Page 001
*BAYA DA ƘURA*
FitattuBiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
_Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bamu aron rai da lafiya har muka kawo wannan lokaci. Ina yiwa kowa barka da shiga sabuwar shekara, ina roƙon Allah ya sada mu da alkhairin da yake cikin ta, ya kiyaye mu daga sharrin da yake cikin ta. Ya zaunar mana da ƙasar mu lafiya, ya kare mu daga duk wata fitina Amin. Ina roƙon Allah ya bani lafiya da numfashin ganin ƙarshen labarin nan kamar yadda na fara lafiya cikin aminci amin._
_Labarin BAYA DA ƘURA ƙirƙirarre ne, ban yi shi dan wani ko wata ba, in yayi kama da labarin wani ko wata ayi haƙuri rashin sani ne._
_Ban amince a canja min labari zuwa wata siga daban ba!._
*BOOK 1*
*Page 001.*
Madaidaicin gida ne mai kyau a unguwar tudun maliki dake cikin ƙwayar birnin Kano, kai tsaye kana kallon sa baza kace wanda suke ciki takalawa bane irin sosai ɗin nan, haka baza kace musu suna da kuɗi ba sosai. Zasu shiga cikin masu rufin asiri wanda suka fi ƙarfin abubuwan yau da kullum. Yana da babban tsakar gida mai tsaho mai ɗauke da bishiyar mangwaro wacce ta mamaye ko ina baka ganin hudowar rana ko kaɗan sai iska da take kaɗawa busassun ganyaye suna faɗowa kan tiles ɗin da yake ƙasa. A share gidan yake tasss sai ganye da yake faɗowa bayan wannan babu ko tsinke a tsakar gidan komai yana mahallin sa.
Mata ne guda biyu masu matuƙar kama da juna sosai, kana kallon su zaka fahimci uwa da ƴa ne duba da yanayin shekarun su. Yarinyar wacce baza ta wuce shekara ashirin da huɗu zuwa da biyar fara ce tass irin farin nan mai kamar madara, tana da haske sosai wanda a kallo ɗaya kawai zai ɗauki hankalin mutum. Tana da idanu masu kyau da gashin gira yalwatacce, ga bakin ƙarami mai ɗaukar hankali. Kallon farko zaka fassara ta a kyakkyawa don ta cancanci ta amsa wannan sunan musamman hasken ta da yake da ɗaukar hankali, suna zaune a kan tabarma ciki inuwar bishiyar suna cin kwaɗon zogale a cikin kwano ɗaya, yadda suke ci suna hira sai ka ɗauka yaya da ƙanwa ne saboda yadda suka shaƙu da junan su.
"Mama!." Yarinyar ta faɗa tana kallon ta. Wacce aka kira da Mama ta haɗɗiye ganyen da yake bakin ta tace, "Na'am." Tace, "Maganin ki ya ƙare, ya kamata mu koma asibiti muga likita kar a samu matsala."Mama ta sauke numfashi tace, "Manal nawa ya ƙare saboda takura min da kike yi da shan sa amma ke bakya shan naki. Ko yaushe tunanin ki akan nawa yake bakya tunanin kanki, ciwon nan kina dashi ina dashi, amma bakya maganar kan ki sai ni."
Manal tayi shiru ta sunkuyar da kanta tana murmushi Mama tace, "Manal koda bana gani da idanuna zuciyata tana nuna min duk abinda yake faruwa, nasan bakya shan magani a ko yaushe ni kike siyawa ke kuma ki zauna da ciwo bayan kina kallon illlar da ciwon yayi min, bakya tsoron yayi miki ke?."
Manal tace, "Allah Mama ina mantawa ina da wani ciwon sugar indai ba maganar kika yi ba, in kika samu lafiya kamar na samu ne. Wallahi koda na sha maganin indai baki samu lafiya ba bazan samu tawa lafiyar ba Mama." Mama ta janye hannun ta daga cikin kwanon zogalen ace, "Meyasa haka? Lafiya fa lafiya ce Manal, babu abinda ya kaita mahimmaci a duniya. Ni na girma har na haife ku keda ƴar uwar ki ke kuwa fa? Kwata-kwata shekarun ki nawa a duniyar? Ko aure baki yi ba balle a kai ga batun haihuwa, rayuwar ki tafi tawa mahimmaci Manal."
Manal tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "Mama taki rayuwar tafi tawa wallahi, da na samu lafiya gwara ace kece kika samu. Shiyasa bana tambayar Baba kuɗin magani na, indai ba shine ya siyo ba bana faɗa masa." Mama ta girgiza kai tana murmushi tace, "Manal ɗin Mama kenan, to ban amince da abinda kika ce ba, da kaina zan sanar da Baban naku bakya shan magani." Manal bata amsa ba Mama ta kuma cewa, "Wannan karon ki tambayi Baban kuɗin naki maganim, bana so wani abu ya same ki Manal. Kin san waccan Yayar ta ki ba hankali ne da ita ba, ta ɗauki rayuwar da tafi ƙarfin ta ɗora a zuciyarta, ta raina ni bata jin maganata saboda tana da kyau, ke kaɗai ce dani Manal, shiyasa bana so wani abu ya same ki."
Manal zata yi magana kenan suka jiyo muryar Mubeena tana faɗin, "Wallahi bazan ci ganye ba, na gaji ai ni ba akuya bace da za'a dinga yanka tsinannen salad ɗin na naira hamsin ana cewa shi zamu ci safe da rana a gidan nan wallahi bazai yu ba. In ku kuna da ciwo ni ai lafiya nake. Haka kawai a dinga tauye ni? Ina! bazata saɓu ba." Mama ta girgiza kai Manal tace, "Kar kici mana, Yay Mubeena cikin ki ai."
"Daman bance zanci ba ai, zan fita na nemo abinda zanci ne yanzu" ta ƙarewa gidan kallo tayi tsaki tace, "Wallahi ni ba kalar gidan nan bace gabaɗaya, ban cancanci zama a gidan nan ba. Tsausayi ne kawai ya saka aka haifo ni a gidan nan, amma ni kalar babban gida ce wallahi."
Manal ta kalli Mubeena sannan ta kalli Mama taga tana girgiza kanta kawai sai ta miƙe ta ƙarasa kusa da Mubeena tace, "Baki da hankali ne wai ke? Yaushe zaki nutsu ki fuskanci rayuwa don Allah?. Ke a ganin ki wannan banzar rayuwar itace wayewa?." Hararar ta tayi tace, "ni kike cewa bani da hankali dan ma kin raina ni?" Ta kalli Mama tace, "Mama yarinyar nan bata san ni Yayar tace ba ko me?" Ta sake kallon Manal tace, "bazan zauna a gidan nan ba, ban cancanci zama a cikin sa ba domin kuwa ni ba kalar wacce za'a ce a nan na rayu bace." Manal tace, "bazan girmama ki ba domin baki cancanci hakan ba, a gaban Mama kike cewa baki cancani zama a gidan na ba?, wallahi baki da kunya."
"ki ƙyale ni wallahi bazan zauna a nan ba talauci ya kashe ni, common abinci irin wanda nake so naci ace ya gagare ni wallahi bazai yu ba. Ke da kika ga zaki iya sai ki zauna ni kam bazan iya zama a gidan nan ba, kinga tafiya ta" kafin Manal tace wani abun Mubeena ta fita da sauri kawai ta bita da kallo zuciyar ta babu daɗi ko kaɗan. Allah ya sani bata son wannan ɗabi'ar da Yayar ta take yi, bata son wannan rawar kan da take ji dashi kamar itace tafi kowa kyau a faɗin duniya.
"Ƙyale ta Manal, zo ki cigaba da cin abincin ki, Mubeena Itace ajalina ita zata ga bayana" ta faɗa murya na rawa alamun kuka zata yi. Da sauri Manal ta koma kusa da ita ta zauna ta riƙe ta tace, "Don Allah Mama ki daina faɗar haka addu'a zaki mata."
"Manal na rasa wacce irin yarinya ce, gabaɗaya bata jin magana abinda taga dama shi take yi. Ita a ganin ta raina ni da tayi shine daidai?, a ko yaushe bata ganin ƙima ta saboda na kasance ni ba irin uwar da take so ace itace mahaifiyar ta ba. Hmmm! Taje tayi ai duniya ce ga ishe ta duk abinda take so tayi. Wanda suka fita ma ya duniya ta bi dasu balle ita ƙaramar alhaki."
Manal tace, "Ki yi haƙuri Mama, ki mata addu'a zata daina in sha Allah." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba Manal tace, "Mama Ina zuwa." Mama tace, "Karfa ki bi bayan ta."
"Ɗaki zan shiga Mama" ta faɗa tana shiga ɗakin da sauri.
Babu komai a falon sai carpet amma a share yake tass sai fridge ƙarami a gefe a ajjiye, ta shiga wata ƙofar da take falon ta ƙarasa wajan akwatin kayan ta tana bincika inda ta ajjiye kuɗin taji babu su alamun Mubeena ta kwashe. Zama tayi a wajan dan daman ta san za'a yi haka a bayyane tace, "Innalillahi, na shiga uku Yaya Mubeena ta kashe ni" ta faɗa tana dafe kanta tana shirin yin hawaye saboda halin da ta jefa ta. Wayar ta ɗauka tecno andriod wacce bata da girma sosai dan ko a hannu ba babba bace, hannun ta har rawa yake ta kira lambar Muneeba tana ɗauka tace, "Yaya kin san da yadda Baba ya samu kuɗin nan ya bani kuwa?, Mama zan kai asibiti dasu fa, meyasa zaki kwashe?."
Daga can ɓangare tace, "Shi Baban zaki komawa ya sake baki, ai kowa ya siyi rariya ya san zata zubar da ruwa, tunda har zai iya riƙe mu matsayin ƴaƴan sa dan yayi asarar wannan kuɗin ba komai bane. Kar ki manta kuma ƙanin ɗan uwan baban mu ne, ko babu aure tsakanin sa da Mama zai sake biya. kije ki tambaye shi in ba haka ba ki nemo kawai ni na kashe su ma" tana faɗa ta yanke wayar. Manal ta dafe kanta zuciyar ta na harbawa cike da ɓacin rai, dan da ace Mubeena ɗin tana kusa da ita a wannan lokacin wallahi zasu iya yin dambe dan kowa yasan halin ɗan uwan sa. Da ya aka samu kuɗin ma bata sani ba kawai burin ta taje tayi ƙarya ita a lallai ga mai kuɗi.
Numfashi ta sauke ta kalli agogom wayar taga huɗu na yamma tayi ta share idon ta ta fito ta tarar har Mama ta tayar da sallar la'asar itama tayi alwala tazo kusa da ita tayi sallar, bayan ta idar ta kalli Mama tace, "Mama zanje wajan Surayya yanzu zan dawo, babu abinda kike so?."
Mama tace, "kin daina zuwa islamiyya dai Manal."
"Ba daina zuwa nayi ba Mama, bana so na tafi na barki ke kaɗai ne shiyass kawai. Kuma mun sauke har sau biyu na samu abinda na samu ai."
Mama tace, "to haka zaki zauna kina tauye kan ki saboda ni Manal?, kin ƙi cigaba da karatun boko tunda idanuna suka rufe, islamiyyar ma gashi kin ajjiye. Ita waccan da bata da amfani a gidan sai ita take zuwa kuma ta raina mai biya mata ƙudin makarantar, ko yaushe a banza take kallon sa saboda bashi da kuɗi kuma ba shine ya haife ta ba."
Manal tace, "Wallahi Mama babu inda zan iya zuwa na barki, ko naje bazan yi karatun ba tunanin ki zan dinga yi. Kuma ni culinary school nake so, na zama fitacciya a fannin girki." Mama tace, "to ai ko ita ɗin kin ƙi Manal."
Tayi murmushi tace, "Zan yi Mama amma ba yanzu ba, zan tafi Mama akwai sabon girkin da na gano mana nake so naje mu gwada da Surayya."
Mama tayi dariya tace, "shiyasa kika iya saboda in dai kin gani zaki ce zaki gwada. Jeki babu abinda nake so Manal sai kin dawo, Allah yayi miki albarka ya baki abokin zama na gari, ya haɗa ki da masu taimaka miki kamar yadda kike taimakona."
Murmushi tayi tace, "Amin Mamana, sai na dawo" ta faɗa tana tashi ta fita zuciyar ta gabaɗaya babu daɗi akan lamarin Yaya Mubeena.
Da sallama Mubeena ta shiga falon gidan babba mai kyau kai da kaga falon kasan mazaunan falon ma ƙananun masu kuɗi bane ba saboda yadda ta tsaru sosai, babar macen da take zaune sanye da glasses a idanun ta tana duba waya ta ɗago ta kalle ta tayi murmushi tace, "Mubeena kece." Murmushi tayi ta ƙarasa ta zauna kusa da ita tana murmushi tace, "Mummy ina wuni?."
Wacce ta kira da Mummy tace, "how was your day?, Ya Maman ki?."
"She's fine Mummy. Tace tana gaishe ki."
"Ina amsawa" ta faɗa tana kallon mai aikin ta tace, "ina so ki dafa min couscous amma baki iya ba." Tayi shiru bata amsa ba Mubeena tace, "mummy ki kawo na dafa miki." Mummy tayi murmushi tace, "noo! Bilkisu tana ciki jeki" da sauri Mubeena ta tashi ta shiga cikin ɗakin ta samu Bily a zaune tana waya ta bita da kallo kafin ta tsaya jikin mudubi tana kallon kanta cikin burgewa. Ita kanta tasan tana da kyau ko ba'a faɗa ba, tana da kyaun da lokaci ɗaya zai ɗauki hankalin ka in ka kalle ta sai ka sake.
Sake kallon kanta take yi kafin tace, "Allah bai yi za'a haife ni a irin wannan gidan ba, da a wannan gidan nake ai sai nafi haka kyaun gani, da wannan gidan na dace ba waccan ba."
Bily ta katse kiran tace, "ke kullum kika zo gidan nan sai kin maimaita maganar nan, dallah ki shiga kiyi wanka mu wuce bana son ɓata lokaci." Bata ce komai ba ta shiga banɗakim tayi wanka ta fito ta zauna tana shafa mai Bily ta kalle ta tace, "Gaskiya Mubeena dole ki dinga baƙin cikin haihuwar ki da aka yi a gidan ku, ke kin ganki kuwa?, kina da kyau sosai, kawai farin Manal da yake mai haske ne yafi burge ni, dan kin ga ita babu masu wannan hasken da yawa a cikin nigeria. Ke kuwa haske dai wanda kowa ya sani ki ke dashi, amma kina da kyau."
Mubeena tace, "bari kawai, bayan talauci ma ga uwa makauniya, ga mai riƙon namu ma talaka, ga ƙanwa soloɓiyo babu abinda ta iya kullum cikin kiyi haƙuri da duniya take faɗa min. Shiyasa ko a school ban taɓa bari na nuna ta matsayin ƙanwa balle kuma na nuna babar ta mu balle kuma gidan namu gabɗaya." Dariya Bily tayi tace, "Shege talauci. Amma bai kamata ki cewa Mama haka ba, kuma a ko ina zaki iya nuna Mama saboda ta fi ki kyau. Kawai dai da ace ke ƴar Alhaji ce da an gama magana." Itama dariyar tayi tace, "Ina jin daɗin haɗuwar mu dake, ke kan ki farkon haɗuwar mu kin ɗauka irin wata shegiyar nan ce ni baki san ganye na baro su suna ci ba."
A tare suka sake yin dariya Bily tace, "Wallahi baki da kirki, ke baki bar kowa ba har Mama." Mubeena ta tashi ta buɗe kayan Bily ta ɗauki kayan da take so ta saka ta tsaya tana kallon kanta a mudubi dan ita kanta tasan tayi kyau ba kaɗan ba. Bily ta bita da kallo tace, "Gab nake da daina baki kayana domin in kika saka sai naga sun fi miki kyau a kaina."
Dariya Mubeena tayi ta shirya tsaf tayi kyau sosai suka dauƙi jaka suka fita ko mummy basu yiwa sallama ba dan su ƴan boko ne babu ruwan su basa tauyewa Bily haƙƙin ta, Bily taja mota suka fita daga gidan.
***** A yadda ya shigo falon zai tabbatar maka da ransa a ɓace yake, cikin fuskar sa da bata da alamun walwala a ko yaushe dan kana kallon sa zaka fassara shi a mutum mara fara'a, kuma baza'a rasa faɗa a wajan sa ba.
Kyakykyawa ne mai duhun fata da madaidaicin jikin, yana da ido da dogon hanci siriri, fuskar sa ɗauke da zagayayyen gashin da ya kewaya ko ina. Cikin glasess ɗin da yake idanun sa ya kalle ta tana zaune kafin yayi magana cikin fusata tace, "wai kai waye gaba tsakani na dakai ne? Yayar ka ma Farida gaba nake da ita balle kai da zaka dinga min shishshigi a cikin lamarin rayuwata, ina ruwan ka da abinda na zaɓarwa kaina?, har nawa aka ke da zaka dinga nuna min daidai da ba daidai ba?."
Wanda take yiwa maganar yana tsaye yana jin ta ya kalle ta yace, "ba yaya ta ba, ko kece kika haife ni baki isa kina yi abu ba daidai ba na zuba miki idanu ina kallon ki. Yasan yana son ki meyasa ya rabu da ke? Ya san zai dinga bibiyar ki har ki dinga shiga motar sa meyasa ya miki sakin da bazai iya mayar dake na?."
"Ina ruwan ka dani?, haka na zaɓa baka isa ka hana ni ba wallahi."
"Ai kuwa zaki ja masa, na rantse da Allah na sake ganin sa ƙofar gidan nan sai na saka n kulle shi ya kwana biyu a cell, in kina musu ki sake gayyato shi kiga nida ke waye zaiyi nasara."
Anty Maryam ta harzuƙa matuƙa kamar zata kifa masa mari tace, "baka isa ba walalhi, ƙarya ka ke Bebi baka isa ka hana ni abinda nayi niya a cikin gidan nan ba. gidan ubana ne kamar yadda yake gida uban ka, ina da iko kana da iko, baka iya ka hana ni abinda nake so ba. In kana hana ƙanen ka ni Yayar kace." Ganin Mamy tazo wajan sai baice komai ba ya juya ya fita ransa a ɓace sosai.
Yana fita ta kalli Mamy tace, "yaron nan yana neman raina min hankali, Mamy kiyi mana tsakani dashi, ni yayar sace babu ruwan sa da abinda zanyi."
Mamy ta kalle ta tace, "Gaskiya yake faɗa miki ai, kishin ki yake matsayin ki na yayar sa shiyasa yake tsaye akan lamarin ki. Ke kuma banza shashasha mara kamun kai miji ya sake ki amma ya dinga bibiyar ki kina masa dariya saboda baki san abinda yake miki ciwo ba. Ya san yana son ki ya miki saki har uku?."
"Mamy su Nabila da Nabil na duba fa."
"Zaki min shiru ko sai na tsinke ki da mari?, babu mota a gidan nan da baza ki hau kije wajan yaran naki ba? Ki aika a ɗauko miki su ko lallai sai kinje inda suke?."
Anty maryam ta sauke numfashi tace, "kenan yanzu Mamy shine mai gaskiya ni mara gaskiya?." Mamy ta Harare ta tace, "ki cigaba da abinda kike yi nan gaba zaki dana sani, sai a lokacin zaki fahimci Bebi gaskiya yake faɗa miki. Bebi gata yake miki wanda uban ki bai miki shi ba." Tana gama faɗa mata haka ta shige ta barta a wajan.
Kai tsaye Bebi ɓangaren mahaifiyar sa Mama ya shiga wacce shi kaɗai yake kiran ta da Mummy kowa Mama yake cewa, amma shi tun yana yaro yake cewa Mummy har girman sa. Yana shiga ya same ta a zaune ita ƙanwar sa Mimi ya ce, "yanzu Mummy abinda yarinyar nan Maryam take yi daidai ne? Miji ya rabu da ita ya sake ta amma ya dinga bibiyar ta har yana ɗaukafr ta a mota? Akan wanne dalili?."
Mama tace, "to Bebi ni me zance? Ina ruwana tasan daidai ai sannan tasan ba daidai ba." Ya kulle idanun sa bala'i kishi yake ji yana addabar zuciyar sa ya kalli Mama yace, "shikenan sai a zuba mata ido kenan?."
"To maganar taka me ta canja? Su mazan yayyen ta akwai wanda ya damu da yayi maganar ne?, kai kaɗai ka ke tayar da jijiyar wuya akan lamarin Maryam da Lubna."
Bebi ya girgiza kai kawai yace, "bazan bari ba kin san da hakan Mummy." Mama tayi dariya tace, "shikenan Bebi, zaka dinga asarar maganar ka kuwa dan ba ji zatayi ba ita da kanwar ta." Kallon Mimi yayi kamar zai yi magana sai ya fasa ya fita ya shiga mota kai tsaye ya bar gidan.
Nana Haleema.