LUBE (BODARA)

8

by @zinariya0102


_________Cikin abinda bai fi awa ɗaya da rabi ba, ta iso garin Kano mai tarin ni'ima da albarka,iskar ƴanci Humaira ta shaƙa ta ce"alhamdulillah gaskiya kowa ya bar gida to kuwa tabbas gida ya barshi" trolly'nta ta ja ga goyon Affan ga gajiya.

"sannu da zuwa Hajiya barka da dawowa" muryar Idi driver ta katse ta, ajiyar zuciya ta saki tana faɗin"yauwa malam Idi mun same ku lafiya" ya ce"lafiya ƙalau Hajiya sannu da hanya" ya karɓi trolly'n buɗe mata mota ta shiga ya rufe, ya buɗe boot sa jakan da hanzari, ya zaga driving sit ya zauna ya fara tuƙi.


Lumshe idanunta ta yi jin ƙamshi da sanyin air-condition na ratsata wani enjoying take, unguwar tudun yola suka nufa, wato gidan Hajiya, horn Idi ya yi take aka buɗe big gate ɗin ya tura hancin motar ciki, har kusa da ƙofar da zata sadata da asalin cikin gidan ya kaita sannan ya parker, ya buɗe mata ta fito ta nufi ciki, ya bita da jakarta.


Insaaf an sha kwalliya cikin kayanta na boutique red grown mai budewa made in India ce jikinta, rigar kaɗai ta bawa fifty K baya, mommy!!!! Insaaf ta faɗa da tsananin murna tana nufar Humaira da gudu, ta rungume ƙafafunta, Humaira ma cikin murna ta ke fara'a Hajiya da ke zaune sai fara'a ta ke tana faɗin" oh ga yarinya yau dai mun huta da maganar an gaji da gidana ga uwartaki nan ai sai ki cinyeta ai" Humaira ta ƙarasa gabam Hajiya ta zauna a ƙasa ta ce"ina wuni" Hajiya ta amsa "lafiya lau ya hanya fatan andawo lafiya" ta ce" lafiya alhamdulillah na same ku lafiya" Hajiya ta ce" lafiya ƙalau to ya kika baro shi ya kuma aikin?" Humaira ta ce" alhamdulillah yana agaisheku sosai" Hajiya ta ce"ma sha Allah, muna amsawa muna nan muna ta addu'a Allah ya taimake shi ya kuma tsare ku" ta ce"amin ya Allah mungode Allah ya ƙara girma" amin Humaira" Insaaf da ta yi ɗare-ɗare a cinyar Humaira ta na ta faɗin"mommy ina Abbana, shi ba zai dawo ba?" ganin Humaira ta Hajiya ta ke Insaaf ta juyo da fuskar Mommyn nata yanda zata kalleta ta ce" Mommy kin yi min shiru" kwalla ta cika idanta, Humaira ta ce"ayya sorry yana nan shima zuwa ai". Cikin murna Insaaf ta ce" an siyo min bindigan irin ta sa?" Humaira ta ce" eh" dan agajiye ta ke.


Bilki kawo wa Humaira abinci mana, ce war Hajiya tana ɗaga murna, Humaira da ta matso ta je gidanta ta ce"a'a na ƙoshi munci abinci a hanya bamu tare da yunwa na gode" Bilki ce ta fito ɗauke da drinks a trey ta na ganin uwarɗakinta sai ta washe baki ta ce"sannu da zuwa Hajiya" Humaira ta ce"ma sha Allah haka ki ka ƙara girma Bilkisu" Hajiya ta ce" ai kuwa ga Bilkisu nan aure ma zaa yi mata, idan Tasalla ta zo wannan karon tare da ita za su koma sai ta kawo miki wata" Humaira ta ce"Allah sarki Allah ya sanyan alkhairi, bari mu tafi Hajiya" Hajiya ta ce" ba za ki huta ana ba za ki tafi" murmushi ta yi kafin tayi magana Insaaf ta ce" a'a Hajiya gidanmu za mu tafi gidanki babu daɗi wari ma yake yi" 

Gaba ɗaya suka sa dariya Hajiya ta ce"iyeee tukwicin da za ki bani kenan mai ƙaton ciki kin zo zaki kwace min Miji to anji nima kin ishe ni sai ki yi ta tafiya gidan naku na gold kin ji" Insaaf ta juya da gudu dan ɗauko takalminta ta na faɗin" Mommy ki tsaya ni takalmina zan sha" Humaira ta ce "Alhaji baya nan ne?" Hajiya ta ce" eh baya nan sun fita tare da Fahad" ta ce" Allah sarki, Allah ya dawo da su lafiya" amin ya Allah ce war Hajiya.


Bilki da Kulu ne suka fito kowacce riƙe da kayanta a leda, Humaira ta miƙe bayan ta gama bawa Affan nono ta ce" ga shi ba mu zo da komai ba Hajiya da ke tafiyar ba shiri bansan yau zan tawo ba ya ce min yau ne, daddawa ce kawai wallahi, ta faɗa tana zuge hand bag ɗinta ta ɗauko wata daddawa a leda ƴar kaɗan ta ajiyewa Hajiya.

Hajiya ta ce" har da wahala haka, babu komai na gode sosai.

Ta tashi suka fita domin komawa nata gidan.


Matsalar Humaira akwai rowa, ba ta da kauta kwata-kwata, ba ta son kowa ya ci dukiyar Mijinta daga ita sai ƴaƴanta sai kuma ƴanuwanta da take nawa duk wani abu kwancen kaya da sauran abubuwa haka dai lokaci zuwa lokaci.



Tsaf ta tarar da gidanta ta na shiga ɗakinta ta kunna a.c ta faɗa toilet kamar baƙuwa tabi toilet ɗin da kallo, bathtub ta cika da ruwa ta janyo drawer ta zuba bath sprays take toilet ya gauraye da ƙamshi ta cire towel ɗin da ta ɗaura ta shiga bathtub ɗin ta kwanta tana mai jin daɗi da nutsuwa, rabon da tayi wanka mai kyau wata bakwai kenan(inji ta fa).

Sai da ta gama ta nannaɗe gashinta da ƙaramin towel ta yi alwala dan ɗaya ta kusa, ta zauna kan stool ta janyo hand dryer ta sa a socket ta kunna ta shiga gyara gashinta.



Ta fi hour tana shiryawa ta sa abaya milk sannan ta sauko, Kulu da Bilki sun tanadar mata abinda zata sa a baki kafin su kammala girki, Insaaf da ke ta kaikawo tsakanin ɗakin Humaira da parlor tana jiran ta gama shiryawa ta kira mata Abbanta.

"Mommy ki kira min Abban tunda kin gama kwalliyan" Humaira ta ce " ko ba ki faɗa ba yanzu zan kira shi" ta ɗauki apple ta na gatsawa ta kira Zayyad wanda ta sarver da life partner.



GULU




Jikinsa babu ƙwari ya tashi ya shiga ɗakin yana jin kewarta da ta Affan wanka ya yi ya fice daga gidan, a waje yake jin wai ansace wata mahaukaciya ƴar shekara goma sha takwas, Zayyad hankalinsa ya tashi ya shiga tambayar garin ya ya, nan fa mutane kowa da abinda yake faɗa.

Wasu suna faɗin duk shekara ko bayan wata goma haka sai an nemi mahaukaciya an rasa ko kuma yara ƙanana.


Ya ce an sanarwa da ƴansanda mahaifin wacce aka sace ya ce" ko an faɗa babu abinda suke akai, kusan shekara biyar kenan muna haɗuwa da wannan tashin hankalin" Zayyad ya ce" Baba shin daman tana fita ta dawo ko kuma tana ɗan kwana biyu bata gida?" Malam Amadu ya ce" a'a Bintalo bata nisa kullum bata wuce ƙofar gida bata duka bata komai, hasalima mari ne a ƙafarta gudun ɓacin rana" Zayyad ya tausaya musu sosai ya ce su zaga garin ko Allah zai sa a ganta, duk da sun san ba ganinta za su yi ba, haka suka dinga yawo har garuruwan da ke kusa da su babu Bintalo babu mai kama da ita.



Lube da ta ke ta faman danna tusa a dandali kowa ya toshe hanci ta na zaune tsakiyar ƙawayenta tana shan rake hango Wattini ta yi ɗauke da farantin gyaɗa tana sayarwa, ta tashi ta ce"ku zo mu je mu ci gyaɗa" ɓuuu su Mara suka bita.


"Wa na kama?" ta sha gaban Wattini tana kama wuyan rigarta, ta ci ɗanmara tana girgiza matasan nonuwanta waɗanda ba su fi girman lemon tsami ba, Wattini da ta tsorata ta riƙe farantin gyaɗarta ta na ba wa Lube haƙuri" ni dai kinga banyi miki komai ba, an yi mana tsakani da ke, ki sake ni na tafi" Lube ta ce" idan aka ƙi fa me za ki yi?" Wattini ta yi shiru ta na tsaye.

"Watsi watsitsi" ce war Lube, aikuwa take ƴan amshi yaran da ke wajen suka fara faɗin" watsiii!" ta kuma faɗa suka amsa ta duma hannu a farantin gyaɗa aikuwa kowa ya duma take suka daka wawa, Watti ta sunkuya ta fashe da kuka, duk suka gudu Lube ta ce" ai alkur'an sai na hanata sakat a garin nan, har ni za su tararwa ita da uwarta su daka ai alkur'an ƙaryar shege ya ce zai ci bulus a kaina" su Mara sai ƙara zuga ta suke yi suna ta cin gyaɗa abinsu.



Da kuka Wattini ta koma gida Inna Maimuna na tankaɗe har ila yau ɗaurin ƙirjin ne a jikinta ta miƙe da sauri jiki duk gari ta ce" ya ya me kuma ya faru?" cikin kuka Wattini ta ce"Lube bodara ce da wasu suka samun wawa a gyaɗar......Wayyo na higa ukku ni da wannan yarinyar!!! ince dai ba ki kula ta ba?" Wattini ta ce" eh har riƙemin kwala ta yi ban kulata ba" yauwa gara da baki kula ta ba dan wannan yarinyar kwalba ce uwassharri alkur'an ni!" 

Ajiye trey'n Allah ya saka mana tashi ki shiga ciki ki huta Allah ya saka mana".



Mudi da yake kwance a ɗaka yana jiran Maimuna ta gama sa sanwa ta shigo ya ji abinda ke faruwa shiru ya yi dan jin ko Wattini ta kuma kulata ya fito da kansa ya danƙata ga ƴandoka dan yi wa tufkar hanci sai ya ji bata kula ta ba.

Gyaran murya ya yi da sauri Maimuna ta nufi ɗakin ta ce" gafara dai" sannan ta shiga Mudi da yake kwance babu riga sai dogon wando tazuge har ƙasa ya ce" ki bata ta ida sanwar ki zo" Maimuna ta ce" haba Malam wanga ai abun kunya ne ƴa tana gida mu hige ɗaka mu kulle" ya ce"za ki yi yanda nace ko kuwa?" ta ce" Allah ba ka haƙuri" Ta fita.

"Wattini, ke Wattini!!" ta kira ƴar, "iyee Inna gani" ta fito tana faɗa har ta cire kayanta ita ma sai ɗaurin ƙirjin.

"Na ɗaura tuwo ga garin nan ki ida tankaɗewa ki ƙarasa tuwon, ga kayan miya can ki daka ki haɗa miyan" wattini ta ce" unguwa ne za ki je inna?" Maimuna ta ce" oh'oh'oh Malam ne ba ya ɗan jin daɗi shi ne zan je wajensa nayi masa fifita ga zafi" cikin tausayi Wattini ta ce" ayyah Allah ba shi lafiya" ta nufi wajen garin ta cigaba da tankaɗen.


Inna Maimuna ta koma ɗaki ta ja ƙofar langa-langa ta rufe, fututu da ita jiki duk gari,kanta kuwa tamkar dandaƙuwa kitson duk ya cure da datti ko tsaga baa gani. 


Mudi ya miƙe yana washe baki, dan shi dai da rana yake samun lokaci da yamma idan ya fita tukubar tsiransa sai ya kai biyun dare bai dawo gida ba.

Tamkar gawa ta nufi gadonta na ƙarfe ta kwanta tana bankaɗe zani wanda shikenan kullum jikinta.


Mudi jikinsa da ke rawa zaa tsinki furen ƙauna ya shiga lagutsa fatun nonuwan Maimuna waɗanda suka zama dogwayen slippers.

Hammata da gabanta tunkus da gashi tankar a kama a kitse, sai kauri take. 

Daɗi ne ya fara kaimata ziyara brain ɗinta ta kama tazugen Mudi ta kwance take hajiya babba ta bayyana, ta kama ta shiga sarrafata da hannunta, in banda ƙari da ƙauri babu abinda suke, haukata juna sukayi, nishi suke saukewa suna ƙara haukata junansu.

Shigarta ya nufi yi, ƙayoyi sun rufe masa hanya, abinda ke haɗasu faɗa da ita kenan, bata gyara hakanan take zama sai a shekara bata cire gashi ba, a haka ya shiga, mantawa ya yi da faɗan da ke cin ransa ya shiga aiki, kamar zata shiɗe dan daɗi ga Wattini na gida ba damar kurma ihu.

Toshe bakinta take yi tana ƙara tura masa ya yin da yake ƙara haƙarta yana jinsa a duniyar maji daɗi.

Cikin fitar hankali ya kurma ihu "wayyo daɗiiii" da sauri Maimuna ta cushe masa baki tana sanin ƴarsu na nan.

Kai kawai yake juyawa yana rawar disko akanta ita ma ihun take son yi sai cusa ɗankwali take a bakinta tana farfar da ido na jin daɗi.


Bige-bige kawai Wattini take ji, tana ta aikinta jin ihun da Babanta ya yi yasa ta yi shiru tana fatan Allah ya ba shi lafiya, ƙila aboniki ne Inna ta sa masa a hanci, sanin maganin akwai yaji.Kuma indai basu da lafiya suna yawan shafa shi.


Sai da suka shafe minti arbain sannan Mudi ya ɗaga Maimuna yana faɗin "alkur'an baki tsufa Maimuna ta, wai ai ke ce carkwai mazaƙwi ɗin, amma do Allah ki dinga aski banajin daɗin wannan ƙayoyin da kike ajiyewa" Maimuna ta tashi ta ɗaura zaninta a ƙirji ta sauko ta buɗe ƙofa ta fice.


"Inna ya jikin Baban man zafi kika shafa masa na ji yana ihu" da sauri Maimuna ta ajiye bokitin da zata baiwa Wattini ta samo musu ruwa ta ce" eh idonsa ya higa ne, amma yanzu ya ji sauƙi, ɗauki bokitin nan ki samo min ruwa" dakan da take ta ajiye ta na tashi riga ta sako ta fito ta tafi, da sauri Maimuna ta koma ɗakin tana faɗin" fito ka yi wanka kafin ta dawo yi maza dan Allah" Mudi ya fito ya na faɗin " ke kam da tsoron wannan yarinya kike yo meye dan nayi wanka kin yi a lokaci ɗaya ba sani tayi ba, ni aurar da ita zanyi ma na huta ƴa mace ko takura mtswww" Maimuna ta ce"yi maza dan Allah" buta ɗatal ya yi wanka ya fito, ita kuma ta ci gaba sa aikinta, sallah ya fita, Wattini ta dawo, sai lokacin Maimuna tayi wanka ta tada dauɗa ta fito.


Sai da ya dawo yake sanar da ita ansace Bintalo mahaukaciya, cikin jimami suka yi jigum-jigum suna Allah ya sa ta dawo, Mudi ya ce" aikuwa da wahala ta dawo dan ba kanta aka fara sace mahaukata ba babu wacce ta taɓa.dawowa" a haka ya gama cin tuwonsa ya fita wajen sana'arsa yaransa sub gama gyara naman tsirensu, ya shiga aiki suna ta magana akan ɓatan Bintalo.




*******




HEADQUARTER D.S.S BAMFAI KANO.



"What still dai a garin ma haka ke faruwa kenan?" Cewar wani Babban mutum wanda sanye da uniform na police mai four star a jikin rigarsa.

"Yes sir, almost five years kenan ana sace Mahaukata da ƙanan yara, a yanzu haka ina kan bincike" good job Expector Zayyad, muna Nan Muna ci gaba da tracking akan issue ɗin" ce war ASP Alkanawi.

Sallama sukayi da Zayyad. Zai ajiye wayar kiran Humaira ya shigo, amsawa ya yi dan jin sun sauka lafiya, kasancewar yana ta kira babu network bai same ta ba.

"kin sauka lafiya?"ta ce" lafiya baby shine baka neme ni ba ko" ya ce" na kira amma babu network ya kika same su" ta ce kowa lafiya ƙalau, ga Insaaf sai nemanka take" Abba shine ka ƙi ka zo ko?" murmushi ya yi ya ce" zan zo Insaaf ga Mommy nan ai ta dawo ko" kai ta ɗaga ta na faɗin" Affan ya zama lukuti na kasa ɗaukan shi, ka ce ka daina shan nono" murmushi ya yi ya ce" okay zan faɗa masa ku kula da kanku kunji ina wani aiki ne yanzu zan kira ku later" ya katse wayar.

Humaira ta ce" kai ka sani ka je can ka ƙarata kai kaɗai..........