Ba Ni Da Masaniyya

26

by @faddabanan

Ranar ɗaya ga watan Muharram ta kasance ranar Laraba, wurin aikinmu an ba mu hutun ranar don haka gidana ranar a cike yake tun daga kan Minal, AK da yaran Yaya Bello, ɗan ƙaramin yaron Muhammad kawai ba a zo min da shi ba. Sai da aka yi sallar magriba sannan Malam Habu ya zo ɗaukarsu.

Mayafina da purse na ɗauka na biyo su, tuntuni nake son zuwa Sahad Stores yin siyayya ban samu dama ba. A tare da ni muka je gidan Yaya Bello muka sauke yaranshi sannan suka sauke ni Sahad tare da Minal. Idan muka gama sai ita ta ƙarasa gida tunda kusa ne.

Muna tsaka da siyayya sai ga wayar Sardauna, ko gaisuwata bai amsa ba ya ce "Kina ina ne haka nake jin hayaniya?" Ban kawo komai a raina ba na ce "Ina Sahad ni da Minal, rage min hanya suka yi zan yi siyayya. Ya ka yini?" Sai da ya amsa da "Idan kin gama ki neme ni a waya." Ya katse. Sai a lokacin na tuna ashe fita nayi abu na ban sanar da shi ba. Ban ma tsaya wata-wata ba, iya abin da na ɗiba shi na tafi na biya na wuce gidana cikin sauri.

Ina kan hanyar komawa gida a keke Napep na dinga kiran shi amma bai ɗaga ba. Ni ma sai na share kawai, ba mamaki ya shiga wata sabgar ya bar wayar. Sai kawai na shiga twitter ina dube-dube. A take gabana ya faɗi, zufa ta fara karyo min. Na mance yaushe rabon da na ga hirarsu da Rahila a bayyane haka. Ta zama cikakkiyar lauya. Kuma daga irin maganarsu kasan soyayyarsu na nan daram. Ban san dalilin abin da nake ji ba amma dai na san tabbas raina a ɓace yake kuma zuciyata ta takura. Namiji dai ai namiji ne.

Daidai ƙofar gida na hangi mutum zaune bisa dakali, duka ƙarfe tara na dare amma sawu ya fara janyewa, kar naje koma waye ya afka min. Jikina na rawa, cikin sauri na fara ƙoƙarin buɗe gidan kuma na ƙi sauke ledoji biyun da ke hannuwana. Ƙofar a buɗe take. Na ɗan tura ƙofar na leƙa ciki don na san ko zan shiga ko baya zan yi sai na hangi motarsa a fake a harabar gidan, hakan ya tabbatar min da cewar ya iso. Alamar mutum na ji a bayana, dama a tsorace nake ko ni ban san lokacin da buɗe baki na sa ihu ba tare da sakin ledojin hannuna. Ya ce "Ke! Ni ne fa."

Duka kwanaki kaɗan ne da rabuwata da shi amma sai na ga kamar ya ƙara haske sannan sumarshi ta daɗa kwantowa, babu tantama ya kwana biyu bai aske ta ba.

A tare muka shiga gidan kowa da abin da yake yawo a zuciyarsa. A firij na tsaya na jejjera abubuwan da na siyo sai da kwalbar jam ɗin ta fashe don haka shi a bola na saka. Na wuce kicin domin adana ledojin, karo na ci da ledoji kala-kala zube a tsakiyar kicin ɗin. Cefane yayi mai yawa ciki har da popcorn ɗin da ya san ina so da yawa a wata babbar baƙar leda. Da yake dama abin shi da na gani da Rahila yana susar zuciyata har lokacin sai kawai na zauna a kicin ɗin, na wanke naman na kuma ƙuƙƙulasu a leda tare da sanyawa a freezer. Komai sai da na ajiye shi wurin da ya kamata. Sanin akwai abinci a falo shi yasa ban yanke aikin da nake yi na leƙa wurinsa ba.

Lokacin da na fito falo na ɗan nutsu, shi kuma yana zaune ne da plate a gabanshi da alama ya gama cin abinci. Talabijin tana aiki amma hankalinsa gabaɗaya ya tattara ne ga wayar da ke riƙe a hannunsa, fuskar ta cika fal da murmushin da babu haufi ko ma mene ya ja hankalinsa cikin wayar yana ba shi nishaɗi. 

Ƙarar wayata ne ya maida hankulanmu gare ta. Yusuf ne, abokin aikina. Ni kaina ganin kiran nasa a wannan lokacin ya ba ni mamaki saboda bai taɓa yi ba. Ƙarar Maryam ya kawo min, ita ma abokiyar aikinmu ce amma a ƙasanmu take, kuma shirin aure a tsakaninsu ake yi. Na saurare shi sosai tare da ba shi shawarar da nake gani ita ce mafita, na kuma yi masa alƙawarin gobe zan yi mata magana idan mun je aiki.

Duk a tunanina Sardauna ba saurara ta yake yi ba, sai da na gama sai na ji ya fara magana "Naga alama ban isa da gidana ba don ga shi har mutanen waje sun sani. To, idan ba haka ba, ina matar aure za ta amsa kiran wani ƙato goman dare? Kai shi da ba zai fara kiran nata ba ma. Gargaɗin fita ba a tambaye ni ba shi ma kin watsar saboda ni ba ni da ƙimar miji a gare ki ko?"

Na yi sororo ina kallon shi kafin na ce "Kayan abin ci naje siyowa fa. Zancen Yusuf kuma da ba ni da gaskiya ai da ba zan amsa wayar a gabanka ba. Taimaka masa nake yi game da yarinyar da zai aura. Kuma iyaka nan ne kaɗai."

"Ohhh! Ashe kin iya gyaran aure shi ne ba za ki bawa naki auren same energy ba? Da bakinka kika amsa duk abin da nace za ki bi. Siyan kayan abinci kin faɗa ba ki da wani abu kika ga ba a yi maki ba? Ko menene shi? Kar ki sake bakinki ya ce ai dama kin faɗa za ki yi..yen...yen. Domin ni a wurin ɗaurin aure an ce ni ne shanki, cinki, suturarki, iliminki kuma duka na amince! Idan ma kina tunanin auren je ka nayi ka nayi to kina yaudarar kanki ne. Ba na son na ƙara ganin wani abu makamancin haka a gidan, kar ki bari na ƙara magana a kai. Kina ji na ko?!"

Na zumɓuro baki na ce "Ba shirin auren Rahila kake yi ba? Don me tawa rayuwar za ta dame ka?"

Duk da kan shi a sunkuye yake sai da hango alamar murmushi a fuskarshi kafin ya ce "Ina ruwanki da ita? Dama tun can baya na faɗa maki kar ki bari lamarin ƙawayena ya dame ki, ni da ke akwai bambanci." Haushi ya ƙara kamani na wuce ɗaki na bar shi a wurin.

Na yi shirin kwanciya ban jira shi ba, har bacci ya ɗauke ni ban ga shigowarsa wajena ba sai da asuba na lura yau a ɗakinsa ya kwana. Komawa baccin da nayi ya ja kusan makara zuwa wurin aiki, da sauri na hau shiri, sai kuma fitowa na yi na ga bayan nan har motar tashi. Kenan tafiya yayi? Zuciyata ta hau suya da tafasa. Ina ofis sai ga text message ɗin shi "Mutum ya kwaso buƙatar shi ta magidanci ya zo wurin da ya kamata a biya masa amma an tunzura shi an kore shi. Ba komai, ki yi yarda kike so Zara. Amma ko menene zan yi daga ɓangarena ki tabbatar ba ki tanka ba."

Wuraren ƙarfe sha biyu kuma sai ga wayar Minal. Daga ji a gigice take, ta ce "Anti Zara kina ina? Ki yi sauri ki zo! Baba ne Allah yayi wa cikawa, ana shirin kai shi ne yanzu." Ta katse wayar ba ta saurare ni ba. Zuciyata ta shiga bugawa da sauri da sauri. Baba ya rasu? Wane Baban? Sai da nayi mintuna sannan ƙwaƙwalwata ta fara aiki na gane Baba mijin Gwaggo ake nufi.

Tun da na baro wurin aiki nake kiran wayar Sardauna amma ya ƙi ɗauka, don haka na shiga twitter na bar masa saƙo ta DM ɗinsa "Na kasa samun wayarka. Baba mijin Gwaggo ya rasu." Na kashe wayata gabaɗaya.

Duk dauriyar mutum idan ya kalli Gwaggo dole ya karaya. Kuka mara sauti kawai take yi, idanunta sun kumbura suntum ba ta jin rarrashi. Tun zuwana ban ji ta furta ko harafi ɗaya ba.

Gab da magriba naga Yaya Bello ya shigo da Sardauna har ƙuryar ɗaki wurin da Gwaggo ta maƙale. Bai kallo kowa ba, can kusa da ita ya je ya zauna ya fara yi mata magana a sanyaye da fulatanci, maganar ta yi kama da lallashi. Zuwa jimawa kaɗan naga tana share hawayenta tare da gyaɗa masa kai. Ya daɗe yana yi mata magana, wanda shi ne kaɗai ta saurara duk yinin yau, kuma karon farko da naji maganarta "Miyettu masin, Allah barkiɗin."

Umma ta umarce ni da na raka shi sauran sassan biyun yayi masu gaisuwa. A hanyar mu ta dawo sashen Gwaggo bayan yayi masu gaisuwar ne ya dakatar da ni tare da riƙo hannayena, an kuma yi sa'a duhun magriba ya sakko ya ce "Haba mana Zara. Ku da za ku kwantarwa da Gwaggo hankali shine za ku zagayeta kuna kuka? Daure zuciyarku ya kamata ku yi sai ita ta samu ƙwarin gwiwar danne tata." Anan ya rarrashe ni. Tuni na mance da wani haushinsa da nake ji ko don yanda yayi wa Gwaggo. Sannan ya tafi masallaci.

Har na kwanta a ɗakin Gwaggo sai ga Yaya Bello wai na fito na bi mijina, gobe sai na dawo. Ina zumɓura baki na fito, dama an bar ni nayi zamana saboda ko mun je gidan babu abin da zan yi masa ai. Da hannu ɗaya yake murza sutiyari, ɗayan hannun kuma yana riƙe da ni yana kuma ƙoƙarin sa ni magana ta hanyar tambayata game da rasuwar ko wani abin. Ya ce "Kin ce Gwaggo tun tana shekara sha uku take auren Baba? Ai dole ne ma ta shiga irin wannan tashin hankalin. A zahirin gaskiya babu wani da ta sani sama da shi, saboda za a ce tayi wayo ta buɗi idonta a hannunsa ne. Ayya! Allah mai yin yanda ya so. Ba ya barin wani don jin daɗin wani. Allah yayi masa Rahma." Allah ma ya sani wannan daren yana ɗaya daga cikin abubuwan da ba zan taɓa mancewa da su a zamana da Ahmad Sardauna ba.

A tare da shi muka yi ta jigilar zuwa gidan Gwaggo har aka yi uku ranar Lahadi, sai ya koma Kaduna akan zai dawo ranar bakwai.

Gwaggo takaba ta kankama, kullum za ka iske ta da tasbaha irin wanda ake ɗaurawa a ɗan yatsa ko kuma da Alkur'ani tana karatu. Idan kuma bacci za tayi za ka isketa tana bacci kuma karatun Alkur'ani na tashi ƙasa-ƙasa a wayarta. Babu raha ko ɗigo a tare da ita bare ma har magana da ba ta dole ba ta shiga tsakaninku. Na daina ganin hawayenta amma duk lokacin da ta shiga banɗaki tana daɗewa ba ta fito ba, kuma da zarar ta fito ka kalli fuskarta sai ka ga idonta ƙozai-ƙozai, duk a zatonta ta ɗauka babu mai gane kuka take kulle kanta tayi a ciki. Na daɗa yarda da abin da Sardauna ya ce game da yanda Gwaggo take ji na rasa Baba.

Abinci kan shi tayi masa adabo. Idan an dame ta da batun abinci sai ta samu ƙaramin kofi ta cika shi da kunu ko yoghurt ta shanye ta ajiye maku kofin, a haka za ta kwana ba za ta ƙara yarda ta ci wani abun ba. Dama can ba jikin kirki gare ta ba, hakan ya daɗa sa ta rame sosai.

Ganewar da aka yi tana jin maganar Sardauna saboda shi surukinta ne, ya sa Umma ta ce ya dinga sa ta a gaba tana cin abincin a gabansa. Kuma muddin ya kawo abinci ya ajiye mata ya zauna ko da ba ta so ba za tayi masa musu ba haka za ta ci. Umma dama tace Gwaggo ta sha faɗa ba a musu da suruki. Na kuma san ba ƙaramin ƙimar shi take kallo ba.

************


Tun da na gane abin da yake haɗa mu faɗa da shi sai na kaucewa abin. Ko abu zan je siya kasuwa ko shagon titin unguwarmu, sai na kira shi na faɗa masa. Idan kuma ya ce a'a, shi kenan maganar ta wuce. Yawanci kuma idan ina da buƙatar abin da ya dangancu kayan girki ina faɗa masa kamar yanda ya buƙata, amma irin wanda nake buƙata a kurkusa kuɗina nake sawa na siya kawai. Yanzu kam kullum a dakon maganar aurensa da Rahila nake amma bai ce min komai ba, gudun tambayarsa nake yi kar ya gwasale ni.