Ba Ni Da Masaniyya

09

by @faddabanan

Gaisuwa ta Musamman

Nauwara Muhammad Indabawa

Uwar Ammar da Mahmud

Our one and only Adda

Bafullatana mai canza side saboda naman akuya 😆

************


Ni'ima da ƙyar ta iya rufe bakin sannan ta ƙara buɗe shi ta ce "Zara? Are you okay? Like okay okay? Hajjo taya ni duba ta mana." Ta ƙarasa maganar ta girgiza ni tare da leƙen fuskata.

Na ƙwace jikina na ce "Ku fa ba ku iya cin ribar zance ba. Ku ɗan tsaya ku ga abin da zai faru mana kafin ku tara mana mutane da wannan ɗaga muryar da Ni'ima take yi. Hold my hand, Abdullahi. Please."

Kallo ɗaya za ka yi masa kasan shi ma mamakin yake yi, amma da yake shi namiji ne sai ya basar ya riƙe hannun nawa a yanayi irin na masu musabaha. Na ɗan yi jim ina nazarin wane saƙo hannun nawa zai isar min. Lokacin da nake shirin buɗa baki na ce ya isa haka nan sai idona ya faɗa kan Nabila budurwar Abdullahin, tsaye take daf da mu tana huci. Na san me tunaninta yake faɗa mata domin ni ma master ce a wannan fagen kishin da insecurity.

Cikin dakiya na ce "Abdullahi, ya isa haka. Nagode sosai." Yana sakin hannun nawa na juya sosai na fuskanci Nabilar na ce "So sorry, i was experimenting something ne. Da da akwai wani namiji a wurin nan da ba shi ba, da ba zan gwada da shi ba. It's not what you think."

Ta É—an yi jim tana kallonmu kafin ya ja ta suka yi gefe. Ban san me ya faÉ—a mata ba, amma daga murmushinta nasan we are in the clear. Ya rakata ta tafi kafin ya sake dawowa wurinmu.

Tun kafin ya dawo su Hajjo suka dame ni da nacin sai na faɗa masu mene ne ma'anar abin da nayi ɗazu. Tun da na ce su jira ya dawo don yana haƙƙi ya san me yasa na yi abin da na yi ɗin, ban ƙara tanka maganarsu ba.

Bayan dawowarsa ne na fara magana da cewa "Wani abu ya ba ni mamaki. Ɗazun Abdulrashid ne ya riƙe min babban yatsan nan, kawai sai na ji kamar wuta ce ta taɓa ni. Na yi wannan gwajin ne don na tabbatar da wani abu, amma wannan riƙon na Abdullahi ba shi da maraba da yanda nake ji idan ke Hajjo ko Ni'ima kun riƙe ni. (Na harari Ni'ima) Kar ki sake ki tambaye ni me ya kawo hakan tsakanina da Abdulrashid ɗin, don ba fuska na bayar ba. Atoh!"

Ni'ima ta fara dariya don kuwa tuni bakinta ya fara ƙaiƙayi. Hajjo kuma ta ce "Kuma lafiyarsa ƙalau Abdulrashid ɗin?"

"Garas yake. Shi wannan idan ba shi da lafiya akwai wanda ya kai shi langaɓewa ne? Chaɓ!"

Abdullahi ya ce "Ina tunanin gaskiya babu so ko kaÉ—an tsakaninki da shi."

Ni'ima cikin sauri ta ce "Ko kuma aljanu gare ki ba."

Na juyo na ƙara hararar ta tare da jan ɗan ƙaramin tsaki na ce "Wani sa'in kanki yana motsi, aljanun ƙaniya? Ke kika sa min su?"

Su Hajjo suka kwashe da dariya har taba cewa "Yanzu dai kina nufin ba hankali Ni'ima ta cika ba kenan." A haka muka rufe maganar muka koma wata maganar daban har zuwa lokacin da Malam Habu ya zo É—aukata. 


Da daddare sai ga Yaya Bello da Anti Hajiyayye sun biyo ta gida, wai daga gidan za su je siyayya ne. Tun da suka zo kam É—iyarsu Ikram tana hannuna na hana kowa É—aukarta. Yawan dariyarta ya sa ni ma nake ta yi kamar mahaukaciya sabon kamu.

Minal dama tuntuni take son zuwa siyan kayan gyaran gashi, don tun shekaran jiya Alhajinmu ya sallameta. Jin tace za ta bi su, sai ni ma na ƙi zaman gidan na bi su. In dai yawo ne, ai daɗi gare shi.

Ni dama idan dai za a ambaci kwalliya to tabbas ba ni a wurin. Haɗina da kayan kwalliya powder ce, ita ma don ba na son fuskata ta yi maiƙo ne sai kuma man leɓe, shi ɗin ma don gujewa bushewar laɓɓan. Sai dai idan an zo ajin gyaran fata ina 'yar gaba gaba, ba ka raba ni da mayuka, sabulai, oils na gyaran fata amma ba na bilicin ba. Sannan ina da matuƙar juriya wurin bautawa fata. Kullum kuma a cikin gwajin sabbin abubuwan kula da fatar nake ko da kuwa a ce na abinci ne.

Sai ƙarfe goman dare suka dawo da mu gida, suka wuce abinsu ba tare da sun sake shiga gidan ba. A falonsu Umma muka yada zango don nuna mata abin da aka siyo. Umma ta ce "Oh ni Minal, dama gashin nan naki zai tausaya maki ya fito ko don irin bautar da kike yi masa. Kalli na Zara da take ko'in'kula da nata har ma ya fi naki tsayi."

Ta zumɓura baki ta ce "To ai ita dama can haka nata yake. Abin ma bai san ina zai je ba, ayi ta wulaƙanta shi yana nacewa." Ai kuwa mu duka muka kwashe da dariya.

Da sati ya zagayo, ranar Litinin muka sake yi da su Ni'ima za mu haɗu a makaranta domin biyan kuɗin registration a bankin cikin makaranta. Na fi minti talatin ina jiransu amma ko mai kama da su ban gani ba. A fusace na dokawa Hajjo waya domin jin ina suka tsaya suka shanyani haka. Kuma ɗaga wayarta ne ya sa nasan ashe a newsite suka za mu haɗu. Ita ma yanzu take tahowa tana wurin ƙofar famfo, na fito bakin gate sai mu haɗu mu rankaya. Sai ma da ta ɗan jirani tunda da ƙafa nake fitowa daga cikin makarantar.

Muna takawa domin ƙarasawa bankin da Ni'ima ke jiranmu watau Fidelity. Muna dariyar wani abu da muka hanga ni da Hajjo muna kuma ƙoƙarin tsallaka titi zuwa ɗaya hannun. Gabaɗaya hankalina na tattara shi akan hannun da ababen hawa ke tafiya a ɓangaren da nake, kula ganin an samu sarari sai muka tafi da sauri domin tsallakawan... Ni da ban san ya ya aka yi ba, na dai ji an buge ni da ƙarfi sai kuma haske kala kala da idanuwa suka nuna min kafin na dawo nutsuwata na gan ni nayi zaman 'yan bori bisa kwalta. Sai kuma a lokacin ne na gane wani mai mashin ne da ya biyo hannun da ba na shi ba ya kwashe ni na faɗi. Gabaɗaya hankalin ɗaliban da ke wurin ya dawo kanmu. Zuciyata ba abin da take yi sama da tafasa.

Hajjo ta yo baya da sauri don har taje tsakiyar titin, sannan ta fara ƙoƙarin miƙar da ni tsaye amma na ƙi ba ta damar hakan. Tun daga nesa nake jiyo kwakwazon Ni'ima da alama nutsuwarta tayi mata nisa kamar koyaushe.

Wanda ya bugenin ne ya ƙaraso yana cewa "Don Allah ki yi haƙuri. Ku taimaka ku ɗaga ta mu miƙa ta clinic (babu nisa sosai da wurin da nake a lokacin)." Sai da na bari ya matso kusa da wurin da hannuna zai iya kai wa gare shi sannan na shammaci kowa na wurin na wanke shi da mari.

Marin a bazata ya je masa don haka a gigice a miƙe tsaya daga ɗan durƙuson da yayi da fari lokacin da yake min magana, hannunsa dafe da kumcinsa yana min kallon mamaki.

A daidai lokacin na samu na miƙe tsaye ina gyara mazaunin jakata a yayinda da idanuwa suka kafe a fuskarsa na ce "Amma ka cika ɗan rainin hankali wallahi! Na farko, ka bi hannu ba naka ba. Idan mu ba mu lura da kai ba ai kai kana ganinmu don me yasa ba za ka dakata ba? Marin da nayi maka kuwa, na takaicin cewa duk yawan ababen hawan da ke cikin gari ba wanda ya taɓa ni bare har ya buge ni sai a cikin makaranta? Ɗan gaba da rainin wayo kawai. Mtswwww!"

Na juya gaba-gaɗi zan yi tafiyata, sai na ji yayi kukan kura wai zai kawo min bugu. Mazan da ke wurin suka tare shi ana ba shi bakin wai ya yi haƙuri ba a faɗa da mata.

Na ƙanƙance idanuwana na ce "Hmm! Wallahi idan ka yi kuskuren ɗora hannunka a jikina za ka sha mamaki. Wayyo Allah! Da alama tsautsayi ne yake jan ka zuwa gare ni yau ɗin nan. Wallahi ka yi wa Allah godiya da iya mari kaɗai na yi na haƙura. Mts!" Na juya na tafi sakamakon jawo ni da su Hajjo suke yi.

Ni'ima ta ce "Al-masifatu! 'Yar bala'i! Tsautsayi ya jawo shi ya taɓa ki. Dama Hajjo ce da babu wanda zai san me ya faru ma."

Na É—ago kai na kalleta na ce "Na yi masifar tsanar rainin hankali! Kuma ni É—in ma da a ce akan hannunsa ne ya buge ni saboda nawa kuskuren da babu wanda zai ji mu. Babban takaicina bai wuce na yanda mashin bai buge ni a wajen makaranta ba wai sai anan! Kyanta a ce na ba shi marin fin sau É—aya wallahi. Jaki kawai."

Hajjo ta ce "Daɗina da ke Zara mita. Abin nan ya wuce a haƙura hakan nan."

Kafin yamma kuwa jikina har ya fara ciwo da alama buguwar nan ba da wasa na yi ta ba. Umma dai ta ba ni magani na sha bayan na gasa jikina da kyau.

**********


Birthday É—in Minal ya zagayo. Na san ba wata kyauta da za a ba ta a burgeta sama da wani man gashi da take ta nema amma ba ta samu ba. Ni kuma an tabbatar min zan iya samun shi a Wellcare. Don haka shi na sa a raina zan nemo mata.

Lokacin da na tashi zuwa Wellcare É—in sai aka samu akasi Malam Habu yayi niss ba zai yiyu na jira shi ya zo kai ni ba, kuma ba zai yiyu na gota yau ban siya ba.

Da yamma liƙis ma hau keke Napep na tafi can. Hoton man na cikin wayata don haka na buɗe shi ina tafiya a hankali ta ɓangaren mayuka ina dubawa.

Har na gota, sai na ga kaman na hango shi ta gefen idona don haka ban lura da irin saurin da na yo baya don ɗaukar shi ba, har sai da na ji na buge mutum da ƙarfi ta bayana. Kuma garin yayi regaining balance ɗinsa sai ya saki kayan hannunsa suka tarwatse a wajen. A tsorace na juyo domin ba da haƙuri da neman afuwa, na fara magana "Don Allah yi haƙuri...." Irin kallon da yake mani ne ya sanya maganar tawa ta katse. Ƙwara ne. Matashin saurayi ne tsaye gaba na yana yin min kallon sama da ƙasa. A take wani haushi ya kamani. Don shi ƙwara ne sai yake yi min kallon banza? Sai ka ce ba cin arziki suka zo garinmu ba. Mts! Na fasa bayar da haƙurin, don haka sai na harare shi na fisgi man tare da tafiya ɗayan ɓangaren ina laluben abin da nake buƙata kamar babu abinda ya faru balle ya dame ni.

Har na gama siyayya na fito waje ban ƙara ganinsa ba. Wayar Hajjo da ta shigo ne ta dakatar da ni a bakin ƙofa.

Ta ce "Zara ke kam ban ga amfanin wayarki ba. Tun É—azun nake pinging É—in ki amma kin kasa gani balle ki amsa ni."

"Yi haƙuri Madam, ina Wellcare ne yanzu, hankalina ba ya kan wayar. Ta samu ne?"

"Dallah. Sunan handle ɗinki na twitter za ki faɗa min sharp sharp, Abdul (ƙaninta) ya buɗe min ni ma."

Na ƙyalƙyale da dariya na ce "Ji Hajjo, sai ka ce tashin duniya? Saurin me kike yi ne? Ba dai sunana na twitter kike so ba?" Na faɗa mata sannan na fito domin samun abin hawa zuwa gida. Magriba ta wuce na san za mu yi ta Umma. Yau nasan sai an kira ni mai kunnen ƙashi har babu adadi.