Ba Ni Da Masaniyya

19

by @faddabanan

Na ce "Dakata mana kanya! Ke idan kika fara zuba kamar an bugoki daga bisa bishiya. Mussadiq ɗin da kike magana ba shi ne crush ɗin Zulaiha ba?"

"Shi ne. Amma ai kin san so gamon jini. Ba ki ga ya daɗe yana ganinta amma bai taɓa cewa yana sonta ba sai ke? Kuma ai kun haɗu lokacin bikina, kawai hankalinku ne bai kai kan juna ba."

Na ɗan yi jim kafin na ce "Ni'ima kin san ni ina matsala, wallahi ba na ƙaunar soyayyar zamanin nan don ba a ƙaramin ruɗani take sa ni ba. Sai na kasa gane shin ni ake so ko kuma halittar jikina."

Ta amsa "Kar ki damu Zara. Mussadiq kintsattse ne na daga abin da na fuskanta. Ga ƙarin na san da gaske aure yake son yi babu wasa a lamarinsa, laluben wadda ta dace da zaɓinsa yake yi ya sa har yanzu bai kai ga yin auren ba. Kuma ke na san ki ciki da bai, don har na tabbatar masa wahalar shi ne amincewar ki amma ba ki da matsala. Shi ne fa tsabar ƙaguwa aka fiddo ni daga gida da tsakar ranar nan zuwa gare ki."

Na yi ƙaramin tsaki na amsa "Ni ban cika son auren haɗi ba ma Ni'ima." Na tsareta da ido na ce "Faɗa min tsakanin ki da Allah, ke da mijinki ne kuka haɗa wannan abun ko ya ya?"

Da saurinta ta ce "Wallahi daga ni har Khamis babu wanda ya fara yin zancen. Mussadiq ne ya fara, ni da kawai na san ni da Khamis mun taya shi saboda lamarin ya kwanta mana. Iya gaskiyar maganar kenan wallahi."

Na ɗauke idona daga gare ta na ce "Ba na son nace a'a, amma ban yi maki alƙawarin komai ba. Idan Allah ya sa mun daidaita ni ma zan huta da pressure ta Alhajinmu, falillahilhamd! Amma idan aka samu akasin haka sai dai a haƙura."

Murnarta ta gaza ɓoyuwa ta rungume ni tace "Yanzu zan ba shi lambar wayarki, dama na jira sai mun yi maganar da ke kafin ki balbaleni da faɗa Al-masifatu."

*********


Tun daga ranar muka fara mu'amala da Mussadiq, duk da cewa sama-sama ce. Abin da ya hanani sakewa da shi a farko bai wuce cewar ina tunanin zai iya faɗawa Khamis komai da ke gudana a tsakanina da shi ba. Amma da yake mutum ne mai raha da barkwanci sai ga shi ya sa na fara sakewa da shi saboda ban dariya irin na shi.

Duk lokacin da ya so ganina kuwa cewa nake ya same ni a wurin aikina, hakan bai taɓa sa shi cikin damuwa ba bare ya tambayi menene dalilin hakan. Ni kuma ina yin haka ne domin na fi son mu fara fuskantar juna ni da shi tukunna kafin na kawo shi gida, don idan wani abu ya bayyana a ido da na bana so a game da shi bayan na kawo shi gida, ba na jin za mu ƙare ta daɗi da Alhajinmu. Yanzu gabaɗaya hankalin Alhajinmu ya tattara ya koma kan ya aurar da ni ne.

Allah cikin ikonsa ko wata shida ba mu rufa, sunanshi bisa allon wayata idan ya kira ni ba ƙaramin murmushi da nishaɗi yake sa min ba. Ban ce na faɗa soyayyarsa ba, amma kam na ɗauki hanya da ƙiris ya rage na rufta ruf a ciki. Yayi nasara mai ƙarfi a kaina da har zan iya tsintar kaina ina tunaninsa ina murmushi ni kaɗai a zaune, kuma wannan nasarar na daga cikin lamarin da ya taimaka min wurin fatattakar Sardauna daga raina na watsar da shi gabaɗaya. Zuwa yanzu kuma yana kawo ziyara har gida don na fara gangarawa ɓangaren yarda da Mussadiq a matsayin miji.

Da dare ina kwance ina game da wayata wurin ƙarfe sha ɗaya da minti shida naji shigowar kiran Mussadiq a wayata. Na yi mamaki ƙwarai da gaske domin shi ma'abocin bacci da wuri ne. Na amsa wayar da cewa "Ya aka yi mai wayar nan bai yi bacci har yanzu ba?"

Yayi murmushi mai sauti ya ce "Haba mana 'yar budurwa, kin hana ni bacci ta ya ya kike tsammanin zan bar ki ki huta ke ma?"

Cike da jin daɗi na ce "Haba dai Saurayi mijin 'yan mata, ni ma yanzu tunanin yanda zan ji muryarka nake yi amma na haƙura na kama game a wayata saboda na san baccinka ya daɗe da yin nisa."

Yayi dariya "Zara sarkin kunya. Da a waje ne kina kallon fuskata ba za ki iya faɗar haka ba, amma idan aka ji ki ta waya sannan aka haɗu da ke a waje sai a ɗauka mutum biyu ne ba ɗaya ba. Dakata ma....saurayi mijin 'yanmata kika kira ni ko? Ashe kina da kishiyoyi nan gaba kaɗan kenan."

Da sauri na tsuke fuska kamar yana ganina na ce "Chaɓ! Ashe zan tashi Kano kenan. Ni gaskiya suɓutar baki nayi, so na yi na ce saurayi mijin baiwar Allah Zara."

Ya dinga ƙyalƙyala dariya da alama maganar ta faranta masa rai. Ya ce "Zara! Sai ki dinga ba ni mixed feelings yawancin lokaci. Sai na ga kamar ba ki damu da ni ba, anjima kuma sai na ga kamar kin fi kowa damuwa da ni. Ni bana jin ma kin taɓa min me kike ji game da ni. Don Allah yau ɗaya dai ki faɗa min na ji mana."

"Haba mana. Ai zuwa yanzu ko kai ka san me nake ji game da kai. Ai ba koyaushe ba ne bakin nawa yake a rufe. Kuma ai an ce action speaks louder than words."

"Ni ba irin wannan ba. Ina nufin we've been together for long, dole akwai wasu exact feelings da za su iya wanzuwar maki game da ni. Irin su nake son na sani. Na san ki da jin nauyi, bari na kashe wayar sai ki rubuto min shi a matsayin saƙo."

Tun da ya katse wayar nake kallon wayar don na rasa me yake son ji. Ni fa ba na son a tarfa ni irin haka, ji nake komai ya goge min a ƙwaƙwalwa. Na gaji da kallon wayar na tura masa saƙon "Wallahi saboda kasancewata cikin mata masu kunya sosai kamar yanda ka sani, kalmomin soyayya na yi mik wahalar fita kai tsaye. Amma ka yarda da ni, abin da kake ji game da ni, ni ma hakan ce a gare ni. Ka kwana lafiya. Sai da safe." Ban ga amsar shi ba don haka nayi murmushi tare da yin addu'ar bacci na kwanta abu na.

**********


Ranar juma'a ina ta sauri a tashi daga wurin aiki, so nake na koma gida saboda baccin da ya addabeni amma sai wayar Yaya Bello ta katse min hanzari. Wai na same shi a gida idan na tashi daga wurin aiki yau, idan ma ban same shi ba na jira shi.

A gidan nasa nayi sallar la'asar bayan nan gani bai dawo ba na shige wani ɗakin gidan na ɗan samu baccin. Anti Hajiyayye tsohon ciki ne da ita. Ikram da me Alhaji ƙarami kam sai Maa shaa Allah, girman yaro babu wuya.

Lokacin da ya iso ma sai da ya gama cin abinci sannan ya fuskance ni sosai. Salon muryarshi na canzawa na san hirarrakin da muka dinga yi lokacin da yake cin abinci sun ƙare yanzu kuma wannan serious tone ne. Ya ce "Wai ni Zara me kika tsarawa kanki ne zuwa yanzu?"

Na kalle shi fuskata ɗauke da ruɗu na ce "Kamar me Yaya Bello?"

"Gani nayi kamar kin kammala samun dukkanin abin da ya kamata ki samu. Kin kammala digiri, bautar ƙasa ga shi yanzu kina aiki. Kuma na tabbatar ba ki da burin sake cigaba da karatu ko? To yanzu a ina aka tsaya,"

Na ji wani gumi ya yanko min, na daure na ce "Yaya na san zancen aure kake magana akai ko? Akwai wani da muke tare yanzu, kuma in shaa Allah kwanan nan zan kawo shi formally. Ka daɗa ba wa Alhajinmu haƙuri don Allah."

Ya karkata kansa ya ce "Allah ya sa hakan ne. Da kin san yanda Alhaji ya ɗauki lamarin nan da kin fi haka gaggawar kawo mijin nan. Shi yasa kika na shiga maganar a halin yanzu. Bayan wannan kuma, me ye shirinki game da albashinki da kike ta tarawa?"

Na amsa "Zuwa yanzu dai ban san me zan yi da su ba tukunna. Amma idan na nutsu na yi tunani zan dawo na same ka mu ga ya za a yi."

***********

Muna zaune a ɓangarensu Umma tare da su Minal da AK muna kallo. Wani ɗan tunani ya ɓijiro min da ya sa na juyo da sauri na kalli Umma na ce "Umma ko kawai na siya mota da kuɗin account ɗina?" Minal da AK suka fara murnar ihu.

Umma ta kalle mu mu duka ta ja tsaki. Sai da suka koma suka zauna suka yi shiru sannan ta ce "Saurin me kike yi ne Zara? Shin ba ki san yanzu 'yanmata masu mota tsorata maza suke yi ba?"

Na yi kicin-kicin na ce "Allah Umma da ne, kuma irin wannan mazan ai bai cancanci a aure su ba saboda insecurity ɗinsu. Saboda Allah ban da raggon namiji wa yake tsoron mace saboda wani abin duniya."

Ta juya min baya tare da cewa "Na ce dai babu wata mota da za a siya a gidan nan. Ki jira idan kin yi auren sai ki siya, lokacin babu mai hanaki."

Na kama ƙunƙuni "Mutum kowace irin magana ya yi sai an sako zancen aure a ciki, ni gara na yi auren nan ma ko Allah zai sa na huta." Na san tana ji na tayi kamar ba ta ji ba.

Abu kamar haɗin baki sai ga kiran Yaya Muna ya shigo, sai ka ce sun yi taro a kaina a bayan idona, to ita ma zancen auren ta yi min fa. Ai kuwa na hau mitar an dame ni har da su kuka tunda ita na rainata ba irin ragowar da suka yi min maganar ba. Ita ma sai ta rufe ni da faɗa sannan ta ƙare maganar ta da cewa "Kar ki daina kukan nan har sai hawayenki ya cika duniya da ambaliya yar gwal! Kin ji ni ko ba ki ji ba?! Mts!" Ta kashe wayar.

Cike da fushi na wuce ɗakina na bamko ƙofar, irin na sanar da 'yan gidan raina a ɓace yake. Babu wanda ya kula ni.

Ko minti talatin ba a yi bayan nan sai ga wayar Mussadiq. Ya ce "Ke ko ɗan baccin ƙarshen mako ba kya ɗan yi."

Na yi murmushi na ce "Ai tun da ina gida, ko da ban samu baccin ba ai na samu hutun da ya kamata. Kai kuma ya aka yi ka tashi yanzu la'asar ba tayi ba?"

Ya ɗan ja ƙaramin tsaki ya ce "Wayata na mance ban sa a silent ba, shi ne wani abokina daga Enugu ya kira ni. Na so na koma bayan yin wayar amma na kasa. So, ya babyna take yau?"

"Lafiya ƙalau fa." Muka ci gaba da magana kafin ya sauya maganar zuwa ga cewa "Allah ya biya mana buƙatunmu Zara."

"Ameen dai"

"Kin san ni yanzu ba ni da burin da ya wuce ace nayi aure wallahi. Don rashin auren nan ba ƙaramin wahalar da ni yake yi ba."

Kaina a ɗaure na ce "Wahala kuma? Wace iri to? Kai da kullum kafin ka fita aiki sai Hajiya ta shirya mana karin kumallo, ni fa ina ganin yanda Hajiya take tsaye akan lamuranka ko mai aure bai isa ya nuna maka wani abin ba."

Ya ce "An ce maki abinci zuwa gyaran muhalli shine kaɗai buƙatar cikakken namiji? Ki yi haƙuri da abin da zan faɗa maki domin zuwa yanzu mun kawo lokacin da ya kamata a ce babu ɓoye-ɓoye a tsakanina da ke. Kin san Allah ɗaya ne ko? Wasu irin feelings gare ni masu hanani jin daɗina. Kin ga kwanakin nan ba ƙaramar wahalar da ni suke ba. Wallahi idan abun ya motsa min, aƙalla ba akasara ba ina iya kaiwa awa biyu a ɗaki ina fama kafin ya sauka. Kuma a rayuwa yanzu daidai gwargwado na samu abin da nake nema saura auren kaɗai yayi min saura."

Duk da na fuskanci ina maganar ta shi ta dosa hakan bai hanani daurewa da cijewa na furta "Ayya. Sannu. Ai komai ya kusa zuwa ƙarshe bi'izinillah."

Ya ɗan yi shiru kafin daga bisani ya ce "Hmmm! Duk yanda nake so na kwatanta maki babu ta yanda za ki gane irin iziyar da nake ciki. Kin ga wannan awa biyun da na faɗa maki? Ba fa sau ɗaya ba ne a rana, safe da dare ne. A irin ranakun nan da muke gida ba na wurin aiki kuwa har da rana. Ni Allah ma ya sa za ki iya ɗaukar nauyina bayan aurenmu domin alamu suna nuna cewar zan iya kasancewa cikin masu damu."

Na yi murmushi mai sauti na ce "To, ba an ce mace daga mijinta na farko take samun horon da zai sa ta a ɓingiren da take tsintar kanta ba? Kar ka damu, zan koya daga gare ka idan lokacin ya zo."

Ya ce "Hmmm. Allah ya sa to. Kin tuna rannan da daddare da na kira ki nace ki yi min text? Wannan abin ne ya addabeni a lokacin nake neman sassauci, shi ne ke kuma kika turo wani bayani daban. Haushi ne ya hana ni amsawa ai."

Na ɗan yi jim kafin na ce "To ai ni ban san me zan ce ba. Ka ji Umma tana kirana, bari na je. Sai an jima." Na katse wayar.

A ranar wurin sha ɗayan dare sai ga wayarsa. Ya sani a gaba da naci wai sai na tura masa wani abin da zai kwantar masa da hankali sai ka ce ni ce na tayar da hankalin nasa. Na tsani a takure ni a sa ni yin abin da ba ni da niyya yanzun nan sai na yi loosing cool ɗina. Da nacin ya ishe ni sai na ce to zan tura. Ni dai na yi iyakar tunanina na rasa me zan tura mashi a rubutaccen saƙo. Don haka na rubuta "Na doka ƙwaƙwalwata iya dokawa amma na kasa sanin abin da zan tura maka da har zai taimakeka a halin da kake ciki. Ta iya yiyuwa saboda ba ni da ilimi ta wannan ɓangaren ne. Duk da na san yau ma haushin saƙon nawa za ka ji, sai da ka yi haƙuri don i couldn't come up with anything. Haƙurin da kayi a baya ba za ka ƙara yin irinsa a gaba ba fa." Na tura masa.

Tun daga wannan ranar idan na ga kiran shi goman dare ta wuce to ba na ɗauka. Zance ko hirar irin wannan soya min zuciya take yi. Na sha ba shi uzurin cewa magana irin wannan nauyi take yi min, kuma irin nauyin ba zan iya ɗauka ba.

Shi kum yana ji a ranshi wani sirrinsa mai matuƙar girma ya sanar da ni, ko don saboda haka ya ci a ce na ajiye jin nauyin nawa na saki baki da shi mun yi magana irin wacce za ta sauke masa zazzafar sha'awar tasa tun da dai ba cewa ya yi nayi masa wani abu a fili ba. Kuma shi a ganinsa aure za mu yi, tunda har mun fara maganar zai turo manya.

Wallahi tun ina rarrashinsa akan maganar nan, don ba zan iya yin ko ɗaya daga cikin abubuwan da yake so ɗin ba, ina yi masa uzuri har ta kai na fara jin haushi. Na fara kallonsa a matsayin mai son kansa. Da kafin ya san ni ta ya ya yake coping? Mun yi watanni tare kafin ya bayyana min wannan ɓangaren nasa, shin a waɗannan watanni ta ya ya ya rayu? Sai yanzu don kawai ya faɗa min abin da ba ni na nemi sani ba sai ya takura min?

Zuwa yanzu kam zan iya ganin kiransa na ƙi daga wayar at any time of the day. Ɗaga wayarsa kam ta koma sai na ga dama ko ya ci sa'a ya kirani lokacin da nake in a good mood. Sannan ni kuma na yanke kiransa a waya, don ba zan iya tuna yaushe na kira wayarshi ta ƙarshe ba. Oh ni Zara!