14
by @faddabanan
Abin da ya faru ba abin da zan iya ba da labari ba ne ga kowane mahaluki don haka na ja bakina na tsuke. Kai babu wanda ma zai yarda da cewar na kwana tare da namiji kuma ina nan a budurwata da nake kafin na je gare shi. Dole ma a ƙaryata ni. Ga ƙarin ikirarin tarbiyyar da nake taƙama da ita an ba mu a gida, to ai abin da nayi sai wanda ba shi da tarbiyyar ne zai yi shu kamar yanda na saba faɗa akan su Khadija Uba. Yanzu ga shi teburin ya juya, ita tana can zaune da mijinta cikin kwanciyar hankali kuma yanzu haka babu mamaki a iya tarihin rayuwarta ba ta taɓa kwana a gidan saurayi ba. Sai ga shi ni Zara mai tarbiyya, me kawaici da kunya na yi! Hmm! Allah ya shirye mu ba ki ɗaya kawai domin abin da Fati ta faɗa kafin a je ko'ina a kaina yake aiki.
Kusan kowanne dare idan na kwanta ni kaɗai a ɗakina sai na yi ta tuna abin da ya faru tsakanina da Ahmad. Abin mamakin ma shi ne ni da shi babu zancen soyayya a tsakaninmu. Sai kuma ɓangaren curiosity ɗina da bature ma da kansa ke faɗin "curiosity kills a cat" ya sa na lura da cewa dukkanin abin da ya faru babu abin da ban san faruwar shi ba don a cikin hankalina nake bai gushe ba kamar yanda nake karantawa a wasu labarai, ni fa zuwa yanzu na fara yarda da abin da Ni'ima take yawaita faɗa na cewar ba ni da lafiya ne shi ya sa.
Ko bayan dawowata ba mu daina chat ko waya da shi ba, amma ko da kuskure daga ni har shi babu wanda ya tayar da maganar abin da ya faru a Kaduna, ciki kuwa har da zuwan nawa. Hakan ya sa na daɗa sakewa da shi tun da dai hirar duniya ce ba irin hirarrakin da ba na so ba ne.
*************
Ranar Litinin ina ta sauri zan tafi lectures, lokacin an yi satittika rabona da Kaduna. Na ƙara kallon agogon da ya nnuna ƙarfe sha ɗayan rana da rabi, ga shi ƙarfe biyu za mu shiga. Na samu ɓacin lokacin nan ne a dalilin gyaran mota da Malam Habu ya tafi kaiwa, shi ma bai san zai daɗe haka ba. Sanin halin malamin da na yi na korar wanda ya makara ya hana shi shigar masa aji muddin ya riga ka shiga da minti goma? ya sa ban saurari faɗin Malam Habu na cewar ga shi nan ya kamo hanyar gida zai zo ya kai ni ba, sai kawai na kama haramar tafiya makarantar da kaina. Turare na fesa a gurguje na fice daga gidan kamar zan tashi sama saboda sauri.
Na ɗan tsaya jiran ɗan sahu, kamar sun san sauri nake yi ko ɗaya ban gani ba sai 'yan tasi da suke ta wucewa don haka ba ni da wani zaɓi da ya wuce na shiga kawai. Tsayawa ɗaukar fasinja da suke yi ne nake gudun su ɓata min lokacin saboda haka, na zo na yi gudun gara na faɗawa zago.
Wata mata ke zaune kusa da ni ɗauke da wata yarinya da ba ta wuce shekara huɗu ba. Ina kallonsu takaici na ƙara kamani saboda ganin yanda ta ƙyale yarinyar sai tattaka kujera take yi da takalminta, har ma tana ƙoƙarin haurawa kujerun gaba ta tsakanin kujerunsu. Haushi duk ya ishe ni, na rasa wannan wane irin halin banza ne wannan. Kina uwa kina kallon yaronki na yin ba daidai ba amma ki ja baki ki yi shiru, idan wani a gefe ya yi magana ki ce za ki haushi.
Direba ya ce "Don Allah Yayata ki riƙe yarinyar nan taki, mutane ne za su zauna a wurin da take takawa a kujerar fa. Yanzu idan wani abin Allah ya kiyaye ya faru, na ja burki ba shiri ai kin ga wani abun zai iya samunta nan ma."
Buɗar bakin matar nan sai ta ce "Malam ina ce kuɗi na biya? Don haka sai a bar ta ta wataya, idan ka samu fasinja ai zan ɗauketa ne." Wannan abin da ta faɗa ya yi masifar ƙona min rai don haka na juyar da kaina gabaɗaya na fuskanci tagar mota ina ta tausar kaina kar na yi magana tun da ba da ni ake yi ba.
Direban ya sake amsawa da alama ya fara ƙuluwa yanzu, ya ce "To Hajiya don kin biya kuɗin mota, ai na ga bana kujerun gabaɗaya kika biya ba, na kujera ɗaya ne. Hakazalika, mota ba ta babanta ba ce bate tayi yanda take so a ciki." Abu dai ya zamar masu cacar baki, ni dai fatana kawai na samu na sauka daga motar.
A garin haka kuwa yarinyar da ƙafar bututu ta taka kayan fasinja na gaba, ga shi fararen kaya ne. Ban saurari masifar da direban ya fara ba saboda taka kayan na juyo gare ta tare da rage girman idanuna na ce "Baiwar Allah, kin san girman Allah? Idan ɗiyarki ta sake ko da tsautsayi ta taka ni da takalminta wallahi sai na kwashe ta da mari. Maganin a yi kar a fara, to kar ki bari ta yo ta ɓangarena don wallahi jikinta ne zai faɗa mata! What nonsense! Mts!"
Mata ta cigaba da masifarta bayan ta janyo 'yarta ta riƙe. Ni kuwa na taɓe baki tare da faɗin "Oho! Wannan duka matsalarki ce." Shi ne muka samu lafiya. Kuma cikin ikon Allah kusan lokaci ɗaya muka shiga da malamin, don yana gaba na ina biye da shi.
Da na tashi ma a tasin na dawo gida, yanzu kam tunda gida zan dawo ai ba sauri nake yi ba shi yasa ban wani damu da sai Keke zan hau ba. Ba mu wuce minti talatin ba ma aka sauke ni kuma na gangaro gida da ƙafa.
Tunda na doso ƙofar falonmu na ke jiyo murya kamar ta Gwaggo, ina kasa kunne na tabbatar ita ce ai da gudu na ƙaraso ciki na rungumeta ina ta murnar ganin ta. Na ce "Nayi kewarki sosai Gwaggona!"
Cikin dariya ta ce "Habawa! Sai yanzu na san gidan nan ya chika."
AK da ya ke zaune kusa da ita ya ce "Dama na sani! Don Anty Zara ba ta nan ne ya sa har kika iya tuno sunana kika kira da kika zo. Allah Gwaggo kina yi mana wariyar launin fata a gidan nan." Kowa ya fara dariya.
Minal ta ce "Kai ne sarkin shisshigi da neman suna ai. Amma ai ka daɗe da sanin babu wurinka a tsakanin Anty Zara da Gwaggo ai. Ba ka ga na rufawa kaina asiri na zauna a gefe ba?" Umma dai dariyarta kawai tayi ba ta sa mana baki a cikin maganar ba.
Gwaggo matar babban Yayansu Alhajinmu ce. Ya auro ta tun lokacin su Alhajinmu na matasa 'yan sakandare. Mutuniyar Yola ce ta Adamawa. Duk daɗewarta a Kano bai sa hausarta ta daidaitu ba, ka na fara magana da ita za ka gani bafullata ce kuma kuma har a kammani ma duk da cewar ita ba fara ba ce, kawai dai tana da haske sosai. Ba ta ƙiba sam-sam sannan duk girman nan na ta tana tare da gashinta da ya sauka har tsakiyar gadon bayanta. Ba ya kitsuwa sam, duk nacina da son yi mata kitso sai da na haƙura saboda ko an samu an yi to ba ya wuce awa biyar zai fara warwarewa da kan shi.
Duk waɗannan shekarun da ta ɗauka tare da Baba (kamar yanda kowa yake kiran mijinta a danginmu), ba ta taɓa haihuwa ba. Yaransa ya samo su ne daga mata biyun da ya auro bayanta. Tana da son riƙe masa yara kamar ita ta haife su amma matan kam sun haɗe mata kai don ba su so ko kaɗan tana raɓar masu yara saboda wani mashahurin kishinta da suke yi.
Duk da cewar ba ta samu na ta yaran ba, wannan lamarin sam bai taɓa fadarta na Uwargidan Baba sam! Idan har za ta ce ba za a yi wani abu a gidansu ba, to ko shi Baban ne yake son yi haƙura yake yi da shi balle waɗanda suke zaune a ƙarƙashinsa kuma. Komai na tafiyar da gida a hannunta yake, daidai da kuɗin makarantar kowane yaro na gidan, ita ce wakiliyar kowane yaro a makarantarsu. Ko laifi suka yi ita za a nema. Watau Allah ya jarabce ta da rashin 'ya'ya amma a wurin miji ko a cikin mata sama da miliyan da wuya ka samu mai fadarta a wurin mijinta haka. Kuma duk wannan damar da Allah ya ba ta sai ta zamo mai matuƙar adalci ga ahalin gidan, ciki har da kishiyoyinta kuma tana da matuƙar kawaici. Amma biyayyarta ga mijinta duk wanda ya gani dole ya jinjina mata, za ka fahimci ko me Baba yayi mata bai faɗi ba. Tana da tsafta har ma za ka iya cewa ta yi yawa. Kwalliya kam sai dai ka nuna mata fentin fuska amma ba ta sutura da kayan ƙyalƙyali ba.
Yanda kishiyoyinta ke janye yaransu daga gareta da zarar sun fara girma sai ita ma ta bar masu kayansu, amma fa ba yanda za a yi ta ga yaro yana yin ba daidai ba ta ɗauke kai. Idan abun ya kai tayi duka yi take yi sai dai idan uwar yaro za ta fashe da fushi ta fashe. Ba ta da wasa ta tarbiyya ko kaɗan!
Su Alhajinmu suna kula da ita sosai, har da yaransu da suka fara aiki saboda kyawawan halayenta. Wannan sallar da ta wuce akan idona sai da aka kawo mata super wax ɗai-ɗai har guda sha ɗaya daga wurare daban-daban. Shi ya sa kusan mafi yawancin lokuta shigarta ta manyan kayayyaki ne, tun da ba a gajiya da yi mata kyautarsu haka mijinta ba ya gajiya da siya mata ta ɓangarenshi ma.
Kaf faɗin danginmu ta fi so na, jininmu ya zo ɗaya. Komai ta samu da 'yan mata ne ya kamata su yi amfani da shi to kuwa ni take ajiyewa. A gaban kowa nunawa take yi Zara ce ɗiyarta, ni ma hakan take a wurina don a zallar uwa nake kallonta a idona. Masu yi mata mita ma sun gaji sun daina sun zuba mana ido.
Tun da na dawo ban bar gefen Gwaggo ba, har sai da Alhajinmu ya dawo suka gaisa kafin ya bayar da motarsa muka tafi rakata gida har da Umma. Har ga Allah matan Baba ba sa gabana. Soyayyar da nake yi wa Gwaggo, idan kai maƙiyinta ne to ba na shiga sabgarka amma in dai kana son ta ni ma son ka nake yi. Akan idona sun sha yanka mata magana na miƙe zan yi masifa ta kama yi min faɗa, ba ta bari a raina su. Idan kuma kana son ku ɓata da ita to ka kawo mata gulmarsu, ta ce rashin sanin me suke ciki shi ne kwanciyar hankalinta.
Yawancin yaran gidan sun girma don da dama daga cikinsu sun yi aure, don haka yanzu abubuwa da yawa sun yi sauki a gidan har da matsanancin kishin nan duk da ba a rasa nono a ruga ai.
************
Tun da sabon sati ya kama na jiyo Malam Habu yana cewa ya kusa yin tafiya ta kusan sati biyu na fara tunanin ya kamata na fara koyon tuƙi. Shi kuma Malam Habu ya dage ba zai koya min ba har na je na tambayo Alhajinmu. Nasan ko hauka ne a kaina ba zan tunkari Alhajinmu da zance irin wannan ba don na dinga lallaɓa Malam Habu har na samu da ƙyar ya yarda akan zai dinga koya min ranar Juma'a da yamma kaɗai. Idan kuma Alhajinmu ya samu labari sai na san ta ya ya zan fitar da shi. Da sauri na amince.
Hakan ce ta kasance, duk juma'a farm centre (ba yanzu da jama'a suka cikata ba) muke tafiya ina koya. Mu kan ɓata awa biyu zuwa uku shi yasa nan da nan na gwanance. Minal ce kaɗai ta sani don ko Yaya Muna ban faɗawa ba, domin daɗin zance zai iya kwasarta ta faɗawa Yaya Bello.
*************
A ɗan tsakanin nan Sardauna ya damu da mu sake haɗuwa. Na san me sake haɗuwar tamu take nufi, don haka na yi ta jan maganar domin na kasa fitowa sak na ce masa a'a. Ban san me yasa nake ganin girmansa a idona ba. Kuma zuwa yanzu ya san ina matuƙar tsoron lamarin nan saboda azabar da na ji ana faɗin cewa yana da shi, kamar yanda na samu tabbaci daga bakin ƙawayena da suka yi aure na abin da nake karantawa, duka waɗannan batutuwan ne suke kafe da ni a ɓangare ɗaya ba ni da niyyar tsallakawa wurin da yake buƙatar na tsallaka ɗin. Ya dinga nuna min cewar zance ne kawai, kwata-kwata ba yanda ake faɗarsa yake ba amma sam na ƙi yarda na gane! To shi da ba mace ba ta ina ya san zuzuta maganar ake yi ba haka gaskiyar lamarin yake ba? Wannan ya fi min kama da daɗin baki.