayoyin da suka tafi cikinsu, sai 'yan ɓigil-ɓigil ɗin riguna a saman wandunan da suka sanya.

Idona na buɗe sosai ina kallon ikon Allah! Ni'ima ce kusan ta ƙarshe a shigowa kuma ɗauke take da abayoyinsu kamar kayan wanki, don ko gabanta ba ta gani sosai.

Akan idona saurayin Khadija Uba, wanda ya haɗa partyn, na hango shi ya rungume ta tare da sumbatar leɓenta, kafin ita ma ta shigo a durƙushe sanye da riga sak vest. Na zazzaro ido ba tare da na sani ba, infact wannan ce ranar ta farko da na ga hakab a zahirance ba a fim ba. Kam bala'i!

Na juyo wurin Hajjo, ashe ita irin gamon da nayi tayi tunda tana tsaye a bayana ban sani ba ashe a tare muke yin gulmar. Hayaniyarsu ce lokacin da suke mayar da abayarsu jikinsu ta ja hankalinmu. Na ce "Hmmm! Hajjo kina ganin duniya?!"

Ta yi ajiyar zuciya ta amsa "Bari kawai Zara, idona ya ga iskanci muraran dai!"

Na fara dariyar zancenta kafin na ce "Wannan ma fa abin da idonmu ya gane mana a cikin makaranta kenan, ina ga a can Minjibir ɗin? Bari na jawo Ni'ima ta zo mu tafi sai ta siyar mana da jaridar a kan hanya. Kai! Allah da na sani na je na ba wa idona abinci."

Da azama na sauko daga tsayuwar da nayi saman kujera na nausa cikin common room ɗin.

Ita an yi sa'a sanye take da abayarta don haka ban ɓata lokaci ba na jawo ta, muna fita muka yi masu sallama.

Ko da muka isa bakin gate ɗin makaranta, maimakon mu tari abin hawa sai kawai na ja ta muka nemi wurin zama, don ba zan iya barin jin labarin nan sai Monday ba. Kai hatta Hajjo da ta dame ni akan mu tafi ɗazu mancewa tayi da batun tafiya. Haha! Kalata kalar ƙawayena.

Mun sha labari, har faɗa mana aka yi cewar gabaɗaya yinin da suka yi a Minjibir, Khadija Uba goye take a bayan saurayin nata. An sha rawa. Kuma abayoyin tun kafin su sauka a can a ka ciresu gabaɗaya aka haɗe su a motar wani Suleiman. Ni dai sai da aka kira magriba sannan na haƙura ranar na baro CAS zuwa gida. Ni kawai takaicin ban je na kalla first hand nake yi. Kaɗan daga irin bin diddiƙina kenan.

Gudun faɗan daɗewata a makaranta yau ya sanya dama tun kafin na taho ma faɗawa Umma cewar za mu tsaya yin karatu domin sati mai kamawa za mu yi general test ɗin organic chemistry. Hakan ne ya sa na tsallake faɗanta bayan dawowata.

A ranar har rasa shirina na Radio nayi, amma da yake gulma ce ta mantar da ni sai na ji ban damu ba.

*******************


Kwana huɗu da faruwar abin da ya faru muka samu saƙon ana nemanmu a ofishin student affairs. Sai da cikina ya kaɗa saboda razana, kowa ya san Garin Babba ba mutunci ne da shi ba. Haka muka ɗunguma kowa a tsorace domin amsa sammaci, eh, sammaci.

Kiran akan zancen zuwa partyn nan ne. An rasa munafikin da ya faɗa masu ganin lokacin da suka dawo yamma ne sosai, daga ɗalibai har Malamai kusan duk an watse don har an rufe gate guda ɗaya na makarantar. Da ƙyar muka samu muka fitar da kanmu ni da Hajjo akan ba mu je ba, shi ma sai da bincike ya tsananta tare da shaida daga wurin masu partyn kafin aka ƙyale mu. Tsorona ɗaya, ina zan kai kaina da a ce Alhajinmu ya ji zancen nan? Ai da na kaɗe daga ni har ganyena. Girma ba zai taɓa hana shi duka na ba don babu abin da ya dame shi.

Su kuma an ja masu kunne akan faruwar wani abu makamancin wannan a gaba, sannan aka basu suspension na sati biyu. Ya ƙara jaddada masu kar ƙafar ɗaya daga cikinsu ta taka makarantar nan sai bayan lokacin da ya kayyaɗe masu. Ni dai tunda na fita daga cikinsu ban wani ji tausayin masu kuka ba.

Umma Tijjani kuwa cewa tayi "Rabu da banza. Ya ɗauka nan sakandare da zai dinga juya mutane haka? Ku daina kuka ku saurare ni. Kawai ku dinga fitowa daga gida kamar makarantar za ku zo har suspension ɗin ya ƙare. Waye zai wani gane a gida? Idan ba ku da wurin zuwa, mu dinga haɗuwa a Library na Ahmadu Bello Way, ko banza ai za mu ragewa kanmu karatun Jamb. Allah ya sa ma mu samu admission mu tattara mu bar masa makarantar ya cinye! Mts!" Ba wani damuwa a tattare da ita. Kuma maganar da tayi sai ta ƙarfafi ragowan. 

Ni'ima kuma cewa tayi hutu za ta ce anyi saboda masu jarabawar IJMB, sai tayi zamanta har sai suspension ɗin ya ƙare.


Makarantar sai ta daina yi min daɗi kasancewar rabin abokan hayaniyar tawa duka ba sa nan. Wani sa'in idan na zo makarantar sai dai nayi zamana a ƙarƙashin bishiyar gaban Geology department mu yi ta surutunmu da su Alious da Kamz. Bai fi na shiga lecture biyu ko uku ba, shi kenan.

Ranar Litinin bayan Malam Habu ya saukeni ya juya, ganin ana rana sai ma saka glasses ɗina domin ya rage min hasken ranar. Muna zaune kamar koyaushe a ƙarƙashin bishiya a kujeru, ranar kam an yi sa'a na shiga aji na fito. Kawai sai ga security ya iso wajenmu yana kuma buƙatar na ba shi glasses ɗin. Tsananin mamaki ya sanya na saki bakina a buɗe ina kallon shi, sannan nayi azama na ce "Saboda me zan ba ka glasses ɗina?"

Ya amsa "An ba mu umarnin cewa a dinga amsar tabarau daga wurin ɗalibai."

Gabaɗaya wurin ala zuba mana ido. Dubu bakwai na siya, ba fa kyautar aka ba ni ba bare na ce ban san zafin kuɗin ba. Kai watarana ma fa da yunwata nake komawa gida har na tara kuɗina amma don latsi kawai sai a ƙwace min? Na kalle shi a kaikaice na ce "Wallahi ba zan bayar ba. Chaɓ! A sakandare nake ne? Da alama har yanzu ba mu fara A-level ba, da lokacin da za ku ɗauke mu a matsayin ɗalibai da kun faɗa SS 4 za mu shigo ai." Wurin kawai ya ɗauke da sowa, kun san halin ɗalibai dai balle sun ganni babu alamun tsoro a tare da ni, ga shi su ma sun gaji da takurawar da ake yi mana.

Security ɗin ya daɗa miƙo hannunsa yana faɗin "Ki rufawa kanki asiri kawai ki miƙo min kar ki ja wa kanki kora."

Na ciro glasses ɗin tare da ƙara kallon logon jikinsa kafin na ɗaga ido na kalli security ɗin na ce "A kan wannan sai dai a kore ni wallahi! Sai dai idan danne ni za kayi ka ƙwata kuma. Ophs! Ashe a shari'a state muke ko? Ko da ban san ofishin Hisba ba, na san anan ba zan rasa wanda zai kwatanta mani ba...."

Wani daga can gefe da ban san waye ba ya ce "Zan ma kai ki har ofishin commander!"

Na juyo na ƙara kallom security ɗin na ce "Tun kafin a je ko'ina ma na samu ɗan rakiya, to, how e go be?" Na buɗe jakata tare da jefa tabarau ɗin a ciki, na kuma rufe ta ruf. Sai kuma na mayar da hankalina kan Alious da yake min jinjina da hannu na share security.

Ta wutsiyar idona na ga ya juya jikinsa a sanyaye ya bar wurin. Tuni na miƙe tsaye ina faɗin "Bari na kama gabana kafin ya yi min taron dangi a kwashe ni zuwa student affairs. Sai an jimanku." Makarantar na baro gabaɗaya ko ta kan Hajjo ban bi ba.

Gidan da nake aron litattafan karatu na hausa na wuce kaina tsaye na kwaso guda uku sannan na koma gida. Ɓuya nayi na fara aikin karantasu don kar mu yi karo da Alhajinmu. Sallah kaɗai take tashina don ko ta kan abincin ban iya bi ba, biskit da lemo na danna kawai.

Umma na dawowa gidan ta sanya ni aikin abincin dare. Raina matuƙa ya ɓaci, ba abin da na tsana irin a sanya ni girki bare kuma yanzu da hankalina ya ɗaukantu ga littafin da nake karantawa. A gurguje na yi girkin don ko ni nasan ba wani daɗi yayi ba bare a ci da yawa. Ina kallon Yaya Muna ta je ta soya kwai ta ci da bread da shayi ta kwanta.