08
by @faddabanan
Jiki da jini sai Allah, domin kuwa ajiye wayar ke da wuya period ɗina ya yi min sallama. Na san yanda cramps ɗina yake kasance min don haka tuni na ƙara karɓar wayar Ni'ima ina ƙoƙarin tuno lambar Malam Habu don na kira shi ya zo ya mayar da ni gida amma ban yi nasarar samun lambar daidai ba. Sai a lokacin nasan ya kamata a ce na haddace lambarsa saboda rana irin ta yau.
Kafin a kira azahar har na fita hayyacina don har na fara amai. Su Hajjo da suka rikice ƙoƙarin kai ni clinic ɗin school suke yi amma ba zan iya tafiya ba. A gida kawai nake so na ganni ko don na samu na sa maganin da nake amfani da shi na rage ciwo. Suna cikin tababar ko a je a samo ɗan sahu don kai ni gida, matsalar kawai ba su sani ko security za su bari mai adaidaita sahun ya shigo cikin makaranta ba. Shigowar kiran Jamil wayar Ni'ima ne ya yanke duk wata tababar da suke yi.
Kallo ɗaya yayi min bayan isowarsa wajen da muke ya tsaya a kaina yana ta zazzare ido yana sauraron bayanin da Ni'ima take yi masa. Bai jira komai ba kuma ya sanya hannu tare da ɗagoni daga dunƙulewar da nayi yana ƙoƙarin tsayar da ni ko kulawa da ture shi da nake yi bai yi.
Kai tsaye clinic muka dosa, sune suka nuna masa hanya ya kaimu. Na ga likita, Hajjo kuma ta tafi da takardar da likitan ya rubutu min magani zuwa pharmacy ɗin ciki ta karɓo min. Sai da na sha sannan Jamil ya tafi kai ni gida. Amai sau uku na yi akan hanya kafin mu iso gida, bai ƙosa da tsayawa don nayi aman ba sai ma tafiya da ya dinga yi a hankali saboda da zarar na buƙaci ya tsaya, tsayar ba za ta yi masa wahala ba. Kuma ba ƙaramin dauriya nake yi ba saboda ganin idonsa.
Mun iso ƙofar gidanmu daidai dawowar A.K daga makaranta. Shi ya riƙe min jakata sannan na daddafa na shiga gidan. Ina shiga kuma na ƙara shan pain reliever ɗin da na saba amfani da shi na kwanta a ƙasa ina ta juyin azabar ciwo. Kowa a gidan nan ya san ciwon nan nawa. Da ƙyar na samu bacci ya kwashe ni can bayan la'asar sosai bayan na yi matuƙar jigata.
Sai dare na dawo hayyacina, ciwon ciki ya yi sauƙi sosai kawai ƙwarin jiki ne babu. Wanka na fara yi da ruwa mai matuƙar zafi sannan na ji daɗin jikin. Sai na zauna ina shan tea bayan Umma ta shigo ta daɗa duba ni da jiki sannan Minal take faɗa min wai Jamil ya kirata kusan sau uku domin jin ko ciwon yayi sauƙi. Ba ta ƙarasa maganar ba ma sai ga wani kiran na shi ya shigo.
Ina murmushi mai sauti na ɗaga wayar na ce "Heyyyy, i'm not dead yet Jamil."
Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Alhamdulillahi kin samu sauƙi tun da har kina iya yin tsokana. Yanzu haka zaune nake cikin mota, da Minal ta ƙara ce min baccin kike yi har yanzu da tahowa zan yi."
Na yi dariyar jin daɗi na ce "Haba dai."
Ya amsa da sauri "Wallahi! Gani nake yi ba bacci kike yi ba, ɓoye min kawai take yi."
"Idan ana sabo da ciwo, ya ci a ce na saba zuwa yanzu ai." Na mayar masa.
"Wane irin ciwo ne? Na ɗauko ko food poisoning kika samu fa."
"Monthly thing ne." Sai da maganar ta bar bakina sannan na tuna da wa nake magana. Sai kawai na maze tunda maganar ta yi halinta na zarar bunu.
Jamil kam babu yanda bai yi ya kawo min waya ba amma sam na ƙi yarda. Na san halin Alhajinmu kamar tafin hannuna. Ba zai kwanto min wutar da zan kasa kasheta daga Alhajinmu ba. Don muddin hakan ta kasance, sai hakan ya janyo na rasa abubuwa da dama domin cewa zai yi tun da na samu mai yi min maganin matsalata shi ke nan mun hutar da shi. Sun taɓa yin haka da Yaya Muna akan mijinta lokacin suna samartaka ko gaisuwa ba a zo anyi a gidan ba. Da ƙyar aka shawo kanshi ya haƙura. Maganin a yi kar a fara, don na ga zahiri.
Idan yana son yin magana da ni idan ina school, wayar Ni'ima yake nema ko Hajjo. Idan kuma ina gida ta wayar Minal, ga ƙarin cewa ita ba sa zuwa da waya makarantarsu don ana gani za a ƙwace, to wayarta tana gida ko da ba ta nan. Yanzu tana aji shida na sakandare, sune masu kammala wa wannan shekarar.
A wannan rububin ne ma muka soma jarabawar zangon ƙarshe na matakin farko na jami'a. Karatun da nayi lokacin ba na jin na taɓa yin makamancinsa a rayuwata. Yanzu kam na daina cewa jarabawa ta yi sauƙi, sai dai na ce jarabawa kam alhamdulillah, gudun na ci mata alwashi ta ba ni kunya. Kawai dai a ƙasan zuciyata ina da kyakkyawan zato akanta.
A ranar da muka kammala jarabawa da daddare ne Yaya Bello ya diro da wayata cikin kwalinta. Ihu na dinga yi, Minal na taya ni. Umma na zaune kawai tana girgiza kai tana dariya.
Alhajinmu na dawowa ko jira ya ci abinci ban iya ba, na je na kai masa wayar ina dariyar jin daɗi. Har yana tsokanar Yaya Bello da cewa "Yanzu da ni nace a samo min waya ai ba za ka samo irin wannan ba, watau kai ga ka mai 'yar uwa ko?"
Yaya Bello ya dara ya ce "Ba haka ba ne Alhaji, kowa daidai shi ake ba shi ai."
*************
Ni'ima na jin na yi waya sai ga ta a gidanmu washegari, wai har zaman gida ya fara isarta dama mu koma makaranta. Na yi murmushi na ce "Watau ga ki 'yar kwaleji ta fi gida daɗi ko?"
Ta duba wayar tare da zazzaro ido ta ce "Ni ina cewa dama ko bold 2 ce ki samu, shi ne da kika tashi yin wayar sai kika ce 'kauce ban wuri'?"
Na ɗago ido ina kallonta na ce "Haba dai? Yanzu wannan ta fi ta ku?"
Anan ta nuna min yanda zan biya subscription na BB watau BIS bayan min fita waje mun nemo katin waya. Ta mayar min da facebook ɗina kan wayar sannan ta buɗe min account ɗin twitter, ta kuma yi min following ire-iren mutanenta da take following. Tana wannan aikin tana ce min "Duk girman social media platforms babu wanda ya kai twitter daɗi, ba wani zancen personal abu Zara. Matsalarsa ɗaya kar ki bari ki kwafsa, they will drag like say u be tiger generator. Gidan gulma ne kuma ina faɗa maki. Abu ɗaya dai, kar ki sake ki fara magana a dandalin ba tare da kin karancesu ba, shi yasa na yi maki following 'yan fitina don za ki fi saurin gane kan abun nan da nan. Daga idan kin ga wasu ba su yi maki sai ki yi unfollowing ɗinsu."
"Na ce maki ni ina buƙatar tashin hankali ne da za ki kai ni wurin da zan dinga tsoron inuwata?" Ina kallonta.
Ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Ke! It's not that bad. Duk wani authentic news yawanci an fi samun sa a can. Don kana fara rumor ko ka faɗi wani abu ba daidai ba, yanzun za ki ga an fito ana cewa ba haka abin yake ba. Kin san Allah, you will enjoy it."
Tana ƙoƙarin sake buɗe min wani platform ɗin na ce ya isa haka, don bana jin ina da lokacin bibiyarsu yanda take yi. Mutanen da na sani ma zaman hira da su yayi min wahala balle wasu da ban sani ba?
Ni tun da ta buɗe min tayi tafiyarta ma sai na yini ban leƙa ko ɗaya daga cikinsu ba, sai idan hankalina ya zo kan wayar shi ne zan ɗan duba har ma na amsa wa waɗanda suka yi min magana. Ni'ima kamar mayya, don gara Hajjo ma akanta? Ina ga dai sallah kaɗai ke tashinta daga wayar don ina mata magana nake ganin amsarta a take. Ni kam na gwammace karatun littafi, sannan na yi sa'a mun yi sabbin maƙota masu karatu kuma babban abin daɗin su siya suke yi.
Yau kuma Alhamis ta zo min ba yanda nake so don na ƙarar da duka litattafan gidan maƙota mu babu sabo balle na ci gaba da sana'a, matar tace sai ranar Asabar za taje kasuwa ta siya sannan ta canzo wasu daga cikin waɗanda muka karanta ɗin. Na zamo soo bored don ko wuta babu balle yau na ɗana kallo. Don Allah sai na buɗe BBM ɗina domin magana da su Hajjo, duk da ita ba ni tabbas ɗin samunta online kamar Ni'ima.
Sai a wannan ranar naji abin da masu hira a social media suke yi. Na ji daɗin zamana a wurin na ranar, ga ƙarin daɗin ganin Jamil ta nan, duk da yana office amma kasancewar aikinsa babu yawa ranar sai muka samu sararin yin doguwar magana. Wannan ne silar da ya sa na zama so addicted to social media. Idan ba ni da chaji shi ke nan hankalina ya tashi. Gudun ma kar chajin ya dinga ƙarewa, ɗauke ƙaramar Nokia ɗin Yaya Muna na yi lokacin da ta zo gida na sanya layina da sanni da shi a ciki, don kar ma yawan kira ya sa chajin wayar chatting ɗin ya sauka.
****************
Alhamdulillahi! Komai na tafiya bisa tafarkin da nake zato ko da yaushe, dole mu godewa Allah. Ga misali, ni da Jamil mun yardawar juna cewa za mu yi aure nan da shekaru uku zuwa huɗu masu zuwa, ma'ana idan na kammala karatun da nake yi yanzu haka. Tun ina shakkar yanayin soyayyarmu har ya zama na yanda yake nunawa a zahirance game da ni ya galabaitar da tunanina na zubar da shakkun da ya mamaye zuciyata a baya.
Yana jure mita irin tawa da saurin fushina, ina ga hakan ne ya sa muke zaune lafiya. Har idan na yi fushi na sakko na dawo na ba shi haƙuri saboda na san ban kyauta ba. Idona ba ya ganin kowa sai shi kaɗai don wallahi ban taɓa ganin wani namiji na ji ya burge ni sama da shi ba.
Akwai abin da ke faruwa a tsakanina da shi, tun ina mamaki har na daina. Misali, akwai wani lokaci da ya zo wurina da daddare ina mura, to washegari kafin ya taso daga ofis mura ta yi masa kyakkyawan kamu. Ba wannan ne abin mamakin ba, don za ka iya zama kusa da mai mura kai ma ka ɗauka. A'a. Abin mamakin shi ne, sau ba adadi idan mun yi waya ko chat, idan ɗayanmu ya ce mura ta kama shi to idan an yi daɗewar duniya sati amma bai wuce kwana 2 za ka ji ɗayan shi ma ya tashi da murar. Kuma wannan ba sai mun haɗu ba. Ya kan ce "Wa ya ga soulmates."
Ba na wahalar da kaina kasancewar na san shi ne mijina da izinin Rabbi. A ɗage nake kallon maza masu so na, amma fa ba hakan na nufin na zubar da abokaina maza ba ne, ba ni da alamar yi ma saboda shi ma ƙawayensa suna nan da yawa ai.
**************
Mun shiga makaranta za mu fara registration na sabon zangon karatu. Tuntuni wannan saurayina Abdulrashid yake damu na yana son zuwa gida wurina, ni kuma da yake ba na ƙaunar yawan zance sai na ce masa ya same ni a makaranta yau don zan shiga. Mun shiga ɗin ne don mun gaji da zaman gida, idan ba domin haka ba ai an mayar da registration online don ko daga gida za mu iya a cafe ɗin unguwa. Kuma dai kun san zaman gida idan kana zuwa makaranta rashin kuɗi yake kawowa, ko don mu ɗan samu canji shi ne duka muka yanke shawarar zuwa da yin registration ɗin a cafe ɗin cikin makaranta.
Makarantar ba ta fara cika ba tukunna tunda ba a fara bayar da hostel ba, don haka na nesa ba su fara dawowa ba. Lokacin da ya iso sai na yi zamana tare da shi a gaban department 'yan Biochemistry, su kuma sun tafi fitar mana da invoice.
Kamar yanda muka saba tsakanin da shi, hira kawai muke yi normal hira ba wai ta soyayya ba, don ni a haka nake tafi da shi tun asali. Amma sai na ga wani sabon salo a tare da shi yau. Na farko dai fara ce ta sauka saman kaina, kawai ya kai hannu wai yana karkaɓe min ita. Abin ya yi min wani iri amma sai kawai na sa a raina da zuciya ɗaya ya yi don haka ban ce komai ba. Kamar a mafarki sai na ji hannunsa ya riƙo babban ɗan yatsana, a take maganar da nake yi ta katse. Wannan jan wutar lantarkin da na taɓa ji a wurin Jamil babu shi balle makamancinsa. Kai ni duk wani abin da nake karantawa da ake bayyanawa akan yana faruwa tsakanin mace da namiji a irin wannan yanayin ban ji ba. Ni abin da na ji bai wuce na kamar an aza min garwashi bisa yatsan nawa ba, ban kuma ɓata lokaci ba wurin zare yatsan ko na ji sa'ida. Ni kaina mamaki jin zafin nan nake yi, dama hakan na faruwa ko ni kaɗai ce. Wannan abin ne ya janye hankalina daga nuna masa rashin jin daɗin abin da ya min, kawai dai na canza mazauni ban ce ƙala ba.
Har su Hajjo suka dawo abin na ci na a rai. Tare suka dawo tare da wani ɗan ajinsu Ni'ima, abokintane sosai, na san tana yin abotar da shi ne don tana ƙaruwa da shi ta hanyar karatu da assignment, ta dalilin ta mu ma duk mun saba da shi. Sunan shi Abdullahi. A lokacin kuma muka yi sallama da Abdulrashid ya tafi ya bar mu tare da su.
Na juyo na kalli Abdullahi na ce "Abdullahi? Wata alfarma za ka yi min don Allah."
Hakan ya sa gabaɗayansu hankalinsu ya dawo gare ni. Yanayim da fuskata ya nuna na babu alamar wasa ya sa suka daɗa nutsuwa zuwa gare ni. Ban kuma jira ya amsa ba na ci gaba da magana " Don Allah ɗan riƙe hannuna, wani abu nake son tabbatar wa." Na yi magana ina miƙa hannuna ta saiti da yake. Su duka ukun suka saki baki suna kallona.