Ba Ni Da Masaniyya

24

by @faddabanan

Kai tsaye daga nan gidan Yaya Bello muka wuce. A can muka ci abinci. Yanda naga suna hira da Yaya Bello sai naji na samu nutsuwa da alama Yayan ya yaba da hankalinsa. Da yamma muka rabu akan zai je gidan 'yar uwarsa ta Jan bulo, ya tafi ya bar ni gidan Yaya Bello. Shi kam Yaya sai yabonsa yake yi bayan ya tafi, har yana tambayar daa jiran me na tsaya yi? Har sai da na bari rayuka suka ɓaci. Murmushi kawai nayi, to na isa na faɗa masa gaskiyar magana ne?

Tun kuma daga ranar, muddin na ga an kawo abu wurin aiki da ya danganci kaya siya nake. Sai kuma a wannan lokacin blings and sparkles (***) suka sameni a matsayin customer. Da kaina na zaɓi colors ɗin luxury veils ɗin da nake so, na kuma san tabbas sai na koma tunda ban gama siyayya ba. Yawancin kayan da na ɗauka na ofis ɗinmu manyan atamphophi ne har guda bakwai amma a bashi, zan biya a cikin wata huɗu. Ba wai ba ni da kuɗin biyan ba ne a take, ina so na yi amfani da kuɗin a kasuwa na siya kaya kai tsaye. Duk wannan sauyin da aka samu tsakanina da Sardauna bai sa waya ta yawaita a tsakanina da shi ba, kowa sabgar gabansa yake yi kamar a baya.

Ranar da ya samu ya kira ni, shi ma ya kira ni ne domin ya ji ko a kwai wani shiri da nake son yi game da bikin. Na sanar da shi cewa na fara siyan atamfofi amma ya ce na ɗan dakata na jira sai ya zo Kano tukunna, har da tsokanata wai tun da shi zan yi wa kwalliya na jira ya zo ya taya ni zaɓa don ba zai duba ta whatsapp ba ko na tura ta can. Ni ikon na shi ma sai ya ba ni dariya, ba mamaki so yake ya gwada ni ya ga ko zan ɗauki maganar shi tun da ya sha faɗar cewa i'm so stubborn and strong willed person.

Satittikan da suka biyo tsakani kuwa ya zo da kan shi ya haɗu da Alhajinmu kamar yanda Alhajin ya buƙata sannan yanzu sai kwatsam na ji a bakin Minal wai danginsa sun zo. Shi bai faɗa min ba haka ma a gida babu wanda ya faɗa min, sai da ina dawowa daga aiki Minal ke ba ni labarin zuwansu. Watau Yaya Bello da Sardauna sun haɗe min kai kenan.

Da na nutsu da daddare sai na kira shi a waya na nemi ya turo min da account number ɗinsa don na mayar masa da abin da suka kawo. A kuma daren na yi amfani da wayata na tura mashi kuɗin. Na kuma rubuta tsararriyar godiyar taimakon da yake yi min. Har na shaida ma shi ko a banza zan iya fitar da kuɗin na bayar don murnar rabuwa da Bashir, balle ma kuɗin da suka kawo indirectly ni aka kawo wa. Sai dai ina ta jiransa ya zo Kano mu je yin siyayyar amma shiru ban ji ma yana maganar zuwan ba, ga shi kuma lokaci yana tafiya.

Da na gaji da jira sai na kira shi game da batun neman gidan za mu zauna, ya kamata mu fara ba da cigiya kar lokaci ya ƙure mu rasa wanda zai yi mana daidai. Sai kuma ya ce min ai goben ma yake shirin shigowa Kano, na jira zuwansa tukunna.

A gidanmu na sauke shi wannan karon, sai kuma a lokacin Umma ta yi katarin ganinsa har suka gaisa. Yana gama cin abinci kuma na kwashe shi muka tafi wurin Gwaggo. Ba ta da wani zance da ya wuce wai yaushe zai zo ya gaishe ta ne? Za ta hana shi matar idan bai zo ba fa.

Muna shiga falonta, kallo ɗaya tayi masa sam ta ƙi yin magana da hausa ta juya harshe zuwa fulatanci. Sun yi doguwar magana a hakan, ni kuma ina zaune gefe ban san me suke faɗa ba tun da bana ji. Na dai sunayen garuruwa a maganar tasu.

Akan hanyarmu ta komawa sai yabon Gwaggo yake yi, da alama an samu haɗuwar jini mai ƙarfi tsakaninsa da ita. Sai da muka nutsu a gida sannan ya sanar da ni cewar ya danƙa batun neman gida a hannun abokinsa na Kano Garzali, so, ko baya nan za a dubo idan an samu za a kira ni na je na duba. In dai yayi min shi kenan tun da ni ce ƙarfin zama a gidan. Da na ƙara bijiro da zancen siyan kayan, sai ya ce "Ki tattara kuɗin Hajjaju zan zo takanas domin ke nan da sati biyu. Wannan zuwan da kika ga nayi na Yaya Bello ne. Wannan awoyin da muka yi tare da ke ma shi ya sammaki. Don haka sai ki gode masa."

Na ce "Lallai ma, watau da bai yarda ba sai dai ka zo ka tafi ban sani ba?"

Yana kallon wayarsa ya amsa "Eh mana. Ko na kira da daddare na ce maki zan zo yau?" Girgiza kaina kawai na yi na bar zancen. Su suka san abin da suka ƙulla shi da Yaya Bello amma dai na gansu tare da Alhajinmu bayan ya dawo suna magana. Ban matsu in ji ba, saboda na san babu wanda zai faɗa min a cikin shi da Yaya Bello. Shi kuma Alhajinmu yanzu 'yar baya-baya nake yi da shi.

Umma har da tsokanata wai a ina na samo jan ƙosai haka? Farin Sardauna take magana na sani. Abu guda yayi min daɗi yanda na jiyo Alhajinmu na kanbama nutsuwar Sardauna, Umma ma na taya shi. Haka ma Gwaggo kafin na kwanta bacci sai ga kiranta, ta yabi zaɓina sannan ta umarce ni da na ƙara dagewa da yin addu'a yanda za mu samu tabbataccen zama don ƙwarai da gaske tana matuƙar sha'awar zama da shi. Wannan abubuwan daga gare su ya sabbaba min tausayinsu a zuciyata. Ji yanda suke farin ciki ba tare da sun san me na shirya ba. Allah ya sa ba alhakinsu nake ɗauka ba. Subhanallahi!

Haka nayi ta jiran gawon shanu har sati biyu tayi. Maimakon na ga Sardauna ya zo sai zuwan 'yan uwansa na gani, kuma babban abin mamakin bai wuce na cewar lefe suka kawo ba, akwatina huɗu da kit sai kuma kayan sa rana daban. Komai da ake buƙata na al'ada duka sun kawo a wannan ranar. Na daɗe ina mamakin hakan domin bai faɗa min komai dangane da zuwan nasu ba, a takaice ma rabona da shi a waya ko chat yau kusan kwana huɗu kenan.

Sai a daren ranar ya kira ni da kansa tun da ni ma ban kira ba na sa masa ido. Ya ce "Sai kika ga kaya ko? Kin san wani abu ne? Mu a gidanmu idan matashi zai yi auren fari, a tsakanin iyaye, yayye zuwa 'yan uwa ake tattara gudunmawa a siya wa mutum lefe. Ni nawa da kika gani aikin yayyena ne. Na kuma san za a yi haka shi yasa na dakatar da ke daga siya saboda ban isa na kawo kaya na ce ni na siya da kaina ba. Surutun da za a yi min ba zan iya ɗauka ba."

Na amsa "Hakan na nufi idan za ka sake wani auren kana da damar da za ka siya da kanka ko? Kar ka damu, babu abin da za a taɓa a ciki, za su zamo tamkar ajiya a wurina. Idan ma batun auren ya taso za mu iya kai wasu kasuwa a canzo."

Yayi shiru bai ce ƙala ba. Ya nisa kaɗan ya ce "Zancen gida kuma Garzali ya samo, daga hotuna da video na gidan da ya turo min na yaba da zaɓen nasa. So, zan tura masa kuɗin yanzu, ke kuma idan mun tare sai ki ba ni kuɗina."

Na yi sauri na ce "A'a, ba damuwa. Nawa ne? Gara na turo yanzu yanda zan sa da nauyinsa a kaina tun yanzu kar na sha'afa."

"Okay oo. Dubu ɗari biyu da hamsin ne a shekara."

Na ɗan yi jim sannan na ce "Amma da na ƙasa da haka aka samo, ai kasan a nan zan ci gaba da zama kar sabgogin su zo su yi min yawa daga baya."

Ina jiyo shi kamar yana riƙe dariya sai dai ban tabbatar ba, yayi gyaran murya ya ce "To na ce ya saki gidan kenan?"

"A'a. Goben zan turo maka in shaa Allah." Kuma a washegarin na tura kamar yarda na alƙawarta.

Ranar da Yaya Muna ta zo ina jiyo su daga ɗakina ita da Umma suna ta shirye-shiryen biki. Ba shiri na fito waje saboda jiyo Yaya Muna tana faɗin kar a yi min gara yanzu, gara a bari sai na haihu tukunna. Chaɓ! Ita ba ta san dawar garin ba, ba ta san cewa ni za'a ragewa aiki ba. Ina fitowa daga ɗaki ko ƙarasowa wurinsu ban bari nayi ba na fara magana "Gaskiya a'a, Umma. Tun da akwai halin yi gara a yi kawai a huta."

Yaya Muna ta ce "Ji mara kunya fa. So kike ki nuna mana kina jin tausayin mijinki ko?"

Na yi murmushi na ce "Ka ji Yaya Muna fa. Sai ka ce ba da ke a cikin masu takura min game da zancen aure ba. To yanzu don na yi magana sai a ce na yi rashin kunya?"

Umma ta amshe maganar da cewa "Ya isa haka. Maimunatu saka gara a list ɗinmu. Da gaskiyarta, gara a yi komai gabaɗaya a huta." Ina jijjigar daɗi na rungume Umma ina faɗin "Allah ya bar mana Ummanmu." Hararar Yaya Muna ba ta daɗa ni da ƙasa ba, na wuce abuna na bar su.

Ni'ima da Hajjo ba ƙaramin gagarumin mamaki suka shiga ba. Sun san Sardauna a bakina, haka kuma sun san ban taɓa relationship da shi balle har a zo zancen aure. Ɗan nisa da juna da muka yi saboda yanayin rayuwar kowa ya sauya ba irin da ba ne da muke a tare kusan koyaushe a makaranta, ya sanya suka yarda da batun cewa daga baya muka tsincin kanmu a relationship ni da shi, ga shi kuma har abun ya koma aure. Sai kuma ƙarin cewa bambancin sati ɗaya ne jal tsakanin nawa bikin da na Hajjo.

Har satin bikin ya kama duk abin da ya taso da kaina nake yi, irin abubuwan da angwaye ke biya babu abin da na nema daga gare shi. Haka shi ma bai buƙaci ya ji ko ina da buƙatar wani abu ba.

Sannan da kunnena na jiyo Yaya Bello yana faɗawa Umma cewa wai Ahmad ya samo gida a Kano ne saboda aikin Zara, amma da zarar ya samo mata wani aiki a Kaduna za su tattara su koma can gabaɗaya. Umma kuma ta ce "Oh! Ji yaro da hangen nesa. Allah ya basu zaman lafiya."

Na haɗa Umma da mai haɗa min turaren wuta, ban san tattaunawar da suka yi ba amna dai na ga an kawo himilin turaren wuta har da tsuguno a ciki. Na kuma dage akan Yaya Muna ba za ta taɓa min turaruka ba, dama na hango tana biyo su sai na kwashe na kai wa Gwaggo ajiya. Sai kuma na dawo na sa ta a gaba da nacin sai ta siya min turaren tsinke na wurin ƙawarta Anty Shamsiyya (***), ni kaina na san don zan yi aure ne kawai ya sa Yaya Muna ta yarda ta siya min. Domin da aka kawo su har da wasu sabbin kala da ɓan taɓa gani ba. Turarukan baiwar Allahn nan unique ne, ba na jin na ga mafiyawancin irin turarukanta a kasuwa sai dai 'yan kaɗan.

Sardauna kam har kwaɓar shi nayi akan kar ya sanar da aurenmu ga mutane da yawa sai 'yan kaɗan na kusa da shi sosai, kar a zo ana yi masa kallon mai auri-saki ko aure-aure, amma sai ya juya maganar zuwa wani abu daban bai amsa ni ba. Kwanakin haka yake yi wa wasu batutuwan da suka fito daga gare ni. Sai ya ga dama yake amsawa.

Duk yanda na so na ji yanda suka yi Rahila game da aurena da shi, bawan Allhan na ya murje ya yi ƙema-dagas ya ƙi faɗa, idan na dame shi sai ya ce ina ruwana da abin da bai shafe ni ba? Kawai daga baya sai zuwa na yi na iske a twitter ana yi masa murna game da batun aurensa da ya taso, kenan bai ɓoye ba. A hannu ɗaya kuma idan ka ga yanda Alhajinmu ya buɗe bakin aljihu kamar a kaina ya fara aurar da 'ya, sai ya ba ka tausayi.

A ranar mother's day a gida aka ce na gayyoto shi ya zo amma na ƙi faɗa masa, sai ma dagewa Umma da nayi akan cewa ba shi lokaci. Autarsu da ke aure a Kano ta zo tare da wasu 'yan uwansa da suka sauka a gidanta, ranar ne muka fara haɗuwa da ita. Bride veils ɗin da aka dinga maganarsu blings and sparkles (***) ce tayi min su, da wasu daga cikin bangles ɗin da na yi amfani da su a bikin.

Shi kam ban samu sanya shi a idona ba sai bayan da aka ɗaura aure da suka dawo gida. A wurin ɗaukar hoto a harabar gidanmu ne Yaya Muna take yi min tsiyar duk rowar shi da nayi mata sai ga shi ta gan shi a arha, dariya yayi kawai suka gaisa.

Gwaggo kam yanda ka san shi ne ɗanta ba ni ba, ta ja ta tsaya ƙyam akan sabgoginsa da abokansa da suka halarci ɗaurin auren sai hidima kawai take yi masu. Kuma ko da kuskure ba ta taɓa mantawa ta yi masa magana da hausa ba. A haka aka kammala bikin aka miƙa ni gidana ranar da marece. Baba mijin Gwaggo sai ya damƙa min sadakina a hannuna kafin a kai ni. Dubu hamsin na gani, abun ya ba ni mamaki tunda ni dubu goma na roƙa daga gare shi.

Da shi da Garzali da wasu abokansu guda biyu suka zo siyan baki. Na biye masu muka yi ta hira har Garzali na cewa shi kenan na hutar da su siyan baki tunda bakina a buɗe yake. Dariya kawai na yi. Da suka tashi tafiya kuma sai da suka ajiye min kayan da suka ce na siyan bakin ne.

Ko ban faɗa ba kun san babu kunya mai tsanani tsakanina da Sardauna. Wankana na yi na nemi rigar baccina mai kauri na sanya. Kafin ya fito daga na shi wankan kuma har na samo plate na juye naman da ke leda. Naman kaza da kuma tsire na gani. Na jera su lemo da ruwa da kofuna ina jiran shi. Yana kammala shiryawa ya ƙaraso gare ni yana cewa "Ban manta yanda kuke da kaza ba, shi yasa na ce su haɗo da tsire."

Na yi murmushi na ce "A haba dai! Ko da bana son ta ai yau ta amarya ce, ka ga ya kamata a ce naci ko da zan yi amai ne. Au! Na ga sadaki, nagode sosai."

Ya ɗauki ruwa yana faɗin "Me ye na godiya to? Gani nayi ba abin da na kashe a bikin nan shi yasa na bayar da hakan. Sannan kin san me mayar sadaki yake nufi ko?" Ya ɗaga girarsa ɗaya yana kallona alamar tambayata yake yi.

Na yi 'yar ƙaramar dariya na ce "Ai dama ban ce zan dawo da shi ba. Godiya kaɗai nayi, don ya cancanta na yi godiyar."

Da muka kammala cin abinci sai ya ja ni yana nunnuna min yanda gidan yakw gabaɗaya tunda ni wannan ne shigata ta farko cikinsa. Falo ne kato har da dining area. Akwai ɗakuna biyu a ɓangaren dama watau nawa da na shi kenan, kuma da bandaƙi a kowanne. Sai kuma fallen ɗaki a ɓangaren hagu shi kuma an sanya katuwar katifa ne kaɗai, irin wadda Sani Haruna Limawa ke yi wa laƙabi da Maigida sauko mu gaisa. Akwai banɗaki a falon ta ɓangaren hagun kusa dakin nan. Ta ɓangaren dining akwai kicin da store ɗan madaidaici. Sannan idan ka fita ta ƙofar kicin akwai ɗaki guda ɗaya a wajen, shi kuma banɗakin a waje yake ba a cikin ɗakin ba. Harabar gidan idan an yi dabara za a iya parking ɗin motoci guda biyu. Kayan da aka zuba a gidan, ni kaina na san su Umma sun yi ƙoƙari.