Ba Ni Da Masaniyya

10

by @faddabanan

Bayan na sallami ɗan Keke Napep ɗin da ya kai ni gida, da yake ta ɗayan hannun ya sauke ni sai da na dakata wata mota ta wuce kafin na samu damar tsallakawa domin shiga gida. Amma fa sai da na bi motar da kallo saboda kyan matuƙin mota. Ai dama na faɗa maku ina matuƙar son abu mai kyau, shine main weakness ɗina, domin ni da abu mai kyau kamar gashi da cingam ne. Kasancewa ta tare da Jamil ne ya sa sai dai na ga abu yayi kyau na yaba amma ba wai na zubar da mutuncina na bi shi ba. Na shige gida.

Minal ta dinga ihun murna tana rungumeni tare da yin rawar jin daɗi. Hakan ya sanya na fi ta murna ma.

*************

Ranar Litinin ɗin da muka fara lectures ɗin semester, muna zaune a albarka restaurant da ke cikin makaranta, Khamis ya kira wayar Ni'ima. Daga ni har Hajjo daina cin abinci muka yi muka zuba mata ido saboda shagwaɓar da take yi masa. 

Tana kammala wayar Hajjo ta riga ni yin magana, ta ce "Ni'ima kin ga yanda kike yin wayar nan kuwa? Botiiiii! Irin wannan shagwaɓa ai sai ki tada hankalin bawan Allah ai."

Ta harari Hajjo ta ce "Dallah! Sarkin sauri, ai kya jira ki ji nawa uzuri. Ni ma ba ni da zaɓi ne, idan hankalinshi ya tashi kin ga an yi kai ɗaya kenan."

Na zaro idanu domin kamar na fuskanci ina zancen nata ya dosa. Na ce "Kut! Kina nufin ke ma naki hankalin a tashe yake kenan."

Ta yi ƙasa da muryarta ta ɗan rusuna yanda za ta ragewa maganar zangon tafiya ta ce "Uwar kwakwazo, to ovulation nake yi. Kin kuma san ai normal ne idan na ji abin da na ji ɗin."

Hajjo tayi dariya, ni kuma sai na ji bangane maganar ba. Don haka na ce "Don kwai zai sauko kafin ya zamo al'adarki sai a ce yana sanya mutum sha'awa? Ta ya ya to?"

Gabaɗaya da Hajjo da Ni'ima suka zuba min ido cike da mamaki. Hajjo ce ta fara magana "Dakata Zara. Kina nufin ba ki taɓa jin hakan ba? Ko da ba mai ƙarfi ɗin nan ba ce? Ko da a ce ya tsaya iya ki ji kina buƙatar a sumbace ki ko kuma hug?

Sai maganarta ta rikita min tunani na ce "To dole sai mutum ya ji ne?"

Hajjo ta ce "Hakan ne dai ban tabbatar ba amma na san mutane da yawa na experiencing hakan."

Ni'ima ta karɓi maganar ta ce "Bari wasa, don Allah da gaske ba ki taɓa ji ba? Sam?"

Na amsa "Kin san wani abu Ni'ima? Ni ban taɓa jin buƙatar abu makamancin wannan ba a kaf ɗin rayuwata balle...."

Ni'ima ta lailayo zagi ta lafta ta koma ta jingina da kujerarta ta rungume hannayenta tana ci gaba da yi min kallon mamaki, sai ka ce yau ta fara gani na. Suka yi shiru su duka, kafin Ni'ima ta sake ranƙwafowa ta ce "Kwanaki da Abdulrashid ya ɗan riƙe maki hannu, zafi kika ce kin ji ko?"

"Yep"

"Sannan a irin karance-karancen ki kin san ba haka ya kamata ki ji ba ko? Ai na tabbata a labaran ana fasalta abubuwa da suka danganci nan ɓangaren."

Na fara dariyar yanda suka ɗauko fuskar ba-wasa suka ɗora akan fuskokinsu, na amsa "To ai shi yasa na sa Abdullahi ya riƙeni don na tabbatar."

Ni'ima ta amsa "Na ji. Duk ba wannan ba, me kika faɗa min rannan akan Abdulrashid? Ina nufin yanda kike jin sa a ranki yanzu?"

Na kasa gane ina tambayarta take zuwa amma kasancewar my interest is piqued sai na amsa "Cewa na yi, gabaɗaya yanzu ya fitar min a kai. Haushinsa nake ji ba tare da yayi min komai ba. Na tsani na ga kiran wayarsa balle ya ce zai zo."

Da saurin gaskiya ta ce "Kin gani ko?! Gaskiya Zara ba ki da lafiya."

Na dalla mata harara na ce "Ka ji 'yar banza, ba ni da lafiya nake zaune a gabanki har nake amsa maki shirmen tambayarki?"

Ita ma hararar da nayi mata ta rama ta ce "Dallah Malama! Ba irin wannan rashin lafiyar nake nufi ba. Ina nufin, duk wani ɗan adam da kika sani lafiyayye wanda yake ci ko shan abin da ransa ke so kuma hankalinsa a kwance ba ya tare da damuwa dole yana da feelings. Kawai dai akwai bambanci yawa da ƙarancin feelings ɗin amma ba wai a ce babu gabaɗaya ba. Sai dai idan kuma lafiya tayi masa ƙaranci."

Na ja lemona tare da jingina jikin kujera cikin alamar ƙosawa da zancen na ce "Malama, lafiyata ƙalau. Hutar da kanki da magana haka nan."

"Matsalata da ke ba kya ɗaukar abu serious wallahi. Ni fa wannan abin da kika faɗa yanzu da kuma abin da kika faɗa akan Abdulrashid ya sa na fara tunanin anya ba aljanu ne suka aure ki...."

Irin kallon da nake yi mata ne ya sa ta katse maganar babu shiri, na ce "Kin manta, matar sarkin aljanu ce zaune gabanki. 'Yar rainin wayo da ke kawai."

Anan wurin da aka yi zancen, a nan na tashi na bar shi. Tunda har na gama makarantar kwana ban kwaso aljanu ba, to kuwa babu wurin da zan same su. Kawai kowa da irin halittar da Allah yayi masa, amma su sun kasa ganewa.

*************


A ƙarshen sati sai ga wayar Jamil cewar ƙannensa sun dame shi suna son ya kawo su wajena, suna son su ganni, sun shigo Kano kuma ranar Talata za su koma Jos. Tuni muka hau girki ni da Minal na tarbarsu. Ni ranar mancewa na yi da ƙiyayyata da girki, don idan kana son ka ɗaga min hankali to ka ce na tashi na ɗora tukunya.

Ƙarfe ɗaya ya sauke min su ya wuce, ya ce idan sun gama mu kira shi a waya sai ya dawo ya ɗauke su. 'Yan mata ne ma, don haka sun yi matuƙar sakewa da mu barin ma Minal da suke kusan kai ɗaya. Sai magriba ya zo ya tafi da su. Wannan abin ne ya ƙara tabbatar min da cewar ba da wasa ya ɗauki maganarmu ba, tun da alamu sun nuna an san da ni a gidansu, ga shi kuma har ƙannensa ma sun buƙaci ganina sun kuma zo.


A wannan lokacin babu wani dandalin sada zumunta da yake ɗaukar hankalina sama da twitter. Kuma duk wanda na haɗu da shi a social media, idan ya tambayi lambata, ban cika bayarwa ba sai dai na ba da BB pin, tun da kusan kowa yana da shi. Hakan ya sa ko na ga wani yayi adding ɗina ba na wani damuwar sai na san a ina ka samo pin ɗin, harkar jama'a sai a hankali kawai. A kuma cikin irin waɗannan jama'ar ne na haɗu da wani Ahmad.


Ranar muna kan hanyar komawa gida daga gidan Yaya Muna, Malam Habu ne ya ɗauko mu. Haihuwa tayi, an samu namiji. Na ga request ɗinsa ta BBM, kamar zan goge amma ganin sunan Sardauna a jiki sai kawai na yi accepting.

Tashi ɗaya ba mu yi baƙuntar yi wa juna magana ba. Ganin hotonshi sanye da kayan fulani ya daɗa ƙarfafa cewa kamar shi da na gani tabbas bafullace ne. Zamana da Jamil kam ya sa na fara koyon fulatanci, domin idan bai ga dama ba daidai da text message idan zai yi min sai ka ga yayo shi da fullanci. Cikin ɗan kaɗan da na koya daga wurin Jamil ne nayi amfani da shi na tsokani Sardauna tashin farko.

Sannan a cikin mutanen da muke biye da juna a dandalin twitter, akwai wani da ya dame ni da yawaita magana ta DM. Tun hankalina ba ya kai wa kai, har ya zama ina gani ina sharewa saboda yawancin mutanen da suke masa magana a TL mata ne, kuma ina kallon yanda yake basar da su bai cika amsawa ba. Ni abun sai ya dinga ba ni mamaki. Shin haka yake yi wa kowaccensu, sai sun saba sun biyo shi TL ya dinga share su ko ya ya?

Ni kuma sai na ƙi yarda na amsa private messages ɗinsa ta DM, amma idan yayi posting abu da ya ja hankalina ko yayi wata maganar da ina da amsar maganar sai na yi masa magana a bayyane na ga ko ni ma zai share ni, amma idan zan yi magana sau goma, to sau goman zai amsa min. Wani lokacin ma shi ne yake jawo ni kan wani batu. Babu hotonsa a profile ɗinsa sai na wasu yara ƙanana guda biyu masu kyau.

Ni kuma da son bin ƙwaƙƙwafi, ranar da na buƙaci ya nuna min kansa ta hotonsa sai yace na ba shi lambata yayi min magana ta whatsapp ko kuma BB pin. Kun san dai ba zan bayar da lambata ba don haka pin na tura masa. 

Ina duba hoton nashi na san na taɓa ganinsa a wani wuri. Amma to a ina? Ai kuwa na dage akan sai ya faɗa min ko na san shi a fili. Ya ce sunansa Anwar, ni kuma tunda nake a rayuwata ban taɓa sanin me sunan ba, don haka da naga yana ta min yawo da hankali akan ko na san shi ko a'a sai na watsar da batun. Na san ban san wani Anwar ba, don haka kama ce kawai.

Sai kuma kamar wasa muka mayar da dare lokacin hirarmu idan mun gama komai. Zai ba ni labarin dukkan abubuwan da yayi a yini, haka ni ma. Ni kam a kanshi ne na koyi zaman chatting na daɗe. Babu zancen kiran juna don ba mu da lambar juna ma bare a je ga kira. Ni ban cika son haɗuwa da mutanen da muka haɗu a social media ba, shi yasa duk wata ƙofa da za ta kai can rufe ta nake yi ruf!

************


A ire-iren zaman hirar da muke yi da Jamil idan ya zo gidanmu ne yau aka dinga kiran wayarsa tana katsewa ba tare da ya ɗaga ba. Tun ina jin daɗin yanda yake shariyar kiran har na fara tsarguwa. Don haka na ce "Wai waye ne yake wannan kiran da ba ka son ɗauka?"

Bai kai ga amsawa ba sai ga wani sabon kiran ya shigo. Ya fisgi wayar sannan cikin ƙosawa ya danna amsa kira ya ce "Hello?! Wai ke idan kika fara kiran mutum ba kya dainawa ne? Ba ni da lokacin magana yanzu haka don Allah!" Ya katse wayar yana yin ƙaramin tsaki kafin ya juyo gare ni ya ce " Ƙanwata ce. 'Yar gidan Baffa ƙanin Mamata. Ita idan ta fara kiran waya ba ruwanta da uzurinka, kawai sai tayi ta kira har sai ka ɗauka. Mts!" Muka ci gaba da hirarrakinmu bayan nan ba tare da zuciyata ta zargi wani abu ba.

Ashe wasa farin girki. Tun lokacin sai na lura saƙonninta sun fi na kowa yawa a wayarshi. Da wuya kuma mu haɗu da shi har mu rabu in dai za mu kai awa biyu ba tare da kiranta ya shigo wayarsa ba.

Akwai ranar da muka yi sallama da shi akan zai je Jos ganin gida, kafin ya isa ma mun yi magana da shi yana kan hanya. Amma tun da ya isa gida sai ya daɗe kafin ya neme ni, ba yanda muke yi lokacin da yana gari ba. Har ga Allah a lokacin wani uzuri na yi masa da har ya kasance ban shiga damuwa saboda abin da nake ganin yana fitowa daga ɓangarensa.

Duk da dama ni ban cika hira da shi ta BBM ba amma muna magana ko da sau ɗaya ne, irin taƙaice ɗin nan a kowanne yini. Rashin maganarsa ta nan ma ban sa shi a raina ya zamo min damuwa ba, ina can muna shan hirarmu da Anwar har na sha'afa ban lura da cewa tunda ya tafi ban ga motsin ya canza hoto a profile ɗinsa, tun da shi ma'abocin hakan ne. Sai da na zauna ina tunanin wai yaushe zai dawo ne shi ne na je duba shi ta BBM ɗin, ko don na yi masa addu'ar Allah ya dawo da shi lafiya. Abin kamar rufa ido don kaf BB contacts ɗina na neme shi sama da ƙasa na rasa.

Ban ce uffan ba sai da na bari ya dawo Kano sannan na tambaye shi ko shi ne ya cire ni daga wayarshi. Yana mamaki ya duba don ganin ko da gasken ba na ciki, ya kuma sanar da ni ba shi da masaniyar yanda aka yi na fita daga ciki. Ya ba ni haƙuri sannan a kan idona ya ƙara adding ɗina. Tun kuma daga wannan lokacin ne abubuwa da yawa suka dinga faruwa wanda nake tunanin ko rashin kula ne tun farko ya hana ni lura da hakan tuntuni.