Ba Ni Da Masaniyya

17

by @faddabanan

Da yamma muka baro Alu Avenue ɗin, kuma har mai adaidaita sahu ya sauke ni gida mamakin ƙarfin halin Abdulrashid nake yi sannan a hannu ɗaya kuma mamakin yanda nake jin ɓacin rai da tafasar zuciya game da shi abin da ko a mafarki ban taɓa jin makamancin hakan ba idan Sardauna ne. Ba ni da abokin shawara akan wannan lamari bare na faɗa masa ya taya ni neman amsar ruɗanin da na shiga.

Wurin ƙarfe sha ɗayan dare ina kwance, kuma har lokacin ƙoƙarin fahimtar me ya sa ba na jin waɗancan abubuwan da nake ji game da wasu akan Ahmad. Sai kawai na yanke shawarar yin maganar nan da Sardauna, duk da cewa a kwanakin nan maganarmu ta ja baya, wanda hakan daga gare ni saboda na tsani ganin yawan maganar shi da mata a TL ɗina na twitter, don haka na bar masu shi su ƙarata. Na sani sarai na fi ƙarfin wulaƙanci daga gare shi amma idan ana hidima irin wannan gara na koma bayan fage na kawo ido na sa kawai, ba na son abin ya zama kamar gasa.

Bayan mun gaisa sai na tura mashi saƙon da yake cewa "Kasan me? Akwai wani abu da yake ba ni mamaki. Watau na rasa dalilin da yasa jikina da zuciyata ba sa yarda sam da wani bayan kai."

Ya amsa "Yarda? Kina nufin you fall for me kamar yanda kike gudu?"

Abin da ya sa ya tambaye ni hakan kuwa, wani lokaci ne can baya da na dinga yi masa turjiyar haɗuwa, da ya nemi jin ba'asi sai na ce ɗaya daga cikin dalilan da yasa ba zan iya yarda da shi yanda yake so ba, bayan tsoron wahalar transitioning daga 'yan mata zuwa woman akwai maganar cewa duk wanda mace ta fara sani ba ta iya rabuwa da soyayyar shi, hakan zai jawo shaƙuwa mai ƙarfi a tsakani sannan tana zama clingy. Ni kuma tsakanina da shi babu soyayya, kuma ba na ƙaunar abin da zai kawo min ƙauna da soyayyar shi a raina.

Na amsa saƙon da "A'a! Ba haka nake nufi ba. Ina nufin ina fuskantar tafasar zuciya na ɓacin rai idan na kasance tare da wani."

"Kamar ya ya? Zara ki buɗe baki ki yi min magana sosai yanda zan fahimta. Daɗina da ke sai ki yi ta zagaye-zagaye akan magana. Ni ne Ahmad fa. Oya speak...ina sauraron ki."

Na tattare nauyi da kunyata na ajiye gefe na ce "Ina nufin idan wani yayi ƙoƙarin riƙe min hannu sai na ji raina duk ya ɓaci, na ji i'm just boiling from inside!"

Ya ɗan jima kafin ya amsa da "Waye ya riƙe maki hannu?"

Sai kawai na ba shi labarin abin da ya faru da kuma yi masa dalla-dalla na irin yanda na ji game da abin ɗazun.

Ya amsa "You know what Zara? Ni kaina a game da ke kin fita daban, wallahi zan iya zama da mace ba tare da na ɗaga hankalina ba ko da kuwa za ta nemi taɓa ni. But, you? Wallahi ba zan iya ba. Bari na yanke maki maganar, kin ga ko tuna abin da ya faru tsakaninmu na yi sai na ji shi a jikina. Bari na faɗa maki gaskiya, burina bai wuce naje third base tare da ke ba, amma na sani ba kya so, second base ɗin ma don na matsa ne shi yasa har kika yarda muka je. Shi yasa har kika ga ina cijewa da dauriya."

Tsigar jikina ta tashi, sai na sake maimaita abin da ya rubuto sannan na mayar masa da amsa "Ni na kasa fane wane irin abu ne wannan."

Ya amsa "Abin da ba ki gane ba shi ne, ba kya iya connecting da kowa sai ni."

Yana faɗar hakan na lura kusan gaskiya ya faɗa, domin shi kaɗai ne da har yanzu ban taɓa damuwa da abin da ya wanzu tsakanina da shi ba balle a je ga batun tsanarsa a zuciya. Da mamaki! Ga shi ban taɓa ji ko karanta matsala da tayi irin shige da tawa ba! What the hell?!

Sai kuma a lokacin na yardar wa zuciyata na yi kewarsa kuma na faɗa masa. Shi kansa yayi mamaki domin bai taɓa zaton jin haka daga gare ni ba. Har gori yayi min yau na cewar tun da ya bar ƙasar ko nemansa ta Chat ban yi ba balle na ce bari na kira shi na ji ya ya yake.

Dariya kawai na yi ban amsa ba domin ni a rayuwata duk abin da mutane suke rububinsa, ni kuma lokacin nake kaucewa abun. Ko ma mene. Idan mutum ne sai na dinga cewa rububin zai sa wa mutum girman kai. Ni kuma ga ni da bala'in son kaina kamar me? Domin ba na ba da damar da wani zai ci min fuska komai ƙanƙantar hanyar kuwa!

Ɗan hutun da na samu sai Yaya Muna ta dage sai naje nayi shi a gidanta. Da safe daga ita har mijinta aiki suke tafiya. Ni ce ke kai Mubarak makaranta, da yake ya fara zuwa yanzu. Sai mai aikinta ta ɗauko shi idan sun tashi. Anam kam ba ta da rigima don haka koyaushe tana wurina.

Ko da muka koma makaranta sai da Alhajinmu yayi wa Yaya Muna da gaske sannan ta haƙura na koma gida. Sai faɗa take yi a gidanta ya fi kusa da BUK kawai na yi zamana, Alhajinmu kuwa for ya ƙi yarda.

Cikin watannin da suka biyo na samu damar kammala makaranta tare da hutun da ake samu kafin fitowar jarabawar ƙarshe. Hakan yayi daidai da ragowar watanni ƙalilan ga Sardauna na kammaluwar karatun shi a Egypt da ya tafi. Yanzu kam sai mu kai sati ma ko 'hi' ba mu ce ba a tsakaninmu. Kai akwai lokacin da sai da muka fi wata guda ko gaisuwa ba ta shiga tsakanina da shi ba. Kuma hakan bai dame ni ba saboda alaƙata da shi wata iri ce.

Maa shaa Allah! Sakamako yayi kyau sosai! Cewar Alhajinmu bayan ya ga sakamakon kammala makaranta da na kawo masa bayan na karɓo. Har Yaya Bello yana cewa dama a nemar mani koyarwa a babbar makaranta watau lakcara. Amma ni akwai ni da gudun wahala don haka na ce a'a gaskiya, gara a nemar min aiki a ma'aikata ko banza na san zaman office zan yi. Alhajinmu ya ce kafin na gama bautar ƙasa zai san ya ya zai yi.

Anan Camp na Kano aka tura mu orientation na NYSC watau ƙaraye. Ni'ima kuma Katsina amma dawowa Kano za ta yi idan an kammala sati ukun nan. Abokin Yaya Bello ne yake aiki da NYSC, shi ne muka samu aka bar mu a gida. Muna fitowa kuma na fara bautar ƙasa a asibitin Malam Aminu Kano a ɓangaren magani watau DMU.

Satin da na fara aikin ne Allah ya yi wa Ahmad Sardauna dawowa gida Nijeriya. Kuma tun da ya rage saura sati biyu ya dawo hirata da shi ta dawo sosai, shi yasa na san zancen dawowar tasa, har ma kwanaki biyu da yayi a Abuja bayan saukarsa kafin ya wuce Kaduna. Ya dame ni na zo na yi masa sannu da zuwa amma na dage akan ba ni da lokaci saboda aiki sannan kuma da ya ce zai zo Kano, nan ma na ce a'a.

Ganin da gaske ba zan zo ba sai ya yi tafiyarsa Yola. Ranar da zai tafi da daddare muna magana ta whatsapp, jin nayi shiru sai ya kira ni ta waya. Yana jin call waiting sai ya katse kiran.

Ina kan wayar da nake yi na tura masa saƙo ta whatsapp cewa "Kira kake yi?"

Ya ce "A'a. Flashing nake yi maki."

Na fara dariya a sarari har wanda muke magana da shi a lokacin yake tambayata me ya ba ni dariya. Sai da na gama wayar tawa sannan na kira shi, sai na ji shi ma wayar yake yi don haka sai na koma ta whatsapp ɗin na ce "Kai ma ga shi nan kana wayar, an yi 1-1 kenan. Allah ya kiyaye hanya zuwa Yola. Ameen." Sai da safe na iske saƙon shi na cewa ya gode da addu'a. Za mu yi magana daga baya.

Tun daga ranar ba mu ƙara magana ba, amma ina sane da lokacin da ya bar Yola ya tafi Taraba ya kuma wuce Gembu. Duka ta yanayin maganarsa da mutanensa a twitter ne nake gane wasu abubuwan sai kuma hoton nan status ɗin shi na whatsapp.

Haka kawai a wannan lokacin nake jin wata irin kewarsa, har dai na sauke girman kaina na kula shi ranar wata Litinin. Kwana biyu bayan nan kuma yayi convincing ɗina da zuwa Kaduna. Yaushe rabo? Zuciyata tana ta tuna min na yi alƙawari wa Allah ba zan sake zuwa Kaduna ba, amma sai mayar da abin nake yi zuwa ga bayan zuciyata tsabar son zuciya irin tawa.

Sai aka yi gam-da-katar wasu ma'aikatan office ɗinmu da nake bautar ƙasa za su je Kaduna seminar amma ranar Litinin. Ina zaune a falo kusa da Alhajinmu sai ga wayar ɗaya daga ciki tana tambayata wasu takardu da suke buƙatar su. Ina faɗa mata wurin da suke sai na juya wurin Alhajinmu na ce ai seminar za a je Kaduna kuma an ce na bi su. Kwana biyu ne kawai. Za a tafi ranar Juma'a a dawo Lahadi ko Litinin da safe.

Ranar juma'a da safe Alhajinmu ya ba ni kuɗi a hannuna ya ce na riƙe kafin ya f8ta da safe, yayi mana addu'ar sauka lafiya tare da jan kunnen a kula.

Tafiyar gabaɗaya marar daɗi ne a wannan ranar. Ina zaune kusa da tagar mota, kusa da ni wani mutum ne da ya zabga turare mai matuƙar ƙarfi, ba mamaki irin turaren ake cewa ɗan-duwala. Ƙarfin turaren ya hana ni sakat da ya zama ba ni da zaɓi da ya wuce na saka kaina ta waje duk da cewa iskar ta yi min yawa. Allah-Allah nake yi mu isa tasha ko ma rabu na huta da wannan iziyar. Kafin mu isa har na fara atishawa da alama iskar da turaren sun sanya min mura. Shi ya zo ya ɗauke ni a tasha wannan karon. Sai tsokanata yake yi wai me nake ci haka da nayi ƙiba, ko kuma don ya daɗe sosai bai ganni ba ne?

A harabar gidan muka ci karo da wadda ke zaune a ɗayan part ɗin gidan, karon farko da hakan ya wanzu. Da shi kaɗai ta gaisa don ni jakata kawai na ɗauka na doshi sashen shi ba tare da na kula ta ba, ita ma haka ta share ni.

Sa'a ɗaya na yi da jakata ba ta rabo da tissue, don jawo ta nayi na fara tare atishawar da ke yi min jerin gwano fitowa. Tsayawa yayi daga bakin ƙofa ya ce "Sarkin mura! Kar da ki ce ita ce tsarabar da kika kawo min tun daga Kano."

"Lallai ma. To a hanyar garinku na samota, ai ka ga ya kamata na bar maku abinku ko?"

Yana dariya ya ce "Ni dai ki taimaka kar ki sa min kafin ki tafi. Bari na bar ki na je na dawo, please."

Tunda ya fita nake kwance da alama ba da wasa murar nan take yi ba don duk jikina ya saki, har ban san lokacin da bacci ya ɗaukeni ba. Motsin da naje kusa da ni ne ya tashi saboda ko kaɗan ba ni da nauyin bacci. Sai dai farkawar tawa ta zo min da wani zazzafan ciwon kai ne. Duk da jiki da jini ba ka cin alwashi amma da mamaki don da wuya mura tayi min irin wannan kamun duk da ina yawan yin ta. Da ƙyar na daure na ɗan tsakuri abincin da ya kawo sannan na yi sallah na koma cikin bargon na ƙudundune na sake komawa wani baccin.

Da magriba da na farka kuwa da zazzaɓi na tashi, na dai yi sa'a tsananin ciwon kan nan ya ragu yanzu. Missed calls ɗinsu Alhajinmu, Umma da Minal na iske rututu. Gabana yana faɗuwa na fara kiran Alhajinmu, kar na je ya ji shirun yayi yawa ya sa a fara neman bayani daga office ɗinmu don ma Allah ya sa yau Juma'a ce, daga haka kuma balli ya ɓalle. Tunda ya ji mun sauka lafiya kuma zazzaɓi ne ya kayar da ni sai hankalinsu gabaɗaya ya kwanta. Umma har tana cewa mu nemi asibiti ko pharmacy ba chemist ba, a yi min allura, shi ne zai taimaka wurin korar zazzaɓin da wuri.

Ban ji motsin Ahmad Sardauna ba tun da na tashi. Sai kawai na ce bari na yi dabarar da muke yi a bakori idan muna zazzaɓi watau wanka da ruwan sanyi. Tsananin sanyi da ya fara ratsa ni bayan wankan da ƙyar ya bar ni na samu nayi sallah, ga shi hancina kamar na buɗe famfo sai yoyo yake yi. Har na koma na kwanta sai ga Sardauna da magani ya dawo, don haka sha nayi na koma na sake kwanciya.

Cikin dare kuma na farka da azababben ciwon cikin da ke nuna min ga al'adata nan! Kowanne wata haka nake fama da ciwon ciki amma irin wannan me azabar sai lokaci zuwa lokaci. Na tsorata sosai ni kaina don ko kusa ban kawo period ɗina a lissafi ba. Maganin da nake amfani da shi yana gida, da alama ba ƙaramin jiki zan ji ba wannan karon. Innalillahi! Da na sani da ban zo ba. Wahalar da bawan Allah kawai zan yi. Haka na dinga cijewa ina juye-juye a hankali kar na tashe shi daga bacci har zuwa asuba.

Dole gari na ɗan yi haske ya je ya nemo min pad. Zuwa yanzu kam zazzaɓi da ciwon kai sun kama gabansu tun da babansu (ciwon ciki) ya ɗiro! Maganin da nasa ya siyo min ma kamar yau ba zai yi min aiki ba don kafin ƙarfe goman safe na fita hayyacina sai birgima nake ta faman yi ga shi na dunƙule. Sardauna ya bala'in firgita don sam ya kasa motsa daga wurin da nake sai bi na da sannu yake yi yana tambayar ko akwai abin da za a sake nemo min ko za a yi min da zai taimaka ya rage min azabar ciwon, amma ko ƙala na kasa ce masa, infact ma, surutansa damu na suke yi.