003
*BAYA DA ƘURA*
FitattuBiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
*BOOK 1*
*Page 003*
Rumana na fita daga ɓangaren Bebi wajan Mama ta wuce tana matsar kwalla ta same ta tana sallah ta zauna kusa da ita har ta idar ta kalle ta tace, "Ruma Lafiya?." Rumana hawaye ya zubo daga idanun ta ta kalli Mama tace, "Mama ina son Adnan amma shi yanzu baya sona, yaƙi manta baya, na amince da abinda ya faru a baya laifina ne meyasa bazai amince ya yafe min ba?."
Mama ganin tana kuka ya saka tace, "Ruma yanzu akan Adnan kike kuka haka?."
"Mama I love him so much, bana son sake rasa shi a wannan lokacin, gabaɗaya ya canja kamar ba wanda na sani a baya ba, ki yi wani abun Mama....!" Ta faɗa tana sake zubar da hawaye. Mama ta girgiza kai tana murmushi domin kuwa ita hakan daidai ya yi mata, ta tashi daga kan sallaya ta zauna kusa da ita tace, "Haba Rumana, ai indai ina da rai ina numfashi Adnan bashi da mata sai ke kawai. Ki daina asarar hawayen ki kece matar sa in sha Allah."
Ta sake komawa kalar tausayi muryar ta tayi rauni tace, "Amma Mama yanzu baya sona, gabaɗaya ya canja ko hira dani baya yi kwata-kwata. Kinga a baya ba haka yake min ba, sai na wuni muna hira dashi amma yanzu ya daina." Mama tayi murmushi tace, "ki kwantar da hankalin ki wannan ba abinda zaki hawaye a kai bane. Ke kin san Adnan bashi da magana sai kun saba sosai, kuma bashi da fara'a ko kusa shima sai kun saba zaki ga murmushin sa, kin san hali ba komai ake yi a burge shi ba hatta ni ba gwanin ta nake masa ba wani lokacin. Ki yi haƙuri yana son ki har gobe, kawai sabon da ku ka yi da ne ya ja baya amma zai aure ki." Murmushi ya suɓuce mata ciki farin ciki da gamsuwa da maganar Mama tace, "Haka ne Mama, yanzu baya sakewa dani, shaƙuwar mu duk ta gushe. Amma tunda kina tsakani naji daɗi bana son rasa shi."
Mama tayi dariya cikin jin daɗi tace, "baza ki rasa ba in sha Allah. Adnan naki ne ke kaɗai, duk wannan zille-zillen da yake yi zai daina." Tayi dariya zatayi magana kenan suka ji anyi sallama.
"Assalamu alaikum" ya faɗa yana shigowa ɗakin Mama ta amsa tana kallon sa yace, "Mummy me aka dafa?."
"Tuwo nayi."
"Tuwo! A daren nan?” Ya maimaita yana kallon Mama. Mama tace, "eh shi, ba kai naji kana cewa kana son cin tuwon semovita ba? Shine nayi maka."
Ya girgiza kai yace, "A'a Mummy gaskiya bazan iya ci ba. Tuwo a daren nan, inaa!." Mama ta harare shi tace, "daman ai ba'a iya maka, sai kaje ka san abinda zaka ci ai." Rumana tayi caraf tace, "Beb ko na dafa maka taliya?."
"Bana so" ya faɗa yana fita ba tare da ya kalle ta ba. Sai ta ɓata fuska kamar zata yi kuka Mama ta kalle ta tace, "meye na jin haushi bayan kin san halin sa?, dan ya gwale ki ba komai bane a wajan sa, ki yi abu yace bai masa ba duk kin san da wannan, meye na jin fushi to?" Ta faɗa tana tashi ta fito falon ta tarar dashi a kitchen ɗin a tsaye yana zuba kunu a kofi kafin ya fito ya zuba madara a kunun ya zauna a falon.
Mimi da Kausar sun fito ya bisu da kallo ganin kayan jikin su na bacci ne marasa nauyi masu kama jiki, ba kamar Mimi da take da jiki ya kamata kayan sosai yace, "baku da hankali ku ka yi wannan shigar a wannan lokacin?." Mimi bata san yana nan ba da bazata fito ba saboda indai ya gani sai yayi magana, tace, "Yaya dare ne fa."
"Na fiki sani ai, Ku koma ku saka hijjab, ku ka san wanda zai zo yanzu?."
Ran su bai so ba suka saka hijjabi suka dawo suka zauna sai mita suke a zuciyar su dan Allah ya sani yana takura musu, ga shegen saka aiki. Mama tayi murmushi, tana jin daɗin yadda yake kula da tarbiyyar ƴan uwan sa, ko ya ya yaga sun karkace zai dawo dasu daidai kuma dole su hau layi. Kallon da Rumana take masa ne gabaɗaya ya dame shi hakan ya saka ya miƙe ya kalli Mimi yace, "in an idar da sallar i'sha dake da Kausar da Lubna kuzo ku same ni" yana faɗa ya fita daga falon Rumana ta bishi da kallo kamar ta jawo shi ta rungume haka take ji.
Murmushi Mama tayi dan tana ganin irin kallon da take masa, shima tana lura dashi kallon ne ya saka ya gudu amma zata yi maganin sa dan ita kam tana son haɗa auren su duk da sai turjewa yake yi bayan a baya yaso Rumana fiye da ko wacce mace. Rumana tace, "Mama nima bara na koma gida gobe na dawo." Mama tace, "to ki gaida Sumayya" ta amsa to ta ɗauki key ɗin motar ta fita.
Mimi ta kalli Kausar bayan fitar sa tace, "ke me muka yi yake neman mu?." Kausar tace, "me muka yi kuwa? Laifin Lubna ne ya shafe mu. Tsoron wannan faɗan nasa nake yi da in ya fara babu full stop, gashi abokan sa in sun kai dubu a falon sa dan ya miki faɗa a gaban su ba komai bane. Shine abinda yake haɗa ni dashi, bana son faɗa a cikin mutane." Mimi tace, "haka ya yi min ranar juma'a, ke kin ji faɗa a gaban Huzaifa wai fita da ƙaramin mayafi?, kuma wai ina magana da maza, Kausar da fa Huzaifa ɗin kawai na gaisa, ai ya bani haushi wallahi."
"Kema ke kika ja, shifa Yaya yafi so in kika ganshi a waje cikin mutane kar ki nuna kin san kowa ki wuce, wannan magana da mutanen ma laifi ne. Balle yaga kina yiwa wani namiji magana da dariya ki sha harara."
"Matar sa ta shiga uku, ɗan mayafin zamanin nan bazai bari ta saka ba. Faɗa a cikin mutane wannan bai ɗauke shi komai ba." Mama na jin su bata ce komai ba suna zaune har akayi kiran i'sha suka tashi da nufin sallah.
Kamar yadda yace ana idar da sallah suka nufin ɓangaren Mamy suka tarar da Mamy da Maryam da kuma Lubna suka shiga da sallama Mamy ta amsa suka zauna tare da kallon Lubna Mimi tace, "to ki tashi boss yana neman mu yace muje." Lubna ta bata fuska tace, "me kuma muka yi?."
"Ke zamu tambaya ai, in ma faɗan zai mana ai ke ki ka ja mana,"
"Mtsw! Gaskiya ni Yaya Bebi yana takura min wallahi, haba shi komai bazai barka kayi yadda kake so ba, ni na gaji da wannam rayuwar."
Mimi tace, "in baza ki je ba sai ki faɗa mu kama gaban mu, Kausar muje in ya tambaya muce tce ya takura mata." Tare suka fita, Mimi haushin Mamy take ji ganin a gaban take wannan maganar ta amma bata ce komai ba. Basu san ya abin ya faru ba sai gano Lubna ɗin sukayi ta fito.
Suna shiga falon nasa suka same shi a zaune yana sanye da glasses a idanun sa fari wanda yake taimaka masa wajan kallon takarda da wani document a hannun sa yana dubawa. Sallama da suka yi ya saka ya kalle su ya amsa tare da ajjiye littafin yana kallon su suka ƙaraso suka zauna akan kan carpet Mimi tace, "Yaya gamu." Kai ya girgiza alamun na gan ku kafin ya ce, "tambayar ku nake so nayi, ina so ko wacce ta faɗa min asalin abinda yake zuciyar ta. Bana son ƙarya ku faɗa kai tsaye kar a ɓoye min.”
Basu ce komai ba ya kalli Mimi yace, "me kika shiryawa rayuwar ki a yanzu? Aure ki ke so?." Yadda yayi tambayar ya saka ta kalle shi suka haɗa ido dan bata kawo abinda zai ce ba kenan ya ɗaga mata kai yace, "asalin abinda yake zuciyar ki nake son ki,aure kike so?." Mimi ta sauke kai ƙasa tace, "ni Yaya abinda Allah ya tsara min shine daidai."
"Kowa ma haka Mimi, but there's something on your mind that you wish to happen in your life, maybe aure maybe kuma karatun kike so ki gama har ki fara aiki."
Mimi tace, "Yaya ina so, amma nafi so na kammala karatun tunda kaga ina final year."
"Are you sure?." Ta girgiza kai alamun eh. Kallon Kausar yayi yace, "sai ke what's your plan about yourself?." Kausar tce, "ni Yaya ina karatu, in auren yazo zan karɓa. Amma kaga yanzu ko saurayi ma bani dashi, karatun shine a kan gaba."
Ya girgiza kai ya kalli Lubna yace, "ke dai daman nasan auren ki ke so ko?." Ta girgiza kai alamun a'a yace, "then what?." Tayi shiru bata amsa ba yace, "in ba haka bane a ranki meyasa kike tara samari? Yau in na ganki da wannan, gobe da wannan an ganki. Kuma dukkan su babu wanda zai aure ki a cikin su duk ƴan ɓata lokaci ne, wannan wanda na ganku ɗazu nayi miki warning a kan sa amma baki ji ba. Taƙamar ki shima ai abokina ne, na fiki sanin abokina ne, shiyasa nace ki barshi sboda na san shi din amma baka jin magana Lubna."
Lubna tayi shiru bata amsa ba yace, "duk wacce take ji a zuciyar ta she's ready to get married please let me know zan tabbatar ta samu abinda yake so. Abu ɗaya ne bana so ku dinga hiding abinda ku ke yi ko ku ke so a gare ni, baku san duk wani motsin ku akan idona kuke yin shi ba shiyasa. Ke Kausar ai baki nasan na san kinje Sufi mart ba Jiya. Mimi ɗazu kinje biki baki sanar dani ba." Shiru sukayi dukkan su ya kalle su yace, "zan muku duk abinda kike so amma ku tsayar da hankalin ku waje ɗaya, bana son kula samari barkai musamman ke Lubna" ya faɗa yan nuna ta da yatsa.
"Kece Babba a cikin su amma kin fi kowa wannan rawar kan, ki dawo hankalin ki kafin ranki ya ɓaci, na sake kama ki da makamancin wannan zan baki mamaki. duk wanda yace yana son magana dake invite him to come over and talk to me, sai muyi magana akan ki na san waye shi da komai na shi, I'll only let him to talk to you if i trust him, otherwise l'll reject to him. Bama ke kaɗai ba dukkan ku, in na samu wata da akasin haka gaskiya ranku zai ɓaci" ya faɗa yana nuna su gabaɗayan su.
Mimi tace, "To Yaya in sha Allah zamu yi abinda kace." Ya sauke numfashi yana kallon su yace, "good. Akwai abinda kuke so?." Mimi da Kausar aka kalli juna kafin Mimi tace, "daman Yaya gobe akwai get together na class mate ɗin mu tun na secondary ina so naje." Ya kalli Mimi yace, "which time?."
"Around 4pm."
"Where?."
"Green pack." Yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "okay zan saka a kai ki." Tayi murmushi tace, "na gode."
"Baku da abin cewa?" Ya faɗa yana kallon su suka ce babu yace, "okay zamu iya tafi, zan tura muku kuɗin kati."Suka yi murmushi dan sun san kyautar sa a gare su akai daɗi suka fita ya bisu da kallo.
Allah ya sani baya so wani abun ya samu ɗaya daga cikin ƙannen sa mata, yana tattalin su sosai musamman yanzu da duniyar ta gama lalacewa kowa ba abin yarda bane, baya son yaga wani abun da zai ɓata musu rayuwa shiyasa bai basu fuskar sauraren ko wanne namiji ba, sannan bai basu fuskar karɓar komai a hannun ko wanne namiji ba. duk da iyayen su suna da halin da zasu basu kuɗi amma yana yawan basu kuɗi da canja musu waya saboda kar rashin basu yasa su tambayi saurayi. Gabaɗaya aikin da mahaifin su ya kamata a ce yayi ya dawo kansa bashi, tunda yayyen sa maza guda biyu kowa yana gidan sa shine tamkar uba a wannan lokacin, shiyasa bashi da nutsuwa sai yaji sun kwana lafiya sun tashi lafiya wani abun bai sake su ba. Gashi Allah ya yi shi a mutum mai kishin ƴan uwan sa, baya so yaga suna kula ko waye balle saurayi.
Ajiyar zuciya yayi a bayyane yace, "Abba!." Kai ya girgiza kawai yana jin haushin halin mahaifin su amma ya zaiyi ba'a canja uba dolen sa dai shine mahaifi a gare shi. Tashi yayi da niyar shiga ɗaki sai yaji ana buɗe gate ya ƙarasa wajan window yana kallo sai yaga motar mahaifin su ta shigo kawai ya saki labulen dan bai ga amfanin dawowar tasa ba dan da safe zai ce zai koma.
Yana zaune yana cigaba da duba takardun hannun sa yaga wayar sa na haske ganin sunan Abba ya saka shi kulle ido ya buɗe ya ɗauka da sallama yayi shiru alamun ana amsawa kafin ya tashi ya fita waje. Kai tsaye ɓangaren Abba ya nufa ya same shi a zaune a kan kujera ya shiga da sallama ya amsa ya ƙarasa ya zauna a kasa yace, "barka da dawowa Abba, ina fatan an dawo Lafiya."
"Lafiya lau Adna, ya aikin naka?."
"Alhamdulillah" ya amsa a taƙaice daga nan bai sake cewa komai ba.
Abba yace, "sai haƙuri aiki ne suke min yawa ga shirye-shiryen zaɓe mai xuwa shiyasa abubuwan sai a hankali." Adnan yace, "amma Abba duk mahimmacin abinda ka saka a gaba bai kai mahimmacin iyalan ka ba."
"To iyalai na me suka rasa Adnan? Babu abinda babu a gidan nan koda babu ni na tabbata baza ka bar wani yayi kukan babu ba. Yadda kake kula da iyayen ka da ƴan uwan ka ko ni bana kula dasu, indai kana da rai ragamar gıdana tana hannun ka dan na yi shekara bana gida bazan damu ba."
Adnan ya kalle shi ɗan daman shi ne kawai mai iya faɗa masa gaskiya yace, "Amma Abba ko mu yaran ka ace babu haƙƙin mu a kan ka akwai iyayen mu mata, dukkanin suna buƙatar kulawar ka wacce a wajan ka kawai zasu samu, ni da ka bar min komai a hannuna bazan iya samar musu da kulawar da zasu samu a wajan ka ba. Idan zan iya kula da ƴan uwana su kuma fa Abba?." Alhaji Mu'azzam Alhassan ya kulle ido ya buɗe yace, "Haba Adnan! Iyayen naka bafa yara bane da kake wannan zancen a kansu, dukkan su babu wacce bata aurar da yara a cikin su ba har da jikoki, to me suke nema a wajena kuma?."
"Kulawar ka suke so Abba domin matan ka ne, na tabbatar ka san suna buƙatar hakan." Yayi murmushi yace, "gashi ai na dawo, zan kuma yi sati a nan duk kulawar da suke so zasu iya samu a cikin kwanakin da zanyi." Kallon sa Adnan yake yi zuciyar sa gabaɗaya babu daɗi yaja bakin sa yayi shiru bai ce komai ba kafin Abba yayi magana Mamy da Mama suka shigo da sallama ya amsa sai Adnan ya miƙe yace, "Abba sai da safe."
"Allah ya tashe my Lafiya, da safe kafin ka fita kazo nan Ina son ganin ka, koda ina bacci ka jira ni. Maganar da na kira ka muyi bamu samu ba zamu yi daga baya." Ya amsa da to ya fita. Kallon Mamy da Mama yayi da suke zaune ko wacce fuskar sa babu yabo babu fallasa yace, "ko wacce ta shigo tana shan kunu kamar wanda aka yiwa dole."
Mama tayi murmushi kawai bata ce komai ba ta miƙe tace, "barka da zuwa muka zo muyi maka daman, da fatan an dawo Lafiya." Yabi Mama da kallo ita kuma ba shi take kallo ba yace, "Sannu da zuwan ce sai an tashi tsaye?."
Mama tace, "Ina sauri ne zan je na kwanta, sai da safe" ta faɗa tana hanyar fita Mamy ma ta miƙe tace, "jira ni mu koma yadda kuka shigo tare" ta faɗa tana tashi tsaye itama.
Mama ta kalle ta tace, "baza ki zauna a nan ba?."
"Lissafina ya kwace min bazan iya banbance wacece ma ya kamata ace ta kwana a nan ɗin ba, ga dai abinci nan Maryam zata kawo yanzu" ta faɗa tana fita ta bar Mama a tsaye dan har ta riga taficewa. Mama na shirin fita tace, "kar ki fita Hauwa, dawo ki zauna muyi magana." Ta juyo ta kalle shi tace, "ko meye ma tattauna da safe in Allah ya nuna mana, ka kwana lafiya" ta faɗa tana fita ya bita da kallo yana murmushi.
Shi kam mamaki matan nan masa suke bashi ko wacce ta girma a cikin su amma basu daina mararin neman wani abuna wajan sa ba, shi ɗauka yake gabaɗaya ma an ɗauke musu wata sha'awar sa tunda ko wacce har jikoki tana dasu. Har gwara ma Mama tafi Mamy ƙarancin shekaru amma Mamy tafi Maman nunawa. Shafa fuskar sa yayi dan shi kam yana da ɗanye jini a waje bai ga abinda zai nema a wajan wannan tsofaffin matan nasa ba, shiyasa ko a jikin sa in suna wannan abubuwan, duk wacce ta kawo kanta ita ta sani, shi ban damu ba.