22
by @faddabanan
Abin da ya faru a wannan daren ne ya tabbatar min da ba zan taɓa iya rayuwa da Bashir ba! Domin kwana zan dinga yi ina tashi da takaicinsa! Hakan ya sanya shawarar da take ta min yawo a kai da nake ganin ba mai yiyuwa ba ce na ga gara kawai na gwada ta. Bahaushe ya ce a rashin tayi ake barin arha. Hakan ya zaburar da ni na ɗauki wayata amma sai na gaza kira. Da na ga dare na ƙara yi, idan har ban daure na yi kiran nan ba za a iya samun matsala. Jikina a sanyaye na latsa kiran, yanda nake jin ringing tone a kunnena haka nake jin luguden dukan zuciyata ta ciki saboda tsananin fargaba. Cikin murya mai cike da bacci ya ce "Hello Zara?" Na amsa a sanyaye. Ya sake cewa "Ya kike? Lafiya dai ko?" Tambayar nan da ya yi min ce ta zubar da duk wani hanzari da dagiya da dauriyar da na naɗo na yi kiran nan mai girma. Nadamar kiran ta lulluɓeni. To me zan ce da na kira?!
Na daure na ce "Babu komai. Koma baccinka. Sai da safe." Na fara ƙoƙarin kashe kiran amma sai na ji ya dakatar da ni da cewa "Zaraaaaaa.... Idan akwai wani abu ki buɗe baki ki faɗa, infact, ni kaina na jiyo alamun akwai magana a bakinki. Yau fa ko 'yar rahar nan da kike yi min idan kin kira ba ki yi ba. Are you really okay?"
Na yi shiru kamar ba zan ce komai ba, amma idan na bari wannan window ɗin ya rufe shin ina da tabbacin sake samun wani courage ɗin ko kuma na same shi so attentive to listen to me kamar yanzu? Na yi ƙundunbala na ce "Akwai matsala Sardauna. Babbar matsala. Kuma alfarma mai girma na kira ka yi min don ya Rasulullah."
Daga cikin wayar ina jin motsinsa da alama tashi ya yi daga kwancen da yake. Ya ce "Alfarma? Alfarma me?" Muryarsa ta washe babu wani alamun bacci tare da shi.
Tun da mun je bakin gaɓar ruwa ba gara mutum ya faɗa kawai ba? Don haka maganar da ta fito daga bakina ban yi nazarinta bare na tattaunata, domin muddin na ce zan yi ɗaya to wallahi ba zan iya faɗarta ba. Na ce "Alfarmar ka aure ni na wasu watanni don Allah."
Dariya ya kama ƙyalƙyalawa kafin da ƙyar ya samu ya tsayar da dariyar ya ce "Watau saboda nace yau babu raha sai kika sauya zuwa sabuwar tsokana kenan. Da na san tsokanata za ki yi da ba zan bari ki korar min baccina ba, wallahi i thought you were serious. Let me sleep, gobe aiki ne mai yawa da ni shi yasa ma na kwanta this early."
Dariyar shi maimakon ta ci gaba da katse min hanzari sai ma na ji ta kamar allurar ƙwarin gwiwa. Na ce "Ka daina dariya, Allah da gaske nake yi."
Ya ce "Ummmm.... Okay toh. Yanzu dai bari nayi bacci kar na makara. We will talk about this another time. Sai da safe." Daga yanda ya amsa ni za ka gane har yanzu ba wai ya ɗauki maganar tawa da mahimmanci ba ne. A haka muka yi sallama. Na kwanta na tashi cikin zullumi.
Washegari ko kusa ban yi nesa da wayata ba, a wautata ina jiran Sardauna ya kira ni domin ji daga gare ni na maganar da nayi masa jiya da daddare amma har dare tsit babu shi babu alamarsa. Damuwata ba tayi yawa ba saboda ai jiyan ya faɗa min aiki gare shi don haka da naga bai kira ba sai na yanke shawarar kiransa wurin ƙarfe goman dare, na san ƙila lokacin ya gama komai na shirin kwanciya, hakan zai ba mu damar yin maganar a nutse. Ina kira na iske wayar a kashe take.
Ni Zara na rasa me ke min daɗi a rayuwa! Wai me ye yake damu na ne? Shin takaicin na nemi alfarmarsa ya share ni ne? Ko kuma haushin kaina na wautar da nayi? Ni kaina ban sani ba. Ire-iren abubuwan da nake ji yanzu ba na iya fassara su, abu ɗaya na sani babu farin ciki a cikinsu ko ɗaya. Wannan ranar kam kasa bacci na yi sam sai gab da asuba na samu ya ɗauke ni, shi ma ana kiran asubar na farka da ciwon kai mai tsanani.
Mun wayi gari a safiyar ƙarshen mako na Asabar. Na san yau kam babu aiki don haka ban yi fushi ba, shin ni yanzu ina bigiren da zan yi fushi ne bayan ni ce mai neman mafita? Na ba shi har zuwa ƙarfe goman safiya da rabi, lokacin da nake tunanin ya nutsu na zabga masa kiran waya.
Dum-dum! Har zuciyata amsawa kiran take yi. Wayar ba tayi ƙara ya wuce uku ba na ji ya katse kiran kuma an rubuta min user busy. Na ɗan dakata ina jiran ko zai kira ni don babu mamaki ma ya katse kiran ne bisa kuskure amma tsit Malam ya ci shirwa. Na ƙara ba shi lokaci na sake sabon kiran, sai kuma na iske ya kashe wayar ne gabaɗaya.
A take wata irin zufa da tashin hankali suka lulluɓeni. Shin hakan na nufin ya daina amsa kirana ko me kenan? Har ƙarfe sha ɗaya da rabi ina gwada layinsa amma har lokacin a kashe wayar take bai sake kunnawa ba.
A take na canza shawara, ai wannan maganar sam dama ba ta waya ba ce, shin wa ya aike ni da farko na fara yin ta a wayar? Desperation! Haka na ji zuciyata ta amsa min. Kamata yayi a ce na fuskance face-to-face na yi masa bayani sosai kuma dalla-dalla yanda zai fuskanta.
A sukwane na shiga wanka, a gaggauce na shirya cikin doguwar riga ta atamfa, ganin ranar sanyin da sauƙi sai ban ɗauki rigar sanyi ba. Jakata na figa da sauri na doshi ɗakin Umma ina ƙwala mata kira cikin tashin hankali don na gigitata "Umma! Umma! Umma!"
A bakin ƙofa muka ci karo da ita hannu ɗauke da zani tana cewa "Ke! Kin gan ni a nan. Me ya faru? Ina za ki?" Tana kallona cike da mamaki.
Na amsa cikin hanzari "Ni abubuwa sun yi min yawa har na mance yau ni ce zan wakilci wurin aikinmu a Kaduna. Yanzun nan Head of department ɗina ya kirani yana tambayata ya hanya. Sauri nake yi. Na tafi Umma."
Ta biyo bayana tana cewa "Ki yi sauri ki tare Malam Habu ya sauke ki a tasha, yanzun nan na aike shi. Allah ya kiyaye hanya. Akwai kuɗin mota a hannunki ko?" Daga waje na amsa mata da cewar an ba ni a ofis.
Ƙarfe uku daidai a harabar gidansa ta yi min kuma har wannan lokacin wayar tasa a kashe take. Don haka wurin a harabar gidan na zauna don ɓangarensa a rufe yake tabbacin ba ya nan. Ban fi minti talatin da zama ba na ga wadda ke zaune a ɗayan ɓangaren gidan ta fito za ta fita tare da wani. Yau kam mun gaisa, sannan ta sanar da ni baya nan kuma za ta rufe gidan ne. Sanin ban san kowa a garin nan ba sai na ce mata kar ta damu ta rufe. Zan zauna na jira har sai ya dawo ne.
Tun da suka tafi ta rufe gidan babu abin da yake min yawo kamar maganganun Gwaggo na kwanaki. Ni me yasa ba ni jin magana ne? Duk abin da suke 'no' sune abokan zamana. To, yanzu ma ga shi na aikata kuskuren da Gwaggo ta kwaɓe ni game da aikatawa watau roƙon namiji ya aure ni. Yanzun ma duk yanda tunanin hakan ya dame ni bai hana ni ɗaukar tunanin na jingine shi a bayan zuciyata ba, amma case ɗina da bambanci da wanda Gwaggon ta fasalta.
A harabar gidan na ga ragowan wani ruwa a buta, da shi nayi alwala na yi la'asar. Yamma na fara yi ai kuwa sanyi ya bazamo kamar da gayya ma. Na dinga rawar sanyu ga shi ba ni da wurin ɓuya har aka yi kiran sallar magriba a takure nake, bishiyar harabar gidan ta ƙarawa sanyin armashi. A cukwuikuye nake a wurin na kasa yin komai, nadamar zuwana ta cika ni ga shi ban isa na sauya shawara na bar gidan ba domin a kulle gidan yake.
Sai wurin tara saura na dare na hango ana buɗe gate ɗin, ban ɗaga daga wurin da nake zaune ba don babu mamaki matar ce ta dawo. Ko ɗazu da take faɗa min ba ya nan tana nufin yayi tafiya ne ko ya ya?
Hasken fitilar mota ce ta haska shi bayan ya fito daga cikin motar ba tare da ya kasheta ya koma wurin gate domin rufewa. Ina zaune ina ƙare masa kallo har ya ɗauko jakar laptop ɗin shi da wasu ledoji guda biyu, ya kashe motar tare da rufeta ya kuma doshi sashensa ba tare da ya lura da ni ba.
Ganin haka sai na miƙe tsaye tare da ɗaukar jakata na biyo bayansa. Jin motsi ya sanya ya juyo da hanzari kamar a razane yana cewa "Waye nan?!"
Da ƙyar na iya faɗin "Ni ce. Zara ce, Sardauna."
Kallona yake yi cike da mamaki amma da gaggawa ya buɗe min ƙofar ganin halin da nake ciki na tsananin kaɗuwar jiki saboda sanyi da ke bugawa. Ina shiga yayi maza ya shigo tare da sauke kayan hannunsa ya kuma ciro rigar sanyin jikinsa ya ɗora min a jiki ya wuce ya jona ruwa a heater, zuwan wutar ma kenan.
Na samu gefen katifa na zauna haƙorana suka fara dukan juna kaf-kaf. Yana kammala jona heater ɗin ya dawo kusa da ni tare janye rigar sanyin ya rungumeni sannan ya ɗora mana rigar sanyi yanda za ta rufe wasu sassan jikinmu ya ce "An ce ɗumin jikin mutane biyu ya fi na bargo bare wata rigar sanyi, riƙe hannuwana yanda transfer of heat ɗin zai fi zama effective. Why didn't you tell me you're coming? Da ko key na bar maki ai."
Da gaske maganar da ya faɗa game da haɗa jiki yake kenan, domin na ji azabar sanyin nan ta fara raguwa don haƙorana sun daina bugun juna zuwa yanzu. Cike da tausayin kaina da ya ɗarsa min raunin da har ya bayyana a muryata na ce "To ba kai ne kayi rejecting call ɗina ba? To na yi ta ƙoƙarin na sake samunka na kas..." Maganar tawa ta katse sakamakon hawayen da yayi nasarar gangarowa da gudu. Hawayen nawa ba ƙaramin mamaki suka ba shi ba, sai da ƙarar tafasar ruwan da ya jona ya katse masa hanzari ya tashi. Shayi ya haɗa mana amma nawa a babban mug ne. Kafin na gama shanyewa ma na samu sauƙin sanyi sannan ya haɗa min ruwa mai zafi na yi wanka, sai kuma a lokacin na ji nutsuwa ta saukar min.
Bayan na samu nutsuwa, shi ma kuma ya gama dukkanin abubuwan da ya kan yi kafin kwanciya sannan muka samu zama. Da tsokanata ya fara ma "Wannan zuwan naki babu notice, anya ba kewata ce ta dameki da har kika nemo ni ba?"
Na ɗan yi murmushi na zame na kwanta na ce "Ka ji Ahmad da tsokana saboda Allah fa, ai dama ni kullum a cikin kewar nake."
Ya kwanta shi ma yana amsawa da "A'a fah. Kar ki zo har nan ki ce za ki yi min daɗin baki 'yan mata. Ban manta zuwana na ƙarshe Kano ba, atoh!"
Ina ƙoƙarin danne dariyata na ce "Na fa ba ka haƙuri har sau babu adadi, amma ba mamaki don ka yi riƙo tun da bafullace ne kai. Amma ai ka san abin da ya kawo ni yanzu ko? Na ga kamar kana ta avoiding ɗina ta waya." Na ƙarashe maganar babu alamun wasa a tare da ni.
Shi ma ya aro fuskar da babu wasa a ciki ya ce "Wallahi ba avoiding ɗinki nake yi ba. Rannan da muka yi waya da ke da daddare ba na faɗa maki aiki gare ni ba? Kin san ƙarshen shekara ya yi, lissafe-lissafen ƙarshe shekara muke yi a ofis, kwata-kwata ba ni da lokacin kaina bare na wasu. Ɗazu da kika kirani muna cikin meeting ne, ina cikin bayani kiranki ya shigo shi yasa na katse na kuma kashe wayar gabaɗaya. Ban ma ƙara tunawa da wayar ba sai da na dawo na ganki a gidan nan. Wait... Tun lokacin da kik kira ni kike cikin gidan nan?"
"A'a. Wurin uku na iso."
"So sorry, Please. Yau fa ina ga tun ƙarfe bakwai na bar gidan nan... Dakata. Kika ce na san abin da ya kawo ki?"
Na mayar da idona kan yatsuna da suke riƙe tam da bargo na ce "Eh mana. Maganar rannan da muka fara yi a waya, wadda ka ce za mu ci gaba daga baya."
Zumbur ya miƙe zaune yana kallona a wani yanayi da ba zan iya fassara shi ba. Ya ce "Au! Dama for real da gaske kike yi? Ni a daren da muka yi zancen na manta da shi ma saboda ban taɓa tunani maganar za ta iya zama gaskiya ba. Abin da ban fahimta ba shi ne me yasa ni Ahmad zan yarda da hakan?"
Na miƙe zaunen ni ma tare da riƙo hannayensa ina faɗin "Saurare ni Sardauna, ba na faɗi haka don na ɗaure rayuwarka da tawa ba ne. Buƙatata ba mai wuya ba ce idan har ka kwantar da hankali ka fuskance ni. Ka fi kowa sanin ba na iya connecting da kowa sai kai kaɗai. Ga shi a gida Alhajinmu ya matsa min akan batun dole sai na yi aure, ganin kuma ban fitar da miji ba ya gaji ya kawo min wani wawan mutumi, wanda ko kallonsa na yi zuciyata tafasa take yi bare kuma idan magana ta haɗa ni da shi. Allah idan na auri gayen nan zan iya mutuwa har lahira don tsaf za a tashi a ga babu ni a duniyar nan. Ka taimake ni Sardauna."
Ya zare hannuwansa ya matsa kaɗan yanda zai kalleni sosai ya ce "Ni duk kin ɗaure min kai da tunani. A je na yarda da proposal ɗin nan naki daga nan sai a yi yaya kuma?" Ya tsare ni da ido.
Jikina na rawa na ɗan ƙara kusanto shi amma ban taɓa shi ba na ce "Abu ɗaya nake buƙata daga gare ka. Ka ga yanzu na fara aiki, so nake idan muka yi auren da zarar na samu ciki kawai ka sake ni, shi ke nan. Da aikin nawa zan iya kula da kaina da babyn ba tare da mun dame ka akan ka yi mana wani abun ba."
Ya zazzaro ido yana kallona cikin kaɗuwa, ya miƙe tsaye a zabure ya yi tafiya da baya-baya yana kallona kafin ya dawo gabana ya yi kneel down yana leƙen fuskata ya ce "Zara me yake damun ƙwaƙwalwarki ne? Shi dama aure girmansa ya kai a yi wasa da shi ne har haka?"
Duk yanayinsa babu abin da ya sauya min na daga ƙudurina. Na ce "Ka tsaya ka ji shirin nawa mana. Ka ga idan mun rabu da kai ina da ciki, zan ɗauki lokaci kafin a ce na haihu, na shayar da bebin har zuwa yaye. Ga ƙarin cewa bazawara na da ikom zaɓawa kanta miji. Wallahi Sardauna ba zan dawo daga baya na addabi rayuwarka game da babyn ba. Idan ma kana jin shakka, ka ɗauko Alkur'ani yanzu na rantse da shi a gabanka, once you are out of our lives, that will be for good. Sannan, idan har ka amince da batun auren, ina ba ka tabbacin cewa ko kobonka ba zai yi ciwo a kaina ba. Da kaina zan yi wa kaina lefe na ba ka ka kai gidanmu. A abu ɗaya ne kawai zan nemi alfarmar shi daga gare ka watau sadaki, ba wai don ba zan iya biya ba ne, a'a, so nake a samu ingancin auren ya zama babu tantama, kuma ni dai na san na fi ƙarfin dubu goma daga wurinka don ko gari na ce ina buƙatar ta daga gare ka, kai me ba ni ne."
Ya ci gaba da kallona kamar kai biyu ya gani a saman wuyana ya ce "Allah ban da a zaune kike a gabana zan iya cewa mafarki nake yi. Shin kin manta zancena da Rahila ne? Me kike tunanin zan faɗa mata? Gaskiya hankalina bai kwanta da wannan abin ba Zara. I do not wish to be part of something as absurd as this!"